Free chapter Β· Read without an account
18
by Salis M Reza Β· UWATA CE SILA
πββοΈ *UWATA CE SILA* πββοΈ
*By S REZA*
A
βοΈ *FIRST CLAAlS WRITER'S ASSO* ....βοΈ
***
*My you tube channelπ please kumin subscribe*
*PAGE* π1οΈβ£8οΈβ£
...................... *BENUE STATE* Jibrin ne zaune a gaban Mom jikinsa har rawa yakeyi Mom ta ce "Kace kunyi magana da Ameera kuma kace itace ta ce kazo ka sameta a gida? Jibrin yace "A'a dama kawai naga ban ganta bane kwana biyu shine na ce bari nazo gida ko ba lafiya ba. Mom ta ce "To kai d'in waye a gurin ta?Jibrin fa ya rikice domin kuwa Mom ta masa kwarjini da zararr zaiyi maga sai ya din ga jin nauyin ta. Ya ce "Dama dama ni friend na tane. Cikin'bacin rai Mom ta ce friend ko? To dan ubanka tashi ka bar gidannan yaro 'karami da kai har zakazo har gida kana cemin wai kai friend d'in tane. Da sauri Jibrin ya fita daga palorn Mom kuwa ta biyoshi har waje tana zagin sa, shi kuwa Jibrin da wani irin gudu ya ture IRO Maigadi wanda ke tsaye ya ki bod'e 'kofar sai surutu ya keyi...
Mom ta ce "Kar ka sake barin kowa ya shigo gidannan "IRO Maigadi dake 'kasa ya ce "To hajiya in an fi 'karfina yazan yi. Mom ta ce "Me kace? Ya ce "Na ce bazan bar kowa ya shigo ba.
Alhaji lawan da Nana da Matarsa sun dawo gida lafiya in da yan uwa da abokan arzi'ki suke ta zuwa musu jaje, saide har yanzu basu san mai ya faruba da Nana ba su a tinanin su saceta a kayi kuma suka kar'bota, haka dai mutane suke ta zuwa suna fita. Washe gari Alhaji lawan ya samu matarsa wato Fatima ya ce "Tindade babu wanda yasan wannan maganar Dan Allah mu rufe wannan asirin mu biyu, Fatima ta ce "Kai a tinanin ka wannan abun zai rufene? Kasan fa zakuje kotu kuma duk abun da yaje kotu ai ya riga da ya baiyana, sannan kuma mutanan da zakuyi shara'a dasu manyan mutanene kaga kenann dole yan jarida su ji, kuma kaima ba 'karamin mutum bane.
Alhaji lawan ya ce "Ni wallhi 'yan babban gidane bana son su sani in har suka sani to wallahi komai ya lalace, Fatima ta ce "To ai kuwa dole su sani domin kuwa suma ai zasuje gurin shari'ar. Alhaji lawan ya ce "No babu wanda zai je ni kad'ai ma na isa.
Fatima ta ce "To amma ai zaka sanar wa da yayanta ko? Nanma Alhaji lawan ya ce "na cemiki bana son kowa ya sani. Haka dai Fatima ta ha'kura ba dan tasoba, kuma duk da hakan bata ha'kura ba sai ta sanar wa da 'yan babban gidan.
'Ban garan gidan su Nusee kuwa Rakiya fa izuwa yanzu itama han kalin ta ya tashi, ita ba damuwar ta 'batan da Nusee tayi ba a'a ita damuwar ta yanzu bata da kud'i, shikuwa Daddy han kalin sa in yayi dubu to ya tashi, babu irin duban da bai yiba amma ko ina yaje sai ace batanan. Har gurin Mom wato gidan su Meera ya je amma ba ita suma har yanzu naiman Meera sukeyi. Ganin haka ne yasa ya ha'kura a kan koma ina taje da kanta zata dawo.
Mommy da kuma Kabir da sauran danginsu da sauran al'umma ne da suka halarci wannan shari'ar ne a gaban al'kali domin sauraron hukuncin da zai yankewa Najib. Gefe guda kuwa ga Uncle wanda shima an fito dashi Saboda shine ma haifin sa, yana staye tare da wani Police a bayansa. Ga kuma Nusee da Meera sun samu guri sun yi zaman sai mun ji 'kwa-kwaf.
Al'kali ya ce "bayan 'kwararan hujjoji da kuma amsa laifi daga gurin wanda yayi laifi, kotu zata yanke hukunci dai-dai da abun da mai laifin ya aikata.
Al'kali ya ci gaba da cewa, dubada cewa mai laifin ba a cikin haiyacinsa ya ai kataba, sannan kuma bai kai she kara talatin (30)ba. Saboda haka wannan kotu mai adalci ta yankewa Najib Bashir hukunci zaman gidan kaso har na tsawon rayuwar sa tare da aiki ma tsananin. Wanda yaga hukuncin bai masaba zai iya d'akaka 'kara nann da watan hudu cikin wannan shekarar. Yana kaiwa nann ya buga wannan gudumar tasu ta al'kalai har sau biyo.
Take kotu ta d'auka da cewa koootuuu. Nann take masu kuka suka fara masu jimami suka fara. Uncle kuwa yana jin hukuncin da a kaiwa yaran nasa hawaye suka fara malala daga fuskarsa, take yaji tamkar ya bud'e 'kasa ya shiga, ko ma Mai ya faru yasan shine sila, shine silar war gatse war rayuwar family d'in sa. Mommy kuwa sumewa tayi a gurin tsabar tashin hankali, Kabir ma kuka yakeyi yana jijjiga mommy yana cewa Dan Allah mommy kar ki mutu kibarni,
Najib kuwa lokacin da yaji al'kali ya ce gidan kaso take han kalin sa ya tashi, yafara tina rayuwar sa ta baya, take yaji ya sake tsanar giya da duk wani Mai shanta, yasan duk sadiyar shangiyane yanzu ga yanda rayuwa tayi dashi, haka yana kallo akazo aka tafi dashi ko magana bai yi da 'yan uwan saba, ga shi agaban sa mommy ta fad'i bai sani bama ko ta mutu, kuka kawai ya keyi yana tsinewa sharin zuciya.
Shima Uncle bayan an gama hukuncin ne yansanda suka mayar dashi station. Meera and Nusee kuwa ita Meera har dariya takeyi ganinn yanda family d'in Uncle ta lalace acikin kwana hud'u kawai, wannan bai maga komaiba tindade shi d'an a kuyane. Nusee kuwa saida taye hawaye lokacin da taga Najib na kuka mommy na kuka Kabir na kuka Uncle na kuka. Take tsoran Allah ya shigeta.
Nusee ta ce "Meera wallhi na tausaya musu yanzufa ki duba acikin sati d'aya ra yuwar gidan su ta lalace sun rasa Yar au tarsu...sun rasa babban yayansu, gakuma mahaifin su, yanzuma gashi Mom d'in suma basu san halin da take cikiba.
Meera ta ce "Kuma duk wannan abun waye ya musu? Nusee tayi shiru.
Meera ta ce "To bari kiji wallhi wannan abun ka d'ai da ya faru da su ya ishi duk wani mai hali irin na Uncle ya Bari, kin gadai su da kansu suka 'bata rayuwar kansu, a hakan ma wallhi bazan bar suba sai na d'auki fansa, baban sa ya lalata min rayuwa shi kuma ya mareni zaisan ya mari Meera yar gidan Alhaji Salisu. Haka dai suka bar kotun duk jikin su yayi sanyi.
*FATIMA* burin ta ya cika yanzune ta samu damar da takeso kuma dole tayi amfani da ita saboda haka wallahi sai kowa yaji wannan abun. Tashi tayi ta shirya domin zuwa babban gida don ta sanar musu da komai. Ita kanta rabon ta da zuwa babban gida har ta manta.
Da sallama ta shiga, kasancewar gidan ba gidan masu hali bane yasa kana huce zauran gidan sai mutan gida. Suna ganin ta suka tashi suna mata maraba, ko wacce burin ta Allah yasa ta zauna a gobar d'akinta domin kuwa sunsan bata shiga d'akin kowa, nann take ta tara matan gidan ta sanar dasu komai, a kan ai fyad'e a kayiwa Nana.
Baba 'karami ne ya je har gidan Mom domin sanar da ita cewa daddy ya dawo, kuma ansamu yarinyar tasa amma kuma wani babban abu ya faru da yarinyar amma shima bai san menene ba. hakane yasa Mom ta shirya domin zuwa babban gida.
*DADDY* Shine babba a family d'in su shine yasha nono ya sakar wa Alhaji Salisu wato mijin Mom mahaifin Meera. Duk cikin family d'in su subiyune Allah ya musu wadatar arzi'ki, saide dukkanin su Allah ya had'asu da mata marasa son dangin mijin su. Shima Daddy hakane matarsa wato Fatima bata kwanar dangin mijinta ko kad'an, hakanne yasa tayi nasarar rabashi da su.
Tin kafin mahaifin Meera wato Alhaji Salisu ya rasu, Fatima tayi nasarar raba Daddy da family sa. Sun koma ABUJA da zama ko zuwa ziyarama baya yi, lokacin da d'an uwan nasa ya rasu wato Alhaji Salisu, bai zoba sai bayan anyi sati d'aya yazo, bayan yazo basu wani dad'e sosaiba ya bar garin domin kuwa ko yarinyar ma bai ganiba, to tin daga wannan ranar bai sake zuwa dubawa ko matar d'an uwan nasa ta aihu ko Ya ya ba.
Daddy yana mata guda d'aya wato Fatima sai kuma d'an su guda d'aya wato Sulaiman, tin daga kansa bai sake samun ai huwa ba, saida sukayi shekara 16 da Fatima amma shiru, daga nann Daddy ya sake aure ya auro wata mata Mai suna bintu. Bayan shekara d'aya ta haifi 'yarta wato Nana, bayan anyi sunane washe gari, an kwanta da ita lafiya amma a ka tashi sai gawarta.
Allah ya mata rasuwa tindaga ranar kulawar Nana ta koma hannun Fatima, ita kuma Fatima fata son Nana amma a gaban mutane tanayi kamar tafi kowa santa. Shikuwa Daddy Allah yasaka masa son Nana fiye da Sulaiman, hakanne ya 'karawa Fatima 'kiyayar Nana. Yanzu haka sun dawo Benue steta da zama, in da Daddy yayi gininn sa a wata ukuwa da ke JIBATA, sun Kai shekara biyar da dawowa Amma Fatima bataje babban gida ya kai sau biyarba, shikuwa Daddy in dai ba abune ya kama doleba baya zuwa, shikuwa Sulaiman babban gida yazama masa gurin zuwa a koda yaushiii, itama Nana in har Daddy baya gida to tafi son zuwa babban gida, yafimata akan ta zauna a gida. Daddy baya son yaga d'aya daga cikin family shi yazo gurin sa, hakane yasa suma suka ja jikin su.
Daddy ya Manta da cewa d'an uwan sa fa ya mutu ya bar mace da ciki shin yanzu ina take!! Babu ruwansa sauran 'yan babban gida suna uba d'aya ne uwa kowa da nasa, shida Alhaji Salisu sune suke uwa d'aya kuma Allah yamata rasuwa wato ma haifiyar tasu, hakane ma yasa zumuncin nasu ya lalace.
Yanzu de babban gida mutanen da suke ciki sune kamar haka..... Babban yayan su wato Malam Sani da Matarsa guda d'aya... Sai mlm uba wanda ke binsa shikuwa matan sa biyu....sai baba 'karami matan sa biyu.... Su ukun nann uwarsu d'aya kuma tananan a raye suna kiranta da hajjo... Wad'annan sune Yan babban Gida sai kuwa yaransu mata da maza da kuma jikokin su, Allah ya basu dukiyar yara. Sukuma su Daddy su ukune a gurin mahai fiyar su wato... Da LAWAN wanda tin yana 'karami a kece Masa Daddy sai kuma Salisu sai 'yar Autar su wato Kadija wacce tayi auranta ta auri miji Mai rufin asiri.
Ita dai yayanta bai manta da itaba kasan cewar ita macece, yanzu haka tana aure a Kano ne.
*CIGABAN LABARIN*..... Daddy ne ya kalli matarsa wato Fatima cikin 'bacin rai ya ce "Fatima wato ke bakida hankali ko? Yanzu saboda wannan yarinyar ba 'yarki bace shine zaki ji har babban gida ki tona mana asiri ko? To wallhi bari kiji na fad'a miki a kan wannan maganar zan baki mamaki.
Cikin tsananin tashin hnkali Fatima ta ce "Daddy kasan cewar kowa da haka yake kiran sa wato Daddy, ta ce
"Daddy in kafasa bani mamaki baka 'kwanar Allah kuma wallhi sai ka sanar dani abun da ya had'a ka da yarannan da muka had'u da su a Nasarawa specially hospital.
Daddy najin haka yayi shiru ya yabar gidan izuwa babban gida domin kuwa ana cen ana jiransa, kowa nason jin gaskiyar lamarin da Fatima ta zo dashi. Sannan Kuma ana so a gabatar masa da matar d'an uwan sa, itama a gabatar mata dashi, sannan Kuma a fara neman Ina Meera ta shiga.....π
*CAKWAKIYA KENANN. GASKIYA ZA'A JI KUNYA A WANNAN LABARINπ€£π€£π€£π€£π€«*
TO be continue.....
Please comment and Shering Dan Allah.
**My friends π€
My FAN'S π
My love* π§‘
One hause π₯°
By S REZA* βοΈ