Free chapter Β· Read without an account

27

by Salis M Reza Β· UWATA CE SILA

πŸ™†β€β™‚οΈ *UWATA CE SILA* πŸ™†β€β™‚οΈ


      ( *By S REZA* )




  



β˜€οΈ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION* .β˜€οΈ





 *KASHI NA ASHIRIN DA BAKWAI*


      *PAGE* πŸ‘‰2️⃣7️⃣


...........Rana bata 'karya saide uwar d'iya taji kunya. Tafiya sukayi mai tsayi kafin suka isa babban gida, wanda Ameera take ji tamkar ta tashi sama tsabar zumud'i, wayar tane tayi 'kara tana dubawa taga sunan aminiyar ta wato my best m. Kallon wayar tayi tana mai jin son 'kawar tata har cikin zuciyar ta. "Ya kike? Nusaiba ta amsa da cewa "turomin da address din gidan da kuka tafi ganinan zuwa?. Ameera ta ce "Au dama da gaske kike zakizo ai inace wasa kikeyi Rakiya bazata barkiba? Saida sukayi dariya sosai kafin Nusaiba ta ce "Haba auran uwar tamu guda ace ban zoba ai kin san 'karyane.


Ameera ta ce "To Allah ya kawoki kiban labarin yanda kuka kwashe da Rakiya uwarki. Ta ce "Waike meye damuwar ki da wannan Rakiya ne? Ke baki tambayeni ya muka 'kare da Abbana ba sai wata can daban. Ta ce "Ai to nasan Abba bazai miki komaiba ita d'inde.


Cikin 'kosawa da maganar Nusaiba ta ce "Ke ya isa haka dalla, ni dai ki turomin ina jiran ki? Kafin Ameera tayi magana ta katse wayar tana dariya, itama dariyar takeyi tana son jin yanda suka kwashe da uwar tata, domin ita har ga Allah tikicin nadu dariya yake bata sosai.


Mom ta kalleta ganin tana cikin farin ciki ta ce "Nusaiba ce ko? "Eh itace Mom Wai zatazo gurin d'aurin auran shine ta ce in tura mata da address din gidan? Mom ta ce "Ok bani wayar sai na tura mata. Haka kuwa a kayi Mom ta turawa Nusaiba address din babban Gida. Suna tafiya suna hira irin ta uwa da diyarta suka 'karaso gidan.


Abun mamaki koda suka iso 'kofar gidan mutane suka tararr yan zuwa d'aurin aure sun cika sosai. Mom ta kalli Meera ta ce "Gashi nann shine dangin mahaifin ki, kuma nann shine babban Gida. Wani irin sanyine ya ratsa zuciyar Ameera take ta fara aiyano suffofin yan gidan a zuciyarta tana mai jin sha'ki.


Baba 'karami ne ya fara hango motar Mom domin kuwa har ya gane motar, hakanne yasa ya nufo gurin da sairi, ai kuwa yana zuwa Ameera na fitowa. Ameera tana kallon baba'karami tafara sakar masa murmishii tana mai jin babu shekka wannan jininn tane. Shima baba'karami haka take a gurin sa, yana ganin Ameera ya ga kamar ta da Anty kadija domin kuwa kamar tace sak.


Da gudu ta fad'a jikin sa tana mai fashewa da kuka, ita duk a tinanin ta shine wan mahaifin nata, dubada yanda taga babu ta mayar dashi tsoho.


'Dagota yayi yana mai kamo hannun ta ya ce "Ameera ki daina kuka nann shine asalin gidan da a ka haifi mahaifin ki, kin zo gida kukan ki ya 'kare. Take ya kamo hannun ta yana shiga da ita babban Gida. Ai kuwa yana shiga kasan cewar kowa ya halarta dukwani dangi na babban Gida mata maza yara man ya to suna cikin gidan, hakanne yasa baba'karami yana shiga ya sanar da cewa ga Ameera yar gidan hajiya Aisha da marigayi Alhaji Salisu ta dawo.


SM shi saida yaga Mom da Ameera a 'kofar babban Gida tukunna ya gane cewa a shefa Amera yargidan Mom ce kenann ma 'kanwar sace!! Take yaji wani farin ciki ya kamashi yana jin kamar ya samu Ameer ne an gama.


Yana kallon lokacin da baba'karami ya kama hannunta ya shigar da ita babban Gida. Take yaji tamkar ya bita a baya amma ya waske.


Zokaga rige-rigen zuwa gurin Ameera kowa yana son ya fara kamota, ai kuwa take Ameera idion ta ya sau'ka a kan anty kadija. Babu shkka ta ganeta kuma da gaske suna kama, take taji son matar har cikin zuciyar ta. Hajo tsohuwa mai ran 'karfe ce tace "Akawo mata Ameera ai kuwa tana ganin ta ta fashe da kuka itama Ameeran kukan takeyi tana mai jin 'kaunar family d'in nata har cikin ranta.


Saida kowa yazo ya ganta gamida gabatar da kansa, masu tsokana nayi masu mata tsiya nayi, ita dai sai murmishii takeyi tana bin su day kallo, domin kuwa batasan suwaye iyayentaba kana bata san abokan wasan taba. Duk yanda anty kadija taso su zauna da Ameera amma Hajjo ta hana. Ta ce "babu wacce zata dameta bari ta huta tukunna.


Ameera ta shiga d'akin Hajjo wanda babu komai a cikin sai gado irin na mutanan da gajere mai 'karfe. D'akin ko laida Babu. Tana shiga taga yarin ya a cikin d'akin tana kallo a waya, da a lamar kallon ya d'auki hankalin yarinyar domin kuwa bata san ta shigoba. Tayi sallama yarinyar ta amsa batare da ta d'agoba. Dede lokacin Nusaiba ta kirata a waya akan cewar ta iso. 


MEERA ta fito ta sanarwa da Hajjo cewar 'kawarta na waje a shigo da ita, bata koma d'akin ba saida Nusaiba ta shigo, ai kuwa tare suka shiga d'akin cikeda ihuun murnar ganin juna, wannan ihunne ya baiwa wannan yarin damar d'agowa taga ko suwaye, ai kuwa tana d'aga ido sai cikin na Nusaiba.


Cike da mamaki Nusaiba ta ce "Nana? Itama Nana ta ce "Anty Nusaiba. Itama Meera ta ce "NANA kece? Ita kuwa Nana cike da murnar ganin masoyiyar tata ta ce "Eh Anty nice ai nann ne gidan mu, yanzu hakama Daddy nane zaiyi aur... "Ai kafin ta 'karasa sukaji sallamar Fatima, ai kafin su amsa saiga Daddy a bayanta shima ya shigo domin yaga Ameer d'in.


"Ina Ameeran ta ke ina ta... "Magar tasa ce ta ma'kale a bakin sa lokacin da yayi ido biyu da Nusaiba ai bai 'kara rud'ewa ba saida ya 'kara had'a ido da Ameera, kafin ko wannan su yayi magana Hajjo da anty kadija suka shigo.


Fatima ce ta ce "Wacece Ameera acikin ku? Daddy kuwa cikin tashin hankali ya kalli Ameera wacce idonta ya fara juyawa ya ce "Meera kece Ameera? Bata bashi amsaba Itama ta ce "Kaine zaka auri Mom kuma kaine yayan mahaifina? Ai tin kafin ta 'karasa Daddy ya fara tari yana nuna Ameera. Da sauri Anty kadija ta fita waje Kiran maza.


Acan waje kuwa gurin d'aurin aure, har an fara raba goro da alawa, aka fara shelar d'aurin aure.


Sai lokacin hajiya Fatima ta ce "Karuwai nefa ku mai ya kawoku gidannan? Ni dama nasan za'a yi haka. Bana tantama ya ta'ba ganin ta tana karuwanci ne a wani guri kod... "Ai kafin ta 'karasa Daddy yayi 'kasa ya zube agurin. Yayinda Meera ke tsaye kanta na juya mata tana ganin abun kamar a mafarki. 


Bata sake rud'ewa ba saida taji ana cewa an d'aura auran Alhaji lawan da amaryar sa Hajiya Aisha akan sadaki dubu d'ari biyu. Take Ameera ta fara wasu irin surutu kamar wacce ta samu ta'bin hankali. Nusee kuwa take komai ya fara dawo mata a kai, Tabbas Alhaji lawan baban Ameera ne, kuma yanzu haka an d'aura auran sa da Mom, kuma shine mutum na biyu da ya fara saninn Ameer a matsayin ya mace, kuma shine wanda ya kusance ni ya kuma kusanci Ameer a cikin rashin sanin mu...


Shine shine shine abubuwa da dama. Ina lillahi wainana ilaihi raju'n, Nusaiba ta ambata ta na mai jin tsaninn tashin hankali a wannan lokacin.


Meera kuwa kamar mai aljannu ta fara surutai. Wallhi 'karyane wannan auran bai d'auru ba, aje a kwance shi, ba babana bane macuci ne ban san shiba, waiyo Allah Mom kizo ki tasheni daga wannan mafarkin da nakeyi, Ni bani da dangin mahaifi wallhi bana son su na yafe bana son su.


Tana gama fad'a ta fad'i agurin ta suma. dai-dai lokacin Mom ta shigo d'akin sanadiyar kiran da tasamu. Nana Anty kadija Hajjo baba'karami da dai sauran mutane dake cikin daikin sai kallon abun mamaki sukeyi ganinn irin abun da sukeyi kamar sun san juna kodan wannan abun ya fi 'karfin saninn juna.


Wajan d'aurin aure kuwa, har an d'aura abokin Daddy sun jirashi Domi yin sallama amma sun ji shiru hakanne yasa kowa ya waste suka tafi suna masa tsiya wai yana gurin amarya.


Cikin gida kuwa Mom ce tafara kuka tana girgiza Ameera, Amma ta'ki farkawa sai da a ka watsa mata ruwa kafin ta far fad'o. Dai-dai lokacin shima Daddy ya far fad'o. Cikin son jin abun da ke faruwa Hajjo ta ce "Shin lawandi dama kasan Ameera ne? 


Kafin Daddy yayi magana Nusaiba ta ce "Ina lillahi wainana ilaihi raju'n, ya Allah kana ganin irin wannan masifar da muka jefa kammu Allah kagani da saninn mu haka ya faruba, Allah ka yafe mana. Wallhi yasan mu nida ita sani ma rashin mutunci.


Kafin Nusaiba ta fara magana wasu daga cikin dangi suka sake shigowa harda SM. Kallon SM tayi sai ta fashe da kuka, yayin da itama Meera kuka takeyi, ita sai yanzuma ta tina da wani SM. Lallai hakane da a kecewa wata masifar gaban wata take.


Baba'karami ya ce "Ke muke jura? 


Kafin tayi magana sukaji muryar Daddy yana cewa "Wallhi na santa nine wanda ya... "Caraf Hajiya Fatima ta cafe da cewa "Zai huce agurin karuwan cin ta suka had'u tindade an ce karuwa ce "Tsawan da baba'karami ya daka matane yasa tayi tsit da bakin ta domin kuuwa tasan halin sa.


Nusaiba ta ce "Wallhi ba 'karya tayi ba hakanne, shine mutum na biyu da ya fara lalata Ameera bayan Uncle Ashe wai wan mahaifin tane. Ta 'karasa maganar tana kuka cikin tsananin tashin hankali.


"Gaskiyane nine wallhi nine, tin ba yanzu ba jikina yana gayamin cewa na ai kata ba dai-dai ba Amma na kasa ganewa shin a inane. Ai kafin ya rufe baki Mom ta zu'be agurin, kafin mutane su kai gurin Mom saiga SM shema ya zube, kamar masu iska saiga Anty kadija itama ta suma.


Ita kanta hajiya Fatima da ta fara yin magar bata yi tinanin cewa da gaske bane kawai dai ita tayi hakane domin Mom taji haushi sai gashi ya zama gaske ai kuwa itama kanta ya fara sarawa. Hajjo kuwa ihuu ta saka tana kuka had'i da salati kowacce kalla in tazo bakin ta. 


Su baba'karami kuwa da mlm Sani da sauran al'umman dake gurin duk shiru sukayi sun rasa abun cewa, kowa sai girgiza kai sukeyi kaman gidan mutuwa, bakajin komai sai ihun wasu matan da suka fara kuka yanzu.


Take Nusaiba taji kanta na sarawa tsabar kukan da tasha, ruwa suka watsawa Mom Amma bata farkaba hakanne yasa suka kamata, izuwa mota, suma su SM da Anty kadija a ka fita dasu, kowa bakin sa da abun fad'a amma ba dama, shima Daddy d'in asbitin a ka tafi da shi. Asbitin Dr Lurwan aka kaisu gurin da Anty Zainab ke kwance, ita kanta Nusaiba d'in neman fad'uwa takeyi tsabar ciwon Kai. Haka a ka fito dasu izuwa emergency.


Babban Gida kuwa su Hajjo sai kuka sukeyi saura kuwa suna zagin Daddy, dama da yawa sun san halin sa nabin yara mata, domin kuwa an ta'ba kawo masa yaro wai nasane wata karuwa saida sukayi fad'a sosai. Wanda daga baya kuma ban san mai kuma ya faruba bayan hakaba in ji wanda ke bada labarin.


Yanzu gashi ya 'kareda yiwa yarsa. Kai inna lillahi wainana ilaihi raju'n. Allah ka tsaremu daga sherrin zina, wallhi zina babu kyu zina babu kyu. In kayi da yar wani to Tabbas za'a yi da take. In kayi da matar wani kaima hk. Haka in uwar wanice. Yanzu gashi an d'aura masa aure da uwarta. Wannan wani irin hargitsine wanda ko a zamamin jahiliya ba'a yiba.


Wani ya ce "Gaskiya bai kamata mu barshi ba dole ya dau kuskuren sa ko bayaso wannan ai zubar mana da mutunci yayiiiiiiiπŸ“






Anya wannan zuminci zai d'aure kuwa idan Mom ta farka?πŸ˜‚



   

Kun rage yin comment fa😫



To be continue



My FAN'S πŸ™

My FAN'S πŸ‘

One hause πŸ₯°

Love allβ™₯️β™₯️

By S REZA ✍️.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.