Free chapter · Read without an account

EPISODE 1

by Khadija Sha'aban · OMAR INTEEYAS

*OMAR INTEEYAS*


_✍🏾Naanarh M Sha'aban (dijartyluv)_



*🌱CHAPTER 1🌱*


*KANO, NASSARAWA G.R.A*

Babban gida ne sosai, kallo ɗaya za ka yi wa gidan kasan ba ƙaramin kuɗi aka zubar wajen ginashi ba, gate ɗin gidan guda biyu ne, kuma daga gate ɗin farko zuwa na biyu wanda zai kai ka cikin babbar harabar gidan da tazara sosai domin kuwa sai ayi tafiyar minti talatin kafin a ƙarasoshi, harabar gidan kuwa idan ka shigeshi ba za ka yi tunanin a nigeria ka ke ba, saboda haɗuwar harabar gidan, gefe ɗaya wani swimming pool ne, tsayawa na bayyana muku irin girmansa ɓata baki ne, part biyar ne a gidan, dukkansu girmansu ɗaya, kuma kowane part ɗauke yake da ɗakuna guda uku, a kowane ɗaki da akwai falo, bedroom da bathroom, sai kuma babban falo wanda yaran gidan suke zuwa kullum da daddare suna kallo wani lokacin ma har da iyayensu suke zama su sha kallonsu suna yi suna raha, abin gwanin ban sha'awa.

kamar kullum yadda suka saba suna zaune suna kallonsu a babban falo, Haniya ta kalli Nyasia tace "Sister kin kalli film ɗin nan na jiya kuwa, ni kam sam bai yi min daɗi ba wallahi"

Nyasia ta buɗe baki zatayi magana kenan Shiza tayi saurin cewa "ko nima wallahi bai yi min daɗi ba da aka ce Omar inteeyas ya rataye kansa ya mutu, dan kuwa idan ya mutu wallahi film ɗin ba zai ƙara yin daɗi ba"

Haniya tace "ai ni na daina ma kallansa wallahi sun ɓata film ɗin gaba ɗaya, Omar inteeyas ai shine tauraron film ɗin".

Nyasia tace "ni kuwa gani nake film ɗin zai cigaba da yin daɗi dan kunga ai kafin Omar inteeyas ya rataye kansa ai an kawo mana Adam show shima kun ga ai yadda yake acting abin burgewa da jan hankali" 

Haniya tace "chabb ni fa wannan Adam show ɗin baya wani burgeni sam"

Shiza tace "to ai shikenan, ni dai in har na ga episode ɗin gaba bai yi min kyau ba wallahi ba zan ƙara kallansa ba".

Haniya tace "ai ba zai yi kyau ba ma kuwa, film idan ba Omar inteeyas ai kamar abinci ne ba maggi"

Dariya su Nyasia suka saka, sosai suke yin dariyar dan kuwa ƴar uwar tasu ta basu dariya.

Shiza tace "kaii Aunty Haniya wannan Omar ɗin ko dai kina ciki ne, kwata-kwata yaushe ma ya fara yin film ɗin ai ko wata ɗaya bai yi ba, kawai dai ya iya acting ne sosai shiyasa yayi suna a duniya kowa ya sanshi"

Harara Haniya ɗin ta wurgawa Shiza tace "ina ciki da me?kawai dan ina son film ɗinsa sai ya zamana kuma ina sonshi ne, ku fa matsalarku kenan mutanan nigeria, ba dama mace ta kula namiji ko ta so abinda yake yi shikenan sai ku ɗauka sonshi take yi"

Nyasia tace "wannan kuma ke kika sani"

Daga haka suka cigaba da kallon film ɗin hausan da suke yi, fuskokinsu cike da annashuwa dan film ɗin yayi musu kyau sosai.

Sai wajen ƙarfe sha ɗaya na dare suka gama yin kallon sannan suka tashi dan su je su kwanta bacci saboda duk kallon da suke yi ba sa huce ƙarfe sha ɗaya suke kashe t.v su koma part ɗinsu su yi bacci, suna shiga part ɗin kowannansu ya nufi ɗakinsa.

Haniya kuwa tana shiga ɗakinta ba bacci ta kwanta ba, kan gado ta hau, ta kashe fitilar ɗakin, wayarta ta ɗauka ta kunna datarta ta shiga youtube searching ɗin film ɗin da suka fara kallo yanzu na Omar Inteeyas tayi mai suna So da ƙauna, bata gama kallon film ɗin ba sai wajen ƙarfe ɗaya, saboda film ɗin yana da yawa sosai, wayarta ta ajiye akan bedsite drower bayan ta kashe data, ta zame akan gadon, ta lilliɓa da bargonta, ko mintina biyar bata yi da kwantawa ba, bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita.


★★★★

Kyakkyawan saurayi ne san kowa ƙin wanda ya rasa, fari ne tas, amman ba irin farin nan ne mai dau ba, siririyar fuskarta ɗauke take da dogon hanci da kuma ɗan ƙaramin baki, yana da saje wanda ya ƙara yi masa kyau matuƙa, gashin kansa a cike yake, sai sheƙi yake dan kuma ka na kallonsa kasan yana shan gyara ba ɗan kaɗan ba, sanye yake cikin wasu ƙananan kaya riga da wando, rigar ja ce, sai kuma wandon fari ne, irin na samarin zamani guiwar wandon duk a farfashe, kuma a tsuke yake wanda turawa suke kiransa da pensil, ya sanya baƙin glass a cikin idanuwansa, gurin mirror ya ƙarasa yana ƙara kallon kansa turarurrukan da suke jere a gaban mirror ya ɗauka ya shiga fesawa a jikinsa, komawa kan gado yayi ya ɗauki jakarsa da yasaka kayansa ya rataya a kafaɗarsa, ya saka takalminsa wanda yake gefen gadon, ƙofar fita daga ɗakin ya nufa, wayarsa ta ɗauki ruri, da sauri ya saka hannu a aljihun wandonsa ya ɗauko wayar tare da karawa akan kunnansa yace.

"Assalamu alaikum ina kwana Ammi"

Ban ji abinda aka ce ba, sai ji nayi yace "Ammi karki damu yanzu ma kin ga, na gama yi musu aiki, jirgi ƙarfe takwas kawai zan biyo na dawo"

Murmushi na ga yayi tare da cewa.

"To in sha Allahu Ammi! Omar inteeyas yana ƙaunarki sosai, ki kula da kanki sai anjima"

Yana gama faɗar haka ya sauke wayar ya mayar da ita aljihunsa, yana fita ya kulle ɗakin da mukulli ya nufi hanyar da zai fitar dashi daga hotel ɗin.

Gurin da yay parking ɗin motarsa ya ƙarasa ya shiga, ya ja zuwa airport ɗin garin Abuja.

Yana zuwa Airport ɗin ya buɗe motarsa ya fito, drivernsa Idris ne ya nufo gurin da yake da gudu, kasancewar ya bashi umarni akan ya zo da wuri dan ya karɓi motar, ya koma da ita, gurin da yake ajiye motoci  a garin Abujan.

Yana zuwa gurinsa ya zube a gabansa tare da cewa "ranka ya daɗe sannunka da zuwa".

Kamar ba zai yi masa magana ba, dan ya ɗauki kusan mintina shida kafin ya buɗe bakinsa yace "Idi ba na hanaka sunkuya min irin haka ba?"

Idiris ya miƙe tsaye yace "Ayi haƙuri, in sha Allah daga yau hakan ba za ta sake faruwa ba"

Omar inteeyas yace "Allah yasa" yana faɗar haka ya buɗe jakarsa ya ɗauko kuɗi yace "gashi nan, idan ka ajiye motar sai ka shigo jirgi ka biyoni, mu haɗu a gida".

Idiri ya karɓi kuɗin yana godiya, shi kuma Omar inteeyas ya wuce zuwa gurin jirgi.


★★★

*HANIYA POV.*

Haniya ba ita ta tashi ba, sai wajen ƙarfe sha biyu na safe, shima sai da Mummy ta zo da kanta ta tasheta, ranta duk a ɓace take yi mata faɗa.

"Haba Haniya baki kwanta da wuri ba ne kika zauna kina ta shararar bacci ba ki da niyyar tashi?"

Haniya tana mistsika idanuwanta tace "A'a Mummy na kwanta da wuri!"

Mummy tace "ƙarya kike, da kin kwanta da wuri ai zaki tashi da wuri! tsaya ma na tambayeki kin yi sallar asuba?"

Haniya ta shiga inda-inda saboda tunda ta kwanta bata tashi ba sai yanzu "Am.....am...Mummy ban"....

Cikin tsawa Mummy ta dakatar da ita da cewa "yi min shuru Malama, wannan inda-indar shi kaɗai ma ya tabbatar min da bakiyi sallar asuba ba, Haniya kina da hankali kuwa? har ki saki leɓe kiƙi tashi kiyi sallar asuba, gashi har Azahar ta kusa"

Haniya cikin sanyin murya tace "Dan Allah Mummy kiyi haƙuri yanzu zan yi sallar, ba zan sake kin makamancin haka ba, daga yau ba zan sake sakin jiki na yi bacci ba"

Mummy tace "to maza tashi ki yi alwala, idan kin yi sallar breakfast ɗinki na kan dinning"

Mummy bata fita daga ɗakin Haniya ba, har sai da ta ga ta shiga toilet, sannan ta fita.

Haniya sai da tayi wanka sannan ta doro alwala, kayan jiyata su ta mayar ta, kasancewar jiya da daddare da zasuyi kallo ta sakasu, hijab ta saka har ƙasa, ta shimfiɗa dadduma ta tayar da sallah, tana idarwa ta naɗe daddumar ta cire hijabi ta ɗauki ɗan ƙaramin mayafi a drower ta fita domin tayi breakfast.

Dinning area ta nufa, tsayawa tayi tana kallonsa cike da tausayi, kafin ta ƙarasa dinning ɗin bakinta ɗauke da sallama.


"Assalamu alaikum Babban yayanmu ina kwana".


Ɗagowa yayi yana sakar mata murmushin yaƙe yace "Lafiya ƙalau ƴar ƙarama, kin tashi lafiya"


Sai da ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun dinning ɗin sannan tace "Lafiya ƙalau Yaya Fauwas"

Yaya Fauwas yace "To Ma sha Allah"

Haniya tace "Yaya Fauwas ya kamata ka daina wannan tunane-tunanan saboda zai iya janyo maka matsala, tunda Abba ya dage akan sai ka auri Faty ya kamata ka haƙura, sanin kanka ne, kasan halin Abba da kafiya da kuma taurin kai, idan ya kafe akan magana wallahi babu wanda ya isa ya sakashi ya chanza ra'ayi".

Yaya Fawas yace "ai wallahi ƴar ƙarama, Abba da ace arne ne yana cikin arnan da basa su taɓa musulunta ba, ko da kuwa za'a yankashi ne"

Mummy wacce take bayansu tana saurarar abinda suke cewa tace "Au mijinnawa ka ke cewa da a cikin arna yake ba zai musulunta ba, ashe zamu saka ƙafar wando ɗaya da kai Fawas"

Tayi magana cikin ɗaure fuska.

Yaya Fawas ya kalli Mummy fuskarsa cike da damuwa, yace "Amman Mummy".......

"Amman Mummy me? karka manta fa mahaifinka ne, kuma ba zai taɓa zaɓa maka abinda zai cuceka ba, ƴar uwarka ce fa, tunda ƴar ƙanin mahaifinka ce, ni dai Fatyn nan na ga ba kofato ne da ita ba, ba kuma tarbiyya ne bata dashi ba, tana da kyau, hankali, tarbiyya uwa uba tana da ilimin addini da na zamani"

Fawas yace "shikenan Mummy ya huce".

Mummy tace "haka nake son ji, ka zauna ka ci abincinka kaje Abbanka na son ganinka, ke kuma Haniya idan kin gama kije part ɗinsu Inna Ladidi zakuje tare da ita kuyo mana siyayya".

Haniya tace "To! Mummy, amman ni a ganina bai kamata ayi masa auren dole ba, saboda".

"To sannu Haniya uwata, ko nace uwar Alhaji Khabir Mai siminti, faɗa mana abinda ya dace mu yi"

Haniya tace "kiyi haƙuri Mummy" Tayi maganar tare da fara cin amincinta ranta duk babu daɗi.

Mummy tace "sai shegen iyayin tsiya" Tayi maganar tare da ficewa daga babban falon ta nufi part ɗin Abba.

Yaya Fawas bai iya cin abincin ba, ya tashi ya fita daga falon, Haniya ta bi sa da kallo, sannan ta komar da kallonta ga abincinta ta cigaba da ci.



*_DIJARTYLUV_*

_***_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.