Free chapter · Read without an account

Page 2

by Sadiya Auwal · KAICO NAH


   🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵


       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......


🏵🏵🏵

...2....


Tassss kakejin karar mari ya bada amsa kuwwa a cikin lecture theater din,Karar shock daga bakin dalibai ne ya kaure ajin ganin irin ta'asa da kuma aika aikar da Inteesar ta aikatawa malaminnasu.

Rike kumatun yayi da hannunsa na dama yana kallonta da wani irin mamaki mai firgitarwa.

KO a jikinta ballantana ta nuna alama ta nadamar abinda ta aikata,saima zare sunglasse din idonta da tayi tareda kallonsa kasa da sama.

Kada yatsunta kuda biyu na hannunta tayi tana wani kanne ido kaman mai shirin makanta.

"How dare you dr Nuhu, am i your play doll,that give you permission to disgrace me in front of this shiiiitttt".

Karisa maganar tayi da alamar tambaya,sannan tana nuna sauran daliban da suke ajin,wani murmushi tayi na hadiye bakin ciki kana ta maidashi tana mai zan tsaki mai tsayi.

Zarar fashion bag dinta tayi wacce complete disigner ne da riga da wandon dayake jikinta,sai kuma black veil din da tayi rolling kanta dashi.

Kwass kwass high heel shoe dinta yake bada kara cikin kasaita lokacin da ta doshi kofar ajin da niyyar barin wajen gaba daya.

Hanyar da zai kaita inda ake parking ta nufa domin daukar motarta zuwa gida,bangare daya kuma ta bar ajin cikin jimami na irin abinda ta aikata.

Speed din da motar take tafiya kadai ya isa ya nuna irin yanayin da matukin motar yake ciki.

Cikin mintina kalilan ta isa gidansu dake unguwar GRA a garin bauchi,horn take ta aikawa ma'akacin dake kulada bude kofar gidan,saidai kash an samu miskila ya kewaya bayan gida domin magance lalurarsa.

Duk da ganin rashinsa a wajen yakamata Sumayyah tayi amsa uzuri amma inaaa ita ta rayune a sanin iya uzurinta kadai,banda wani dan adama kuma.

Jin karar horn din ya tafara tsyawa ne yasa baba mai gadi saurin fitowa daga cikin bandakin yana gyaraa tazugen wandonsa,wanda tun a vandakin yake kokarin zugewa amma ya gagara kasancewar yanda hannun sa yake rawa saboda bala'in dayake jiransa a waje.

Tun kafin ya karisa bude get din Sumayyah ta jefo hancin motarta sa karfi,dan ma an samu sa'a kafarsa ta goce,da tuni tayi awun gaba da kafar tsoho batare da hakan ya dameta ba ko kadan.

Tun kafin ta karisa parking ta fito daga motar tareda wucewa cikin gidan da sauri,amma hakan ma bai hanata tsayawa da gallawa baba mai gadin harara ba ta wasu yan mintuna kafin tayi cikin gidan kaman ana figarta.

Tun kafin ta karisa cikin harabar falon karar takalminta ya rigata isa cikin gidan,cire gyalen wuyanta tayi sai gumi take tana huci kaman macijiya,sakin baki hajiya mama tayi tana kallonta wacce take magana da masu aikin gidan akan albashin su na wata.

Suma kallonta suke,duk da sunsan bata da mutunci amma kuma fushin yau yafi na kullum yawa.

Karemusu kallo tayi batace komai ba ta haye stairs da sauri tana bada kara mai karfi.

Jijjiga kai hajiya mama tayi cike da takaicin yar tata,dan tasan tunda ta dawo safiyar nan to akwai abinda tayi a makarantar,dan dama halinta ne na kullum.

"Allah ya kyau ta"

Shine kawai abinda tace kafin ta kokarta ta tashi tana haki,saboda yanayin cutar sugar da take dashi da kuma kiba da tayi mata yawa.

Tun da sumayyah ta shiga dakinta take huci ita kadai tana huci tareda cizon yatsa,ba wanda ya shigo kuwa domin ya ji mai ya faru,dan kowa yasan halinta sarai.

Muhibbah ce ta fito daga ajin su ta nufi wajen da ta ajiye motarta,dan dama lecture daya ce da ita kawai.

Maryam ce ta nufo da gudu ta tsayar da ita,waiwayawa tayi tareda cewa,

"Anty maryam lafiya yana ganki ke kadai,ina anty sumayyan?"

"Eh to dama wani abune ya faru a aji dazu da safe,golden girl ce ta mari dr Nuhu dan ya fito da ita bakin aji ya nunawa kowa cewar taci zero over 30 na test dinta,sannan yasa kowa yayi mata dariya kuma ya zazzageta.

Tun dazu ta tafi gida cikin matsanancin gudu a mota,to ban saniba ko ta isa gida lafiya"

Jan numfashi Muhibba tayi tareda furzar da iska.

"Kai kai,wai yaushe anty sumayyah zata daina halinta ne wai,yanzu dan kawai malami yace kaci zero sai ka mareshi ,kaman wani sa'anta? Kullum tafiso tayi ta zawo abun magana a cikin gidannan kaman wata karamar yarinya",

"Hmm Nima anime yaban mamaki,kinsan idan ranta ya baci babu abinda bata yi,bari na je tun dazu Ahmad yake kirana yanaso yaji mai ya faru,hankalinsa gaba daya ya tashi"

"Shima ya Ahmad na rasa mai yagani a wajen Anty sumayyah dayake son aurenta,kwata kwata wahalar da kansa yakeyi kawai"

"Karki ce haka Muhibba,mu cigaba da addu'a wata rana sai labari inshaallah"

Da haka Maryam ta juya tayi cikin makaranta,yayinda ita kuma Muhibba ta shiga motarta tayi hanyar gida.

Shigowa Muhibba tayi falon dauke da sallama,jin babu wanda ya amsane yasata karisawa dakin hajiya mama wanda yake floor din kasa,dan ita kadaice a dakin kasa sai jikokin ta da suke gidan suma.

Daga labulen tayi ta sameta tana sallahr nafila kafin a shiga sallahr azahar,zama tayi a bakin gado kafin ta idar da sallahr.

Zuyowa hajiya mama tayi ta kalli Muhibba tareda cewa,

"Sannu da dawowa,yana ganki da wuri haka,ko bakida lecture da yawa ne yau?"

"Eh wlh hajiya mama,dama iya biyune dani daga na 8 to 10 sai na 10 to 12"

"Naga yar uwarki ta dawo dazu cikin fushi,tunda ta haura sama bata saukoba har yanzu,nikuwa bazanje naji menene ba,dan nasan bacin rai kawai zan debo,gashi ba lafiyace da niba"

"Hmm gwanda da bakije ba,dan wlh ina fada miki ashe malaminsu ta zabgawa mari dan kawai yace taci zero a gaban aji"

Dafe kirji hajiya mama tayi tareda rafka uban salati da sallalallami.

"Ohh ni diyar mamuda,dan allah sumayyah ina zata kaini da neman maganarta ne,ita ko tausayinmu bata jine,kullum cikin jawo magana take?"

"Kiyi hakuri hajiya mama karki sa ciwonki ya tashi,barinaje nayi na ga mai takeyi a dakinnata"

"Ahah Muhibba karkije,yayunta ma ya take Karena d'azu bareke kuma da take ganin tafiki,ki bari yayunta da ubanta su dawo sai su san abunyi ,dan nikam wannan neman magana ta sumayyah tafi karfina,yarinya kinzama kaman mai yin kashin zinare dan girman kai,ohhhh"

"Karki damu,babu abinda zance kawai ganota zanyi na sauko"

Ta shi Muhibba tayi ta hau sama domin zuwa wajen sumayyah.

A hankali ta murda kofar kamar mai tsoron shiga,daga baya kuma tayi sallama.

Gwiwarta ce ta sare jin sumayyah bata amsa mata,duk kuwa da tasan tana jinta sarai,amsawar ne kawai bata da niyya.

Shiga tayi a hankali ta sameta da bom short da kuma T-shirt a jikinta,kitson kanta kalaba sun babbaje,hankalin ta kwance take zuba chatting.

Har Muhibba ta sanda ta zauna a bakin gadonta amma bata dago ba bare ta kalleta,cikin karamar murya ta fara yiwa sumayyah magana,

"Aunty naji abinda yafaru a ajinku da safe...........'

"Eh to dakikajin shine sai kinzo wajena kin tabbatar ko,eh abinda kikaji gaskiya ne na mareshi,kuma in ya karama zan sake marinsa,dan haka karki faramin wannan kaudinnaki dan ba ji zanyi ba,ki kama hanya ki barmin dakina"

Cikin masifa ta katse Muhibba da maganarta ta fara balbala madifa,tashi Muhibba tayi cikin sanyin jiki ta bar da nufin barin dakin,har taje bakin kofa sai kuma ta juyo tana kallon Sumayyah fuskar ta dauke da yanayin rashin son halin yayrtata saidai babu yanda zatayi dole ta juya ta bar dakin.

A can kuwa maryam komawa tayi aji domin suna da wani ajin na malami daban.

Duk hirar da ake a ajin na abinda sumayyah tayi da safene,kowa yana fadan albarkacin bakinsa,har maryam ma bata tsira ba,dan kowa nuna ta yake a matsayin kawar sumayyah.

Lokacin da suka fito ko kallon gaban ta batayi saboda wahalar a suka sha na karatun ranar,ji tai tayi kari da mutum,ja baya tayi tareda dafe goshinta tana kallon Ahmad wanda yake kallon yana murmushi har dimple dinsa yana lotsawa.

"Ina kike kallo har kina buguwa bakisaniba uhm?"

'Ahh Ahmad wallahi gajiya ce kawai,yau throughout muka yi lecture tun safe"

"Eh nagani ai,gashi dama ke raguwace "

"Habadai kasan kuwa nafi sumayyah karfi ai"

Dariya yasaka don ya gano mai yasa ta fadi hakan,dan ta tsokaneshi ne.

"Haba kin is a ki kaita,dazu nakejin abinda ya faru,na duba wurare da dama amma ban ganta ba,yanzu ma kuma na ganki ke kadai,gashi ina kiran nunberta bata shiga kwata kwata"

Sunkuyar da kai maryam tayi cike da tausayin Ahmad,dan tasan sumayyah blocking dinsa tayi,dan tayi hakan ya fi a kirga,amma har yau ya gagara hakura,ko yaushe yana cikin siyan sabon layi,saurin dagowa tayi tareda cewa,

"Uhm inaga takashe wayar ne,dan yamma tayine gashi kuma nagaji sosai,da na bi ta gidansu naga ko lafiya"

Daga kai yayi wanda yake nufin toh,dan yasan ba kashe watar tayi ba,tayi masa abinda ta sabane kawai wato blocked,gashi har yau zuciyarsa ta gagara fada masa wani abu daban akan soyayyar dayake yiwa sumayyah,dan shiyasan sonta a jininsa yake,bayajin akwai ranar da zatazo yarage son da yake mata ballantana kuma dainawa.

Dahaka ya na tunani da kuma zullumi a zuciyarsa ya tafi gida.

Tun ana sallahr azahar sumayyah take chatting,babu abinda take sai zuba mulkinta mutanen social media suna jigata tareda sake fasa mata kai,dama kuma wannan shije burinta,wato ta burge masoyanta su ji babu wacce ta kaita.

Sai wajen karfe hudu kafin ta tashi ta hada azahar da la'asar tayi su tare.

Bayan ta idar ne taji cikinta yana kara,ma'ana yana jiran hakkinsa.

Ta shi tayi ta dora kimono akan kayan jikinta kafin ta sakko kasa cikin tafiyar kasaita.

Tun daga bakin stairs ta hadu da yayanta Yah Mu'azzam wanda mutum dayane a tskaninsu,kallonta yake cike da takaici ganin kayan dayake jikinta,

"Ke Wai yaushe zakiyi hankali ne,haka kika ga kanwarki tana saka kaya?"

"Ita daban ni daban,ni dama ai kullum nice abin zagi a wajenku,duk kunbi kun washeni kaman ku hura wuta ku jefani ciki kuke ji kumq..........."

Saurin buge mata baki yayi wanda hakan yasata saurin yin shiru tana kama baki,duk da hakan kuwa idonta bai daina harararsa ba.

"Shahshasha kawai marar hankali,har ni zaki kallah ki fadamin magana,ko Asma'u da take yayarki batamin rashin kunya sai ke ko,in baki shiga hankalinki ba wata rana sai na karyaki a gidannan kafin na tafi"

Cikin kunkuni tace,

"Gwanda ma katafi mu huta,jarabbabe kawai"

Dawowa yayi da sauri tareda cewa,

"Mai Kik ace wai?"

"Ni babu abinda nace,mu kwan lafiya"

Daga haka ta shige cikin kitchen din domim deban abinci.


Washagari babu ko kunya ta shirya cikin riga da wandonta suma designer masu matukar kyau da tsada,komai yau kam kalar sunan nata tayi komai golden da baki,har mota ma golden ta Dauka.

Ta fitowa tayi mata key sai makaranta,inda tafi bukatar yin tunkahonta kenan,ta baje taci karenta babu babbaka,tasan babu mai taka mata burki saboda matsayin ubanta.


Tohhh fahhh.............




🏵🏵*sadi-sakhna*🏵🏵


 

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.