Free chapter 路 Read without an account
Page 1
SO DA ZUCIYA!!!馃挒
NA
NANA HAFSAT
(MX)
ZAFAFA BIYAR 2022
SHAFI NA DAYA
FREE PG: 1
___________
RIMIN KEB'E
GADA MAI 'DOYI
GIDAN ARDO BORKINDO
(AURE-AURE)
"Wahidi...! Sadaka..! Almajiri bara iya, Iya dan Allah dan annabi, Iya yunwa batada hankali, Iya ko 'kanzo ne ba miya. Ko gaya ne ba miya...Iyaa...wahidin wahidiya..!"
Almajirin nata rera baitin barar sa. Dadaa nata ce masa yayi hak'uri, yaki tafiya, Ya rike robar barar sa ahannun hagu, Dayan hannun kuma ya sakashi a hanci yana sakato daskararren tasono yana gogewa a kodaddiyar rigar shaddar jikin sa ruwan bula, Kayan sun fattatake.
**Fatimah-Zahrah (Zaarah) Yar bafulatanar budurwar na kwance akan shamilalliyar katifar kwanciyar ta irin ta boarding school dinnan. 'Kulaficin nacacciyar baitin rera barar almajirin ce ta tashe ta daga baccin yunwar dole data dauke ta. Ta ja tsaki tana sosa manyan gashin idanun ta da suka jike da ruwan hawayen ta. Ta juya kanta gefe, Ta sauke idanunta akan mahaifiyar ta dake zaune tana yanke faratan hannun ta.
"Dadaa.."
Ta 'karasa tana rufe bakin ta, Bayan bahaguwar hammar data taho mata.
"Kin tashi?"
"Na tashi Dadaa! Bansan bacci ya dauke ni ba ma."
"Ai wannan wanki da kika tula dole ki baccin gajiya, Allah ya yi albarka."
"Aamin Dadaa"
"Ga abinci can cikin kwanon ki. Tun da zafin sa yanzu nasan ya huce."
Da azama ta janyo kwanon ta bude shi, Dauke yake da danwake da man 'k'uli da jan yaji.
"Wayyo Allah na! Danwaken Iya fatsuma. Dadaa ina su Hamma Modibbo Da Na'eelah da Raheelah?"
"Su Raheelah sun tafi Islamiyya, Hamman ku kuma bai jima da barin nan dinba. Shi ya kawo danwaken nan ma."
"Allah sarki Hamma, Allah ya kara budi."
Cikin haka mahaifin su Malam Ardo borkindo ya shigo cikin gidan bakin sa dauke da sallama.
"Atuwaa,Dadaa ku fito"Ya zunduma musu kira yana daidaita zaman da yayi akan wata 'ballalliyar kujera da ta gaji da lalacewa.
Mama Atuwa ta fito daga cikin d'akinta tana susar kunne da gashin kaza. Ta tsaya 'kerere akan sa sanye cikin riga da zani kowanne kalar sa daban. Yaja tsaki yana girgiza kai.
Atare Dadaa da Zaraah suka fita tsakar gidan nasu,
"Bappah Barka da dawowa"
Zara ta tsugunna har kasa tana yiwa mahaifin nasu sannu da zuwa. Ya amsa fuskar sa a daure. A 'darare ta koma cikin da'ki. Don inda sabo ta saba da tsangwama da kyarar mahaifin nasu.
"Sannu da zuwa..." Dadaa ta masa sannu ta rakube a gefe ta zauna.
"Ayau yau, Nakeso a share dakin abincin can. Jibi i war haka amarya zata tare."
Gaba d'aya Dadaa da Mama Atuwa sai suka zube masa idanun su. Kowannen su kallan sa yake cikin tsantsar mamakin kalaman sa. Dai dai lokacin da almajirin nan ya sake dawowa zaure yana kurma barar da yake. Hade da bubbuga 'kafar sa a kasan fashasshen dab'en da akayi wa zauren.
"Wahidi...! Sadaka..! Almajiri bara iya, Iya dan Allah dan annabi, Iya yunwa batada hankali, Iya ko 'kanzo ne ba miya. Ko gaya ne ba miya...Iyaa...wahidin wahidiya..!"
"Kundugurin uban ka, Nace kaci malafar kan uban ka. Zaka fita ko sai na kirb'a ka anan?" Cewar Mama Atuwa hade da daga hannu ta masa dak'uwa.
Almajirin ya tsaya sararo baisan abinda yasa take masa fada ba Kamar yayi wani lefin? Zara dake daki ta kirawosa ta bashi sauran danwaken da takasa ci. Saboda maganar auren da taji bappan su zai sake karowa a karo na ba adadi. Yayi ya sake su kamar hular sawa.
"Me muka rage ka da shi da zaka sake karo wani auren Ardo? Nace mai ka nema ka rasa agare mu. Allah ya tsinewa dubu goman da ka samu nasan da ita zaka sake karo auren nan." Cewar Mama atuwa dake huci Kamar tsohuwar zakanya.
"Toh Malam Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lapia." Dadaa tafad'a tana mikewa tsaye hade da komawa cikin daki.
Mama Atuwa ta buga tsallen albarka tana doddoka hannunta ajikin bango.
"Ardo! Tselen uban can, Abu ta kazar uban can kayya kai, Wabillahil gidan nan zai babbake akan amaryar nan da zakayo. Ke kuma tsohuwar munafuka kina wani dudduk'e kai, Kamar sabuwar amarya, Har da wani yi musu fatan alkhairi. Toh baki d'aya na hadaku nayi Allah ya isa.."
Malam Ardo yamike yana girgiza kai, Zai fuce ta jawo kasan rigar jikin sa yar shara,
'Yar karamar 'yarta da ta taso daga bacci alokacin ta tsaya a tsaye ta sau fitsari, Hancin ta dagaje dagaje da majina, Ta riko fatattakakken zanin Mama Atuwa tana cewa,
"Mama yunwa nake ji."
Atuwa ta sake damk'o kasan rigar Malam Ardo bata ko bi takan Farillatu yar autarta ba, Cikin tsananin takaici hade da kwakwaso rantsuwa ta dire, Da d'oriyar nanawa cinyarta duka tacigaba da cewa,
"Ni da kai sai Allah ya mana hisabi Ardo. Lokacin da kazo neman aure na mekace shekarun baya? Ca kayi da gani babu kari, Matar ka ta farko ma had'aku akayi ba kai ka ganta kana so ba, Kace ni da kai, Bayan aure zamu gwangwaje mu gyagije, Muci duniyar mu da tsinke, Tarin alkawarurrukan da kayi mun sunada yawa Ardo. Harda cewa Kullum zamu dinga shan shayi da buredi mai yanka yanka Ardo, kace da lemon kwalba da shinkafa. Amma tun sati biyu da auren mu ka dena mun komai. Shekaru sha 15 kenan kadena duk wasu hakki na dana yara na dayake akan ka. Aure 8 kayi Ardo, kowacce da tazo tayi yan satinnai Sai ka rabu da ita, Saboda tsabar bakin hali Irin naka. Samun miji Irin ka nayi dana sani, Dana kori manema na a baya, Na bi kyau ba halin kwarai Irin ka, Allah sarki idi mai kifi. Kullum sai ya aika mani da sukunbiya jela...Rana"
Bata kasara ba Malam Ardo yaja dogon tsaki yana girgiza kai,
"K'ofa abude take, Duk sanda kika shirya fita... A shrye nake na baki takardar sallama."
Mama Atuwa ta wulla masa harara tana tab'e baki,
"Saki? Hohoho ai naga gidan zama Ardo, Na tara yara har 5 kace na fita? Babu inda zani. Na zame maka kadangaren bakin tulu , Akashe ka a fasa tulu a barka ka 'bata ruwa. Ahayye Atuwa maman sailuba da Sameerah, Uwar Hajaara da Farillatu..."
Malam Ardo yaja tsaki hade da bige hannun ta daga rikon rigar sa da tayi, Ya fice yana mita. Ita kuma Mama Atuwa ta figi hannun Farillatu ta goyata tana jera tsaki, Had'i da yadawa Dadaa maganganu. Ranar kaf dangin Malam Ardo na kusa dana nesa sai da Atuwa ta zage su tas kowanne ta kamo sunan sa, Sai ta aibata shi.............
WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana
ZAFAFANKU BIYAR 馃敟馃敟馃敟馃敟sune suka sake dawo muku da wasu nau'in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA
SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance
GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA 茦WARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi
JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE
DEEN MARSHALL馃憠馃従 Mamuhghee
HALIN GIRMA馃憠馃従hafsat rano
TAKUN SA茦A馃憠馃従billyn abdul
SO DA ZUCIYA馃憠馃従miss xoxo
茒ABI'AR ZUCIYA馃憠馃従huguma
HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU馃馃徑馃馃徑馃馃徑馃馃徑馃馃徑
#team zafafa biyar