Free chapter Β· Read without an account
28
by Salis M Reza Β· UWATA CE SILA
πββοΈ *UWATA CE SILA* π
*BY S REZA*
βοΈ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*βοΈ
*KASHI NA ASHIRIN DA TAKWAS*
*PAGE* π2οΈβ£8οΈβ£
...........A Hospital kuwa duk yanda likitoci suka kai da 'ko'kari wajan ceto Mom daga fad'uwar da tayi abun ya 'ki, jinin tane yayi 'kasa yakai mizanin da ba'a so wanda yafi a ce jininn mutum ya hau. SM kallon ledar rowan dake hannusa ya keyi ya murza idonsa domin farkawa daga barcin da yakeyi amma yaga dai dagaske ba mafarki bane, tashi yayi ya cire ledar ruwan da 'karfi yayi hanyar waje. Dai-dai zai fita sukayi karo da wata noss zata shigo guransa.
Kallon sa takeyi cikin tsananin mamaki ganin hannun sa na jini amma yana 'ko'karin fita waje a haka, da sauri ta ce "Yalla'bai please dan Allah ka dawo a Kara... "Ai bai bari ta kai aya ba ya ban gajeta ya huce.
Yana fitowa ya hango su baba'karami a tsaye kowa yayi ta gumi ana jiran fitowar likita daga gurin Mom, ai kuwa yana isowa gurin yayi dai-dai da fitowar Dr Lurwan, kafin Dr Lurwan yayi magana SM ya ce...
"Baba 'karami please dan Allah ina Daddy? Shin dan Allah abun da Daddy ya ce gaskiya ne kodai mafarki nayi please dan Allah ku sanar dani? Baba'karami shima cikin wata karyayyar murya ya ce "Sulaiman muma babu da tabbacin cewa hakane ko ba haka bane amma yanzu dai ka kwantar da hankalin ka in sha Allah komai zai yi sau'ki. "Pls ina Ameera? SM ya tam bayi su cikin kuka?
Baba'karami da mlm Sani suka kalli juna kafin ya ce "Suna wancen d'akin 'kawarta ta fad'i bata da lafiya ya 'karasa had'i da nuna masa d'akin da Nusee da Ameera suke, ai kuwa ko gama magana baiyiba ya nufi d'akin.
*KABIR* Tin da su SM suka tafi yake tananin maganar da Nusee tayi wai auransa zatayi da gaske. Kasan cewar baya 'boyewa Mommy komai ne yasa yaje ya sameta da maganar, ai kuwa Mommy ta goya masa baya ta ce "To ai wannan ita ce kalar matar da akeso, tunda gashi saida bamuda komai ta ce tana son zama damu kaga kuwa ai wannan abun farin ciki ne, to Allha ya saka mata da alkairi Allah yasa ayi muna raye.
Amin Kabir ya amsa yana mai jin dad'in Addu'ar Mommy d'in tasa, gakuma wani yanayi da yakeji tare da ita Nusaiba d'in a duk lokacin da ya tuna da ita.
( *SHIN MOMMY TASAN NUSEE KARUWA CE?)*
Hakanne yasa Kabir ya amin ce da soyayyar Nusaiba har ya sanar mata kuma suka fara soyayya, daga jiya zuwa yau da safe har sunyi sha'kuwar da ta huce misali, amma yanzu ya kira number ta bata shiga duk sai yaji babu dad'i, hakanne yasa ya shiga damuwa duk da baisan me ke faruwaba amma jikin sa na bashi ba lafiyaba.
*DADDY* kuwa tin da ya farka ya zama ba umm ba um um, sai kallon sama ya keyi yana mai tariyo komai da ya faru tsakanin sa da Ameera da Nusaiba ba, shin a wannan lokacin mai yasa baiga kamar da Ameera keyi da d'an uwan saba sai yanzu?!! Shin meyasa bani da hankali ne wai shin dama haka Allah yake kama masu aikata zina tin a duniya da irin wannan jarabtarr?
Daddy ya fara magana a fili wanda yasa Hajiya Fatima dake zaune a kusa dashi zuba masa ido kamar idanuwan ta zasu zubo. "Allah kana gani nasan laifinane na rashin ri'ke zumunci da ka turo d'an aikenka Annabi Muhammad sallalahu a w s, yayi umarni damu a kan re'ke shi shikuma ya sanar damu, amma Ni kuma nayi watsida shi ganin na tara abun diya, ya Allah ka yafemin na san na jarabtu haka. Ita kuwa hajiya Fatima wani dad'i takeji domin kuwa ita burinta bai huce araba wannan auran ba, duk da kuwa tasan wannan auran kamar an rabashi ne, haka Daddy ya cigaba da ro'kon Allah yana kuka.
*ANTY KADIJA* Itama ta farka ai kuwa tana farkawa ta fara cewa "Daddy ka cucemu ka 'bata mana zuria'a wannan wani irin 'kazantane wanda ban ta'ba jin ko ganin irin saba, wallhi Allah ya isa bazamu yafe ba ka cucemu ace 'yarka wacce kaine ubanta ita ce ka lalata!!! Ta fashe da kuka tana cewa ina Ameera?.
Nusaiba kuwa tin lokacin da taji kanta na harbawa had'i da sarawa ne yasa Itama ta nufi gurin Dr wanda yasa a ka bata gado amma likitan ya ce "Za'amata kwaji domin duba me ki damunta. Ta kwanta a kan gadon sai barci wanda tin d'azu ta kejin sa amma wannan tashin hankalin ya hanata yi.
*AMEERA* Tin da aka kawo su Mom da Daddy asbiti ta ji bata son had'a ido da kowa a cikin su, duk haushin su ta keji, tana jin inama ace ba'a samu dangin mahaifin nataba, in ta runtse idanun ta sai ta dinga hango su tare da Daddy lukacin da suke sikata abun. Wai ashe baban tane, ta ce dama zuciyata tana bani cewa baizai yowu ace nagama aikata wannan abun alokacin da nakesoba kuma nazo na ce na daina amma Allah bai nunamin kuskure naba...
Tabbas wannan abun ma yana daga cikin tawa jarabtar, Tabbas karuwan ci ba itace hanyar da ya kamata ace nabi wajan 'batawa Mom ba, yanzu gashi na ja komai ya dawo baya, an rabu da Uncle ashe gamu da a salin Uncle a gida, tana cikin hakane anty kadija ta shigo d'akin da wani irin sauri kamar zata tashi.
*MOM* Ahankali take bud'e idanuwanta wanda suka mata nauyi tsabar dad'ewa da sukayi a rufe, Bata saukesuba sai a kan d'an uwan nata wanda shine uwa uba yaya kai komai ma a gareta wato Uncle Bala. 'ko'karin me'kewa takeyi domin isowa gurin da yake amma ta kasa tsabar rashin kwarin jiki, shine ya 'karasa gurin da take yana mai mata sannu sannu, ita kuwa sai ta fashe da kuka tana cewa ina Ameera? Uncle Bala ya bud'e baki zaiyi magana Mom ta ce "Itafa sai taga Ameera.
Hakafa Mom ta firgice Dr Lurwan yace tabari ruwan da a kasaka mata ya 'kare amma Mom ta ce itafa wallhi sai an kaita gurin Ameera. Ita Mom a tinanin ta Ameer ta sumane koma ta mutu ne an 'ki sanar mata hakane yasa ta ki yarda.
Dr Lurwan ya ce "Acire mata ruwan a kaita, haka kuwa a kayi a ka cire ruwan sannan a ka fita da ita izuwa d'akin da Ameera da Nusee suke tana tafiya kamar bazata iya ba.
Shima Daddy ganin har yanzu babu wanda ya shigo in da yake ne yasa ya ce akai shi gurin da Mom ta ke ya nemi ya fiyarta kar je ko shi ya mutu ko ita ta mutu basu yafewa junaba, shima saida kyar aka yarda aka fita dashi izuwa d'akin Ameera domin kuwa Mom na cen.
SM... anty kadija... Mom da Uncle Bale... Daddy da hajiya Fatima... baba'karami da mlm Sani. Dukkanin su ne a cikin d'akin da a ka kwantar da Nusaiba ita kuwa bata san me a keyiba sai barcin ta takeyi cikin farin ciki, ita kuwa Ameera tana jin shigowar su Amma babu Wanda ta kalla, dama-dama ma ta kalli SM lokacin da ya shigo.
Daddy ne cikin kuka ya fara magana kamar haka "AISHA Dan Allah ki ga farceni wallhi tallahi ban s..."Ya isa dan Allah Kar kowa yayi magana duk laifinane ba na kowaba.
Da Ameera tana cewa uwarta ce sila muna 'kar yatawa harda zah
gin ta da cewa bata da hankali ashema ita bata iya fad'ar kalmar ba, domin kuwa babu shkka uwarta ce sila, wallhi ko shkka babu komai da ya faru nice silar komai saboda haka karkowa yayi magana uwarta ce sila.
Kowa dake cikin d'akin yayi shiru yana jin irin kukan da Mom da Ameera keyi tam kar ana yanka wani sahi daga jikinsu, kafin kowa yayi yayi magana Mom ta sake cewa "Da a tinanina kalmar da Ameera take yawan cewa uwarta ce sila, ina ce ko tana nufin uwartace silar yin karunwanci a she ba haka kalmar take nufiba, Mom cikin kuka tace "Kunsan me wannan kalmar ta UWATA CE SILA take nufi? Kowa yayi shiru sannan ta share hawayan ta harda face hancin ta kafin cikin kukan ta ce...
Kalmar uwata ce sila tana nufin abubuwa da yawa, bari Kuma kujisu... uwarta ce silar rabata da dangin mahaifi ta dabadan hakaba to da wannan abun kunyar bai faruba. Uwart ce silar kawo wanda zai fara lalata mata yayuwa har wannan abun kunyar ya faru.
Uwarta ce silar sakata a harkar bin maza wajan nuna mata cewar kud'i saida ilimin Boko a kesamu ita kuma ta fad'a harkar karuwanci domin nunamin cewa basai da karatun Boko a ke samun kud'i ba. MOM ta kalli duk yan cikin d'akin sannan ta ce "Shin wannan kalmar da Ameera take fad'a bata zauna a mahallin taba? Kowa yayi shiru sannan ta ce "Yanzu nidai ban san abun da zanceba a kan wannan abun, tagarasa maganar wacce tafara zaicewa.
Daddy ma cikin kuka irin na masu cikekken nadama ya ce "Aisha wallhi duk wannan abun laifi nane ba nakiba, domin kuwa tin farko lokacin da d'an uwan ya rasu da kace na tai maka muka da wasu abubuwan kokuma Ina zuwa ina duba ku da duk haka bai faruba.
Anty kadija ma cikin kuka ta ce "Tabbas muma duk da namu laifin domin kuwa duk rashin zumunci ne ya kawo haka, da munayin zuminci da duk haka bata faruba. Sai a lokacin MLM Sani yayi magana ya ce "gaskiyane wannan abun da ya faru Allah ya nuna mana cewar wallhi zuminci ba 'karamin abu bane...
Saboda d'an uwan mu ya rasu kuma mun San da cewar yabar iyali amma duk cikin mu a rasa wanda zai je koda ganin sune kuma muna gari d'aya, ha'ki'ka mun yiwa Allah laifi Kuma gashi tin a duniya ya fara bar mana misali. Shin yanzu zuminci muka 'kyara kodai muka lalata? Shin kunsa da cewar yanzu mun zubar da mutuncin mu a idon duniya ne in har maganar ta fita.
Hajiya Fatima cikin rashin iya magana dakuma tsananin kishi da kufciyar baki ta ce "Ai yanzu abun da zaisa Kar manar taje waje shine kawai a raba auran tin dade ai babu dama kasan 'ya kuma kasan uwaba. Ai kuwa maganar da taji Anty kadija nayi ne yasa ta me'ke tsaya zata fara masifa.
Maganar da hajiya Fatima tayi Saida kowa ya kalleta cikin mamaki domin kuwa kowa yasan ta da rashin iya magana. Anty kadija ta ce "Shin kunsa Sulaiman da Ameera suna soyayya harda Al'kawarin aure???
Ai kuwa kafin kowa yayi magana hajiya Fatima ta tashi cikin rashin iya magana da kuma rufewar Ido ta fara magana cikin ihu kamar haka wanda har saida ta tashi Nusaiba daga barcinta. Hajiya Fatima ta ce "Karya kikeyi kadija wallhi 'dana ba zai auri karuwaba sannan kuma ace ubansa ya kwanta da ita shima ya kwanta da ita wallhi ba zai ta'ba sabuwa ba karma ki sake wannan zance karuwa karuwar ma ta ubansa.
Karuwa karuwa sune kalmar da Mom da Ameera da Nusaiba suke mai-maita wa azuciyoyin su. Mom tana jin kalmar tamkar ana d'iga Mata ruwan dalmane a jikin ta, gashi na gidama kenann.
Ita kuwa Nusaiba wacce yanzu ta tashi daga barci tayi karo da wannan maganar da ga bakin Hajiya Fatima, Tabbas ta ganeta itace matar Alhaji lawan wato Daddy kenann dai itace mamar SM. Take taji ta tausaya Ameera ganin irin masifar da take ciki, take itama ta fara tausayin kanta domin tasan itama dole sai Allah ya nuna mata nata jarabawar kamar yanda Itama Ameera take fuskantar tata yanzu.
Dr Lurwan ne ya shigo d'akin ri'ke da ta'kardar kwajin da a kaiwa Nusaiba. Ai kuwa ya taranr da hajiya Fatima sai masifa takeyi kuma kowa ya mata tsit. Dr Lurwan ya ce "Ina mai gidan ki yake? Yana tambayar Nusee. Ita kuwa cikin rashin fahimta da jin kunya tayi shiru sai Dr Lurwan ya ce "Congratulations kina d'auke da ciki na sati biyu........π
*IKON ALLAH ASHEDE ITAMA NATA JARABTAR NA TAFEπ€*
To be continue...
My FAN'S π
My friends π€
Love all β₯οΈβ₯οΈ
One hause π₯°
By S REZA βοΈ comment