Free chapter · Read without an account
Kai ka jawa kanka Chapter 5
Kai ka jawa kanka 5
Ikilima Adam
Kyauta Daga Allah
Page 5
ina nufin banda mazakuta kwakwata bana jin shaawar ko wace ya mace
dan Allah karkice zaki rabu dani kitaimaka min naboye mikine saboda karki gujeni kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro yake.
fatima da rudani yacika zuciyarta takasa magana babu abunda takeyi banda hawaye dake kwaranya daga idanun ta.
rungume ta yai yana kuka stil kallon sa take bakin ta yai mata nauyi kukan zuci take ita macece me burin zama uwa baya da hk duk mace me lafiya tanada shaawa ahaka ita zatai rayuwa ga wanda babu kofar rahma dazakaji sassauci inda matsalar shi rashin haihuwa ne ,yanada lafiya abun zezo dasauki.
Hannu yasa ya tallabo fuskar ta nasan kina, nadama kikeyi akan aure pls kiyi magana ko zanji sauki a zuciya ta.
Zuba mashi jajayen idanun ta tai ,zatai mgn saita fasa, zaunar da ita yai kan kujerar dakin tareda dauko mata gyalen ta ,tissu yasa yana goge mata hawayen ta ,tareda kama hannun suka sauka kasa .
Umma tace fita zakuyi ne kuke ta zuba uban sauri haka ,amsa mata yai agajarce eh saimun dawo. Wayarsa ta fara ruri yana dubawa yaga ,manager auwal ,gefe daya yatafi dan amsa wayar.
Manager auwal yace kace in same ka gida ganinan zuwa yanzu ,nida hajiya hussaina , khalid ya amsa masa da saikun zo tareda komawa cikin gidan .
Fatima yahango zaune kusa d umma sai mgn umma ke mata takasa saida hawayen ta ,cikin tsananin damuwa umma ta tsare khalid da idanu me kaimata ne?
zazzare idanu yai yace nikuma , wani abun tace namata cikin ta ne ke ciwo tun safe .
Umma tace amma dai baka kyautaba hannun takai jikin fatima , sannu yata tareda kwantar da ita a cinyar ta .
Deen da aisha tare suka dawo ,daga makaranta su ahanzarce yakaraso ganin fatima na kuka ya gigice yafita hayyacin yakasa gane shin meyasa in yana tare da ita yakejin nishadi ,in yaga bata walwala tashi ma daukewa yakeyi .
Aisha tace umma meya sameta tana kai hannun jikiin fatima dake sheshekar kuka .
umma tace indo cikin ta ke ciwo ,maza dauko mun waya inkira docto hamza da to ta amsa mata tashi dan dauko wayar.
Deen gabadaya ya nemi nutsuwar sa ya rasa dan kukan fatima ya fassara shi da kukan bakin ciki yana gane duk wani yanayi na fatima a dan zaman dayai da ita ,ko kallon khalid beyi ba bare yasa ran ze masa magana,
Direct dakin sa ya nufa kifewa yai a gadon ,
Yana kuka ,ahankali ,karar bude kofar yasa shi ,saurin juyawa ,
Khalid yagani abakin kofar sa tsaye yana kallo sa da mamaki kwance akan fuskar sa.
Karasowa daga ciki , hannayensa goye abaya yana magana ,cikin kakkusar murya ,deen nakasa gane wace alaka ce tsakanin ka da fatima.
Deen murmushi yai tareda sauko wa daga kan gadon dafa khalid yai, fatima ai matar yaya na ce ,wannan shikadai ne alakar mu.
Ajiyar zuciya khalid yasauke yana fuskatar deen , nace maka inason karinga kwana dakin fatima.
Amma kaki bin umarni na , tun lokacin nazuba maka idanu ,amma yau shine last dinka inhar baka kwana dakin ba ,wallahi wallahi babu ni babu kai kuma karka tambayeni dalilin turaka ,sannan na yarje maka kai komai na mu'amala da ita ,amma iya dare ,batareda kabari tasani ba, barin dakin yai , yafita ,yana tafiya kaman ze tashi sama.
Innalillahi wa,inna ilai rajun DEEEN YASHIGA MAIMAITA WA.
dafa kansa dake juya masa yai nan take jiri yafara dibar sa.
Acen bangaren umma ,docto hamza yaduba fatima , magunguna ,yarubuta mata tareda rokon abarta tahuta.
Manager auwal ya iso cikin shiga ta alfarma ,rikewa hajiya hussaina jakarta yai khalid yai musu jagora babban falon su.
Umma sai kallon hajiya hussaina takeyi zuciyarta na tsanan ta bugawa, still momyn fatima ita take kallo ,aisha ce dauke da tray hannun ta itada balaraba nusy nabiye dasu abaya.
Nusy cikin muryansu na yara tace umma kinga yanda kike kama da matar nan tana nuna ,momyn fatima da yatsa.
Murmushi mommy tai tareda kamo hannun nusy tace yan mata ya sunan ki
Sunana nusaiba amma anty aisha ta samin nusy .
Khalid ya kama hannun nusy zonan karki cikasu da surutu maza kibi ,sumayya ku tafi ,
To daddy tareda bin hanyar dakin indo.
Sun samu samu tarba me kyau dakyar sukaci abinci kadan ,hankalin momy nakan rashin ganin fatima.
Daddy yai karfi hali wai ina diyar taku take .
gabadaya gidan sai rarraba ido suke suna inda inda yanza zasu ba iyayenta amsa.
Sumayya tace ai tana dakin batadan jin dadin jikin ta, ku taso in rakaku ,jin hka caraf khalid ya karbi zancen , kibarsu zan rakasu, mummy da alhaji auwal tashi sukai sukace wa su umma da inna farida ,zamu leka ta ,muna dan sauri akwai inda ,zamuje
Fuska asake ,umma tace saikun fito .
Direct dakin ,fatima suka nufa khalid nagaba suna biye dashi abaya ,dauke da sallama bakin su, suka shiga dakin , hango fatima kwance alamun tayi zurfi da tunani bama tasan da zuwan su ba.
FATIMA! FATIMA!
Firgit tadawo hayyacin ta, mamaki ne yacika ganin iyayen ta ,zaune gabanta ,rungumi mummy tai tana kukan farin ciki ganin su.
Khalid yakasa ya tsare yana tsoron kada taba su labarin abunda yafaru .
Daddy yace daughter meke damunki ne.
Caraf khalid ya karbi zancen da cewa au kana nufin bakasan ciki gareta ba, yana tsotsa keyar kansa alamun kunya.
Murna yacika daddy da mummy suka hada baki wajen fadin ,mashALLAH.
TACE AYYAH MUMMY AI KINSAN DA KUNYA IN GAYAMIKI ,HIRA SUKA TABA ,komai zasu fada ayi gabansa nace ikon ALLAH, DRING TAKAWO MUSU SUKACE AA SUNGODE , haba yazaai kuce haka , daddy yatashi tsaye tareda dafa kan fatima yana mata adua kamar haka.
Allah yazaunar dake lafiya gidan mijin ki .
yabaki zuria dayyaba yakare ki da sharrin magauta inshAllah rayuwar ki ,zata inganta Allah ya rabaki da cikin jikin ki lfy .da amin suka amsa dukan su banda fatima.
daddy yace ,zamu sauka kasa da mijinki akwai abunda zamu tattauna, ke kuma dakin gama ki sameni kasa saimu wuce amma karki dade .
inshAllah bazan dade ba tabashi amsa.
fita dakin sukai shida khalid.
ajiyar zuciya mummy tasauke tace fatima duk uwa ta tana gane farin ciki ko akasin hk akan fuskar yarta .
cikin naki yakai wata nawa?
rarraba ido fatima tasoma ,tace wata daya tareda yin kasa da kanta .
Gud yata ina farin ciki, ki kula da kanki please ,kinga ke kadai kika rage mana yayan ki , yabata ,tun kina yarinya amma ,mun barshi akan ya rasu ne dan shikadai zesa hankalin mu, yakwanta ,indai yana raye wataran zedawo gare mu.
Fatima kwantar da kanta jikin mummy tai .
Tana shakar kamshin jikin ta ,azuciyar ta, tana tausayin kanta , tasan dai ta auri khalid ne , bin umarnin daddyn ta.
Bataso ta watsawa iyayenta kasa a idanu mussaman ,daddy daya bata gata ,soyayya ,mummy tayi iya kokarin ta dan ganin ta inganta rayuwar ta ta hanyar addinin islam.
mummy tashi tai tadauro alwala dan gabatar da sallah tare sukai itada fatima.
kudade masu yawa mummy taba ,fatima koda bukatan hk yatashi dakyar ta amsa ,kasancewa kullum khalid ke ajiye mata kudi, bata tabawa, tare suka sauko kasa.
mummy , taiwa umma da inna farida, sumayya ,da aisha dake chattin da isma,il.
sallama tai musu ,yayin da umma taciko leda da atamfofi,leshi masu tsada taba ,balaraba tasa musu a mota.
mummy taji dadin karamci su, tareda musu godiya .
a compound din gidan ,khalid da daddy ne suke hira .
ganin su fatima yasa sukai musabaha da daddy tare da rakosu har mota.
daddy yace oga khalid nagode sosaai kekuma daughter ki ,kula dashan magani.
dariya tai tace inshAllah , Allah yatsare hanya saida suka wuce kowa yakoma cikin gidan .
Deen ne ke saukowa daga kan step suka hadu da fatima shi yana sauri zeje sallar magrib.
kallon ta yai tareda dauke kansa gefe ,bece mata komai ba,
mamaki take toshi Deen kalau yake kuwa ,barin wani tunani tai .
tashiga dakin ta ,ta canja zanin gado ta gyara dakin tsaf tareda kunna turaren wuta mai daddan kamshi.
direct toilet tashiga tai wanka tashirya cikin doguwar riga cotton pink couleur ,gyara gashin kanta ,tai tasa rinbon tai parkin sa.
simple makeup tai tareda shimfida darduma dan gabatar da nafila.
bayan ta idar tazauna jiran sallah isha'i tareda lulawa duniyar ,tunani toshi khalid baya da lafiya ,ya akai ya haifi nusy?
sanin babu me bata amsa ,saishi tai shiru tana nazartan mijin nata.
sallama yai tareda nusy yashigo kallon su take ta tsurawa nusy idanu.
khalid yace ga nusy nabaki kyauta yanzu kece mahaifiyar ta .
ya kalli nusy yace kinga wannan itace maman ki ,itace zata ringa kai makaranta tana dauko ki.
nusy matsowa gaban fatima tai tace mama ,dady Yace ke mama ta ce shin hakane?
dariya fatima tai yanayin yanda yarinyar tai fuska .
eh nice maman ki duk abunda kikeso ki tambayeni nice komai naki daga yanzu agidan nan.
tsalle nusy tasaka tareda cewa nidai bara inje inkwaso kayana.
gyada mata kai tayi alamun to tana dariya ,Allah yasani tanason yara ,gashi yarinya tace mata mama ,dadi taji aranta.
kallon khalid tai zatai magana ,saita fasa .
dan Allah amarya kimun mgn kozanji sauki ,amma bazan matsa miki inkince in sakeki zanyi banda zabi ,kasancewa dake shine burina.
rufe bakin khalid ,fatima tai dan jikin ta yai sanyi ,tace kayi hakuri abunda naimaka dazun kuma namaka alkawarin zama tareda dakai bazan taba fitar da sirrinka ba.
farinciki fal aransa , gyara daddumar tai dan gabatar da sallah ,fita yai zuwa massalaci shida abba.
bayan sun idar ,hanyar ta dawowa gida abba yace khalid ina fatan ka gayawa fatima , zancen da mukai da kai .
eh abba na gayamata amma fa da farko kaman zataban matsala daga karshe ta rungumi kaddara.
dariya abba yai yace to dana saika kula sossai ,deen dafatan ya karbi tayin ka?
khalid yace eh abba dan yau yaga banmasa da wasa ina sa ran zeyi abunda nasashi ,itakuma fatima nasan yanda zanbi da ita
dariya sukai abba rike da hannun khalid suka shigo falon .
direct dakin sa yanufa abba da mamaki yaga umma adakin tana karanta suratul bakara .
abba yai murmushi ke naga ba sallah kike ba .
kuma bazaune kike ba kinata zagaye mun daki.
matsowa umma tai gaban abba tace kasan daki inyai shekara da shekaru ya tara tarin zunubai adua shine ze rage , sannan na tabbata an aikata tarin zunubai adakin nan shine nazo ko Allah ze wanke dakin da rahmar sa.
saukan mari taji wanda yasa kanta yafara juyawa taje tabugi bangon dakin nan take ji.
nan take jini yafara kwaranya ,kafa yasa yature ta ,takarasa faduwa kasa, yana huci sama -sama ai wlh hassanaa kinyi kadan bar ganin ina daga miki kafa .
Kokarin mikewa takeyi rike da kanta ganin hk yasa shi karasowa gaban ta yasa kafa ya shure ta ,kara ta saki nan take ihun ta ya doki kunnuwan yan gidan ,deen dake kokarin shigo yaji ihun ,umma a hanzarce duk gidan sukai dakin ,abba.
Abba najin motsin tafiya ,yai sauri ya dagata tareda daurata kan kujera ,kyalle yasamu yana goge ,mata jini .
Karar buga kofa yaji ,yabasu izinin shigowa.
Suna shigowa ,fuskar su cikeda damuwa ,sukace meya sameki ,umma.
Abba yai murmushi yace saida nace mata tadaina hawan kujera dan ta goge hotunana dasukai kura, amma bataji ga irin ta nan tafado daga sama.
Aisha tasoma kuka,umma meyakaiki ,please kidaina ,inna farida da sumayya ,deen sunata juyayin al'amarin ,kowa zuciyar sa ba dadi.
Deen da yakeji kaman yai kuka ,ya tallafo ta fatima ,zata taimakashi hannu yai mata ,alamun tabari .
Ahaka ya dauketa cak ,yai dakin da ita, kowa na biye dashi abaya ,khalid kadai ya tsaya .
Yace abba yanda naga buguwar umma na tabbata ba faduwa tai ba.
Cikin hade rai yace eh ba faduwa taiba ,nine nabuge ta, bawa khalid labarin abunda yafaru ne, yasa khalid tsaki.
Abba yace ko bakaji abunda nace maka taimun bane .
Abba naji naji aiba karyatai ba amsa zaka bata daidai da maganar ta .
Daman dan adam be rayuwa saida zunubai, kallon kan ta ,takeyi ustaziyya mai tsoron ALLAH AMMA ZUCIYAR aBA HAKA TAKE BA.
nidai pls karka sake daga hannu ka buge ta , uwa uwa ce koda a titi take yawo.
Yana kai karshen zancen nasa , yafice daga dakin.
Abba cike da mamaki waishi khalid ke fadawa uwa uwa ce , kodai kanshi ya kwance ne.
.......
dakin umma yanufa direct da sallama bakin shi, suka amsa masa zama yai kusa da ita ,yana kukan zuci ,rabon shi dayaji ,umma tabashi tausayi tun sanda tafara samai idanu akan aure ,auren shi.
sannu umma, ya jikin ina ke miki ciwo, cikin tsananin rudewa , umma tace dasauki ahankali muryan ta ,ke fita.
kallo yakai ga deen da suna hada idanu ya dauke kai.
aisha dauke da ruwan dumi ahannun ta ,ta saka kyalle aruwan tareda kama umma , ta zaunar da ita .
gasa mata ciwon tayi ,
umma zufa sai zufa take duk karfin Ac dakin.
sunkai karfe goma wajen ,na dare adakin umma sukaci abinci dukansu banda khalid , da abba..
Deen yasoma hamma alamun barci' yakeji .
Maganar da sukai da khalid ne ya fado masa.
Tareda saka hannu kan blanket din data rufa dashi rintse idanun sa
Yai yana girgiza kai' alamun ina bazeyu ba.
Jin nauyi tsayuwar mutum akanta 'yasa ta bude idanun ta ahankali 'idanun ta,sauka Akan deen amma sai yana mata gizo tana ganin kaman Khalid ne 'kokarin juya wa ,yake yi .
Tace pls tsaya mana 'mutuwar tsaye yai, yakasa magana .
Jawo hannun sa ' tai tace haba Khalid kashigo kaki mgn , harzaka juya ,pls zo mu kwanta ,kusa dani zaka kwana.
Hankalin deen yai mugun tashi 'cikin tsananin kaduwa har bakin shi, n'a rawa .jan hannun sa t'ai ,tareda kwantar dashi 'ta kwanta bisa kirjin sa.
Babu abunda kakeji ,sai bugun zuciyar su' na tsananta bugawa .
Kara shige jikin sa t'ai 'har dukiyar fulanin ta n'a gogan jikin 'innallilahu wa'inna ilairajun yashiga maimaita wa ,a azuciyar sa, suna ahaka har barci yai awon gaba da ita hannun ta saitin bakin sa.
Jin ta saki jiki ya tabbatar barci yai awon gaba da ita'ne ajiyar zuciya yasauke tareda dagata ahankali ya kwantar da ita .
Sanda sanda yafito yabar dakin ta direct dakin sa ya nufa 'yashiga toilet shaya ya sakar wa kansa yana kuka mai suma rai , a tarihin rayuwar sa ' be taba koda taba hannun mace ba, saina Yan uwan sa, suma bisa lalura .
Gashi yau kwance da matar Wansa a shinfidar ta '( pourquoi ) meyasa Khalid saini zaka zaba da zan maka kazamiyar aiki , yana ahaka har yaji zuciyar shi tasoma 'sanyi ,d'auro alwala yai yatada sallah raba dare yaii ,yanata neman yafiya gun ubangiji hannayen sa asama yana kuka .
Har asuba yana nan zaune ,shiryawa dan zuwa sallah asuba ,tare suka sauko da khalid kan step din.
Ahanzarce suka wuce massalaci kasancewa ana kokarin tada sallah.
Bayan Sun idar sallah suna zaune ,suna lazimi Saïda haske yafito sannan suka dawo gida '
Khalid ya dafa deen yace kanina ina fatan ka aiwatar abunda nasaka .
Jim deen yai yai shiru besan yanda ze fada masa bé aikataba ' eh n'a aikata yabashi amsa ataikace .
Murmushi Khalid yai tareda kama hannun deen cikin nasa ,kallo kallo sukewa juna .
Deen inason kullum zaka ringa zuwa harsai sanda nace kadaina kafahimta 'gyada masa Kai yai ,deen bece komai kasancewa barci ,da damuwa Sun masa yawa .
Yaiwa Khalid sallama tareda zuwa dakin sa
Dan ya kwanta.
Khalid direct dakin fatima yazarce 'sallama dauke abakin sa yashiga dago Kai t'ai takallesa nusy n'a gaban ta 'tana sa mata Kayan makarantar boko'
Murmushi ta sakar masa ta tuno daren su n'a jiya duk da bawai wani Abu akai ba hakan yai mata dadi sossai.
Ina kwana tace mishi ' nusy ta juya ta ga Khalid aguje ta rungume sa tana dady ina kwana.
Lfykalau ya amsa mata .
Yana murmushi yace har mama tashiryaki '
Eh daddy anmun wanka n'ai brek gsk mama n'a ta daban ce ,tafi mama Maryam kula dani.
Rau rau da idanu khalid yai yace nusy maza muje ki gaida umma da abba sannan ,maman ki takai ki.
Makaranta.
Fatima tace ai kabar tare zamuje dubo jikin umma sannan mu wuce aida sauran time tana kallon agogon dakin.
Rike hannun nusy t'ai zasu fita 'yariko hannun fatima yai mata mgn kamar Haka ina fatan kinji dadin daren jiya.
Murmushi ta sakar masa tareda kwace hannun ta 'tai gaba tawuce sashin umma.
Kiran aminu yai awaya yace Kai dan iska shawarar dakaban Akan fatima da khalid yana tafiya daidai ' aminu ya bushe da dariya yace angayamaka nidin Wasa ne , kaide ai shaani kawai amma kasan me?
Khalid yace A'a ina tausayin ka .
Saboda ace Macé iya Macé kamar fatima wadda ta hada komai da komai , ace zumar ta bakaine zaka lasa ba asshh ansha dakai.
Ranka Khalid yagama baci ,nan take yaji kishin sa ya taso daurewa yai yace to ai tsaron lalura so kake in barta wataran tabar gidan bansani 'gwara ayi tuwo n'a maina
Dan iska sai anjima
.
Fatima rike da hannun nusy sukai bangaren umma 'ta same ta zaune ,Aisha n'a gasa mata kumburin da fuskan yai .
Aisha ta kalli Fatima cikin sakin fuska tace anti inakwana '
Lfykalau alhmdulillah fatima ta bata amsa ya maijiki .
.
Dasauki 'anti harkun fito Kenan zakije Kai nusy boko.
Tace eh naga Time yakusa .gaban umma takaraso taduka ta gaisheta a ladabce '
Lfykalau alhmdulillah fatima naji sauki ' kallon nusy t'ai taji tausayin yarinyar n'a kamata' .
Sha kan nusy t'ai tareda masu fatan adawo lfy.
Hartakai bakin kofa 'aisha tace anti dan Allah in zakije dauko nusy boko zamuje tare saboda zanje siyayya supermarket aljazira .
Tom babu matsala indo Allah yakaimu.
Dan bata fuska Aisha t'ai tace nidai nace muku banson kunace min indo sunan fa 'tsoffafi ne '
Umma t'ai dariya tace saiki gayawa uban naki daya samiki 'sunan uwar sa.
Da dariya fatima tabar dakin dan bata fiye surutu ba.
Ahanzarce tadau mota 'mai gadi ya bude mata Gate 'bata zarce ko'ina ba , sai makaranta su ,nusy
Sauko daga mota t'ai tareda mata rakiya har kofar Shiga .
Mai gadin makarantar sai washe baki yake 'yace amma hajiya wannan diyar taki kuna kama sossai.
Nagode tacemishi ataikace tareda juya akalar motar ta '
Abunda ta hango a wani motar dake kusa dasu ya girgiza mata tunani .
Alhaji nura rufe idanun ta 'tai tare da kara bude su,kodai ba daidai take ganiba ,again dai shidin ta hango .
Cikin mota rungume da wata classemat din ta 'Alisa.
Innalilahi wa'inna ilai rajun tashiga maimaita wa 'tsayar da motar t'ai.
Yai daidai da fitan alhaji nura daga motar abokiyar alfashar sa.
Ahanzarce take tafiya harta tuntube babu Wanda taji taba tausayi lokaci daya 'sai inna Farida.
Alisa ! Alisa! Alisa.
Arazane ta juyo dan ganin wacce ke mata wannan uban Kira.
Kallon kallon suka fara yiwa juna.
Alisa zare idanun ta t'ai tace daman fatima kina kasar nan 'naji ance kinyi aure.
Daidaita nutsuwarta t'ai tace eh fa nayi aure , kefa kinyi aurenne tana tsareta da idanu.
Numfasawa t'ai tace 'aa aini aure ba yanzu ba dan saina gama da wancen dan iskan surukin sani yaro.
Kinsan me fatima ta girgiza Kai 'wlh wancen mutum nan da kike gani yana tafiya tana nuna wa fatima motar shi'''
Eh inajinki Alisa .
Numfasa tai tareda gyara tsayuwar ta jikin motar ta.
Yamin alkawarin ze aure ni kuma yace min beda mata, yabari nagama sakan kancewa dashi fatima,duk nakori masoya n'a , Wanda keso n'a da aure ,saida tafiya t'ai tafiya yace min , shifa beyarda dani ba .
Nacemishi kamar ya ?
Shine yake cemin wai so yake ya tabbatar bantaba sanin da namiji ba inbahakaba baze aure ni ba.
Nashiga tashin hankali fa ' dan n'a mugun kamuwa da son shi a lokacin 'kullum maganar da yakemin Kenan in bashi kaina sbd ni yar jami'a ce beson ya aureni ban cika Macé ba' ya sakeni ba girman sa bane.
Harga Allah nadauka dagaske yakeyi saboda yanda yaketa 'kiran sunan Allah abaki' daga karshe n'a sallama mishi kaina.
Rintse idanun ta ,fatima t'ai tanamai tausayawa Alisa.
Alisa ta kara da cewa tunda yasamu ya kusanceni yace ai alhamdulillah ni kamila ce 'inyagama abunda yake ,ze turo manya ,Alhaji nura kullum sai ya maidani kaman. Karuwar sa babu rana ta banza da bezo ya daukeni munyi lalata ba 'tun inajin banson abun 'har abun yafaramin dadi.
Muna cikin Haka nasamu ,ciki ina fadamai yace indai bincika saida nai masa dagaske n'a nuna masa zankai karar sa ,kotu sannan yace saide azubar da cikin 'hawaye shar a idanunta .
Ya cire min ciki wajen sau uku 'na karshen ne likita ya tabbatar min da bazan kara haihuwa ba saboda yawan cire cikin yataba mahaifata .
N'a sanar dashi 'yace min aishi wannan ba matsala bane ba haihuwa bane gabansa ya kwantar min da hankali 'nima nacire wani tunani araina.
Kwasam rana daya nazo super market nagan shi da wata yar yarinya da bazata wuce 16yrs ba haka' rike da hannun sa
Yana da dariya suna hira' gabana ne ya tsananta bugawa nace to mezeyi da yar karama yarinya Haka dan sam ban lura da kamannin da sukeyi da itaba.
Gaban sa nasha nace 'ranka yadade kwana biyu Inna kiraka baka dagawa 'shan kunu yai kaman betaba dariya ba 'yace min baiwar Allah lfy kuwa.
Hankalina yai mugun tashi nace alh nura, nice kake cewa bakasanni ba.
Yarinyar da suke tare naga tanamun kallon tuhuma 'ta kalleshi tace daddy wai wacece wannan .
Bansanta ba, shine amsar da ya bata .
Tsaki taja yarinyar tace mun kawai kuga ya da uba suna tafiya kita bin mu' sorry daddy be bukatan Karin aure fuuu taja hannun dadyn ta suka bar wajen.
Wallahi fatima 'sati n'a biyu kwance ban lfy tun daga ranar ' nafara bincike akansa har nagono surukin SANi yaro ne
Har kofar gidan sani yaro naje kwanaki nasa Aka kiramin shi.
Yana ganina ya razana 'daukata yai a motar sa 'mukabar unguwar ,cikin lallashina yaita yi yace wallahi Alisa inaso auren ki ,banso boye miki inada mata , nasan bazaa Bari inkara aure ba' nan naringa zagin sa macuci azzalumi 'wallahi sai Allah ya saka min .
Haka dai yake zuwa wajena tun banyarda harna soma biye masa kamar yau dinnan da kika ganmu 'nayi alkawarin saina ruguza masa rayuwar sa 'sai yazama abun tausayi.
Fatima numfasawa t'ai 'cikin kaduwa da zancen ta ' tace amma Alisa kin tafka babban kuskure koda yake ai yariga da yafaru .
Bangaren haihuwar da akace bazaki taba samu 'inshaAllah zan taimaka miki 'tareda dafata 'suna kallon juna ido cikin ido.
Alisa inason kimun alkawari bazaki kara kulashi ba, abunda yai miki tabbas zamu dau fansa 'inason kirike darajar ki 'na ya mace.
Kallon agogon hannunta t'ai ,tace Alisa zan tafi saboda surukata ba lafiya amma ai zamuyi waya.
Karanto mun lambar ki .
Bata number t'ai fatima t'ai save 'Alisa tace waini baki gayamin unguwar da kike aure ba.
Murmushi fatima t'ai 'tace ai dan sani yaro nake aure.
Wanne daga ciki .
Kinsan akwai Khalid izza
Yusuf mai gaskiya
Deen dan kanin sa ne akace amma yazama danshi tunda hannun sa yake.
Dariya fatima t'ai saida fararen hakoran ta 'suka bayyana tace.
Inaga izzah shine mijina .
Wow amma fa wlh kinyi saa wannan hadadden gayen ,mai kama da larabawa ,gashi ya hadu da Macé daidai class din sa irinki.
Uhmmm Fatima tace .
Nidai zantafi saimunyi waya sallama sukai Alisa taimata godiya sossai Akan shawarwarin data bata.
Shamsu n'a hango bakin Gate din makarantar nusy Wanda a kullum saiya zo yatsaya yai ta kallon yarinyar yana kuka 'ahaka yakoma gidan nasu.
Maryam' da Inna l'ami ne zaune suna dama fura da nono 'itakuma ummu 'tun dazu take fama da wutar gawayi yaki kamawa hayaki duk yacika wajen 'sai rurrufe idanun su sukeyi.
Maryam tace me zehana aba baba ado yasiyo mana kalanzir tahada mana wutar nan nidai wlh yunwa nakeji.
Inna l'ami tace naga ai wannan furan zedan rage mana yunwa shiyasa muke damawa .
To ai Maza a dama cewar ummu .
Shamsu ne yakaraso wajen yazauna dirshan 'cikin gajiya yace wlh yau ma dai wlh banyi nasarar sato yarinyar nan ba 'saboda marikiyarta inta kawota bata wuce wa 'sai taga shigarta Haka kuma intazo daukanta 'wallahi tana wajen Zaman jira fitowar ta .
Ummu tace shikenan anrabani da ya ta shamsu'cikin kuka take magana yau shekaru nawa Kenan da rabon in sa yata a idanu n'a.
Kiyi hakuri ummu duk tsanani yana tare da Sauki karki manta fa 'nima fa ubanta ne.
Amma nasan tana samun kulawa sossai agidan 'musamman inkikai duba da umma.
Mikewa tsaye ummu t'ai fuskarta alamun babu Wasa aciki take magana kamar Haka.
Sai yaushe zamu daina boye kanshi shekaru n'a shudewa kawai mu fito ,mu nuna wa duniya muna raye 'ace yata banda ikon ganinta iyayena ,ma Haka.
Dafata shamsu yai 'yace kiyi hakuri fitowar adaidai lokacin ne barazane ga rayuwar mu 'harda n'a iyayen mu 'na tabbatar bazaki so akanki akashe iyayenki ba' yana dubanta .
Girgiza kanta tai'
Yace pls dan Allah kidan kara hakuri komai yakusa zuwa karshe.
Inna l'ami 'tace nagama dama furar kuzo kusha amma dai yau da daddare nakeson kuban tarihin rayuwar ku 'tana bata rai .
Maryam ' da ummu suka kwabe baki 'ahhh sannu Inna l'ami ai mun gayamiki sai nusaiba tazo garemu zamu baki labari.
Shamsu yai dariya yace Inna karki damu anjima dakaina zan baki labarin 'asalin mu 'suwaye insha Allah Yauwwa yanzu naji magana amma wayannan masu bakin jemagu kullum sai Jamin rai suke.
Ummu da Maryam suka tafa hannu wai mune masu bakin jemagu mungode Inna kedai 'kira mana mijin ki 'yataimaka yasiyo mana kalanzir kinsan dai ba fita muke ba.
Kwafa t'ai tace kwaji dashi acici mala'ikun tauna.
.......
Direct fatima gida ta 'nufa a farfajiyar gidan ta hango Aisha da isma'il 'suna hango ta suka nufo ta.
Ismail yace inawuni anti ta amsa masa fuska asake lfylau alhamdulillah
Aisha tace harkin dawo eh nadan hadu da wata kawata ne acen shine muka dan tsaya firan yaushe gamo 'batareda ta tsaya ba tawuce ciki tabarsu..
Isma'il yace Aisha banta samun Macé da kesona irinki duba da irin yanayin gidan Ku matsayin ubanki akasar nan.
Amma kike min biyayya 'sanadin yi biyayya kikai accident hankalin Yan gidan mu 'duka yatashi bazan gaji da baki hakuri ba' sorry am sorry sauraniyan mata 'mahaifina sunce ana nema musu izini zasu zo 'neman auren ki.
Ranan jumaa nan take annurin dake kan fuskar Aisha yadauke , hawaye take shar idanunta.
Mamaki ne yakama Ismail yace maganganuna Sun bata miki rai ne 'ta girgiza kai alamun 'aa
Dakyar ta iya furtawa Allah yakaimu zan sanar 'nizan shige kaine ke ciwo.
Subuhanallah shine baki gayamin ba masoyiya muje inkaiki pharmacy .
Aa kabar shi inada magunguna aciki zansha daga Haka ta fice tabar shi nan 'yana ganin tawuce cike da tausayin ta da sonta dake karara ruruwa acikin zuciyar shi yaja motar sa yabar gidan.
Kowa n'a falo zaune 'har umma da sumayya ta taimaka 'mata takawo ta falon .
Inna Farida tace ke indo lafiyar ki 'kike kuka Haka 'kowa gidan yakai Duban sa akanta.
Bakomai tabasu amsa tareda wucewa side dinta.
Inna Farida tace nidai Allah yanunamin auren nan naku 'aisha keda sumayya .
Sumayya tace au hardani nidai bankai aure ba tana turo baki gaba.
Fatima ta amshi zancen da cewa au baki Kai aure ba ko?
Kai ta gyada mata 'tace Toni zankira yusuf in sanar masa indai yasamu wata a maiduguri yai auren sa.
Gab gab gab Haka sumayya taji zancen ya Doki zuciyar ta 'tace uhmmm anti Fatima karmuyi Haka dake kinfa san halin sa .miskilin mutum ne saiya dauka serieuse kike .
Au daman nacemiki da Wasa zan mai magana kedai kice inkira shi kisha mamaki.
Afuwan anti babba tashi t'ai tareda rufe idanun ta 'tai hanyar dakin su .
Fatima dawo ga dubanta Akan Inna l'ami d umma dasuke hira t'ai.
Gabadaya jikinta yagama yin sanyi 'tausayin Inna l'ami ne kawai yacika mata zuciyarta dayan bangaren kuma tausayin Alisa takeji ' murmushi t'ai da ita kadai tasan ma'anar shi tace azuciyar ta 'inshaAllah ni fatima saina koya maka hankali nura.
zazzare idanu yai yace nikuma , wani abun tace namata cikin ta ne ke ciwo tun safe .
Umma tace amma dai baka kyautaba hannun takai jikin fatima , sannu yata tareda kwantar da ita a cinyar ta .
Deen da aisha tare suka dawo ,daga makaranta su ahanzarce yakaraso ganin fatima na kuka ya gigice yafita hayyacin yakasa gane shin meyasa in yana tare da ita yakejin nishadi ,in yaga bata walwala tashi ma daukewa yakeyi .
Aisha tace umma meya sameta tana kai hannun jikiin fatima dake sheshekar kuka .
umma tace indo cikin ta ke ciwo ,maza dauko mun waya inkira docto hamza da to ta amsa mata tashi dan dauko wayar.
Deen gabadaya ya nemi nutsuwar sa ya rasa dan kukan fatima ya fassara shi da kukan bakin ciki yana gane duk wani yanayi na fatima a dan zaman dayai da ita ,ko kallon khalid beyi ba bare yasa ran ze masa magana,
Direct dakin sa ya nufa kifewa yai a gadon ,
Yana kuka ,ahankali ,karar bude kofar yasa shi ,saurin juyawa ,
Khalid yagani abakin kofar sa tsaye yana kallo sa da mamaki kwance akan fuskar sa.
Karasowa daga ciki , hannayensa goye abaya yana magana ,cikin kakkusar murya ,deen nakasa gane wace alaka ce tsakanin ka da fatima.
Deen murmushi yai tareda sauko wa daga kan gadon dafa khalid yai, fatima ai matar yaya na ce ,wannan shikadai ne alakar mu.
Ajiyar zuciya khalid yasauke yana fuskatar deen , nace maka inason karinga kwana dakin fatima.
Amma kaki bin umarni na , tun lokacin nazuba maka idanu ,amma yau shine last dinka inhar baka kwana dakin ba ,wallahi wallahi babu ni babu kai kuma karka tambayeni dalilin turaka ,sannan na yarje maka kai komai na mu'amala da ita ,amma iya dare ,batareda kabari tasani ba, barin dakin yai , yafita ,yana tafiya kaman ze tashi sama.
Innalillahi wa,inna ilai rajun DEEEN YASHIGA MAIMAITA WA.
dafa kansa dake juya masa yai nan take jiri yafara dibar sa.
Acen bangaren umma ,docto hamza yaduba fatima , magunguna ,yarubuta mata tareda rokon abarta tahuta.
Manager auwal ya iso cikin shiga ta alfarma ,rikewa hajiya hussaina jakarta yai khalid yai musu jagora babban falon su.
Umma sai kallon hajiya hussaina takeyi zuciyarta na tsanan ta bugawa, still momyn fatima ita take kallo ,aisha ce dauke da tray hannun ta itada balaraba nusy nabiye dasu abaya.
Nusy cikin muryansu na yara tace umma kinga