Free chapter · Read without an account
24
To ALLAH yasoku ban makaraba lokacin dana isa gidan, ko masu gidan basu tashiba, dama ba'a saka su husna alayi, dansu tashi yin sallar asuba baya cikin tsarinsu, ko k'arfe tara suka tashi zasuyi sallarsu ne.
Sashin Munneerah nanufa, dan nasa acan zan samo rahoto, mai gamsarwa.
Dady ne zaune kan sallaya da'a lama yau agida yay sallah, yana zaune yana karatun,"ALKUR'ANI MAI GIRMA" bayan yagama yay addu'a ya tashi, gadon yanufa yana murmushi, Munneerah tana k'udindine cikin lallausa bargo, tanata barcinta, yasa hannu yagyara mata gashinta daya rufe mata fuska, ya sumbaci idaninta dake lumshe, gashin idonta gaxar gaxar gashi bak'i, tad'an motsa kad'an.
"cikin muryar nan tasa mai d'ad'i yace my beauty 'yar rigima..
Cikin kunnanta yace my beauty!!! tashi kiyi sallah, kinga kina k'ara makara, tasa hannunta dasauri ta toshe kunnanta,yacire hannun yana fad'in places, ta bud'e ido ta lumshe, yamik'e yana fad'in inazuwa, bayin yashiga yahad'a ruwa mai zafi yasaka detol aciki,sannana yadawo wajanata.
Yad'agota tashi muje kinji autar baffa, tafara kukan shagwab'a yaya please kabarni barci nakeji.
"To tashi idan kinyi sallar basai ki koma ki kwanta ba, takuma kwanciya.
"yace okey bari nahawo gadon sai ak'ara irin najiya, dan nakula baki gaji ban....
Aikafin ya rufe baki ta mik'e zaune, ya d'auketa gaba d'aya yana dariya, kedai matsora ciyace my beauty, itakam tasa hannu tarufe fuska🙈.
dakansa yagasata tana kukan shagwa6a, shikuma yana aikin lallashi, ya taimaka mata tayi wankan tsarki, atawul yanad'ota kamar wata jaririya, yadire ta akan gado, riga yaska mata tai sallah shikuma yanufi kichin.
Break ya had'o mata mai sauk'i, ta idar tuni harta kwanta akan sallayar, tafara barci, yatada ita yabata, kad'an taci tace ta k'oshi, bai takurataba tunda lalla6ata yakeyi, yabata magani tasha suka koma kan gado, yarungume matarsa suka lula duniyar barci.
Sai k'arfe 11:am suka tashi Munneerah ta shiga wanka, shima yatafi d'akinsa domin yin wankan, dukda batajin dad'in jikinta haka ta daure tagyara d'akin fes,ta kwalliya mai sauk'i, tana fesa turare ya shigo jikinsa sanye da wando iya guywa, da k'aramar riga tashan iska ya rungumeta ta baya my beauty kinyi kyau, ALLAH yabani baby mai kama dake, tasa hannu tarufe fuska, yay dariya cikin kunnan ta, ai yanxu my beauty babu xancen kunya ko, ita dai hannunta yana kan fuskarta🙈 tanad'an murmushi, yakama hannunta zomuje kiyi break ko??
"Yaya break kuma waye ya dafa?
"Ya d'anja hancinta daga gidansu mom aka kawoman, ta zaro ido waje 😳, ginsu mom kuma yaya?
😳shima yazaro ido yanda tayi eh gidan su mom my beauty, haba yaya maimakon katasheni na girka"
"Yaja hannunta suka nufi falo yana fad'in waneni dasaka my beauty aiki a wannan rana mai tsada, ai yau ranarkice, my Angel.
Dakansa ya bata break d'in, kai jama'a yau naga tattali da tarairaya, iri iri da salon so.
~~~~~~~~~~~®
Hakarayuwa tacigaba da tafiya agidan dady, suna zuba soyayya kamar zasu cinye junanasu, sun iya tattalin junansu, wannan yasa kishiyoyinta auka k'ara tsananta kishi akanta dukda atsakaninsu ma babu zaman lafiya kullum fad'a kamar kaji, gashi kullum iyayensu suna k'itsa musu mugayen halaye, iyayensu mazakuma kullum burinsu tayaya zasu mallaki dukiyar dad, shikuma su kaudashi a doron k'asa.
yaukam na iso amakare dan natarar da maigin har yafita, dukda da alama ba a 6angaren Munneerah ya kwana ba, tana cikin bayin d'akinta tanata wanke kayan dady, sai dai na lura kamar dauriya takeyi, kawai dankamar batada lafiya, lokaci lokaci takan d'an cije le6enta na k'asa, sai kuma tacigaba da wankin.
Dahaka dai harta gama wankin tadawo palo tazauna, tana kallo, gani nai tamik'e da gudu tanufi bedroom d'inta, niko nabita, tana zuwa, bayi tashige ta shiga kwalaya amai, kamar zata zaxxagar da kayan cikinta, tayi sosai har k'arfinta yak'are, inason zuwa na taimaketa, inatsoron kartace daga ina, saina hak'ura na tsaya inakallonta.
Dayake jarumace haka ta daure tagyara jikinta da inda6ata, tafito ta kwanta kan gado barci ya kwasheta
" sai k'arfe biyar dady yadawo yaje 6angarensa yay wanka, yanufo d'akin Munneerah, danyau ad'akinta yake, yasha mamaki dabaiganta apaloba sai ya nufi bedroom d'inta, a'a my beauty lafiya kuwa barcin da la'asar????
Yak'arasa jikin gadon ya ta6a wuyanta zafi rau, ayya my beauty zazza6i yake damunki shine baki kiraniba, bai tada'itaba yanufi masallaci.
Saida yadawo yatada ita, ta tashi tana fad'in lah yaya yaushe kadawo ban saniba, kuma baka tadaniba??
"Shikam cikin tausayi yake kallonta, yace jekiyi sallar, sai naji abinda yake damunki"
Bayan ta idar da sallah tazo zata zauna kusa dashi yajawota saman cinyarsa, my beauty mike damunki ne ??
"Tad'an yatsina fuska ALLAH yaya nima bansa niba saidai kawai 'yan kwa nakinnan banajin jikina dai dai wlh, yakuma matseta ajikinsa my beauty kona samu baby ne?.
hannu tasa tarufe fuskan ta 🙈, kai yaya ni bani dakomai,
Yakama hannunta yana dubawa, kai my beauty gsky ban yardaba, akwai ajiyana acikinnan naki, yafad'a yana shafa cikinnata.
""Ta k'ara tura kanta cikin k'irjinsa tana wata 'yar darya, wadda yakejinta har cikin tafin k'afarsa, yaja ajiyar zuciya, yana k'ara manneta dajikinsa, har saida tad'anyi k'ara.
Kinga tashi muje d'akaina na dubaki, dan nasan irin maganin dazan baki.
Ta mik'e cikin sanyin jiki, dan itama tayi laushi,suna fitowa saiga husna tafito daga b'angaren ikilima,
Munneerah tafara k'ok'arin kwace hannunta dagana dady, shiko yak'i sakin hannun,
"Husna ta kallesu taja tsaki, da sauri dady yace wakikema tsaki??
"Husna tace wanda ya tsargu mana""
Yafara k'ok'arin kwace hannunsa dagana Munneerah, zaikaima husna duka, Munneerah tarik'eshi sosai yihak'uri yayana, dukan mace babu kyau, kaifa mai hak'urine, minene tsaki dahar zai b'ata ranka, tasumbaci hannunsa, kaga muje kadubani,taja hannunsa suka nufi b'anharan sa.
Dagudu husna tanufi 6angarenta tana kuka, wai ita yazatayi da wad'annan tsinannun matanne, tasan tana son dady, tana kuma kishinsa, bakama shegiyar Munneerah d'innana wlh ta tsani yarinyarnan, tayi alk'awarin sai Munneerah tabar gidanana, itada ikileema, dan Abdul'aziz natane ita kad'ai, 😜😜
Koda suka shiga d'akin Munneerah rarrashin dady tak'arayi, tare dafad'a masa magana mai dad'i, daga nan akazarce soyayya, saida suka soyu a soyayyar🙈😜, sannan ita Munneerah ma abin kunya yabata, shikuma yashige bayi yana mata dariya😂.
"Ya fito,"
Yace" tashi kishiga wankan.
Tatashi tana kare fuska, tashige bayi,
Ya girgiza kai yana murmushi, my beauty sarkin kunya, ALLAH yasa ki haifa mini yara masu irin halayenki k'anwata, nagodema dad, da mom, da baffa dasuka za6a minke amatsayin mata, ALLAH yasada su da aljannarsa.
Tafito d'aure da guntun tawul, yabita da kallo, saiyaji wata sha'awar ta kuma bijiro masa.
Itama tad'an kalleshi, ganin ya tsuruma idani yasa tad'au hijjabin sallarta dake d'akinsa tarufe jikinta da sauri, dantasan k'arshen zancen.
Ya lumshe ido, yana d'an murmushi..
Munneerah dai ciwo yak'ara karfi harsaida ta kwanta asibiti 2days, ciki ya bayyana d'an wata biyu.
Karkuga murna wajan dady, za'asamu d'a, mom kullum tana hanyar gidan dan duba Munneerah, dad ma yazo dubata sau uku, shima yayi farin ciki zai samu jika, daga tilon d'ansa namiji, mai kuma biyayya agareshi.
Mutanan yola dai basu saniba, su ikileema kam jin maganar cikin nan yatada hankalin su, suda iyayensu, da kakarsu, sunanan sun bazama bin malamai da bokaye, dan a6ararda cikin, 😜
Mom tace yadawo da'ita gidansu, sai cikin yayi kwari, tadawo, dady yad'an sosa kai, mom, idan tataho wazai rink'a yimini abinci??
"Mom tayi dariya, babana indai dan abincine kullum zamu rink'a dafawa da kai anan, kuma baga ma matanka nanba, ai suma zasu rink'a dafa maka""
Dady yakuma sosa kai to mom aikuma........ sai kuma yaya shiru.
"""Sai kuma mi?? babana k'arasa mana"
"Yatashi yafita yana dariya.
Mom ma dariyar takeyi, ALLAH ya shiryaka babana.
Yola.... matan su sadiq ne suka haihu suduka, dady yace Munneerah ta shirya suje.
Aiko tadaka tsallen murna ta ruk'unk'ume shi, yarik'eta sosai, ke bi ahankali baby na baiyi k'wariba, karki zubarmin.
Kai yaya ina murnanefa, ya sumbaci bakinta ai bakinkine murnar, saima afasa.
Tashagwa6e fuska yi hak'uri yayana na bari.
Ranar juma'a suka tafi yola, harsu mom, da 'yan biyu , suna a air port, Munneerah taga mai agwaluma,
Tace" yaya dan ALLAH kasiya min,
Yace" mizan siya miki??
Tace" agwalu6a, yay dariya agwaluma sunanata ba agwalu6a ba.
Mom tace, kairat taje tasiyo mata.
Dady yaja hancin ta, babyn nanfa yacika kwad'ayi.
Mom tayi dariya, to ai babana cikinka ya biyo, lokacin da'ina da cikinka, haka narink'a kwad'ayinnan, ai har namafi Munneerah.
Gabad'aya suka sa dariya har kairat data sayo agwaluma,
Badad'ewa ✈ yad'aga zuwa yola.
Sun sauka yola gidan su Munneerah, dagudu Munneerah tashiga cikin gida tana ihun kiran ummanta, ummanta tafito daga bedroom d'inta tana fad'in muryar wa nakeji kamar autana,??
Taje tashige jikin umma, umma tarungumeta sosai tana murnana ganinta.
Su mom suka shigo sunama Munneerah dariya, umma tasaketa tana fad'in, a'a kice hardasu haj. Bilkisu, nan suka zauna ana gaisawa, dandanan aka cika musu gaba da kayan ciye ciye.
Mama kishiyar umma ma tashigo suka gaisa, dady kam tuni ya wuce wajan abokansa, suna can gidan jafar anata kwasar hira,Bayan sun gama suma suka nufi gidan masu jegon.
Gidan su jafarne k'arshe, su Munneerah suka shiga palon yayan nasu dan sugaishe da su, suka gaisar dasu suka fito.
Safwan ya kalli dady, brother naga 'yar yarinyaka kamar mai cikifa??
"Dady ya hararesa to d'an sa ido wayakai idonka gurin"
Gaba d'aya sukasa dariya.
Jafar yace d'an uwa yaushe ka afka,?hardasu tsaraba, kace kwallonka tashiga raga.
Dady yace daga kai sai mai tsaron gida na buga ai, suka kuma saka dariya suna tafawa.....✍️