Free chapter · Read without an account
Part 12
Page👉🏻12
....Zan iya cemuku biki yanata matsowa, dan shirye2 akeyi na garari agidan Alhaji buba, gidansu faisal kenan, shirin biki suke na d'an gata, dukda shi yana America abinsa, amma duk shirin da'akeyi da saninisa.
Yau tunda safe hajiya jumai tasa balarabe yakawo mata yasmeen gida.
Tunda balarabe yazo da sak'on kiran yasmeen ta had'e girar sama da k'asa😉, harga ALLAH bata son zuwa.
Umma ta ce, "wai yasmeen banaji balarabe ya ce, "hajiya na nemankiba??.
Yasmeen ta matso 😢hawayen datake matsewa tun d'azu, ta shagwab'e murya umma dan ALLAH kibarsu nikam babu inda zanje.
Dak'uwa🖐🏻 umma tayimata, kinci gidanku, hajiya ba mamarki bace ba, za kitashi kije kosaina Ci k'aniyarki, ko kin manta nanda wata d'aya kin zama surukarta.
Yasmeen tafashe dakuka, umma yanzu nan har fata kikemini nazama matar d'anta😭??.
Umma tayi murmushi mai ciwo, wanda ya nuna ainahin damuwarta, ta kamo hannun yasmeen tayi, ta zaunar da'ita gefenta tana shere mata hawaye, kinga mamana bar kuka, ba fata nake miki ba, amma yakama ta kisa a zuciyarki hajiya uwace awajenki, kuma bamusan abinda ALLAH ya shiryaba nan gaba, karki manta da irin hidima da d'awainiyar dasuke damu, komi muka zama a Najeria sune sila.
Umma aii badan ALLAH sukayi manaba, sunyine domin d'an iskan d'ansu.
Umma ta harareta banace karna sake jiba wai.
Jiki asanyaye yasmeen ta tashi, to umma na daina.
Bawata kwalliya tayiba kaya kawai ta canja ta k'ara turare ta fito.
Umma ta ce, "adawo lafiya d'iyar kwarai.
Amin kawai yasmeen ta ce, "dan idan tayi magana mai tsawo kuka zai iya zuwa mata, tasan umma ma tana cikin damuwa, tana dannewane kawai saboda ita.
A k'ofar gida suka had'u da yaseer yadawo daga islamiyya, ya ce, "sisto sai ina haka??, ta ce, "anguwa zanje.
Shiyyasa bakije islamiyyaba??, malam Dawud yanata nemanki!!.
Yasmeen ta zaro idanu da gsk kakeyi yaseer??, ALLAH karkiji wasa, dan aunty Amina ta ce, "ya karb'i hadda yau.
Yasmeen ta ce, "naga banu, bari nadawo naje wajen Aminar.
To saikin dawo, yaseer yafad'a yana nufar gida.
Tunda suka tafi take sharar kwalla, balarabe yana kallonta, harga ALLAH yana tausayama yarinyarnan, duk da bata tab'a fad'a masa damuwarta ba, amma ya fahimci bata son maigidansa, inama yanada hanyar taimaka mata wajen rushewar wannan auren K'ADDARA ko BIYAYYAR (book d'ina danafi k'yauna❤ ), amma zai gwada sa'arsa yagani.
Dahaka suka isa gidan, mai gadi ya bud'e musu get, balarabe yasamu guri yay parking.
Da sand'a yasmeen tashiga falon tamkar wata muna fuka, tai turus dan ganin samari guda uku zaune suna kallo, ta gaishesu sannan ta shige bedroom d'in Hajiya jummai dan babu inda bata shiga a gidan.
Tunda ta tafi suka bita da kallo tamkar goyon mayu, saida tashige suka kalli juna, d'aya ya ce, "kai gays badai wannan beautyn ce sakarannan zai auraba.
D'aya ya ce, "mudai tsaya mugani.
Suna nan zaune yasmeen ta fito itada hajiya jummai, suka zauna, sai asannan yasmeen talura da kwallo suke kallo, tashiga baza idanu dan son ganin mugun nan ko yananan.
Cikin sa'a kuwa aka hasko fuskarsa, yana tsaye zai buga kallon jikinsa sanye da jan JC sunyimasa k'yau, a bayan rigar anrubuta Modeebbo, kasa ansak 10, ya take kwallo da k'afarsa, da'alamadai penerrity zai buga, dan naga kowa tsaye yana kallonsa, yasaki wani murmushi maikama dana mugunta, sanna ya harba kwallon⚽, cikin sa'a tashige cikin ragar, gurin ya kaure da ihu, yayinda sauran 'yan kwallon suka d'agashi sama suna ihu, sumadai samarin saida suka furta 🗣gooooooo.
D'aya acikin samarin ya ce, "kai gay d'innan lucky nefa wlhy, kaga yacimana kwallon nan.
Hajiya ta ce, "umm kullum kudai bakuda aiki sai kallon kwallo da wak'a, ni bari na shige ciki, ga yasmeen d'innan.
Yasmeen ga abokan mijinki nan, tare suke karatu a america su sun kammalane shiyyasa, sunzo ku gaisane.
Yasmeen ta ce, "to momy.
Hajiya jimmai ta shige, sai asannan yasmeen tad'an kallesu, saitaga ai ita suke kallo suma tai k'asa da kai tana fad'in sannunku da zuwa.
Suka amsa da yauwa 'yammatanmu ykk?, ya Najeria??.
Cikin jin kunya ta ce, "lfy lao kuma ykk, ya turai??.
Suka amsa da lfy lao, d'aya ya ce, "sunan izziddin, wannan kuma hisham, wannan kuma hashim, mu abokan angonkine kodayake baki tanbayemu ya yakeba??.
Yasmeen tayi murmushi mai ciwo ta ce, "karku damu ai nasan yana lfy, d'ayan data kula yafi kowa surutu iziddin kenan, ya ce, "duk da haka yakamata a tanmbayemu.
Cikin kosawa ta ce, "to ya yake??.
Sukace yana lfy ya ce, "agaidaki dak'au.
Ta ce, "ina amsawa ngd.
Nan dai sukayita zuba mata surutu, harda wanda bata tambayesuba, tanaso tatafi dan tagaji, amma bataso suga kamar ta wulak'antasu.
Saida suka gaji dan kansu, konace saida suka gama kallon kwallon sannan sukai musu sallama suka tafi.
Bayan tafiyarsu yasmeen ta ce, "mom nima bari nawuce magriba tayi.
Hajiya ta ce, "aii nazata anan zaki kwana.
Yasmeen tad'an sosa gefen wuyanta tana fad'in A'a mom, zanje gida nayi karatu dan gobe inada test a school.
Okey to ALLAH ya taimaka d'iyata.
Amin yasmeen tafad'a.
Babudai wata matsala ko??, hajiya ta tambaya?, yasmeen ta d'aga kai alamr babu, to shikenan ina balaraben yazo ya kwashe miki kayannan dasuka kawo miki.
Lah mom to kema d'iba mana.
A'a d'iyata ke suka kawo mawa, dan haka jeki da abinki.
Har wajen mota hajiya jummai tarakata, dan har zuciyarta tana k'aunar yasmeen, tamafi d'annata sonta.
Ana sallar magriba yasmeen tashiga gida, balarabe ya tayata d'aukar kayan suka shiga, sallah tafara k'ok'arinyi dan kar lokacinta ya shige.
Abangaren samarin nan kuwa tunda suka fita suke santin k'yawu irin na yasmeen, ixiddin ya ce, "hisham gafa hanya mai sauk'i ta d'aukar fansa, dan maida murtani ga abokin dambe ba laifi bane.
Hashim ya ce, "gsk yarka iziddin, hisham yakamata ka rama abinda faisal yayi maka, dan wannan itace dama ta k'arshe dazaka iya samu, karka bari ta k'ub'uce maka.
Kuma tabbas idan muka aikata, munyi jihadi, dan na lura yarinyar kamilace, bata dace da d'an iska irin faisal ba.
Hisham ya dafa kafad'un abokan nasa, ya ce, "karku damu abokaina, kudai kusaka idanu kusha kallo, amma tabbas gsky kuka fad'a yasmeen kamilallaiyar mace ce, inhar ta airi faisal d'an giya manemin mata tofa tabbas ta cutu.
Dan haka ku biyoni domin kallon wasan, kud'auka nine zanyi wining, faisal zai samu game over, yafad'a yana wata dariyar mugunta.
Na ce, "tofa ana wata ga wata, to bamusan waye keda nasaraba saimunyi bulayiiiiiiiii........................✍🏻