Free chapter · Read without an account

23

by Salis M Reza · UWATA CE SILA

🙆‍♂️ *UWATA CE SILA* 🙆‍♂️


      *(By S REZA* )





☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*



 *KASHI NA ASHIRIN DA UKU*


       *PAGE* 👉2️⃣3️⃣


.............. *AL'KALI* ya buga gudumar sa take kotun kowa yayi tsit, kana ya ce "Ko lauyan Wanda a ke 'kara yana magana? Barista Sani ya me'ke tsaye sannan ya ce "Bani da abun cewa ya mai shari'a. Al'kali ya kalli Barista Muhureez ya ce "Kotu tana sauraron ka. Barista Muhureez cikin tsananin farinci da jin dad'in ganinn ya samu nasara ya je gurin Alhaji Bashir ya ce "Shin wannan record d'in da kowa ya saurara shin dagas ke muryar kane? Alhaji Bashir yayi shiru yana tinanin yaufa asirin sa ya gama tonuwa bashida wata hanya da ta rage masa. Ya ce "Eh muryata ce. Barista Muhureez ya ce "Kenan da gaske ne kune kuka yiwa Nana fyad'e?


Alhaji mudi ya harari Alhaji Bashir yana masa a lama da ido a kan kar ya fad'a, shi kuwa Alhaji Bashir ya kalli gurin da Nana take tsaye sannan ya kalli gurin da Mom take kana ya kai kallon sa izuwa gurin da Kabir da Nusee da Meera suka, take yaji hawaye suna bin kumatun sa. Ya ce "Eh mune muka mata.


Take kotu ta sake kacamewa da surutai kowa na tofa albarkacin bakinsa, shikuwa Daddy wani irin dad'in yaji ganinn cewar yaude gaskiya ta baiyana, ya kai kallon sa izuwa gurin da Mom take, ai kuwa yaga ta had'e fuskarta tamkar taga wanda ya kashe mata miji. Kabir kuwa duk abin da Meera ta ke cewa acikin kunnuwansa amma tsananin tashin hnkali da yake ciki ya kasa maga, sai ma yanzu da yaji Daddy d'in ya ce sune suka yi fyad'e sai yaji lokaci d'aya ma ya tsani Daddy d'in nasa.


Barista Muhureez ya ce "Ko zaka iya sanar wa da kotu gaskiyar lamarin da kuma kai da waye? Cikin kuka Alhaji Bashir ya ce "Eh zan iya. Nann take Uncle ya fara basu labarin tin daga lokacin da sukaje gurin BOKA har zuwa lokacin da BOKAN ya basu tabbacin samo maniyin karuwa wacce bazata huce shekara 16 zuwa ashirin 20 ba, da kuma jaririya da yarin ya yar shekara goma 10 zuwa sha biyu ba.


Zuwa lokacin da suka kai masa komai zuwa kwanciyar da sukayi da ita, zuwa mutuwar da tayi, zuwa d'auko ta da sukayi a motarsu zuwa jefarta da sukayi, zuwa burin su da ya cika, zuwa had'uwa da yarinyar a asbiti zuwa kawosu kotu da a kayi zuwa yanzu zuwa zuwa zuwa.


Kotu tayi shiru domin kuwa kowa yana tsoran karyayi magana shima hukunci ya shafeshi. Barista Muhureez ya kalli Alhaji mudi ya ce "Alhaji mudi ko kada abun cewa gameda labarin da abokinka ya bayar? Alhaji mudi yayi shiru ya sun kuyar da kai yana mai jin wata irinyar kunya wacce bai ta'ba jin taba, Barista Muhureez ya ce "Kotu kai take sauraro Alhaji mudi.


Alhaji mudi ya ce "Gaskiyane mune mukayi amma wallhi ni ban "Ya isa haka bama son jin komai tin dade har ka fad'i gaskiya da bakin ka.


Barista Muhureez ya ce "Ya Mai girma mai shari'a duba da yanda masu laifi suka wahalar da shari'a sannan suka kashe rai na jinjiri da kuma 'bata rayuwar yarinya 'karama, Muna so wannan kotu mai a dalci da ta yankewa wad'annan bayin Allah hukunci dai-dai da abun da suka aikata. 


Kotu tayi tsit Al'kali ya shiga rubuce-rubuce har zuwa wani lokaci kafin ya d'ago kai ya kalli ilahiran jama'ar da ke cikin kotun kafin ya bud'e baki ya ce "Abisa kwararan hujjoji da aka bayar da kuma amsa laifi daga gurin masu laifi kotu tayi duba da niyar kashe rai da masu laifi sukayi har guda uku amma Allah bai yiba saboda haka, s tsarin hukunci na addinin muslinci ya ce duk wanda ya kashe to a kashe shi. Dawannan koyarwa ta addinin muslinci wannan kotu mai a dalci ta yankewa Alhaji mudi da Alhaji Bashir hukuncin kisa ta hanyar rataya, da kuma tararr kud'i kimanin miliyon bibiyu kowannansu izuwa gurin iyayan jinjirar da a ka kashe, sannan kotu da bada umarni a nemo iyayan jinjirar acin kwana biyu.


Take jama'a suka manta da batun al'kali kowa ya shiga tofa albarkacin bakinsa masu zaginsu nayi masu tau sayawa nayi masu cewa gaskiya ba'a mu adalciba nayi.


'Ban garan Nusee kuwa ganin masoyin nata a cikin damuwane yasa itama ta fad'a damuwa, take ta jin kamar itace a cikin damuwar. Ita kuwa Meera tamkar ta mi'ke tsaye ta takarawa tsabar murna. Al'kali ya sake bada umarnin kowa yayi shiru kafin yayi magana sai sukaji, ta me'ke tsaya ta ce "Ya mai girma mai shari'a na kawo 'kara.


S M Sake kallon gurin ya keyi da Kyu domin tabbatar wa ko dai gizo take masa, murza idon sa yayi yasake bud'ewa, ai kuwa ya sake saukesu a kanta, sai wani farin cikine yake baiyana a fuskarta take ya me'ke tsaye da niyar zuwa gurin da take amma jin abun da Mom ta cene yasa ya koma ya zauna.


Take kotu tayi tsit ana sauraron Mom, ta nuna gurin da Uncle ke tsaye ta ce "Nakawo 'kararr wannan matsiyaci ne ya lalatamin rayuwar yarin ya ya gudu. Al'kali ya ce 


"Hajiya Kotufa ba gurin wasa bane saboda haka "Gaskiya ta fad'a 'Karana ta kawo nine na 'bata rayuwar yarinyar ta. Cikin tsananin mamaki al'kali Kevin sa da kallo sannan ya ce "Ok muna jinka.


Uncle ya fara bada labarin abun da ya faru tsakanin sa da Meera tindaga lokacin da yafara zuwa koya mata karatu har izuwa yanzu da abun ya ke faruwa. Cikin tsananin tashin hnkali Daddy cikin zuciyar sa ya ce "Kai yana nufin duk yarana kenann yayiwa fyad'e kenann Yar gidan Mom da a kace ta'bata Yar gidan 'kaninn sa uwa d'aya uba d'aya!! Ya lalata yarin ya ta ya kuma lalata ta 'kanina!!!? Kodan dama haka a kace in dai kayi da yar wani kaima za'a yi da naga, amma kuma shi ai nashi abun yayi yawa har yara biyu!??. Haka dai Daddy yake ta zan cen zucin sa.


Bayan Uncle ya gama bada labarin saida kowa yayi mamaki, barin ma su baba'karami da su mlm Sani da Sulaiman. Meera tana jin haka ta ce "Nusee su tashi su tafi amma Nusee ta ce "Ita tana nann tareda Kabir. Hakanne yasa ta ha'kura ta na mai jin zafin abun da Mom d'in tayi, shin mai yasa bazata rufa mata asiriba zatazo cikin mutane tayi kalar wannan maganar. Wallhi badan batason tayi magana a gane cewa itace ba da sai tace kartane.


Har izuwa yanzu Kabir bai ko 'kara kallon suba ya sun kuyar da kansa izuwa 'kasa yana ta kuka.


Al'kali ya ce "Alhaji Bashir ka amin ceda abun da kafad'a kaine ka ai kata? Alhaji Bashir ya ce "eh nine.


Al'kali ya ce "Duba da cewa mai laifi yana 'kar'kashin wani hukuncin to hakan bazai hana mu 'kara yanke masa hukunci a kan hukunci ba, saboda haka kotu ta yankewa Alhaji Bashir hukuncin tararr kud'ad'e kimanin miliyon goma sha biyu bayan hukuncin kisa da ke kansa. Nann take kotu ta fara watsewa Mom taje gurin da Alhaji Bashir wato Uncle yake ana 'ko'karin fita dashi ta ce "Wallhi kayi sa'a bamu had'u da kai a bayaba da nanuna maka Kai 'karamin shegene, kodan yanzu ma gashi a kagani abun da kakoma kuma wallhi² sai na. Sai kuma tayi shiru tana kukan ba'kin ciki da na nadamar da tasaba tun lokacin da Meera ta fara wannan rayuwar.


Akan idon SM su Meera suka tashi zasu tafi, ai kuwa ya tashi ya bi bayansu cikin zumud'i, da sauri ya 'karaso gurin da suke had'i da sallama, as-salamu alaikum. Koda bata juyoba tasan mai wannan muryar wannan d'an a nacinne mara zuciyar nann dai wanda ya ta'kurawa rayuwar ta wato d'an wahala. Wa'alaikum salam Nusee ta amsa tana mai zaro ido na mamaki ganin Sulaiman. Ta ce "SM ya gari? Ya ce lafiya lau Alhamdu lillh.


Meera ta ce "Kinga mlm in zakizo mutafi kizo in ba hakaba wallahi zan tafi in barki. S M ya bi kayan jikin su da kallo wanda suka sha kyu iya Kyu ga sunayen su nann a bayan rigunan nasu abun burgewa ya ce...


"Meera gurinki fa nazo amma kina nuna baki son ganina? Naje gidan ku an cemin wai an saceki wai kin 'bata shin dan Allah ina kika shiga? Meera ta juyo da nufin tayiwa S M cin mutunci kamar yanda tasa a baya amma idanuwanta sukayi gamo, ida nuwanta suga han gamata abun da yasata saida ta kware tsabar rud'ewa.


Alhaji lawan ne tareda Mom suka fito, yayinda Mom ke kuka shi kuma yana bata ha'kuri kamar zai run gumeta, sannan kuma ga a lamar sanaiya nann mai 'karfi a tsakanin sa da Mom. 


Meera cikin mamaki ta ce "Dama Mom tasan Alhaji lawan baban NANA ne!!? Ai bata sake shiga rud'ani bama saida taga sun nufi mota d'aya kuma Alhaji lawan d'in ya bud'e mata gidan gaba tashiga kafin shima ya shiga, acikin motar kuwa Daddy ne ya tambaye ta cewa dama shine wanda ya 'bata Meera? Shine mai koya mata karatun.


 ai take ta fara jin kanta na juya mata, shin meye tsakanin ta da mahaifin Nana!!?.


Muryar wata da taji daga bayanta tana kiran sunan ta ne ya ka tsemata tinanin da ta keyi. Ameera Amaera Ameera har sau uku, juyowa tayi caraff suka had'a ido, duk da cewa basu san junaba amma jininn su ya tabbatar musu da cewa suda dangan taka tsakanin su.


Kadija ce, tana zuwa ta zaro wayar hannunta ta shiga dubo hoton da Mom ta tura mata na Ameera ai kuwa ta zubawa hoton ido sannan ta zubawa Meera ma ido, babu shekka itace, sai kawai ta nunaea Ameera hoton tana dariyar farin ciki. Ita kam Meera gaba d'aya kanta ya kulle takasa fahimtar komai.


Kadija ta ce "Baki sanni bako? To ni 'kanwar mahaifin kice Uwar d'aya uban mu d'aya, shine yasha nono ya bani, sannan shima yanada yaya, wato babban yayan mu. Ita Anty kadija sam batama kula da Sulaiman da ke gurin ba saida taji ya ce "Anty kadija...


Ta ce "S M dama kasan tane? Ya ce "Eh ai itace yarinyar da nake fad'a miki, ta ce "To ai itace yar gidan. Kafin ta 'karasa maigidan ta ya kirata cikin sauri ta ce "Ameera Ina zuwa tare zamu tafi gida karfa ku tafi.


Cikin d'aurewar kai Meera ta ce "S M Mai kazo yi Nasarawa? S M cikin jun dad'i ganin ta sake fuska ya ce "Munzo gurin shari'ar nanne.


Mera ta ce "Kasan yarin yar da a ke shari'ar a kanta ne?? 


S M ya ce "Eh 'kan watane.


Cakk Meera da Nusee suka tsaya suna kallon S M cikin tsananin mamaki. Nusee ce tayi 'karfin halin cewa "kanwar ka ta jini kodai?


S M ya ce "Baban mu d'aya da ita. 


Ai yana gama fad'a Nusee ta ce "A'uzu billahi mai ka ce? Ta 'kara tam bayar sa cikin tsananin mamaki, ita kuwa Ameera take ta fara min sa da kallon 'kurilla wanda bata tab'a masa ba, tason sai ta gano ta ina yayi kama da Nana ko kuma Alhaji lawan. 


Nusee ce ta ce "S M kabiyomu zamuyi mgn amma ba a nann ba. Kafin Anty kadija da dawo Nusee da Meera da S M sun bar gurin cikin sauri a motarsu. Take ta d'auki waya ta kira Daddy a kan cewar taga Ameera a Nasarawa kuma a cikin kotu kuma suna tare da Sulaiman, take Mom ta 'kar'bi wayar kasan cewar suna tare, ai kuwa take Daddy ya shiga kiran number Sulaiman amma bata shiga.


Take aka fara sana da dangi anga Ameera. DADDY ya kalli Mom ya ce "Dama kin ce ko yau a ka ganta to gobe za'a d'aura aure ko? Mom tayi dariya tana rufe ido. Tana jin wani sanyi a zuciyarta na jin anga Ameera kuma suna tare da Sulaiman yanzu ta ke jin zata iya yin wani auran.


Ta ce "Eh amma ai sai a bari ta 'Karaso ko, kaga itama ai sai tasa albarka ko? Daddy ya ce "Kawai dai gobe za'a d'aura aure kowama ya huta, kinga itama Ameeran sai kawai ayi tuwona miyata kawai a had'a ta da d'an uwan nata Sulaiman ko? Mom tayi shiru tana tinanin in dai Kam ba had'i za'a yi wa Meera Babu na mijin da zai aureta ko shi Sulaiman d'in saide a masa Dole.


Daddy ya ce "kin yi shiru kuma? Ta ce "Tom Allah ya kawo su d'in kuma Allah yasa shima Sulaiman d'in yana sonta......📝





 *ANGAMA WATA SAI KUMA GA WATA* .



To be continue........



ReeeeeeeeeeeeeZaaaaaaaaa



MY FAN'S 🙏

My Friends🥰

One hause🤝

Love all♥️

By S REZA ✍️.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.