Free chapter · Read without an account
Chapter 3
*MASOYA UKU*
_(The three lovers)_
_(True love, intense jealousy & betrayal)._
Page 3
Cike da wannan karfin guiwar Amatullah ta mik'e ta wanke fuskar ta ta saka hijjab ta fito daga d'aki, Dady ya kalle ta yace, "ina zaki je?".
"Dady zan shiga wajan Rahma ne sabida zamu je gidan Yaya Yasir tare da ita". Hamza dake zaune a yayi caraf yace, " Aunty Amatullah zan biki muje".
Mama tace, "Tashi kuje, sai kuyi ku dawo kafin malamin islamiyya yazo," cike da murna ya mik'e ta rik'e hannun sa suka fita dafa parlourn.
Suna tafe suna hira har suka k'arasa gidan sarki, da sallama ta shiga part din Umma kanta a sunkuye, a guje Humaira tazo ta d'afe ta tana fad'in, "Ga matar Yaya oyayo". Yake tayi kawai tace, " Hajiya Humaira kenan, ina Umma da Bestie?."
"Umma dai tana part din Abba ita kuma Rahma Umma ta aike ta amma yanzu zata dawo."
"Okay! To ni sauri nake zanje gidan Yaya Yasir in Umman ta fito ki gaishe ta ita kuma Bestie mayi waya da ita" ta fad'a tana k'ok'arin Barin wajan.
Ahmad da ya fito daga dakin Umma lokacin yace, "A'a kace matar Yaya ce da kanta gwara muzo mu kwashi gaisuwa ai," ya fad'a yana k'arasowa wajan cike da zolaya.
Tabe baki tayi cike da shagwab'ar da ta saba tace, "kaga ka daina bana so Allah zan hada ka da Umma." Dariya yayi yace, "Ayi hak'uri yar gatan Umma na daina, ina zuwa haka?".
"Gidan Yaya Yasir zamu je nazo mu tafi tare da Rahma Ashe Umma ta aike ta". Ahmad yace, "Muje na sauke ki to nima hanyar gidan zanyi".Tare suke fito suna hira cikin nishadi.
______________
"Finally dai Ammar zaiyi aure, ikon Allah gaskiya zanso naga wannan Amatullah din naga ta yarda akayi ta sace zuciyar aboki na haka" Khalid ya fad'a cike da tsokana.
Yasir yayi dariyar keta yace, "baka San wani Abu ba Khalid wato sai kaga gogan naka ya matse lemon tsami a kofi yana kurba yana runtse ido tsabar jaraba."
Dariya Khalid yayi sosai suka tafa da Yasir yace, "Wato mutumin anji yanayi dole a nemo lemon tsami daman ai ka girma ka rik'a kwara kayi auren tun baka fara tare yaran mutane a lungu kana lalube su ba." Dariya suka sake yi shida Yasir suka kalli Ammar dake zaune yana danna waya kamar bada shi suke ba.
Khalid ya kalli Yasir ya d'aga masa gira yace, "Yau mutumin yan miskilancin ne a kansa ya dai ka Mata ka ajjiye Wannan miskilancin sabida aure zaka yi malam." D'ago ido yayi ya kalle su ba tare da yace komai ba ya mai da kanka kan wayar dake hannun sa.
Yasir ya matso kusa dashi yace, "Ammar shirin biki ya kamata mu fara yi fa ba wai ka zauna kayi shiru muna maka magana kayi mana banza ba kamar baka ji mu ba." Yatsine fuska yayi yace "kunga ni ba wani shiri da zanyi daga an daura aure shikenan".
"Hba kai ka isa ma, ai dole ayi mana dinner ko guda d'aya ce balle ma har ball zamu had'a auren soyayya fa zakayi bana kiyayya ba malam" Yasir ya fad'a yana duban Ammar.
"Ku kadai ne kuka San auren so zanyi amma bayan Ku babu Wanda yasan da hakan dan haka zan bisu muje a a auren biyayya ne kawai."
Khalid yace, "Bafa ka isa ba dole ayi mana evens ko kad'an ne tunda mun San kana son yarinyar nan kamar ranka so why baza ka nuna farin cikin samun ta ba?."
"No Khalid ba haka bane yarinyar bata da kunya sosai ni kuma kunsan bana son rashin kunya in na nuna mata ina son bikin zata samu damar raina ni ne gwara muje a haka kawai" ya fad'a yana cize lebe.
Tsaki Khalid yayi yace, "Raini kuma na nawa? Kar ka manta yanzu auren ta zakayi kuma in ka aure ta ba zuba mata ido zaka yi ba dole ka juye mata wannan lalurar taka so ni banga abinda raini a nan ba."
Da sauri ya kalle shi yace,"What! Allah ya kiyaye ni ai ko gado d'aya banjin zan had'a da wannan yarinyar, wato ta samu damar sake Raina Ni."
Yasir da Khalid suka kalli juna suka yi murmushi sannan Yasir yace, "To kenan ba zaman aure zaku yi ba?". Mik'e zaune yayi sosai ya kalle su alamun ya gaji da magana yace, "kunfi kowa sanin dalilin da ya saka ban furta ina son ta ba sabida tayi min yarinta da yawa ina cewa ina sonta shikenan raini ya fara shiga yanzu kuma da zan aure ta kawai sai naje mata da wata bukata, kanwa ta tace fa mu dinga fadar abinda zaiyu Mana" ya fad'a yana mik'ewa daga wajan.
Khalid ya rik'e baki tare da fad'in, "kanwar taka fa ba matar ka zata zama ba? Kuma ba itace wacce kake so tun kana shekara goma sha biyu a duniya ba, so ni banga wani problems a nan ba.
Yasir ya kyalkyale da dariya yace, "Kai Khalid easy mana sirikin kune a gaban Ku fa ya kamata Ku dinga tauna magana fa". Tsaki Ammar yayi ya juyar da fuskar sa.
Dake suna zaune a varandar da duk Wanda ya shigo suna kallon sa hakan yasa suka ga shigowar motar Ahmad, bud'e motar akayi Amatullah ta fito daga gaba Hamza kuma ya fito daga baya, fuskar ta d'auke da fara'a dan hirar sukayi sosai da Ahmad, kamar an jefa mata a Abu a ido haka taji lokaci d'aya hakan ne yasa ta yi k'ara tana murza ido, k'arasa Ahmad yayi yace, " Amatullah lafiya?". Bata yi magana ba sai nuna masa idon ta da take yi.
Hannun sa ya dora goshin ta daya kuma ya bud'e idon ta dashi yana hura mata iska a idon, wani irin wuci Ammar yake yana daga zaune bai San lokacin da yace, "Kai Ahmad me kake yi Haka?"
A zabure suka d'aga kai tare suna kallon inda suka ji sautin maganar, yadda ya bata rai ya kuma zubawa Ahmad ido yasa yaji tsoro ya kama shi gaban sa ya fara fad'uwa duk da bai nuna hakan ya fuska ba, Khalid ne ya taso ya dafa shi sannan ya kalli Ahmad yace, "Jeka" kamar jira yake ya fad'a mota ya bar gidan.
Ita kuwa tana ganin sa ta d'auke ido taja hannun Hamza suka nufin cikin gidan.
Komawa Ammar yayi ya zauna yana sauke ajiyar zuciya, ruwan sanyi Yasir ya mik'a masa ya karb'a yasha yana lumshe ido fuskar amatullah tana yi Masa gizo.
Sai da suka ga ya dan samu relief sannan Yasir ya zauna kusa dashi yace, "Ammar ya kamata ka rage wannan zafin kishin naka tun baka auri yarinya ba kana kishi da dan uwan ka da kuke ciki d'aya ina ga ka aure ta, kishin ka yayi zafi tun ba yau ba nasha fad'a maka meye dan Abu ya fad'a mata Ido ya taimaka mata ta cire ai ba laifi anan, ko zaka hanata mu'amala da Dan uwan tane? Pls Ammar control your self."
Khalid dake tsaye ma yace, "Gaskiya ne abinda Yasir yake fada maka an San so ke kawo kishi amma naka yayi zafi da yawa ka sassautawa kanka."
Ajiyar zuciya yayi kawai ba tare da yace musu k'ala ba ganin hakan yasa suka yi shiru, Sallamar Amatullah da Hamza ne ya katse musu shirun suka amsa ta k'araso ciki, kallon su tayi tace, "Ina wunin Ku." Yasir ya amsa da fadin "Lafiya qalau Amatullah yasu Mama suna lafiya?".
" Lafiya lau suke tana gaishe Ku". Murmushi yayi yace, "Muna amsawa, ina islamiyya kika fito yanzu?". Dan Sosa kai tayi tace, " Anjima kad'an zamu tafi kafin Malam Isa din yazo." Yasir yace, "Okay! Yayi kyau."
Shi kuwa Ammar tunda ta shigo ya lumshe ido yana jin saukar muryar ta har kahon zuciyar sa, wani irin sanyi yake ji yana ratsa shi tun daga kwakwalwar sa har yanyatsun kafar sa, hakan yasa yayi shiru kawai yana lakwasa yanyatsun hannun sa suna bada sautin k'asss kamar yarda ya saba.
Tashi tayi daga inda take zaune ba tare da ta kalli inda Ammar yake ba tace, "bara mu koma k'asa wajan Aunty." Khalid yace, "kin gaji da zaman nan din kenan?."
Murmushi tayi cikin muryar shagwaba tace, "Nan ba'a hira can zan koma" ta fad'a tana juyawa, Yasir yace, "Dawo ki zauna Ammar yana son magana dake, kai Hamz muje lokacin sallah ya kusa" ya fad'a yana mik'e suka fita daga parlourn gabadayan su.
Gudun kar tayiwa Yaya Yasir gardama yasa ta zauna kawai tana b'ata rai tare da turo baki gaba, shi kuwa tunda ya bud'e ido yake kallon fuskar ta cike da so da kauna ji yake kamar ya jawo ta jikin sa ko ya samu saukin yadda zuciyar sa take beating.
Saita nutsuwar sa yayi ya had'e fuska yace, "Ke yar lukuta baki iya gaisawa bane?." Shiru tayi ranta ya baci ya kira ta da sunan da bata so a duniya, ganin yadda tayi shiru sai motsa baki take alamun rashin kunyar take son yi yasa yayi murmushi kad'an ya sake cewa, "Ba magana nake miki bane" ya fad'a cikin muryar fad'a-fada.
Jin yadda yayi maganar tasan Dan ya taso ya mare ta ba wani Abu bane yasa cikin murya k'asa tace, "bana gaishe Ku Dana shigo ba kaine kaki amsawa, kuma ni wallahi ka daina cemin yar lukuta ni ba haka sunana yake ba" ta fad'a kamar zata yi kuka.
"Allah? To ya sunan naki yake fad'i naji." Shiru tayi bata amsa masa ba shima kuma bai kuma magana ba har suka kwashe tsahon 10mint, kiran Anwar ne ya shigo wayar ta hakan yasa ta kalle shi ta mik'e tana k'ok'arin Barin wajan.
"Dawo ki zauna". Juyowa tayi ta kalle shi amma kamar bashi yayi maganar ba ya sake bata rai, dawowa tayi bata zauna ba tace, " To ni mai zan maka bana son zaman din ne fa ni."
D'ago kai yayi ya watsa mata idon sa masu saurin narkar da zuciya da laka yace, "Ni kuma ina son zaman naki, kin tabbatar min bakya sona tunda har kika amince da aure na kamar yadda muka yi dake meyasa bakya sona haka?".
Bata rai tayi itama tace, " Sabida baka min ba kuma zan aure Kane na zauna dakai na wani lokaci shima kuma dan na nuna maka bana son naka ne yasa na amince." Kallon ta ya d'ago yayi yace, "Kin nuna min ai kuma na gani, amma fa akwai abubuwa da dama da zasu nuna kina sona din."
Da sauri ta kalle shi idanuwan su suka sark'e lokaci d'aya cikin sauri ta dauke kai tace, "Kamar me dame?".
"Good girl, kinga Wannan bikin da za'a yi in kika nunawa mutane bakya so kina bata rai lokacin bikin to ya tabbas a zuciyar ki so kike sabida kar na gane yasa kike haka, amma in kika saki ranki akayi biki sosai to zan tabbatar bakya sona".
Shiru tayi tana tunanin maganar da ya fad'a, aikam baza ta bari hakan ta faru ba dole ta daure ta cize ta nunawa masa bata son zama dashi ta haka ne kawai zata samu ya daina raina Mata wayo.
Ganin ta tafi tunani yasa yayi murmushi yana shafa heart side nasa yana jin farin ciki na ratsa shi dan yasan ko babu komai yayi mata wayo, kallon sa tayi ba tare da tace komai ba ta bar wajan zuciyar ta cike da tunani dan yadda yake zak'ewa yana mata magana ma abin mamaki yake bata dan tasan koda Umma baya iya maganar minti biyar.
Fitar ta yasa ya mik'e tsaye ya koma inda yake lokacin da suka shigo gidan yana murmushi shi kad'ai, ita kuwa tana shiga parlourn Aunty Sakinah tace, " My Aunty wata kawa tace zata zo nan ta same ni to tana bakin layi bara naje na tawo da ita". Aunty Sakina tace, "Kiyi sauri to kar ki jima".
Yana tsaye yaga fitowar ta ta bud'e gate ta fita har tasha kwana yana kallon ta haka nan kawai yaji bai yarda da fitowar ta ba yana shirin sakkowa daga saman Khalid ya shigo hakan yasa ya fasa gudun kar su zargi wni abun amma zuciyar sa cike take Dan son sanin inda Amatullah ta tafi.
A bakin motar sa ta tarar dashi yayi wani iri kamar Wanda aka yiwa mutuwa, dake layin baby mutane sosai hakan yasa itama ta tsaya bakin motar tana kallon sa.
Cikin zak'uwa yace, " Beauty ke nake jira baki sanar Dani dalilin kukan ki na jiya ba, me yake faruwa Dan Allah?."
Ajiyar zuciya tayi ta Zuba masa ido tace, "Kayi hakuri My Anwar duk abinda kaga baka samu ba daman ba rabon ka bane kuma....." katse ta yayi da fadin, "kinga kiyi min bayani yadda zan fahimta bana son zagaye-zagaye".
"My Anwar Dady ya bada ni yanzu haka biki na saura two month."
Kamar saukar aradu haka yaji maganar ta ta sauka a cikin kunne sa, cikin rawar murya yace, "Amatullah bana son irin Wannan wasan dan Allah stop it."
Hawaye ya fara zuba daga idon ta tace, "Ba wasa nake ba Wallahi da gaske nake ya bada ni ga Yaya Ammar."
Innalillahi wa'inna ilaihir raj'iun, hasbunallahu wa ni'imal wakil, shine abinda Anwar yake furtawa cikin kidima da tashin hankali, babu shiri hawaye ya fara sauka daga idon sa ya kalle ta yace, "Meyasa Dady zai mana haka Beauty? Meyasa zai datse mana farin cikin mu? Amatullah bazan iya rayuwa babu ke ba ban dan wanne irin so nake miki ba, ki tausaya min Amatullah kar ki rabu dani dan Allah" ya fad'a yana rik'o hannun ta.
Kuka take sosai tana girgiza masa kai tace, "Inda ina da yarda zanyi bazan tab'a bari a raba mu ba, kasan kai nake so kai na fara so kuma kai kad'ai zanso har karshen rayuwa ta, babu yarda banyi ba amma Dady yaki fahimta na akan Wannan auren Dady zai iya tsine min."
"Duk laifin kine tun lokacin da nake ce miki ki bani chances nazo nayi introducing kaina a wajan a matsayin mai Neman auren ki kika ki kika ce ke ba yanzu Ba gashi yanzu muna ji muna gani zamu rabu zaki auri wani bani ba".
" Bamu rabu ba Anwar zan aure shi ne kawai sabida umarnin iyaye na amma zan kasance da kai a koda yaushe, kwanaki kad'an zanyi agidan ya sake ni na dawo muyi aure babu wata mu'alamar aure da zata faru tsakani dashi dan shima ba sona yake ba nima haka, Wannan alkawari nayi maka kuma bazan karya shi ba ka kwantar da hankalin ka Dan Allah" ta fad'a tana kallon fuskar sa.
Murmushi kawai yayi Mata baice mata komai ba ya bud'e mota ya shiga yaja ya bar wjan.
Da kallon tabi motar har ta daina ganin ta sannan ta juyo da niyar komawa gida.
Ganin Wanda ke gaban ta yasa gaban ta ya fad'i nan take ta fara addu'ar Allah yasa bai ji abinda ta fad'a ba.