Free chapter · Read without an account

Kai ka jawa kanka Chapter 8

by Ikilima Adam · KAI KA JAWA KANKA

Kai ka jawa kanka 8

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah


Page 8


To pls akwai bithday din nusaiba Khalid ranar 'asabar dan Allah kazo .


'murmushi yai yace yanzu kina nufin bithday nusy ne zesa in bar maiduguri inzo katsina ' to zan duba mugani.


Daga Haka sukaci gaba da hiran su ' kuku ya ajiye abinci 'be lura ba 'dan lubayya ta rufe 'masa idanu....





Shamsu ne sunata tsara yanda ummu zataje bithday din nusy ka sancewa yau saura kwana uku taron.


Gabadaya fadin Nigeria maganr bithday din yar gatan baban ta ' da kakan ta 'ya karade nijeria.


Taron bithday din harda gwamnoni zasu halatta.


Nace tofa Abu n'a manya ne .


Gwamnar katsina *aminu bello masar* tareda *abdullahi ganduje kano* sai kiriku watau *el rufa'i* kaduna state 'suna daga cikin jiga jigan 'manyan mutane dazasu halarta 'kansewa abba ' amininsu ne 'harkan shiyasa ce kadai beyi .


Sossai aketa shirye shirye an canja wa gidan tsari 'kyale kyale babu Wanda ba ayi ba .


Sossai gidan ze baka shaawa inkaje tun da farfajiyar gidan ansara ko ina .


Nusy tasha gyara sossai 'dan abba yai mata siyayya Kaya tundaga turkey akai mata siyyay komai n'a taron.


Shamsu yace 'zan rakaki 'ummu ' saboda idan 'nahango zaa samu matsala zan san yanda zanyi 'yanzu de zan yi kokarin insamo mana invitation card din.


Maryam t'ai jugum.tace oho nice zaku Bari 'sai Inna l'ami agida.


Kiyi hakuri aida babbar waya zamu.'zamu.dauko miki 'duk wani'abu awayar.


Cikin gamsuwa da zancen nasu tace Allah yakaimu......




Fatima ce tasauko ahanzarce tana neman nusy 'dan ayi mata.kunshi da kitso.


Kansancewa ta duba dakin ta 'bata ganta ba.


Shiyasa t'ai tunanin kotana wajen maigadin gidan su .


Mallam isa ne.


Ahanakali take.tafiya 'tunda.ita ma'abociya nutsuwa ce.


Harta wuce abba data hango yana waya 'taje gun mallam isa 'ta tambayeshi nusy yace aikuwa yanzu tashige gidan tace zata gun umma.


Ok to bara inje insameta c'en ',godiya t'ai masa.


Tajuya da nufin Shiga falon su 'takara Kai dubanta 'ga abba dake waya .


Ji..t'ai.yana fadin *murhu* ance kacalle yana hotal din *Marhaba* yana daki mai lamba 12


Ka tabbatar kacalle yabar duniya ayau din nan .




Caraf maganganun suka sauka kan kunne fatima


Jikin ta 'yadau rawa cikin tsantsar tsoro daya shigeta lokaci daya


har cikin ta ' n'a murdawa ga wani zazzafi da taji yana neman rufe ta.


Abba dayagama wayar waigowar dazeyi 'saiyaga 'fatima tana kokarin faduwa 'ma'ana jiri n'a Diban ta.


Kallon ta , yake tareda son fahimtar ko taji wayar dayake yi ne.


Wata zuciyar tace aa 'itada yanzu tafito daga cikin gidan 'kila dai jikin ta ne begama warware wa ba ' da wannan tunanin ya tunkarota .


Cikin son tabbatar da abunda kedamunta 'yace diyata 'bakijin dadi ne.


Fatima da kanta ke 'aduke tace 'abba tun safe cikina ke ciwo 'nusy nafito nema.


Ajiyar zuciya yasauke dan ya tabbatar batajin wayar dayakeyi ba.


Sannu diyata ,zomu shiga in kaiki asibiti 'yana magana cikeda kulawa..



Abba kabar shi 'daman dan bansha maganina 'bane kasan bithday nusy yadauke hankali da tunani na 'tana magana cikin muryan dake 'nuna lallai cikin ne 'ke mata ciwo.


Sannu kinji abba yace mata 'lallaba kishiga gida 'nizanje kamfani sai nadawo .


Daga Kai 'tai tana kallon sa har yafice daga gidan.


Cikin sarewa da al'amarin gidan 'tace kaji munafiki 'kamar n'a Allah harda wani yakaini asibiti dan yasamu yakasheni acen ya jefani jejin sambisa.



Direct dakin ta 'tana nufa Kayan jikinta ta cire ' ta dauko Kaya marasa nauyi cotton tasa ajikin ta doguwar Riga.


Sai Safa da marwa taketayi adakin 'tareda ciza labbanta '.


Cikin kuka dayazo mata 'tace mommy nasan hakkin ki 'dana dauka baze barni inzauna lfy 'gidan mijina ba.


Daga hannayenta sama t'ai cikin kuka' tace ya Allah ina neman afuwan ka kayafemun laifukan danai wa mahaifiya ta .


Tun baaje ko'ina ba 'naga ishara ni fatima.


Daukar wayarta 'tai ta dannawa 'mommy Kira 'ko gaisawa basuyi ba' cikin kuka' tace mommy hakika ke uwa tagari ce kinsoni alokacin da bansan me so ba.


Dan Allah kiyafemun laifukan 'dana aikata miki 'na ganganci 'dana rashin 'sani keda daddy musaamman ma ke.



Jikin mommy yai mugun sanyi tace fatima kullum cewa nake nayafe Miki 'pls kidaina sa ,damuwa aranki ' nasan kila haihuwa ce kike tsoro ko?


Karki damu inshAllah Zaki haihu lfy 'Allah yaraba lfy .


Mun dade da yafemiki teema Dina.


Murmushi t'ai tace tace mommy nagode 'kawaide nakira ki ne .

Dan innemi yafiyar ki



Mommy taji dadin kalaman yarta daga hk sukai sallama.



Rike da bakin tace oh ni fatima ni banzo duniya a saa ba , amma a gidan miji n'a.


Wai wace irin gidane nake rayuwa 'acikin 'tana kallon dakin ta' gida mai cike da kazanta.


Ganin 'batada mafita 'yasa ta dannawa safiyya kira'


Safiyya tace kawa yau antuna ni Kenan tana gaban laptop dinta 'tana wasu aika aikace eapace a kunne ta take wayar.


Fatima da duk batada wani kuzari tace ai gashi nakira wai dan Allah yaushe salamatu zata dawo ne?


Safiyya 'tace ai ance intazo zaa gayamin .


Lfy kike nemanta 'awannan lokacin 'cikin zurfi cikin irin Nata 'tace no daman n'a kagu 'mu hadu da ita' ki turomun adiresh diin gidan su


Tom safiyya tace 'yanzu zantura miki ya mijin naki 'dafatan yana lfy .


Lfykalau alhmdulillah'. Yama fita aiki.


Daman fatima ashe ke munafuka ce .


Cikin bata fuska tace 'munafuncin menai miki 'ehee .


Safiyya dariya t'ai dan tasan ta tabo abunda Fatima batason ace mata.


Haka nace fatima 'ashe ciki gareki shine kikaki 'sanar min dan kada in amshi tukwuci hannun Khalid.


Jimm t'ai tareda gyara zamanta 'tace shikenan in ta shela inada ciki babu ko kunya ko?


Yi hakuri naga kina wani turo baki 'duk da ban gaban ki 'amma nasan abunda kike yi 'kenan.


Naji dai inajiran sunan unguwar daga Haka ta katse Kiran.


Wadrob din ta 'tabude tadauko mayafi maron color .


Cikin hanzari ta zira takailmun ta.


Cikin sanda 'sanda tasauko kasa ' daidai inda motar ta 'take ta nufa cikin hanzari da bataso aga fitar ta.


Deen n'a lure da ita yana zaune yana karanta jarida.


Gwanata ina zakije ne ' atsorace ta juya taga deen ne ajiyar zuciya tasauke .


Deen zan je wani wurine 'kuma sauri nake.


Gara inkaiki inbabu matsala.


Muje tabashi amsa tareda zama kujera mai zamn banza 'cikin hanzari yaja motar suka hau titi daidai da suna kokarin fita layin gidan nasu' yai daidai da khalid zeshiga layin caraf idanun sa 'akansu kallon yake babu ko kiftawa .


Deen yaci gaba da tukin sa 'dukan su 'babu Wanda yaga Khalid.


Karar shigowar texte awayar ta 'ya tabbatar mata safiiya ce .


Ahanzarce tabude sakon inda taga tarubuta.


Kije *jabiri layin Yan bokolo* ki tambayin gidan ssst Muktar nan ne gidan su.


Deen takalla dake tuki hankali kwance 'tace kaga sunan unguwar ta fadamai 'juya akalar motar yai.tareda bin hanzar daze sada su da unguwar.



Khalid nabiye dasu abaya .


Tafiya suke mai dan nisa ka sancewa akwai dan nisa unguwar da zasu je.


Deen ta madubin mota yahango 'motar Khalid dake biye dasu abaya.


Gyara murya yai 'yace gwanata kinga 'mijin ki 'yana bin mu 'abaya .


Leka madubin motar t'ai taga eh lallai shine'murmushi t'ai tace yaro besan wuta ba saiya takashi azuciyar ta 'take magana.


Kallon deen t'ai 'tace tunda yana biye damu 'kaini restaurant pls.


Kallon ta yake da mamaki 'restaurant kuma gwanata .


Eh Haka nace tunda yayanka yana bin mu ,abaya.



..............


Shamsu ne 'yatura wani yaro yace yaje gun mallam isa mai gadi yace , abokan khalid sunce abasu invitation card shikuma tunda yaji ance Khalid ,bé musa ba 'yabada guda uku tunda khalid Nata turo mutane suna karba wajen sa.


Shamsu cikin shigar buzaye hade da rawani 'dan bazaka taba iya gane shi ba.

Yaron yakawo masu invitation card din .


Amsa yai tareda yi masa kyauta yaron yatafi yana farin ciki.



Direct gida yakoma cike da farin cikin 'samun invitation card din.


....


Khalid n'a biye dasu fatima ,yana mejin kuna acikin zuciyar sa.



Daidai wani katafaren restaurant deen yai parking.


Shiya zaga yabudewa fatima mota ta fito tareda amsar jakar ta 'yarike mata.


Tana gaba 'tafiya takeyi kamar hawainiya 'duk taku daya datake 'kowa da suke cikin restaurant suna cin abinci 'sai da suka jiyo da kallon wace wannan da idon kowa Akan ta.


Cike da nutsuwar ta isa réception tabasu uwarni akai musu fruit salad .


Deen ma yasha kallo 'wata tsabar kallo saide ta tsiyaya lemun da takesha a jikin ta.


Fatima n'a lure da 'ita sannan ta hango parking din motar Khalid hakan besa hankalin ta yatashi ba.



Harara ta watsawa wacce take kallon deen din.


Tareda zama kan kujera ita da Deen 'suna fuskantar juna.


Khalid dake kallon abunda sukeyi '


Yace deen wallahi saina koya maka hankali yana ta huci sama-sama


Barin wajen yai tareda juya akalar motar sa 'zuwa gida.sai saké sake irin hukuncin dazema deen yakeyi

********


Yusuf zaune office dinsa 'yana duba file din case din kisan 'ummu da akai da Maryam wayanda baa tsinci gawar su ba.


Tirkashi ni yusuf taya nabar case dinnan ya dade Haka.


Abdullahi ! Abdullahi !


Aguje yashigo yace ranka yadade gani tareda risina wa kansa a duke.


Yusuf yace ya shirya, zasuje katsina.

Ayau dinnan.


Ok babu matsala da wani Time zamu wuce ya tambaya?



Karfe uku 'kazauna ready 'zanje gida ina dawowa zamu wuce .


Daukar takardun yai 'yakira Ahmed yace Kai wannan case din danabar maka 'har yanzu ka ,kasa kawo karshen sa.


Yau shugaban mu yakirani 'yakemin korafin case din 'taya zaa bar maganar ayi shiru'haryana fadin innakasa ne ,shi ze dau case din hannunsa 'wata daya yaban kacal 'kaga zama bé ganni ba .



Ahmed yace yww ranka yadade wlh inkazo 'sai anfi cimma abunda akeso Kai tsaye.


Ok inanan tafe ayau dinnan kaje gidana agyarmin nida abdullahi zamu zo tare.


Ok ranka yadade angama da Haka sukai sallama.



Karar wayarsa yaji 'cikin gajiya da waya 'yadauko wayar 'fuskar wayar rukayya yagani tsaki yaja .


Cikin kosawa yadaga yace inawuni ta amsa da lfykalau alhmdulillah.


Dan Allah yallabai yaushe zakazo katsina ?


Bata rai yai kaman tana gabanshi ' yace wani abunne yafaru kike nemana.


Eh wlh abba n'a yakeson ganin ka.


Cikin zare idanu yace bangane yake nema ba to Akan me Kenan.


Shiru t'ai 'cikin inda _inda tace kila saboda yaga yanda nakeson ka ne 'kuma Nina fadamai muna soyayya nidakai.



Ke tsaya ingayamiki 'inada wacce zan aura ' ankusa 'sa mana rana .


Ina me baki shawara dan Allah ki hakura dani


Bejira cewanta ba 'ya katse Kiran .


Yanata jero tsaki akai akai zancen banza yarinyar nan 'inta matsa mun zan sa nombar ta a black list .


Ita sumayya ai dan umma tasa baki 'da wlh banda shaawar auren gida.


Kuma koda zanyi auren sai nagama cika burina

Amma zaa sako wata 'cikin rayuwa ta.


Ko me zanyi da mace oho dai.


Haka yaketa 'surutai shikadai cikin bacin rai.


Abdullahi yashigo yasame shi 'sai fada yaketayi 'cikin sanyi murya mai cike da ladabi.


Yace yallabai wajen mutane goma ne zazzaune 'sukeson ganin ka.


Zama yai kan jurer office din sa '


Yace ai yau nakarbi mutane sunfi goma 'kuma atsarin aikina mutum goma nake amsa arana.


Amma tunda tafiya zanyi .

Kana iya turo Wanda ke kan layi.


Ok to yallabai abdullahi yabashi amsa tareda fita.




Bangaren rukayya yusuf n'a katse Kiran 'kuka tasoma mai tsuma rai.


Mahaifiyar ta tashigo dakin rike da baki 'tace wai yaronnan kodai asiri yai maki ne?


Dago jajayen idanun ta 'tana kallon uwarta 'tace mama da asiri yamin da zesoni 'zama t'ai 'tana fuskantar yarta 'cikin muryan lallashi 'tace kiyi hakuri inhar yusuf mijin ki ne!


To ze nemeki dakansa.


Yanzu kimun alkawari Zaki daina kiransa awaya 'azumin litini da alhamis karmuyi Wasa 'dashi .


Sannan kiyi istakhara akai 'inhar babu alkhairi Allah yacire miki son sa acikin zuciyar ki.


Indai kikai Haka kikaga befita aranki .


To kringa tashi karfe ukun dare kina Kai kukan ki 'ga ubangiji Akan ya juyo miki da hankalin sa.


Wallahi ina me tabbatar miki indai kinyi da zuciya daya sai yaji sonki yashiga zuciyar sa.


Kidage kullum kinayi kinji nikuma zan tayaki.


Rungumi mama t'ai tana

kukan dadi mama nagode inshAllah zanyi yanda kikace.



****** .





Sai karfe takwas n'a dare


Yusuf da abdullahi suka shigo katsina.


Direct gidan su 'yanufa yaje yaga umma kafun yatafi gidan sa.


Horn yaketa yi .


Mallam isa yabude yaga motar yusuf ce aguje yabude masa yana ta masa barka dazuwa mai gaskiya adalin mutum



Yusuf n'a fitowa gun mallam isa yanufa sukai musabaha cikin sakin fuska yusuf yace baba Kana nan dai abunka


Eh wallahi oga yusuf inanan cikin kewar ka 'kaine me tayani fira 'sai deen .


Yanzu deen bema da lokaci ayyuka yai masa yawa.


Abdullahi yace inawuni baba ya amsa da lfykalau wannan kuma fa yusuf .


Yusuf yace baba daga maiduguri yake bara mushiga in gaisa da umma inazuwa .


Direct gidan suka nufa shida abdullahi.



Mamaki ne yacikashi ganin yanda Aka kawata gidan da kyakyale ta ko 'ina wasu fitilu akasa 'kowacce fitila yana rubuta happy bithday nusy',sossai abun ya burge su .


Kai tsaye falon yanufa inda nan ma still kallon yakoma sama yanda Aka kawata duk wani lungu da sakon gidan' kasancewa gobe ne bithday din .



Falon babu kowa sai karar tv dake tashi .


Nunawa abdullahi waje yai yazauna .

Shikuma yana kokarin wuce wa sashin umma.


Caraf suka hadu da khalid daya fito dakin abba.


Murmushi yusuf ya sakarwa Khalid .

Inawuni yaya khalid yace mishi yana me kallon sa.


Khalid dake masa.kallo'n tara saura kwata yace


Lfykalau ciki ,ciki yabashi amsa..


juyawa yayi zewuce sashin umma.


Khalid yace dakata nan cikin tsawa .


Yusuf kaman jira yake ya waigo cikin dan hade fuska yace lfy kake min tsawa naga yanzu muka gaisa dakai.


Dole inmaka tsawa ahaka zaka gaisheni dan takama da rashin kunya .


Sannan abba yana daki kawuce sashin sa .

Zaka wuce wajen uwar taka.


Dariya yusuf yaringa yi 'saide hantar cikin Khalid ya motsa .


Wallahi dakansan dalilin zuwa n'a 'katsina ayau da wallahi da ladabce zaka min magana.


Ok wannan bedameni ba nasan in kere n'a yawo zabo n'a yawo wataran zasu hadu ne.


Wuce shi yai direct dakin umma yanufa.


Yabar Khalid tsaye yanata juya kalaman yusuf meyake nufi?


Kenan ba bithday yakawo shi ba tirkashi ya furta tareda komawa dakin abba.



Deeen dayanzu yashigo ya iske abdullahi zaune banda kallon sa 'babu abunda yakeyi 'tsantsar kamannin dayaga abdullahi keyi da fatima ne yabashi mamaki.


Cikin son tabbatar da abunda yake gani 'ya iso falon 'sannunka yace mishi


Ya amsa da yawwa barka da shigowa.


Nasan anti Fatima kake jira ko ta shanyaka anan.


Caraf maganganun Akan kunne fatima dake saukowa daga matakalan step.


Zuciyar ta 'ya tsananta bugawa dakyar ta karaso fallon rike da kirjin ta.


Idanunta suna sauka Akan abdullahi ' shima abdullahi still itama yake kallo Zuciyar sa n'a buga wa .


Cikin tsananin kidemewa ze bude baki yai ......


Innalilahi wa'inna ilairrajun


Mama kina ganin 'abunda Salma taimin' kin kasa magana 'jijjiga mama takeyi tana kuka mai tsuma rai.



Mama ta dago jajayen idanun ta 'dasuka ciko da kwallah ' cikin bakin ciki da bacin rai ' tace Rahma 'kiyi hakuri kanwar ki ce.



Sharr 'sharr 'idanunta suke zubar da kwalla 'da radadi hade zallah bakin ciki 'take kallon sama 'ta daga hannayen ta sama' t'ai cikin sheshekar kuka tace *kanwa ta* kin cuceni .



Cikin tsananin kidemewa ze bude baki yai magana .


Yaji harshen sa yakasa furta komai sai zallan mamaki daya cikashi.


Bawan Allah daga ina ? Kuma wakake nema wajen wa kazo 'duk ta jero masa tambayoyi lokaci daya.



Abdullahi kallon ta 'yake ya lula duniyar tunanin bemasan tana magana ba.


Deeen yace au kina nufin ba wajen ki' yazo ba .


Wannan tsantsar kamanni dakukeyi gwanata yai yawa '


Uhmm tace tana kallon deen tace nima bansan daga inda yafito ba 'inaga dai wani yake nema.


Sai yanzu hakanlin sa yadawo jikinsa ' kallon su yake yace kuyi hakuri nida oga yusuf ne 'muka shigo 'shiya shiga daga ciki yabasu amsa kansa akasa dan be jure kallon fatima.


La la la ashe yaya yusuf yazo Chab nasan yana sashin umma bara inje c'en ahanzarce yai bangaren umma yanata buga uban sauri.


Yaya ! Yaya. ! Yaya!


Yusuf dake manne kusa umma kamar dan yaye 'yace oh umma kanina n'a kwadamin Kira.


Dariya umma tasoma' aikunfi kusa.


Sallama dauke abakin sa.yashigo.

Amsa masa sallama sukai .


Yaya yusuf barka dazuwa wannan zuwan bazata ahaka'.


Fadada fara'arsa yai yace aikuwa gashi nazo dan Inga kannena 'dafatan nasameka lfy ya matar khalid da jikin.


Alhmdulillah yabashi amsa yana me neman wajen zama.


Umma tace 'dan Allah kuban hankulan Ku.


Dukan su 'nutsuwa sukai suna fuskantar ta.



Cikin muryanta dake nuni da muhimmanci abunda take son fadamusu ' tace yusuf ,deen 'duk suka dago Kai suna kallon ta'cikin kosawa dajin maganar dazatai musu.



Zanfara dakai yusuf 'kaga yanzu gobe 'jibi zaa kawo kudin sa ranar indo sonake ahada da naka kamalar mutum 'becika saiyanada aure 'inason kan kabar garin nan kahada komai n'a aure da akeyi n'a al'ada ka bayar 'lefe kuma , katuron kudi in hada maka ' nan take idanun sa ' ya canja launi zuwa ja!


Umma kinsan bazan bijire 'zancen naki ba' amma inada sharadi pls dan Allah in anyi auren tazauna wajen ki 'harsai n'a shiryawa tarewa 'karki hanani dan Allah kuma karki tambayeni dalili.


Jimm 'umma da Deen sukai ' deen yace yaya yusuf inkai Haka uwarta bazataji dadi ba ' kuma baka rasa muhalli ba' .


Umma kallon yusuf take 'tana nazartan sa' cikin hade fuska tadawo a hassana din ta 'cikin bacin rai dake nunin ta isa dashi 'tace wlh yusuf inhar akai auren nan banyarda sumayya 'takwana gidan nan 'ba inba a dakin ka ba'. Sannan wlh ina me tabbatar maka inason sumayya tazama cikakkiyar Macé aranar data tare gidan ka.


Daga Yusuf har deen dago Kai sukai suna kallon umma ' nan take deen yaji kaman kasa ya tsage yashige dan kunya.


Yusuf azuciyar ya furta ya ilaihi shikenan matar nan ta daureni ' wai to yazanyi in kusanci 'wacce nakewa kallon kanwata ya sallam .


Afili yafurta 'umma naji Allah yakyauta.


Kallon sa take again .


Bangane kalmar Allah yakyauta ba yusuf tana hade rai.


Yusuf yai kasa da murya yace ina nufin yanda kikace Haka za'ai.


Ummmm dadai yafi maka 'kasan zuciyar ta' sai fadi take 'inba Haka n'ai masa ba 'wannan miskilin yaron rainamun hankali zeyi 'ace ashekaruna ban tara jikoki ' ba jikata daya nusy habdai afili kuma kallon deen take tace nadawo kanka.


Shiru dakin yadauka banda karar fanka babu abunda kakeji .


Deen inason kafitar da matar aure 'ina wannan yarinyar nan Karima wacce kafun tafiyar sudan kuke tare.


Nan take hantar cikin deen ya kada 'yanajin ina baze iya gabatar da matar aure ayanzu ba 'sainan gaba.


Kallon umma yake yaga ta tsareshi da idanu ..

Uhmm umma ta .


Ai ingayamiki Karima bata gari sainan da shekara daya zata dawo.


Yanayin yanda yake baynin sarai umma ta gano karya ce yake shimfida mata 'ita taraini deen tun yana da wata shidda da haihuwa' yanada shekara shidda a duniya mahaifin sa 'yarasu 'kula babu Wanda bata bashi ba' dan inba tafadi bane 'babu Wanda yasan ba itace bace uwar sa.


Wannan Kenan 'duk a yayan ta 'tafison deen 'darajar sa daban yake awajen ta 'duk da ya kasance mahaifin sa kanin abba ne uwa daya uba daya.


Saitake ganin wautar sa' dan beda wayon daze nuna mata 'saina zamani.


Uhmm tace naji deen, to Allah yadwo da ita lafiya yanzu ai sai kasake sabon lalabe ko?


Sunkuyar da kansa yai kasa azuciyar sa 'sai fadi yake umma dakinsan abunda zuciya ta 'takeso da muradi da bakimun tunanin wasu matan ba.


Afili ya furta inshAllah akwai wacce nasamu amma bamu gama daidaitawa ba.


Allah yadaidaita Ku 'tabashi amsa .

Yusuf da Deen suka amsa da ameen.


Yusuf ya Mike cikin kasala da gajiyar dake jikin sa 'yace umma zantafi gida ,gobe inada ayyuka ga tarin gajiya.


Murmushi t'ai masa 'cikin kaunarsa tace Allah yakaika gida lfy yatsare gabanka da bayanka Dana.


Da ameen suka amsa Dukan su.


Kusan atare suka fito shida yusuf din.


Umma nabiye da su a baya dan tayiwa yusuf rakiya.


Sumayya da indo sunfito daga dakin su.


Suma falon suka nufa.


Umma cike da mamaki take kallon abdullahi da fatima ta tsareshi da surutu.


Fatima sannu da fitowa taiwa umma taje gabanta tace dan Allah umma duba kigani bamu kama nida shi.


Eh bashakka kuna kama sossai yata .


Ina kika samo shi,. yusuf sai alokacin ne shima yakalli abdullahi da fatima ya tabbatar da abunda take fadi din.


Kallon fatima yai 'nawasu dakiku .


Yace matar yaya .


Naam ta amsa masa cike da kulawa.


Inason kiban lambar mahaifin ki hakan zeyu kuwa?


Ina fatan dai lafiya fatima ta tsareshi da idanu.


Eh lfylau karantomun lambar.


Cikin yarda dakai takaranto masa.


Save din nombar yai .


Sallamar aisha da sumayya yasa ya waigo caraf idanunsa suka sauka Akan n'a sumayya 'nan take babu abunda yafara tunawa 'sai kalamin 'umma tanason sumayya tazama cikakkiyar Macé a ranar da Aka kaita..

Kwabe baki yai yana kallon ta daga sama har kasa.


Sumayya ta lura da kallon 'da yusuf ke mata yai yawa 'yasa har ta tsargu da kanta dayawa.


Komawa da baya tai''tareda zama kan kujera .

Cikin zazzakar muryan tace inawuni yaya yusuf.


Kallon yakeyi babu ko kiftawa 'kowa afalon ya Lura da hakan .


Umma murmushi t'ai 'tabar falon .


Lfykalau alhmdulillah yabata amsa


Deen yace to.tunda abun n'a masoya ne dan Allah kubar falon nan 'kuje dakin umma 'kokuma kuje falo nabiyu ehee.


Gaba yayi yai hanyar daze sadashi da dayan falon .


Aisha tace yaya aibamu gaisa ba 'murmushi yai yace daman jira kike ingaishe indo n'a.


No bahakabane naga zuwan mu falon babu abunda kake kallo sai sumayya shiyasa n'ai shiru.


Kunya ta kamashi Sakai yai yanufi dayan falon.


Aisha idanu taiwa sumayya alamun tabi bayansa.


Tashi t'ai jiki a sanyaye tabishi 'inda ya zaune dan nesa dashi tazauna .


Shiru ne ya ratsa wurin 'cikin saurin dayakeyi yabata rai yace ke kinga matsalar ki 'saiki kasa magana .


Yi hakuri ya hanya tacemshi .


Lfykalau alhmdulillah .


Gobe ne bithday ko ya tambaye ta da kulawa.


Eh gobe inshAllah.


Gobe dasafe in Allah yakaimu Aisha taroki office Dina kuzo tare misalin.karfe goma nasafe '


Tareda mikewa tsaye zanwuce agajiye nake.


Allah yahuta gajiya tabashi amsa shikuma yasakai 'tareda Kiran abdullahi suka wuce .


Sumayya dawowa falon t'ai 'saiwani yauki takeyi .


Indo tace yayadai sumy.


Yau inacikin farin ciki 'tunda har zama yai dan yai fira dani wayyo Allah dadi .


Aisha dariya takeyi Kai amma sumy kinason yaya yusuf dayawa fa .


Pls inkinganshi kidinga ja mishi aji wlh namiji inyaga baka da aji rainaka yakeyi .


Sumayya tace Haka indo kinga cewa yai gobe muzo office dinsa nidake .


Kina ganin yadace muje kuwa?


Aisha tace aikuwa bazaki je ba 'yazo dakansa karfa kiyarda duk da yaya'na ne.


Kinuna masa kema cikakkiyar macece yawwa.


Deen da fatima sai dariya suke' Khalid n'a saman bene yana kallon su.


Deen kawai yake kallo yana shu'umin dariya



Fatima hango inuwar khalid t'ai asama batareda ta kalli saman ba.


Yasa tagane shine.


Fuskantar deen t'ai tace wayyo deen kafana keciwo dan Allah dauko man zafin c'en ka miko min inshafa .


Cikin hanzari yadauko mata yabata yana jero mata 'sannu.


Ina kemiki ciwo Yana tamabya cike da kulawa.


Nuna masa wajen tai' shiko ya amshi man yaringa shafa mata ' tana zabga shagwaba ashh ashh zafi wayyo deen zafi barshi Haka.


Khalid dake sama 'yacika yayi fam dan haushi da takaishi zuciyar sa 'yanata tafarfasa.



Sai kusan karfe goma kowa yakoma sashin sa .


Fatima bayan tai'wanka tasaka Kayan barci .

Dakin nusy tanufa tareda gyara mata kwanciya adu'oi tai mata tareda rufa mata blanket .


Kiss taimata agoshi tana mejin kaunar ta.


Kaman ance mata je dakin khalid.


Kai tsaye t'ai hanyar dakin sa.


Samun kofar t'ai abude sabanin kullum dayake a kulle .


Muryan sa 'taji yana waya kasa kunne t'ai taji meyake fadi.


Zazzare idanu waje t'ai.


Lokacin da taji khalid n'a fadin .


Inason gidan 'gonata gobe abude duk gas din gidan a tabbatar da iskan gas din ya mamaye duka gidan .


Sannan nikuma zanje da Deen wajen muna shiga ciki .


Zan baro sa gidan.


Yana kyafta ashana gidan gonan zata Kone gabadaya har shi deen dinn.



Fatima tasoma baya baya tana kokarin fita dakin cikin..



Tana ajiyar zuciya . cike da tashin hankali da baa samishi rana.


Khalid yana gama waya 'yafito Kai tsaye yana leka sako da lungu gidan ko babu wani alabe dan yaji ajikin sa 'kamar tsayuwar mutum 'ganin bakowane 'yasa yafara tunanin bara ya leka dakin fatima dan zuciyar sa 'bata yarda dari bisa dari ba babu Wanda yatsaya wajen.kofar sa ba.


Da wannan tunanin yai hanyar dakin fatima 'jin karar tafiya yasa fatima goge hawayen ta' tareda kwanciya cikin 'sauri Tarufa blanket .


Ahankali yaturo kofar dakin 'nata 'fitilar dakin Nata ya kunna haske ya baibaye ko'ina kallon yake tana barci' tsura mata idanu yai dawani lokaci dabefi minti daya'


Zuciyar 'sa tagama aminta eh lallai barci takeyi kuma ta dade da kwanciya.


Juyawa yai tareda ja 'mata kofa ahankali bezarce ko sai dakin abba.


Zaune yasameshi 'shida umma suna tattauna Akan bithday din da zaai gobe .


Abba yace Dana kaine awannan lokacin 'cikin yin kasa da murya 'yana watsawa umma kallon 'me takeyi adakin 'ta lura dashi amma hakan besa ta tashi ba' azuciyar ta 'sai fadi take .


Har wani Abu zan dauka adakin uban naka.


Abba lura da khalid akwai magana abakin sa' kallon umma yai cikin tausasa murya 'yace hassana jeki nanda minti goma ki dawo.


Ko gezau taki tashi 'yakara maimaita nace kidan bamu waje inason magana da Dana.


Still banza tasakeyi dashi.


Cikin tsare gida abba yace hassana ba magana nake miki ba.


Khalid yacika yai fam da haushin ta .


Sai asannan tadago Kai 'ta kalli Khalid cikin fushi 'tace dan ubanka ' mara mutunci 'naga ai ba *sani* kadai ne ya haifeka ba 'nice nan daka Raina hassana 'ninadau cikin wata tara nashayar dakai ' ta dalilin haihuwar ka 'naso rasa rayuwa ta.


Khalid kwabe baki yai' iyeeh tofah abba kanajin ta ' yana kallon ta.


Umma duk abunda kikamin kema fa 'anyi miki 'ahaka rayuwa take tafiya'' ni wlh kidaina fadin nakwanta cikin cikin ki har tsawon wata tara.


Bé Ankara ba 'saide yaji saukan mari 'rike da kuncin sa yace hassana ni kika Mara.


Eh n'a mareka khalid ko zaka rama ne dan banza Mara mutunci.


Dunkule hannayen sa 'kamar irin.zekai mata duka 'sai abba yarike mai hannu .



Khalid Kai hakuri kasan karfin mu 'da nasu ba daya bane.


Cikin bacin rai umma tace aikuwa daman taya karfin mu 'zezama daya Kana ganin agabanka 'yake fadan magana harda Kiran sunana Kai tsaye .


Ankira sunanki din to aiba karya yai ba 'koba sunan ki hassana ba.


Kinmance akauye n'a auro ki garin *(dikke)*


N'a taimaka.na auro ki 'dan incire cikin kangin wahala ai banyiwa yaya n'a adalci ba 'dana zaba musu uwa irin ki.


Kuka take mai tsuma zuciya tace inshAllah ni hassana nakusa barin gidan ka.


Zankoma rayuwar baya ze taimaka min Akan Zaman gidan yari


Hakadai sukaita fada itada abba Khalid n'a tsaye yana kallon su .

Akarshe kama hannun umma yai yafita da ita dakin tareda rufo kofan da karfin tsiya.


Umma tsuguna jikin kofar t'ai tana kuka ahaka ta rarrashi kanta dan batason 'yayanta 'susan abunda yafaru .



Khalid zama yai yace abba gobe ne fa 'nashirya barin deen duniya dan nagaji da abunda yakemin


Abba har cikin ransa yaji babu dadi zancen mutuwar deen amma yazeyi yafison khalid.


Jiki a sanyaye yace Khalid inaganin basai ankashe shi ba' karka manta dan kanina ne 'kuma baya rayé shikadai yabari.


Abba wlh kokaine ka haifeshi 'saina kashe shi


Tom.Allah yakaimu yafada da Haka sukai sallama.



Bangaren fatima

Khalid nafita daga dakin tashi zaune t'ai banda salati babu abunda takeyi 'kuka da tausayin deen ne yakamata.


Wayyo deen naja Maka innalilahi wa'inna ilai rajun .


Tashi tsaye t'ai tarike kugu idanunta Sun kada sunyi jajir kaman an watsa mata barkono.


Tunani tashiya yi menene mafita 'zura takalmin ta 'tai da niyan zuwa dakin deen dan ta gayamai.


Daidai lokacin data bude kofar 'tafara jiyo taku Wanda ya tabbatar mata Khalid ne .


A hankali ta ja kofar dakin Nata 'tahau gado 'tanata sake-sake Haka barci barawo yai awon gaba da ita batareda data shirya ba.



Kiran sallah asuba akunne ta 'koda ta tashi agurguje tashiga toilet t'ai wanka ta d'auro alwala.


Sallah tai tazauna yin azkhar tana 'neman mafita Akan wannan abun.


Tana tashi daga kan sallaya 'dakin deen ta nufa t'ai buga kofar taji hakan ya tabbatar mata.


Ba dawo daga masallaci ba .


Ya sallam tafurta' tareda komawa daki dan ta tashi nusy t'ai sallah.



Su deen ne 'da Abba ,da khalid alh nura nagaba yana sauri yashiga daga ciki.


Abba yana kallon deen cike da tausayawa 'yace Dana 'deen ya waiwayo fuskar dauke da murmushi yace naam


Kujerar falon suka zauna kusan atare Dukan su.


Abba yakara kallon deen babu ko kiftawa yace daman bawani abu bane nasiyo maka kayayyaki masu tsadan gaske Wanda zakasa wajen bithday .


Dadi kasheni deen yafurta yace nidai nafi kowa sa'ar uba .


Yaya khalid katayni godiya murmushin yake Khalid yai yace to ai abban ka ne kunfi kusa.


Deen tashi yai zeyi hanyar dakin sa.

Dakata yaji Khalid yafurta.


Juyowa yai tareda dawowa kusan Khalid kansa akasa saboda yasan magana ce mai muhimmanci.


Khalid yadafashi yana murmushi yace daman gidan gona ta 'zamuje dakai karfe takwas n'a safen nan 'akwai Kayan da zamu je 'mudauko


Kayan dring n'a rabo ba dukansu ' Aka kwaso ba .


Kuma kasan taro zefara ne daga karfe goma har zuwa la'asar.


Tom yaya Allah yakaimu yabashi amsa asanyaye hakan yaji jikin babu kwari ahaka ya haura kan matakalan step yawuce dakin sa.



Fatima komi takeyi adakin sam sam batada nutusuwa tuno da maganganun Khalid data ji .


Ahankali tagama ayyukan ta koda zata fito karfe takwas har da kwata .


Kai tsaye dakin deen ta nufa 'saide tabuga har tagaji jin shiru yasa tabude kofar tareda shiga dakin .


Kallon dakin take 'sai faman Kiran deen 'deen take shiru 'tace kila ko yashiga toilettes da wannan tunanin ta sauko kasa.


Direct dakin umma t'ai ganin fuskar umma duk ya kumbura alamun tayi kuka 'jiki asanyaye takaraso wajen ta .


Tace umma inakwana dafatan babu abunda kedamun ki ta tsareta da idanu.


Umma tace lfylau diyata jiya nakwana ciwon cikine amma dasauki 'maza kuje afara gyara wuraren da zaa gudanar da taron .


Fatima tace to umma 'amma deen yasauko kuwa?


Eh yanzun nan sukabar gidan nan shida Khalid amma bazasu dade ba.


Batajira cewar umma ba tafice ahanzarce Kai tsaye dakin aisha ta nufa ko sallama babu ta iske sai waya sukeyi kowanne da saurayin sa .


Kamo hannun Aisha dake waya t'ai tareda karban wayar hannun ta 'ta katse Kiran.


Mamaki ne yakamasu ganin abunda t'ai 'suna kallon junan su.


Cikin rawar murya tace Aisha dan Allah kinsan gidan gona n'a khalid dake sabon gari.


Eh nasani taba amsa tana nazartan fatima .


Yimin kwantance pls zanje dauko wani Abu mai muhimmanci ne .


Aisha dauko papper t'ai tarubuta mata unguwar tareda Mika mata .

Tana karba ta ajiye wa aisha wayarta Akan kafarta tafice cikin hanzari.



Sumayya tace wannan Anya lfylau kuwa bazamu bi. Bayanta bakuwa.


Indo tace kila mijin ta nacen ne shi zatabi.


Hakadai sunata saka da warware inda sukaci gaba da wayoyin dasuke.



Dakin ta 'tanufa Kai tsaye tariko hannun nusy tareda daukar Jakarta da gyalenta .


Suka sauko kasa tareda nusy 'nuna ma hanyar dakin su Aisha t'ai dataje c'en ta Jirataa.



Cikin hanzari tashiga motar ta ta cillashi kan titi 'gudu take sharara wa kaman zata tashi sama.


Tana ta sauri 'cikin ikon sai gata ta iso gidan gonar ko gama parking din motar ta 'batai ba .


Tafito aguje ta nufi cikin gidan gonan



Deen ! Deen ! Deen


Sai cusa kanta take tayi cikin gidan gonan batareda tsoron komi ba.


Kara gudun ta 'takeyi kan matakalan step deen Deen kawai bakin ta 'ke furtawa.


Deen dake tsaye kusa da gas da ashana ke hannun sa yana kokarin kyafta ashanan yaji sautin Kiran sunan shi.


Waiwaye yasoma yaga alamun babu kowa .


Hankalin sa ya maida kan abunda zeyi .

Yakara jin deeeennnn

Deeennn da wani irin murya mai karfi duka gidan ya amsa.


Kankace me waigowa dazeyi idanun sa 'suka Akan


Idanunsa suka sauka Akan fatima 'buge hannun sa t'ai ashanar dake hannun sa yafadi kasa' kallon ta yake cike da mamakin ganin ta nan wajen.


Cikin rawar murya takama hannun sa, tana jan sa 'shikuma rike da baki yace wai me hakane fatima saiwani Jana kike kinki yimun magana.


Nokewa yai alamun baze tafi ba 'ya tirke waje daya.


Fatima da ranta yakai kololuwa wajen baci 'wanke shi da mari t'ai zata kara masa wani marin 'yarike hannun ta .


Yace haba anti meye Haka kin wani zo kin kamani kina Jana babu Karin bayanin inda zamuje.


Bata kara bi takansa ba 'tai masa wani riko mai karfi Saïda ya tsorata yace Anya fatima batada iska akanta' ganin dagaske bazata sakeshi ba.


Yacigaba dabinta abaya 'suna sauka kasa .


Ta tsaya ta kalleshi kuka ta saki mai tsuma rai idanunta Sun kada sunyi jajir .


Khalid keson kasheka shiyasa nazo in ceci rayuwarka.



Tamkar saukan guduma Haka Deeen kalamanta keta masa yawo akai.


Girgiza Kai yaso ma 'yaya a'a wallahi karya kike Khalid baze taba iya kasheni ba 'yaya ne fa.


Yarikeni tamkar ciki daya muka fito saiyanzu kiwani fitomun da banzar zance aa bazan gaskata kalaman ki ba.


Cikin kuka' fatima tace deen meye ribata dan naiwa khalid karya karka manta fa 'mijina n'a ne.


To in baka gaskata ni yanzu zan tabbatar maka da abunda nake nufi.


Kallon benen gidan gonan t'ai tace Kai yanzu bakaji iskan gas ba ya dabaibaye Dukan gidan ba.


Tobari kagani ashanar dake hannun 'ta tadauko jansu t'ai suka koma c'en baya tana kyafta ashana ta cilla shi .

Aiko gidan gonan yatashi da wuta bal bal bal .


C'en wani kango sukaje suka buya saboda yanda wutar ke tashi bulbulin wutar sai ci gaba yakeyi.


Cikin tsoro da Deen yace kina ganin wutar nan baze zo nan inda muke ba..


Rufe masa baki t'ai tace yi shiru baze zoba..


Khalid dake wajen gidan gonan yana ganin yanda wutar take ci 'dan yakasa karasowa wajen .


Daukar wayarsa yai yakira jami'ai yasanar dasu anyi gobara yana murmushi dan da bakuwar lamba yakirasu.



Jan motar sa,da dayai parking dagacen nesa 'yana shiga motar hamdala yai burin sa yacika , Kai tsaye gida yanufa.


Jami'an sunzo wajen inda akaita kokarin ganin an kashe wannan wutar datakeci hatta motar fatima Saïda ta Kone baka ganin komai' sai karafunan ta..


Allah yabasu iko suka tsaida wutar nan amma kash tayi mugun barna duk wani Abu mai amfani agidan duk ta Kone murkus.



Fatima ta dago Kai taga l'allé jami'an da jama'ar gari da Yan jaridu duk Sun watse bayan sungama abunda yakawo su.


Ahankali ta jawo hannun deen cikin Nata 'suka fito waje kallon inda t'ai parking motar ta 'tai taga motar wuta tacinye shi.


Ajiyar zuciya tasauke 'tareda yin sujadda akasa

Tanayiwa Allah godiya daya bata nasara ceto rayuwar dan Adam.



Deen da haryanzu da zuciyar sa 'bata gama aminta eh lallai Khalid ne keson kashe shi imagin fa sune suka raineshi why zata ce yanason kashe shi.


Ajiyar zuciya fatima keta saukewa akai akai .


Bakin titi suka nufa suka tare me napep tareda masa kwatancen gidan su.




Jama'a antaru gidan Sani yaro anshirya nusy tsaf cikin wata doguwar rigar Peak irin rigunan turkey 'gashin kanta anmta parkin dinsa da rinbom 'simple make-up akai mata. MashAllah t'ai kyau kaganta kaman yayan larabawa sai murmushi take zubawa


Baki sai shigo suke nesa Dana kusa .

Umma ahankalin ta atashe bata ga fatima ba 'ace tana uwar nusy bata wajen.


Duba sako da lungun gidan tasomayi tana Kiran sunan fatima .


Ya sallam tafurta' tunawa t'ai su khalid da Deen basa gidan to ina sukaje ne.


Inna Farida tafito cikin adon ta n'a tsaddan leshi tasha make-up kallon umma take bakin ta dauke da murmushi tace umma waiko kinga su Fatima kuwa.


Ace kirjin biki basanan .


Abba dake zaune yana jiran isowar gwanonin Aminu bello masari 'da kiriku elrufa'i da ganduje mai katoton ciki .


Shima.tashi yai tsaye yace to ina sukaje ne yana kallon umma..

Fuskarsa dauke da damuwa tace wallahi nima kam bansaniba .


Zama t'ai dirshan kan kujera afili ta furta Allah ka karemin yaya n'a.

Duk inda suke.


Bata gama rufe bakinta 'saiga Khalid yashigo .


Yanayin dataga Khalid gabanta Saida ya tsananta bugawa 'karasowa gaban t'ai 'tace ina deen yake naga tare kuka fita.


Shiru ne ya ratsa wajen hankalin abba yai kololuwar tashi.


Girgiza shitakeyi tace Khalid Kai magana nace ina deen yake kuma banga fatima ba.


Hawaye tagani shar shar a idanun Khalid nan da nan idanunta suka kada tana girgiza shi 'cikin kuka tace me kakeson kace min Khalid yi magana mana.


Abba yataso yariko hannun ta yace hassana ki sassauta masa wannan rikon da kike masa Haka kibashi daman yai magana.


Kallon khalid yai yace Dana gayamin wani abunne yafaru .


Khalid yace munje gidan gona , sai nafita siyen kati nabar deen agidan kafun nakoma n'a iske gidan gonan ta tashi da wuta.


Gabadaya gidan kowa Saïda yarikice cikin kaduwa umma tace Kana nufin wutar da Deen ta tashi Kenan tana kuka mai tsuma rai 'har tana neman faduwa jiri n'a dibanta .


Inna Farida ce 'tarike umma tareda zaunar da ita kan kujera stil itama kuka takeyi 'tace hassana inaji ajikina wannan wutar bata tashi da Deen ba 'kiyi hakuri dan Allah abincika agani.


Murmushi khalid yai azuciyar yace to tunda zuciyarki tabaki bé mutu ba 'kina iya yin cikin sabon deen saiki Haïfa mana tareda dan iskan mijin naki .


Bude kofar da akai idanun kowa yakai wajen kofar dan son ganin Wanda zeshigo din


Fatima ce tashi go bakinta dauke da sallama Kana deen n'a bayan ta .


Umma n'a ganin deen da sassarfa tana tuntube taje ta rungumeshi tana kukan farin ciki.


Saké shi t'ai tana kallon sa Dana dafatan wani Abu be sameka ba.


Mutuwar tsaye khalid da abba sukai suna kallon al'ajabi.


Fatima kallon khalid take tana murmushi shima kallon yake cike da tarin mamaki ganin su tare da yai



Deen yace umma babu abunda yasameni Allah yakareni itakuma anti Fatima anan conpound din gidan muka hadu da ita' shine muka shigo tare.


Khalid da komai ya kwance masa yataho yarike hannun deen cikin nuna damuwar sa yace kanina yafashe da munafikin kuka yace .


Nashiga tashin hankali Dana ga wutar nan ta tashi agidan bansan baka ciki ba 'dana Kira wayarka Alhamdulillah tunda babu abunda yasameka ya rungume deen .


Kowa gidan sai hamdala suke Allah ya dawo da Deen lfy.


Umma cikin kwarin Gwuiwa tace maza deen je kadau wanka kashirya cikin hadadun Kayan ka.


Kekuma fatima maza kuje kishirya keda Khalid kune iyayen nusy amma ji bé ku dan Allah.



To fatima ta amsa tareda haurawa saman matakalan step Khalid nabiye da ita baya .



Tana Shiga dakin taji sallamar khalid juyowa t'ai takalleshi tana murmushi shima murmushin ya maida mata.



Karasa shigowa dakin yai 'tareda rike hannun tace yace mata congrat ya tsareta da idanu.


yawwa ta amsa masa tana murmushi


Uhmm.kana iya fita wanka zanshiga 'mun hadu anjima .


Ya'akai naganki de deen kina nufin tare kuka dawo daga gidan gona.


Eh tare muka dawo .


Murmushi yai cikin son tabbatar da zargin sa yace to taya kikasan yanacen ya tsareta da idanu.


Cikin rashin tsoro tace wayar danaji kanayi ajiya duk n'aji komai kuma shiyasa naga bazan iya barin jinin masoyina ya zuba abanza ba shine naje n'a ceto rayuwar sa Akan mugun kudirin ka.



Uhmm yai yana girgiza Kai 'yace fatima Kenan inaga bakisan wanene Khalid Sani yaro ba.


Kaima inaga bakasan wacece Fatima Auwal ba.


To muzuba mugani FATIMA Auwal kwana nawa Zaki dauka dan ceto rayuwar Deen.


Kwana daya 'wata daya' shekara ko Dukan watanni nan Dana lissafa Zaki tsareshi n'a tsawon lokacin ne .


Ina me tabbatar miki wallahi saina kashe Deen


Fatima cikin fargaban kalaman sa 'ta zuba masa idanu amma saita dake tace to mu zuba mugani Wanda yafasa acikin badan halak bane


Haka kikace ko eh Haka nace.


Fita yai daga dakin ransa abace direct dakin sa 'yanufa dan shiryawa .


Itako fatima dirshan tazauna bakin gado rike da kanta 'tana nazarin taya zata iya yaki da khalid alhalin tana ya Macé?


Wata zuciyar tace mata ai abun daga gaskiyar ki ce nasarar ki da wannan tunanin tashiga toilette t'ai wanka 'kayan dazata tadauko wata haddan shaddan gezner anmasa adon stone ' tana sa Kayan cas yazauna mata ajiki 'yanuna kyawun surarta da kyawun hallitar da Allah yai mata gaban mirror ta nufa 'tai simple make-up ita kanta tasan tahadu 'feshe jikinta da turarruka masu dadin kamshi, karamin gyalenta dake gefen ta 'tadauko tadan yafa 'cikin hanzari.tadau Jakarta da takalmin wanda suka kasance kala daya.


Daidai da zata fita ne taci karo da khalid dake shigowa 'kallon ta yake babu ko kyafta .


Mallam ya ka tsareni da kallo kaman zaka daukeni da idanunka .


Dan bata fuska yai yace dan n'a kalleki haramun n'a kallah ne?


Kwarai kuwa ,haramun ne ka kalla yanzu gayamin meya kawoka dakina sauri nake.


Gyaran murya yai yace wayannan Kayan Dana siyo miki 'shi zakisa anjima in taro yai taro .


Ok Shiga ka ajiyemin kan gado 'daga Haka tawuce tabarshi adakin.


Rike da baki da 'yace lallai wannan yarinyar batasan da Wanda take buga game ba.


Ajiye kayan yai tareda sauka da sauran kayayyaki kasa 'wanda zebawa 'su Aisha 'sumayya'' .



Kusan tare suka sauko itada khalid hannunsa rike da Kaya .


Iske su Aisha t'ai 'da sumayya da Deen zama cikin su t'ai tana musu sannu.


Deen n'a kallon ta, ta kashemai idanu 'kasa da kansa yai 'saboda bemance abunda yafaru agidan gonan ba .


Khalid yace heee kannnena kubude kayan ko wacce tazabi kalan daze mata.


Nan da nan suka fara dubawa 'sumayya ta kalli deen tace yaya deen dan Allah wani kalan ne Zemin kyau tana gwada Kayan da jikin ta.


Dariya yake yace indai nine gaskiya nafison pink color 'murmushi fatima t'ai jin deen ya ambaci kalan da yafi so.



Sumayya tace amma gsk yaya deen ka iya zabe jibi yanda sukaimin kyau .


Fatima tashi t'ai tashiga kitchen sai gata da Coffe yanata turiri zafi.


Gaban deen ta nufa 'tace nasan kana bukata 'kada mata Kai alamun 'a'a


Haba deen Dina kasha man kaida kasha gwagwarmaya ayau din nan kasha mana please tana shagwabe fuska.


Karba deen yai daga hannunta 'yana Kai baki 'wani dadi yaji ya ratsashi lumshe idanun sa 'yai yace amma gaskiya cofee din nan yahadu 'dan karomin kara zuba masa t'ai .


Tana kallon khalid tana murmushi shiko Khalid ransa abace yake .


Cikin son boye fushin sa yace fatima dan zubo min cofeee dinnan insha nima.


Ok to t'ai kaman zataje tazuba 'sai jiyai tace kash nayi mantuwa adaki.


Sumayya kizubawa yayan naki zanje indawo.


Wuce wa t'ai tana murmushi.


Khalid da ransa yagama baci mikewa tsaye yai


Sumayya tace yaya khalid ina zakaje ga Coffe n'a zuba maka banza yai da ita yabi bayan fatima .


Yana shigowa dakin yace ke mekika dauki aure ne?


Murmushi t'ai tace aure ai sunnah manzon Allah ne saw.


Cigaba dayin abunda takeyi t'ai inda tadauko Kaya pink color 'tana kokarin canza n'a jikinta .


Sake da baki yace ai wannan ba Kayan danace kisa bane ina Wanda nakawo miki.


Nunamasa gadon t'ai tace gashi cen .


Wannan kuma Dana dauko naga masoyina deen shiyafi burgesa shiyasa zan Sakata.

Batai aune taji shakar dayai mata ya hadata da bangon dakin nan 'nan da nan taringa zazzare idanu 'cikin son kwatar kanta da rikon da yai mata takasa kwakwaran motsi ,sakin ta tareda jefata saman gadon .


Kara masowa kusa da gadon yana kallon ta cikin kwayar idanu cikin tsananin bakin ciki 'yake wallahi fatima saikin san dani kike zan koya miki hankali banza kawai wacce batasan darajan aure ba.


Afusace yabar dakin cikin kunan rai.


Fatima dasai zazzare idanu take 'ajiyar zuciya tafara saukewa dan bakaramin wuya taci ba 'shakar da Khalid yai mata.



Tashi t'ai tanata shafa da marwa acikin dakin ta ayyana acikin zuciyarta bakin rai ,bakin fama.


Karar wayarta tasata neman inda ta ajiye jakarta 'tana dubawa kan screen din wayar Alisa tagani.


Daga wayar t'ai cikin sanyin murya tace Alisa saiyau kika nemeni.


Dagacen bangaren tace yi hakuri alh nura yace mun bithday akeyi n'a yarki hakane ko?


Eh hakane kina nufin kin gayamasa kin sanni ne


No bangayamasa ba jinai yace diyar Khalid nasan aikece uwarta.


Murmushi fatima t'ai tace hakane yau ake bithday namance ban aika miki da invitation card ba.



Gashi inason inzo to yazamuyi Kenan.


Cikin zazzare idanu fatima tace Alisa kozaki Bari nangaba kinzo dan bazasu barki kishigo awannan ranar ba 'nikuma bazan samu fitowa ba bare inshigo dake.


Amma akwai bikukuwa n'a yayan gidan .


Cikin gamsuwa da bayanan ta Alisa tace to inason ganin koda bayan bithday ne yazaai?


Dan nisawa t'ai 'sannan tace Zaki kwatantamin inda zan sameki dakaina zanzo banson alh nura yasan nasanki dan inanan Akan kudirin kwato maki yancinki daga Haka sukai sallama.



Ajiye wayar t'ai cikin hanzari tasaka Kayan da tayi niya din.



Kan ta sauko kasa taro yai taro inda akace ga gwanoni nan Sun iso.



Abba sai washe baki yana lale lale ashigo dasu.


Ganduje ne agaba yaci farara shadda da babban Riga



Aminu bello masari

Shima shadda yasa Maroon color shima da babban Riga.



Waiyyo kuzo kuga haduwa wajen


Gwanan elrufa'i


Dayasaka suite black yasa gilashi a idanun sa komai nasa kolabo yai sai washe hakora yake kaman gonan auduga


Nace su kiruki manyan dodon kaduna an iso



Babban waje da Aka gyara Domin su' sukaje kowannen su 'anatse ya zauna cikin isa da takama.


Nan da nan Yan jaridu kaman jira suke kowanne yana kokarin daukan vidéo halatar manyan baki.


Ganin hakane abba yace msu dan Allah su dakata abar baki suhuta tukunna .



Sai shigowa aketayi masu invitation card


Shamsu 'da ummu suka shigo atare yayi shigan buzaye itako tayi shigan larabawa sanye take da nikaf cike da nutsuwa suka shigo falon.



DJ ne yaketayiwa manyan baki sannu da izuwa inda ya hango manager auwal shida matar hajiya hussaina .


Kallo yakoma kansu ganin irin haduwar dasukai


Cike da murmushi mommy takaraso falon inda tahango umma c'en zaune suda Inna Farida sai tarban baki suke .


Sunata baza idanu suka yarsu fatima amma shiru kakeji.


Aisha da sumayya ne suka shirya cikin Kayan da Khalid yakawo msu 'suna kokarin fita .

Umma ta hango su' tsaidasu t'ai tace Ku ina zakuje ne?


Aisha tace yaya yusuf ne yace muzo nida sumayya office dinsa.



Umma tace bazakuje ba sarakan yawo' yana nufin baze zo bithday din bane .


Kiran sa awaya t'ai cikin fada tace yusuf bansanka da Haka ba Kana nufin bazakazo bithday ba



Haba umma ina tarin ayyuka fa bithday ne kuma fa bidi'a ce umma ba wata farilla bace.


Nasani yusuf amma nabaka minti talatin inganka gidan nan batajira cewar sa ba 'ta katse Kiran .



Abinci me rai da lafiya tasa Aka kawo wa bakinta harda mommy dakyar datakeci


Gwamnoni sukace su badadewa zasuyi ba .


Agabatar musu da iyayen yarinyar da yarinyar cikin washe baki abba yafara neman Khalid da fatima.


Hango fatima yai tana saukowa daga matakalan step Khalid nabayan ta.


Nusy n'a gaban fatima tana takawa ahankali kaman wata hawainiya.


Aikuwa kowa yadauki tabi harda su gwanonin da abba .


Cikin tafiyarsu me daukan hankali suka karaso murmushi kwance Akan fuskar su.


Yan jaridu sai vidéo suketa dauka da hotuna Aka zagaye da daukan hotuna .



Khalid rike hannun fatima yai nusy n'a gaban su.


Suka nufi wajen gwanonin da manyan kasa masu mukami suka gaishe su 'hakama nusy tabi kowanne daya bayan Daya tagaishe su.



Hotunan tarihi Aka dauka harda fatima acikin su.


Gwanonin suka dauka da nusy suna rike da hannunta 'cikin fariciki kowannen gwana ya ajiye check n'a millions hamsin agaban fatima masu mukami 'suma sunbada kyaututuka .


Duka fatima ta hada takwashe takai dakin ta.


Bayan tafiyar gwanoni asaki dj gidan babu abunda kakeji sai kida da ke tashi


Inda Aka nemi uwar nusy tazo ta taka.


Hango deen zaune shikadai abokansa sunwuce yana kallon abunda ake yan murmusawa 'fatima t'ai masa alamun yataso babu musu ya taso .



Rike hannun sa t'ai tace rawa zamuyi 'babu matsla ya amsa mata kasancewa kida ke tashi agidan babu Wanda yakejin maganar dasuke


Fatima tace asa musu wakar (Fanan) farin cikin zuciya.


Ana sakin wakar 'suka fara rawa deen da fatima rawa suke daidai da wakar kaikace dansu akai.


Kowa yadauki tabi 'khalid dasuka fito dakin abba atare da babansa idanunsa yasauka akansu .


Wannan rawar da suke takawa .


Kallon abba yai abba shima shiyake kallo kama hannun abba suka koma cikin dakin.


Mu haɗu a na 9

Marubuciya

Ikilima Adam

Kyauta Daga Allah

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.