Free chapter · Read without an account
Page 15
by Sadiya Auwal · KAICO NAH
🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......
🏵🏵🏵
...15....
Sanyin asuba ne ya busa sumayya,wanda hakanne ya zamo sanadiyyar farfadowarta daga suman da tayi a dukan da mutari yayi mata.
Yunkurawa tayi zata tashi amma ciwo yace gashinan zuwa,dan wani bala'in ciwone ya ziyarci mararta,kara ta saki cikin mawuyacin hali kafin ta daure ciwon ta mike tsaye,dan tasan babu wanda zai kawo mata agaj koda kuwa numfashintane yake shirin fita na karshe kaman yanda taga kallon da suke mata jiya.
Dakinnasu ta shiga tana daddafa bango har ta kai bakin gadon ta zauna.
Waiga fuskarta tayi ta kalli mutari ya baje sai bacci yake abinsa,wani bakim cikine ya kamata da ta tuna irirn dukan dayake mata tareda tsinewa iyayenta ta uwa ta uba,dan kawai ya ga wani a dakinsu,in kuwa zai mata shaida ai yasan ta kawo masa budurcinta,meyasa ma ta kasa ganin shi wane irin mutun ne har saida lokacin ya kure,tirr kuwa da irin wannan soyayya mai makance idanun mutum,kaico da irin taurin kai nata.
Gashi ta auri mijin daya zubar mata da ciki,mijin daya boyemata komai nasa,mijin da yakasa yarda da ita,mijin daya yi mata dukan da ko zata mutu bai damu ba,mijinda zai iya barinta a waje ta kwana a sume bai damuba.
Share hawayenta tayi tareda dawowa daga tunanin da ta tafi,karar kiran sallahr asuba ne ya sakata yunkurawa ta sake tashi ta nufi bandaki dan yin alwala.
Sallayarta ta shimfida tareda saka hijabinta ta tada sallahr nafila kafin a shiga sallah.
Dan ma Allah ya taimaketa tayi karatun addini dadai gwargwado.
Bayan tayi sallah addu'a take tayi wata ma bata san mai take fada ba saboda cika ha'ula'i da ta shiga.
"Aikin banza sai ayi ta sallah ana mika kai,nan kuwa mutum mazinacine mai cin amanar mijinsa"
Sallama sumayyah tayi tareda cewa,
"Duk abinda kake mutari ka cigaba dayi idan aiki alkhairi kakeyi,ka yanke min hukunci akan abinda kai kanka kasan ba gaskiya bane"
Magana take masa tana kuka amma ko a jikinsa sai ma tsuka da yayi tareda zuyawa yaci gaba da baccinsa.
Tana zaune akan sallayar har gari ya waye inna ta fito dora wutar kokonta,tashi tayi ta nade abin salahr tareda fita wajen,har sannan mutari bacci yake baiyi sallah ba.
Saurin dakatar da ita inna tayi tareda cewa,
"Kinga tsaya karki tabamin kayan sana'a kisaka min najasar zina,wato kin maidamu yan iska saiki kawo mana gardi gida kuna shekewa,kin iya kuma fallasa wata dan tayi,ai gwanda itama batada aure,kefah kinada aure kina cin amanar mijinkkin,nasan cikin jikinsa ma ba nasa bane,an kunso za'a kawomana muyi raino,tun wuri ki nemi uban cikin danki ehe"
"Haba inna karki fadi haka mana,yanzu abin har ya kai ki sheganta jikanki?"
"Kull ina rabaki karki kara danganta jinina da cikin dake jikinki,dan wallahi har abada bazan amsheshi ba,anyi walkiya munga komai ai"
Ita dai sumayya bata sake cewa komai ba sai komawa dakinsu da tayi,da alama zuwa yanzu abin yafi karfinta.
Shema'u da take bayan labule tana jin duk abinda ake,wata shewa tayi tareda kunna wayar ta kira wani,
"Hhhhh ai stone ina fada maka komai ya tafi yanda muka tsara,duk sun dauka cewar dagaske kai kwartonta ne,Baka ga yanda mutari yayi mata duka ba jiya da daddare,dadi kaman zai kasheni,hmmm ai naso ma ta kasa tashi yau ba ita munafuka ba.
Kuma ka birgeni da kace kayi masa shima duka jiyan,dama nasan zaka rama min ai,yanzu dai sai mun sake haduwa kawai"
Lokaci yadan ja har yakai zuwa yanzu cikin sumayyah yayi wata takwas yana shirin shiga wata na tara,wahala ta gidan duniya babu wanda bata sha ba kokuma take kan sha.
Ga karancin abinci mai gina jiki ga kuma aiki,sannan uwa uba ciwon mara wanda take fama dashi.
Fitowa tayi daga bandaki ta ajiye butar hannunta wacce ta wanke kafarta da kuma hannayenta.
Dakin nasu ta shige a kanjale kaman ba sumayyah ta da ba,dan duk wanda yaganta a yanzu ba lallai ya gane ta ba,ta rame babu komai a jikinta sai ciki kawai.
Mai ta dauko ta shafa kafin ta dauko yar atampa a cikin kayanta wacce ta adana,dan ma allah ya taimaketa kayanta basu gama karewa ba.
Wata koriyar atampa ta dauka ta saka tareda wani hijabi shima mai adon koren.
Bankada katifarsu tayi ta dauko wata gudar dari biyar a cikin wasu kudi da ta gani a wajen,daga yanda take daukan kudin kasan ba nata bane bata da gaskiya.
Ficewa tayi a gidan sikaf sikaf babu wanda ya ganta a cikin su inna da shema'u.
Tafiya take tana waige waige har tq iso bakin titi,dayake wajen da yar tazara har ta galabaita ta fita a hayyacinta sosai.
Wani mai acaba ta tara tareda yi masa kwantancen wani asibiti tace ya kaita .
Ajiyar zuciya tayi da taga an fara tafiya babu wanda ta hadu dashi da ta sanshi,kalle kalle take tayi a bakin hanyar,dan rabonta da fitowa daga cikin gidannasu wanda tayiwa lakabi da kurkuku tun ranar da ta shiga ciki.
.................................
Back to business
Tunda sumayya tafara bada labarin abinda yake faruwa salma da rike fuskarta da hannunta ta kafa tagumi sai yanzu ta sauke tana jinjinawa.
"Tabbbb cakwakiya kenan"
"Hmm wlh salma abinma yafi karfin cakwakiya,dan said mutum yaji kaman a mafarki gashi kuma a gaskene abin yake faruwa,to yanzu kinji abinda ya faru salma,nasan kema yanzu haushina kike ji kaman ki shakeni,mamaki nayi ma da tunda nafara baki labarin baki tashi kin tafi ba"
"Haba sumayyah menene abin tashi a tafi kuma,karki a damu ai muna tare koda ma bare yanzu dakike bukatar taimako,tabbas kam bazan boye miki ba kin yi kuskure sannan kin aikata ba daidai ba amma kuma ai an ce dan adam ajizine yakan yi kuskure ya dawo kan hanya.
Yanzu dai ina labarin Ahmad da matarsa to?"
"Hmm ina zan sani salma,najidai labarin wai ya bude shaguna har guda hudu,bansan dai yanzu ya suke ba,nibanason ma tuno dashi sosai,dan nasan yanzu yayi min nisa sosai"
"Toh yanzu ya za'ayi kenan,saidai ayi ta addu'a,amma abinda su inna suke ya wuce gona da iyaka"
Hakadai sukayi ta jimamin abinda yafaru har suka kwanta da niyyar idan am gama mata karin jinin salma ta sauke ta a gida a gobe.
Can cikin dare salma taji sumayyah tana ihu tareda dafe cikinta,tashi tayi domim ta taimaka mata amma ta rasa yanda zatayi,hakanne yasa ta yi saurin fita tareda kiran nurse din da suke da dutyn lokacin.
Suma da suka zo abin gagararsu yayi,domin sun duba sun tabbatar ba haihuwa bace,amma kuma gashi tana ciwon masu haihuwa.
Daga karshe allurar kashe zafi sukayi mata inyaso gobe sai suyi mata scan.
Saida allurar ta fara yin tasiri akan fa kafim ta fara sakin numfashi bacci ya dauketa.
Itadai salma aikinta kallo da ido,har sanda suka so sukayi mata allurar daren tareda sake daura mata wani jinin.
Da safe nurse ta shigo tareda gaishesu sannan ta cirewa sumayyah ladar jinin domin ta samu tayi sallah da wasu yan laluranta.
Bayan sun gama abinda zasuyi sai ga aika daga wajen maman salma na kayan shayi,sannan ta ce a gaida mai jikin bazata samu damar zuwa ba taje gaisuwa.
Itadai sumayya duk da haka itace da godiya,dan ko iya abincin da taci jiya da yau saida taji sanjin jikinta.
Yanzun ma salma shayi mai kauri ta hada mata tareda biredi da butter sai kuma soyayyan kwai.
Yanda tafara cusawa a bakimta tana hadiyewa har saida salma ta rike hannunta tana murmushi,dan yanzu ta daina mamaki tunda taji abinda ya faru lokacin da bata nan.
Koshi saida sumayyah tayishi harda wanda bana musulunci ba,dan da kyar take motsawa saboda cikar da cikinta yayi.
Lokacin da likita yazo ya ganta cewa yayi a dakata da saka mata jinin,saboda iya abinci ma zai iya taimaka mata kafin lokacin haihuwar.
Ita dai da to kawai take binsa,dan tasan ikon allah ne ma yakawota wannan lokacin bata mutu ba.
Wanka ta sake yi salma ta bata wata doguwar riga mai laushi ta saka,ga kuma kayan marmari da ta yanka mata tana sha,apple ta kai bakinta ta tauna tareda kallon salma tace,
"Salma silar danayi a makaranta aka fadar ki jarabawa ki yafemin kinji,wallahi sai yanxu nagane banida kirki ko kadan,banda aiki sai cutar mutane,gashi yanzu nice abar taimako,sai an taimaka min,da Allah yasa ban hadu dake ba da bansan yanda xanyi ba wallahi,dan Allah karki taimakeni dan halina salma"
Share hawayenta tayi tareda cusa sauran apple din a abakinta,dan duk jan aji da fadin rai irin nata bata jin zata iya hakura da kayan marmarin a lokacin.
Itadai salma murmushi kawai tayi tareda,
"Ki daina fadar haka golden Girl,komai ya wuce ai,beside ma aikkema kin taimakeni dan dai kim manta ne iya na tsiyar kika tuno,nasan kina da taurin kai da kuma cire duk wanda yake gabanki,amma bakya da mugunta haka kawai ko kuma munafurci,sannan idan akayi munfurcin wani a gabanki zaki hana ko kuma ki shigawa mutum,ta haka nake alfahari dake summy"
Itadai sumayyah da toh kawai ta bita har tagama abinda zatayi ta saka kayanta na jiya a leda.
Ita kuma salma ta fita zuwa office din likitan domin karbar sallama,maganin da suka bayar ta mikawa sumayyah tareda nuna mata yanda zata sha,sannan ta tattare kayan nasu ta kai mota.
Lokacin da suka doshi hanyar gidannasu jikin sumayyah ne yayi sanyi,ita kanta salma ta kulada hakan,ganin yanda duk surutun da take sumayya ta daina amsa mata,sai uhm da to.
Kallon unguwar tayi da mamakin wai sumayyah a wajen take rayuwa yanzu,wanda ko a gidansu tafi kowa ji da wanka da kuma dagawa,amma itace a cikin wannan mataccen wajen batada cin yau bare na gobe,kuma hadda cinkin da ko ubansa yace bai karba ba gashi babu yadda zatayi.
Sannan iyayennata da yan uwanta da gatanta suna raye bawai sun mutu ba,lallai ikon Allah saidai a barshi,tabbas duk wanda yace zai taba Allah Allah bazai barshi ba hakane wannan.
Hannun sumayyaa salma ta kama tareda jijjiga mata kai alamar komai zai zo da sauki wata rana.
A haka suka iso kofar gidan babu wanda yasake cewa komai,har sumayyah ta fita zata shiga gidan saikuma ta koma wajen salma tareda cewa,
"Nasan Sauri kike amma please ki taimaka ki shigo koda bazaki iya zama ba,amma ki shigo cikin gidan,dan tunda nazo gidan babu wanj nawa daya taba taka kafarsa a cikin gidan,ina so ki karya min wannan record din salma,koda wata rana zan iya cewa wani nawa ya taba zuwa inda nayi aure,duk da ina ji a jikina ba lallai nayi tsawon rai a gidanann ba da irin wanann wahalar danake sha."
Saurin fitowa salam tayi a motar tareda jan hannun sumayyah suka shiga gidan,dan in ba haka tayi na tasan bazatayi shiru ba,ita kuma zuwa yanzu ta gaji dajij irin wannan kalaman daga bakin kawartata wanda suke karyar mata da zuciya.
🏵_*sadi-sakhna*_🏵