Free chapter Β· Read without an account
29
by Salis M Reza Β· UWATA CE SILA
πββοΈ *UWATA CE SILA* π
*BY S REZA*
βοΈ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION*βοΈ
*SURATUL NISA'I, AYA TA ASHRIN DA UKU ALLAH YANA MANA NUNI DA MATAYEN DA AURAN SU YA HARAMTA A GAREMU. KU KASAN CE DANI A CIKIN WANNAN PAGE D'IN DOMIN JIN SUNAYEN SU.*
*KASHI NA ASHIRIN DA TARA*
*PAGE* π2οΈβ£9οΈβ£
...........Cikin tsananin tashin hankali da mamaki Nusaiba da Ameera harma da sauran yan d'akin duk sun d'ago suna kallon Dr Lurwan jin abun da ya ce. Nusaiba ta ce "Ciki fara kace? Dr Lurwan ya ce "Yes sabon cikine na sati biyu ko bakiyi murna bane? Cikin tsananin mamaki Amera wacce tin d'azu batayi magana ba sai yanzu ta ce "Dr wani irin ciki kuma?
Kafin Dr Lurwan yayi magana Mom ta ce "Dr mungode rabu dasu yarane basa son haihuwa ne. Haka Dr Lurwan ya fita yana cewa "Zaki iya tafiya gida domin cikin lafiyar sa lau, Zan turo noss da magunanki saboda yawan barcin da kikace kina yi kwana biyu. Yana fita Nusee da Meera suka kalli juna cikin tashin hankali. Wannan shine a kecewa ba'a rabu da bukar ba sai gashi an haifi habu. Zasuyi maga Mom ta ce "A tashi aje gida asan abunyi, hajiya Fatima kuwa cikin rashin kunya da b'acin rai ta ce "Ai ga irinta nann yar uwarta na da ciki itama ya kamata a dubata tindade ai duk tafiyarsu d'aya.
Sai alokacin baba 'karami ya ce "Wallhi Fatima in bakiyi mana shiruba zan manta da d'anki dake gurinnan yanzu in tarwatsa miki ha'koran bakinki, Wai ke bakida hankali ne bakiganin irin halin da d'anki da mijin ki kecine amma kina 'kara 'kara musu wata damuwar. Ai kuwa take tayi shiru domin kuwa tasan waye shi tsf zai iya tarwatsa mata bakin da yace.
SM kuwa tinlokacin da Maman nasa ta fara magana yakejin wata iriyar kunya dama yasan Bata iya magana ba komeye yazo bakinta bata tsayawa ta tauna take fad'a, yana jin yanda take ta ciwa su Mom da Ameera da Nusaiba mutunci.
Nusaiba kuwa take ta fashe da wani irin kuka tana kallon cikin nata, itama Meera kuka takeyi har suka tattara dukkan su sai babban gida. Mom tasa Nusaiba ta kira Abban ta, ai kuwa take aka kirashi kuma ya ce yana hanya yanzu.
Nusee ta shiga tina yanda sukayi da Abban ta lokacin da ta je gida.
Bayan SM ya sau'ke ta a 'kofargida ya ce "Bari nazo na rakaki har cikin gidan? Ta ce "A'a kabar shi bakomai. Sukayi sallama ta shiga.
Bakowa a cikin gidan hakanne ya bata damar shiga cikin d'akin Rakiya, aikuwa tana shiga Abba zai fito sukayi karo, yana ganinnta ya ce "Tabar Masa gida shi bai santaba, ta ce "Abba nicefa Nusaiba? ABBA ya ce "shifa bashi da wata 'ya mai wannan sunan. Itama Rakiya ta fito tana ganin Nusaiba ta fara salamulai tana tattafa hanu tana cewa... "Innalillahi wa inna ilahi raju'n, An dawo daga yawon barikin ne? To ina ribar barikin da a ke samowa, nasan de ba'a dawowa haka hannu Rabbana ko, ganin hakane yasa Daddy ya saka ta'kalmin sa zai huce.
Ai da sauri Nusaiba ta kama 'kafafunsa tana kuka akan walhi ta shairyu kuma ta tuba bazata sake bujiremasa ba. Ganin irin kukan da takeyine yasa ya ji tausayin ta ya ce "Nusaiba kin bani mamaki ace kina 'ya mace ki bar gidan iyayan ki izuwa duniya, kinsan irin tashin hankalin da kika sakani a ciki kuwa?
ABBA ya ce "To naji zan ha'kura amma inada sharad'i? Ta ce "tom Abba Ina ji, ya ce "kifitar da wanda kikeso domin in aurarr dake in kuma bakida shi to nabaki sati d'aya ki samo in ba hakaba zan samomiki wanda naga yadace dake. Kuma daga yau Kar kisake fita ko nann da waje in dai ba da izininaba, haka Nusaiba ta ce tayarda.
ABBA ya bargidan yana Mai jin dad'in dawowar da taye domin kuwa har ga Allah yana sonta, ita d'aya Allah ya bashi a matsayin 'ya shine yasa ya ke sonta sosai.
Bayan ya fitane ta share hawayan ta ta kalli Rakiya dake tsaye tana Mata kallon 'kurilla kamar taga sabuwar fuska. Zata fita kenan taji Rakiya na cewa "andeyi a sara wallhi ace kina mace ki shiga duniya sai da kika gama yawon ta zubar kafin kika dawo gida, Allah dai yasa ba'a kwaso mana abun gunyaba, haka Nusaiba ta fita har ta bar d'akin Bata ko tanka mata ba.
Ta shiga d'akin ta tayi wanda ta d'auro alaula ta gabatar da sallah ta dingawa Allah godiya dayasa komai yazo Mata cikin sauri, tayi Al'kawarin bazata sake kula wani ba har sai tayi istubura'i sannan ta sanarwa da Kabir yafito. Yanzuma wannan fitowar da tayi Abba bai saniba.
Take ta fashe da wani irin kuka tana kallon cikin nata wanda take da tabbacin cewar wannan gayan da suka had'u a hospital ne ya mata, bata San waye ba bata ta'ba ganin sa ba sai lokacin yanzu in na aihu mai Zan cewa d'an da na haifa ko 'yar?!!.
Zaune suke kowa dake cikin family d'in babban gida to ya hallara amma banda yara. Sai kuma Abban Nusaiba da kuma,..shek malam imamu wanda abokin MLM Sani ne sune zasu fad'i hukuncin auran Daddy da Mom. Kafin afara komai aka sanarwa da Abban Nusaiba komai da ya faru da su Nusaiba d'in, tin daga tafiyar da sukayi har dawowar su da kuma cikin da a kace tanada shi.
ABBA ya ce "Shi Wallhi babu ruwansa da ita domin shi bai ai ketaba kuma ya ce mata karta sake fita saboda haka in dai duniya ce gatanan ta je ya bar mata ita, shi wallhi bai shirya renon d'an shege a gidan saba. ABBA dai idonsa ya rufe ya ce "shi fa bazai 'kar'betaba taje can gurin wanda ya mata cikin wallhi ya bar masa ita kyuta.
Sai alokacin mlm imamu ya fara magana cikin isar sa ta malumta ya ce wa Abban Nusaiba "Kasani shi Allah yana son mai yafiya sannan Allha yana son mai tuba, yarinyar ka tayi kuskure kuma ta dawo tayi nadama ta ce bazata sakeba, shin kai baka neman yafiyar a gurin ma haliccinka? Rashin yafe mata she zai sake jefata a cikin damuwa, ina mai baka shwara a kan kayi koyi da sunnanar annabin mu wajan yafiya da tausayawa... Wato Annabi Muhammad sallalahu a w s. Yana da yafiya ga tausayi, shin Kai bakason yin koyi dashi?.
Jikin kowa dake gurin yayi sanyi jin maganar da shek malam imamu yayi. ABBA ya ce "Tom Malam nagode sosai Allah yasa da al'kairi in Sha Allah ni dai na yafe mata sai Kuma ta nemin yafiyar uban gijinta da kuma d'an dake cikin ta. Haka Abba da Nusaiba suka tashi suka tafi Nusaiba na kuka Ameera ma haka, suna ganinn irin hukuncin da Allah ya d'ura musu.
Kafin kowa yayi magana Mom ta ce "MLM wannan auran kawai a rabashi wallhi bazan iya zama dashi a matsayin mijinaba, hajiya Fatima ma ta 'kar'ba da cewa "to ai ko a addinin muslinci ma ai bubu aure a tsakanin ku Kuma ai..."Hajjo ta katseta da cewa "Kede wallhi Fatima Allah waidai da wannan bakin naki da baya furta al'kairi, burinki ki 'kara tar watsa mana zuria'a kuma in sha Allah wannan auran babu Mai gogeshi, kuma kiji koda lawandi ya saki Mom to wallhi Sulaiman shine mijin Ameer.
Hajiya Fatima ta bud'e baki domin yiwa Hajjo rashin kunya kamar yadda tasaba amma baba'karami yayi saurin kallonta alamar karta sake tayiwa mahai fiyar sa rashin kunya a gabansa, ai kuwa dole tayi tsit da bakin ta ranta a 'bace.
Bayan an gama sanarwa da shek malam imamu duk hargitsin da ya farune ya ce "Ina lillahi wainana ilaihi raju'n, gaskiya wannan abun yana da d'aure kai, gaskiya kunyiwa Allah babban laifi shiyasa ya fara nuna muku laifinku tin a nann duniya amma yin hakan bashi zaisa Allah ya 'ki yafe mukuba.
Ya ce "Yanzu aure tsakanin Mom da Daddy ya halarta amma saide in ita taga zata iya zama dashi, domin kuwa Allah subahanahu wata ala ya saukar mana da aya a cikin ALQUR'ANI mai girma adadin matayen da suka hararmata a garemu.
*(_SURATUL NISA'I, AYA TA ASHRIN DA UKU) 23*
ALLAH YA NUNA MANA MATAYEN DA SUKA HARAMTA A GAREMU SUNE KAMAR HAKA...
An Haram ta muku auran uwayan ku...da 'ya'yayenku... da 'yan uwanku mata... da kuma goggonninku... da kuma innoninku... da 'ya'yan d'an uwanku wanda kuka fito ci d'aya... da 'ya'yan 'yar u'wanku...da kuma uwayenku wanda suka shayar daku... da kuma 'ya'yan wannan wacce ta shayar da ku mama... da kuma uwayan mstanku... da kuma agololin ku wanda suke cikin d'akunan ku daga matanku...
Wad'an nann sune mataye da ALQUR'ANI mai girma ya haramta mana da aura, ayar ta 'karene da mana misali da Muguji auran wad'annan suffofin.
Shek malam imamu ya ce "To kun gani ita Mom matar 'kaninn sa ce kunga a'kwai aure tsakanin su. Baba 'karami ya ce "To mlm amma fa Kar ka manta ya kusanci 'yarta kuma itama ace ya kusan ceta? Ya 'karasa maganar da a lamar girmamawa. MLM ya ce "Wannan kuma wani 'bangare na daban tsakanin su da uban gijinsu, saboda Allah bai haramta aure tsakanin sa da uwar yarinyar ba, saida ita yarinyar Koda a ce bai ai kata mata komai ba to babu aure a tsakanin su, amma dai aure ya hallatta saide in ita taga bazata iyaba sai a raba.
Kowa ya Jinjina Kai a lamar ya gamsu kafin mlm ya tam bayi Mom cewar zata iya zama dashi a matsayin mijinta kodai a raba auran? Mom babu wani dogon tinani ta ce "Araba bazata iya ba. Kowa yayi shiru wasu suna ganin raba auran shine dai-dai wasukuma suna ganinn ai tindade Allah bai haramta ba ai ba komai.
MOM ta ce "Tabbas na yarda da cewar Allah bai haramta auranmuba amma ai ana barin halak da kunya ko, to Tabbas bazan iya zama dashi ba kawai ya bani ta kardata. MLM ya ce wa daddy "to kaji abun da ta ce wai ka bata ta kardarta?
DADDY ya ce "In dai haka ta keso zan bata amma dan Allah ta yafemin ta dubi girman Allah karta rabudamu dalilin wannan abun, duk wannan maganar cikin kuka Daddy keyi kamar 'karamin yaro.
Cikin tsananin rashin jin kunya da bata dashi hajiya Fatima ta ce "To ai sai a yi sakin yanzu kowa yana gani ai? Babu wanda ya tamka mata sai Daddy ne ya ce "abashi ta karda da biro? Bayan an bashi ya rubuta wa Mom saki d'aya sannan ya sake rubutawa hajiya Fatima saki d'aya itama ya zama biyu kenann dama ya mata d'aya tin a baya.
Bayan ya mi'kawa Mom Itama ya mi'kamata had'i da runtse ido yana jin son Mom har cikin ransa,. Ai kuwa take Anty kadija ta ce "Sulaiman ya ce Yana naiman auran Ameera domin sun dai-dai ta kansu. Ai kuwa caraf Hajjo ta caffe a kan baba 'karami da MLM Sani su naimi auran Ameera a gurin Daddy a d'aura yanzu.
Hajiya Fatima kuwa da abun ya zama mata biyu tana ganin sakin da Daddy ya mata sai taji ta kasa magana sai bin ta'kardar takeyi da kallo sai yanzu ta samu damar yin magana... "Wallhi Babu Wanda ya isa ya aurawa d'ana karuwa wacce ta gama zubar da mutuncin ta a kan hanya wallhi bazata sa'buba.
Ganinn hakane yasa Daddy ya ce "Tabar Masa gida tindade ya saketa, ai kuwa haka ta bar gidan cikin masifa. MLM ya ce "Ai babu damar aure dele sai ta gama istubura'i tukunna kafin ayi batun aure.
Sai alokacin Ameera tayi magana domin ita tinda Nusaiba ta fita takejin cewar shikenan rayuwar Nusaiba ta lalace Kabir bazai yarda ya auretaba, in ta tina da irin son da take masa sai taji duk ta shiga damu, ita duk batasan abun da a ka 'kullaba, Sai ji tayi anaiwa MLM godiya, ya tashi ya tafi. Kowa ya fita daga d'akin ya rage daga Mom Sai Ameera sai SM.
MOM ta kalli SM ta ce "Sulaiman da gaskene kana son Ameera? SM ya ce "Wallh Mom tin kafin nasan ita d'in 'kanwatane na keson ta. MOM ta ce "Ameera kina son Sulaiman? Ameera ta kalli SM ta sun kuyar dakai domin ita yanzu ba ta SM take ba, sai ta ce "Mom Nusaiba dan Allah muje gidan su, Mom ta cewa SM ya tashi ya tafi.
*NUSAIBA* har sukaje gida Abba bai ce mata komaiba, suna zuwa ya bud'e kofa tana fita ya ja motarsa sai gidan mahaifiyar Nusaiba d'in. Tana shiga gidan ta ciro wayarta ta Kira Kabir ai kuwa ringi d'aya ya d'aga, yana d'agawa ta fashe da kuka ta ce "Kabir please Dan Allah Kar ka gujeni? Cikin rikicewa ya ce "Lafiya kuwa?
Nusaiba ta ce "Kabir cik cik ciki ne dani na sati d'ay... "Ai Bata 'karasaba ya ce "Ciki Kuma wani irin ciki!!? Cikin kuka ta ce "Cikidai dai wanda kasani please wallhi kuskur...'kit taji ya kashe wayar.......π
HAMMM BAZAN CE KOMSI BA.
Nasan zakuyi comment sosai a kan wannan Page d'in. Duk Wanda keda abun fad'a Ina sauraron sa. Love all my FAN'S by S REZA βοΈ
to be continue....
Commentπ
My FAN'S π
Love youβ€οΈβ€οΈ
One hause π₯°
By S REZA βοΈ