Free chapter · Read without an account

15

by Salis M Reza · UWATA CE SILA

🙆‍♂️ *UWATA CE SILA* 🙆‍♂️

       *By S REZA ✍️*






☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️


***


 *My you tube channel. 👆 Kubin subscribe. MASOYANA.* 




     *PAGE 👉1️⃣5️⃣*


..........Nana kuka takeyi tana nuna gurin da Alhaji mudi ya ke tsaye. Meera... Nusee... dakuma likitan da shima shigo warsa kenan yanzunnan, dukkanin suka kai kallon su izuwa gurin da Nana take nunawa. Alhaji mudi ne tsaye yayi mutuwar tsaye har ya saki wayar dake hannunsa, shima kallon ta ya keyi yana son tabbatar wa shin da gaske itace!? Babu ko shakka wannan itace, Alhaji mudi cikin tashin hankali da kuma rashin gaskiya da suka baiyana a fuskarsa ya juya zai bar gurin.


Nusee ta ce "Nana ki nutsu babu abun da zai sameki kiyi shiru ina son duk abun da na tambayeki tom ki bani amsa kinji? NANA kam ta gama tsorata sosai domin kuwa takasa nutsowa d'in. Saida Nusee ta rarrasheta sosai kafin ta nutsu. Nusee ta ce "Shine Abban naki? NANA cikin She-she'kar kuka ta ce "A'a ba shibane.


Nusee ta ce "To waye wancen d'in"


NANA ta sake fashewa da kuka kafin ta ce "Anty shine wallhi shine su biyu ne suka kaini wani guri kuma suka yanka min gabana tana nuna gurin da hannu. Cikin mamaki Dr ya ce "Dame suka wanka miki?


NANA ta ce "Abun fitsarinsu suka sakamin a cikin nawa kuma suka dinga yankani a gurin ina kuka amma basu daina ba, aikuwa Dr najin haka yayi waje cikin sauri. Nusee da Meera kuwa kallon junan su sukayi kafin suka kalli Nana wacce duk tabi ta furgice. Nusee ta ce "Meera ina hoton Uncle da Nana ta gani? fito dashi mutam bayeta ko shi din waye agurin ta domikuw...."Nusee tana dubawa sai taga babu kowa a cikin d'akin daga ita sai Nana.


Dr shida Meera babu in da basu dubaba amma ba Alhaji mudi babu alamar sa, sannan ga motarsa nann, ai kuwa take a ka hana fita da shiga a cikin hospital d'in, a ka kira duk ma aikatan cikin hospital d'in aka ce kowa ya shiga dubashi, ana cikin hakane yansanda da Dr ya kirasu sukazo.


Tafiya takeyi wanda Rabin hankalin ta basa tare da ita, Tabbas itace sila itace silar komai kuma koma meye tasan alhakin sune dole ta je ta nemi yafiyar su tin yanzu sannan ta sanar dasu halin da suke ciki na rashin sanin inda Ameera ta ke. Awani anguwar talakawa ta tsaya tana mai bin gidan da wani irin kallo, kallon da ke 'dauke da nadama, raboton da wannan gidan zatayi shekara a shirin koma tafi.


Gidan nanan a yanda ta sanshi saima 'kara lalacewa da yayi, in ta tuna irin wula'kancin da ta dinga musu a baya sai taji bazata iya shiga gidan ba...


Tana tsaye a gurinne wani ya fito daga gidan yana tafiya yana zabbga masifa kai da ganin sa kaga masifaffe. Tsayawa yayi yana kallon ta itama kallon sa takeyi. Babu shekka ya ganeta Aisha ce matar d'an uwan sa wacce ta rabasu da shi tin yana raye bayan ya mutu kuma ta yi masu iyaka da abun da ya shafeta harda d'iyar cikin ta.


Babu shekka Mom ta gane shi wannan shine abokin rikicin ta shine 'kanin mijin ta wannan masifaffannan amma ta manta sunan sa. D'auke idon sa yayi daga nata sannan ya na 'ko'karin barin gurin. Cikin tsoro da fargaba Mom ta ce "Salamu'a laikum "W slm kawai ya ce yana mai cigaba da tafiyarsa.


Mom ta ce "Dan Allah ka saurareni gurin ku nazu Dan Allah. Cikin masifa baba 'karami ya ce *Wallhi Aisha tin muna cikin ruwan sanyi ki bar 'kofar gidannan in ba hakaba zansa yara su koreki . Duk da kuwa yayi mamakin ganinta a 'kofar gidan nasu. Mom ta ce "Dan Allah ka saurareni Wallhi ha'kuri nazo baku nayi na dama "Baba 'karami ya ce "Mukuma mai kika mana da zaki zo kibamu haguri? Ai mu babu abin da kika mana saboda haka ja motarki ki bar gidannan tin yanzu.


Dr ce takira yansanda suka tafi da Najib sannan tayi hospital da IKLIMA amma suna isa Specially hospital suka tarar an hana shiga da fita yansanda sun za gaye asbitin. Dr ce tafito tana tambayar wata ma ai kaciyar su shin lafiya kuwa? Itama ta sanar mata bata san mai ya faruba. Dr ta takira babban likitan nasu ta sanar dashi cewa emergency ne take tafe da ita kuma fyad'e ne, nan take Dr ya ba da izinin a shiga da ita amma da amin cewar police d'in da suke siki a gurin.


Cikin asbiti kuwa police babu inda basu shigaba amma babu Alhaji mudi, har d'akunan marasa lafiya an shiga an duba amma babu shi. Meera kuwa gurin motarsa ta je ta tsaya ko Allah zai sa taga yazo da niyar guduwa, domin ita bata son an hana shiga da fitaba.


Police sunyi iya bin cikensu amma fa sun kasa gano gurin da Alhaji mudi ya shiga, d'aya daga cikin police d'in ne ya ce "Daga wani room ya fiti? Kuma bayan ya fito zaiyi minti nawa kafin kuka biyo bayan sa? Dr ya nuna masa d'akin da yafito daga ciki kuma ya tabbatar masa da cewa ko minti biyu baiyiba suka bi bayansa.


Police d'innann ya dubi a gogon hannunsa sannan ya fara tafiya saida ya d'an yi tafiya kafin ya shiga wani d'akin marasa lafiya, marasa lafiyan su hud'u ne a d'akin kuma kowanne bacci yakeyi. Har zai fita sai kuma ya fasa ya je ya bud'e fuskar d'aya daga cikin marasa lafiyan... yabud'e na biyu... Yana zuwa na uku yana bud'ewa ya ganshi kwance ya lumshe ido tam kar baya numfashi. Police d'in nann ya kallishi, babu shekka shine domin kuwa da wannan kayan suka ganshi a STV camera.


Abban NANA kuwa suna gama waya ya tashi cikin sauri ya sanar wa da Maman ta Itama ta Shir ya suka d'auki hanyar Nasarawa. Abun da zai baka mamaki shine...Abban Nana kaman zaiyi hauka tamkar yayi tsun-tsu ya ganshi a Nasarawa. Itama dai maman nata duk tabi ta rikice amma ba kaman abban nataba. Sun iso Nasarawa lfy. Ai kuwa ko hutawa basu tsaya yiba suka nufi Specially hospital. Bayan sun jene suka kira number da Nusee ta ce in sukazo sukira.


Take tasanar dasu d'akin da suke. Da jagoran d'aya daga cikin yansandan suka shiga cikin hospital d'in, kasan cewar an sanar da su cewa sune iyayan yarinyar.


Daddy kuwa gida ya fara zuwa bayan ya shiga gidane ya tarar da jinin IKLIMA har yanzu domin kuwa ba'a gogeba. Babu kowa a gidan hakanne yasa shima ya fita daga gidan yana kiran number Kabir yana tam bayar sa a wani asbiti suke. Kabir ya ce "Muna Specially hospital please Daddy kayi sauri domin kuwa an tafi da Najib harda mommy. Cikin sauri Daddy ya kashe wayar yana tsaki!!!


Take suka kamoshi suka tasa kyeyar sa har d'akin da NANA take. Abun mamaki haryanzu bai bari kowa yaga fuskar Saba bayan wannan Police d'in, shi kuwa Police d'in yana ganin fuskar sa ya gane shi. Police ne suka cewa NANA ta natsu ta daina kuka ta musu bayani.


 Haka NANN ta fara bayani tin daga lokacin da suka kaita gidan BOKA har zuwa ranar da suka dawo shida abokin sa suka mata fyad'e. Alhaji mudi ya ce "Shi Wallhi bai ma santaba bai ta'ba ganin ta ba, ya dinga rantse-rantse kai da kagan sa kaga mara gaskiya, ana cikin hakane Meera ta shigo d'akin bayan ta gama jira a bakin motarsa, kallon sa tayi ganin irin rantsuwar da yakeyi.


Police ya kalli NANA ya ce "Zaki iya gane fuskar d'ayan da suka miki abin? Nana ta d'aga kai a lamar eh zata ganeshi. Kafin Police yayi magana sukaji an turo 'kofar d'akin had'i da sallama. baban NANA ne ya shigo shida mahaifiyar ta. Ai kuwa Nana tana ganin sa ta fashe da kuka tana cewa "Daddy please ka tafi da ni gida dan Allah bana son ganinn wannan mutumin, tana nuna gurin da Alhaji mudi ya ke.


Abban Nana... Nusee...Meera... Cikin sekon d'aya duk su ukun idanuwan su ya had'u da na juna. Cikin tashin hankali Meera ta me'ke tsaya tana nuna Abban Nana bakin ta na rawa ta ce "Kaine mahaifin Nana? Nusee kuwa a rikice ta ke bin mutumin da kallon mamaki jin cewa shine baban NANA. Shima abban Nana cikin tsananin tashin hankali ya ke bin su da kallon mamaki, me sukeyi a gurin Nana shin dama sun san Nana yarin yar sace!?


Kabir ya kalli baban nasa sannan ya ce "Daddy likita sun 'ki subarni na ganta wai dole sai kaz... "Ai ko 'Karasawa ma baiyiba ya ce "Muje d'akin. Babu shekka dukkanni mairai mamacine yau kan Allah yayi IKLIMA ta cika, innalillahi wa inna ilahi raju'n shine abun da Daddy ya ke furtawa cikin rud'ewa. Shidama Kabir tin a gida yasan IKLIMA ta rasu kawai Dr kadija ta 'boye musune.


Daddy ya je ya bud'e gawar IKLIMA ya na kallo yana kuka tamkar ba na miji ba. Kana ganinn sa kasan mutuwar nan ta ta'bashi. Kallon likitan gidan nasu yayi wato Dr kadija ya ce "Wani police station a ka kaisu?


Dr Kadija ta ce "Ranka ya dad'e ai basu bar cikin asbitin nan ba, suna nan ana yin wani kess d'in ne amma yanzu zasu fito. Daddy ya ce "Shin ita matata Mai tayi da zasu kamata inace yaron da ya aikata kawai ya kamata a ce sun kama? Dr Kadija ta ce "Ranka ya dad'e ai bin cike zasuyi kuma ita ai ba komai zasu mataba kawai dai a matsayin ta na ma haifiyar su duk su biyun to dole sai sunyi magana da ita. 


Daddy cikin masifa da 'bacin rai ya ce "No babu wanda zai tafi min da mata saboda haka muje ki nuna min gurin da suke? Ita kuwa Dr kadija ganin yanda ya canja mata fuskane kamar ba shiba yasa ta bashi hanya ta nuna masa d'akin da shugaban Police d'in ya ke, wanda shi haryanzu ma bai san da wancen kess d'in ba.


Cike da kwarin gyiwa ya sa hannu zai bud'e d'akinn amma ya ji shi a 'kulle, hakane yasa ya shiga bubbugawa da 'karfin sa tamkar mara hankali, abun da Daddy bai saniba kuwa shine... Matarsafa Bata cikin d'akin nann, kuma shigar sa d'akin nan a halin yanzu tofa...


Zaune suke a babban zauran gidan, duk wani babba dake family d'in nasu to ya hallara a wannan gurin, babban yayan nasune ya bud'e taron da addu'a sannan ya ci gaba da bayani kamar haka... "Kaman yanda kuka sani wasu kuma basu saniba, wannan itace matar marigayi Salisu yana nuna gurin da Mom take, nasan wasu sun ganeta wasu kuma basuma santaba ko? To gatanan dai itace a baya ta rabamu da d'an uwan mu, wanda kowa yasan shi da kyutatawa a garemu, Amma ta shiga tsakanin mu da shi. Bayan rasuwarsa kuwa ya rasu ya barta da ciki amma ta ce "Bata bu'katar kowa daga dan ginsa, wanda tin da a kayi rabon gado muka samu abin da muka samu ta raba hanya da mu...


Nida kaina naje har gidan nata domin ta bani yarin yar na ri'ke kafin tayi aure amma ta cimin mutunci harda cewa karna sake zuwar mata gida, haka d'in bai mataba har saida tazo gidan mu da kanta ta zazzagrmu, tin yarinyar ta bata fi wata takwas ba (8) yanzu haka ko sunan ya rinyar ma babu saniba. Tom yanzu nadawo daga kasuwa zan shigo gida na gansu itada baba 'karami suna cecekuce akan wai tazo neman yafiyar mune?.


Nan take d'akin ya kacame da surutai masu cewa basa so sai musu cewa to mu ai bamuma san da ita a family muba, saboda haka su yarinyar ce dangin su ba itaba saboda haka su bata musu komai ba yarinyar ki ki ka cuta da kikaraba ta da dangin mahaifin ta.


 Wani ne daga ciki ya ce "Ya isa haka kowa yayi shiru. Bayan sun natsune ya ce "Aisha yanzu ina yarin yar ta ke?


Mom ta share hawayan da ke zuba a fuskarta ta ce "Dan Allah ku yafemin Wallhi nice sila. Cikin 'bacin rai Baba'karami ya ce "Bama son rainin hankali kece silar kece sila na me?


Mom cikin kukan da yafi 'karfin ta ta ce "Ameera ta 'bata an saceta ban san inda tashigaba. Baba'karami ya ce "Mlm mufa bamu fahimci abun da kikeson cewa ba? Kina nufin kice kece silar da yasa a ka saceta d'in? . Mom ta ce "Eh nice silar komai. Take Mom ta kwashe komai ta sanar musu, tin daga abun da Uncle ya mata har zuwa yanzu.


Inalilahi wa Ina ilaihi raju'n shine kowa yake ambata a cikin zauran. Kafin wani yayi magana, Baba'karami ya ce "Yanzu dai mujira Abba ya dawo shima sace masa yarin ya a kayi yau kwana Sha shida kenann Amma yau sunje 'kar'bota shida matar sa.


Wani d'an matashi daga cikin su ya ce "Amma wallhi Aisha kinyi a Sara a kan wani banza karatun BOKA kin cutar da yarinyar ki, kin lalata mata rayuwa, Walhi Allah sai ya saka mata "Wannan ma ai maganar banzace cewar wani daga baya... Ya ci gaba da cewa yanzu wa gari ya waya, wato ki yar Boko ko? To gashi nann an miki halin Yan BOKON, tindade d'an Boko ne ya lalata miki 'diya.......📝



 MASU KARATU KALLO FA ZAI KOMA SAMA???🤣🤣




Please comment and Sher Dan Allah🙏 ku dinga yin Shering.



My friend🤝

My FAN'S 👍

My love♥️ 

Love all🥰

BY S REZA ✍️ comment

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.