Free chapter · Read without an account
30
🙆♂️ *UWATA CE SILA*🙆♂️
*By S REZA*
☀️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSOCIATION☀️*
***
*Ina kuke masoyan littatafen S REZA? 🖕 kumana subscribe a YouTube channel d'in mu domin samun dad'an littatafai* 🖕🖕🖕🖕.
*KASHI NA TALATIN*
*PAGE* 👉3️⃣0️⃣
..........kallon wayar tayi taga dagaske ya katse kiran kawai sai ta fashe da wani irin kuka mai ta'ba zuciya, du'kawa tayi a gurin ta dinga kuka tana ta'ba cikinta har Rakiya ta ji. "Lafiya kikazo kikacika mana gida da kuka kamar anyi mutuwa? Cewar Rakiya tana shigowa d'akin. Ai ko kallonta batayiba saima cigaba da tayi da kukanta tamkar bata jitaba.
Rakiya kuwa dama cike take da haushin ta ganin tinda tadawo ko magana ma ta'ki yarda suyi kuma tanason ko wani abu ta bata amma sai wani shareta takeyi Rakiya. Cikin tsananin b'acin rai ta ce "Ke dan uwarki badake nake mgn bane? Meye ya samu cikin naki? Aikuwa in dai fankan da ke cikin d'akin ya amsa mata to itama Nusaiba ta amsa. Ganin hakane yasa Rakiya ta kamo hannuta tana mai juyowa da ita ta ce...
"Nusaiba wallhi kud'i nakeso ki d'an aramin zan yi... "Kafin ta 'karasa Nusaiba ta tureta had'i da cewa "Wallhi in baki fita a harkataba zan miki abun da bazaki ta'ba mantawa ba. Ai kuwa dama Rakiya abun da take nema kenann sai kawai ta fara masifa had'i da zage-zage. "Yo dama ina wani mutunci a gurin yarinyar da tabar gidan iyayenta tabi duniya, ai dama in bakimin ba ai baki cika cikakkiyar yar duniya ba, babu mamaki ma cikine kika kwaso daga can gurin yawon tazubar d'in muna fika.
Haka Rakiya ta cigaba da zaginta tamkar an aikota, ita kuwa Nusee tana jinta amma masifar da take cike yafi ta tsaya tana biye mata, amma har cikin zuciyar ta tana jin zafin maganganun da take fad'a a kanta, ganinn hakane yasa ta hau gado ta rufe kanta da bargo har tagaji da zagin kafin ta bar d'akin tana mai cigaba da zagin harda kiran mahai fiyar Nusaiba din ta zaga.
*ABBAN NUSAIBA* Yana zuwa bayan an masa sallama da ita tafito, cikin tsananin b'acin rai ya ce "Tom gashi nann burinki ya ciki tin dade ke baki damu da itaba, yanzu wa gari ya waya? Cikin rashin fahimta ta ce "ban ganeba me kake nufine?
Ya ce "Nusaiba na d'auke da ciki, Saboda haka saikisan ya zakiyi da ita, yana kaiwa nann ya shiga motarsa yabar gidan cikin 'bacin rai. Mommy ta tsaya tana mai-maita maganar ciki!². Sannan ta ce ai kuwa wannan karan saide duk Abu da zai faru ya faru amma sai ta kawo yarta gidannan koda mijin ta bayaso to saide in rabuwa zai da ita surabu. Haka ta shiga gidan tana mamaki yaushe Nusaiba d'in tadawo kuma dama yawon bin maza taje!!! Ai kuwa dole yanzu ta rungumi yarinyarta domin kuwa dik laifin tane amma in Allah ya yarda zata gyara komai, wata zuciyar kuma ta ce bayan komai ya b'aci mai kuma zaki gyara!?.
*AMEERA* Kuka takeyi sosai domin kuwa Nusaiba ta kirata ta sanar mata da cewa Kabir ya 'ki d'aga mata waya, yanzu in takirama bata shiga tasan blocked d'inta yayi. Ita kuma gashi yanzu babu damar fita Mom ta ce bazata sake fita ko inaba har sai ta gama istubura'i tukun, harta wayar ta an kwace wannan ma wayar Mom ne da tadameta da kuka shine ta ce zata kirata sau d'ay she kenann kuma ta yarda. Yanzu ita damuwar ta wani hali take ciki. Tana mutu'karr tausayawa Nusaiba domin kuwa yanzu abar tausayi ce, amm in sha Allah zata san yadda zatayi.
*KABIR* Shi duk a tinanisa Nusaiba ba karuwa bace domin shi yayi tinanin Ameer ce kawai karuwa ganinn yanda take da saukin Kai, amma wai ace harda ciki!! Inana lillahi wainana ilaihi raju'n. Ace 'yarda nakeson zan aurane da ciki!! kai ina gaskiya bazai iyaba, hakanne yasa yayi blokend number d'in ta harda number Ameera domin kar ta kira ta number, duk da irin sonda ya kemata amma gaskiya yana da kishi sosai, bazai iyaba.
Haka yayi watsi da lamarin Nusaiba ya ci gaba da har kokin sa. Idan Mommy ta tambayeshi labarin Nusaiba sai ya ce ai sunanan lafiya, har Mommy ta gaji ta daina domin ita burinta kawai Kabir d'in yace zai aureta tindade yanzu komai Alhamdu lillh, amma taji shiru hakanne yasa itama ta zuba masa ido taga gudun ruwansa. Kullum kuma soyayyar ta na ransa amma in ya tina da cewa tayi ciki sai yaji ta bar tnanin sa.
*ANTY ZAINAB* Kwance take ta d'aga kanta sama tana kallon slim d'in cikin asbitin, ta lalace ta rame tayi ba'ki tamkar ba anty Zainab yar kwalisaba. Kadija ce Aisha ce yar gidan Uncle Bala a kusa da ita. Cikin kuka anty Zainab ta ce "Aisha ina Mom? Wallahi mutuwa zanyi please dan Allah ki nemomin ita harda Uncle Bala please. Da sauri Aisha ta fita domin kiran Uncle Bala.
Na cuci kaina na za lumci kai na Allah ka yafemin. Wani farin ruwane ke fitowa had'e da jini daga 'kar'kashinta, lokacin da uncle Bala ya shigo sai ta kama hannun sa ta fashe da kuka tana ro'kon ya yafe mata. Uncle Bala ya ce "Zainab Ni bakimin laifin komaiba Allah kikaiwa laifin kuma shine zaki ro'ka, saboda haka ni dai na yafe miji, yana kaiwa nann ya bar d'akin domin kuwa baya son ganinta...
Acinkin zuciyar sa ya ce "ai kwara abun da Ameera tayi a kan naki, wallhi duk lokacin da na ganta tamkar na kasheta nima na kashe kaina, yara biyu kawai sun 'bata mana suna duk inda na shiga sai a dinga nunani, damma har yanzu babu wanda yasan abun dake damun ta, sai mu da likita!! Allah ka shirya mana yaranmu daga fad'awa irin wannan rayuwar.
*BAYAN WATA BIYAR* Acikin wanan wata biyar d'in abubuwa da dama sun faru, a'ciki harda mutuwar auran Maman Nusaiba, domin kuwa mijin ta ya ce Nusaiba bazata zauna a gidan saba "Wallhi bata isaba saide in zata bar gidan ai kuwa haka a kayi ya mata saki biyu dama kuma yayi d'aya sai ya zama uku.
Cikin Nusaiba kuwa izuwa yanzu ya baiyana domin kuwa kana kallonta zaka ganshi yayi d'an duma-duma abunsa. Har yanzu bata sake samun number Kabir ba kuma kullum sai ta kira amma bata shiga, haka number Ameera bata shiga duk ta sake lalacewa. Saboda tsabar masifar Rakiya yasa mamanta ta 'dauketa daga gidan nasu suka bar un guwar gaba d'aya. gidan wani yayanta wanda suke uba d'aya ta koma shima ba wani haline dashi ba domin kuwa d'aki ciki d'aya ya basu ita da Nusaiba d'in, haka suka cigaba da rayuwarsu. ABBA Yana zuwa ya kawo musu abun da ya samu.
*AMEERA* izuwa yanzu ta kammala istubura'i d'inta ammafa ta ce ita sam bazata iya aure tabar Nusaiba ba, gashi yanzu batasan ina Nusaiba d'in takeba, taje gidansu batanan kuma Rakiya taki sanar mata da inda suka koma domin itama bata saniba, sannan ita yanzu batada waya tin da a ka kwace wayarta har yanzu ba'a bataba. Hakane yasa ta kira SM ta sanar masa halin da Nusaiba ke ciki.
Yanzu Nana ta dawo gurin Ameera da zama wato gurin Mom. Kullom suna tare da ameera sunyi sabo sosai, Kuma kullum sai Nana ta ce a kaita gurin anty Nusaiba. Haka dai kowa ya zubawa Ameera da Sulaiman ido ganin basa batun aure.
*HAJIYA FATIMA* Saida tayi wata guda agida kafin Daddy ya dawo da ita hakanma ta dalilin Sulaiman ne da ya je ya bashi ha'kuri harda kuka. Badan yasoba ya dawo da ita, sannan ya d'auke Nana ya kaita gurin Mom ya ce ta zauna ita kad'ai a gidan. Duk da haka Hajiya Fatima bata ha'kura da batun auran Sulaiman da Ameera ba dominn kuwa ita ta ce sam bazata yardaba.
Hajjo ce ta tara duk mazan gidan babban Gida akan batun auran Sulaiman da Ameera Wai me a ke jira? Kowa ya ce dama suma sun gaji da jira tindade sun shirya kawai a sa rana mai ya ra'ge!, Haka dai suka bar maganar akan ranar JUMA'A sai a saka rana.
*NUSAIBA* Kana kallonta kasan tana Shan wahala domin kuwa cikin yana bata hawala gawani irin haske da ta'karayi, kullum sai tayi kuka na rashin Kabir wanda har saida mamanta tagane ai kuwa bata boye mata komaiba ta sanar Mata, ai kuwa ta ce mata kawai ta ha'kura Allah zai kawo Mata wanda ya ke sonta da gaske. Jin wannan maganar saida ya haifar mata da ciyo mai tsanani domin kuwa saida sukaje asbiti.
Ansa ranar auran Sulaiman da Ameera wata hud'u masu zuwa, wanda Sulaiman yake gannin sun yi nisa domin shi atinanisa irin wata d'aya za'a sa ko biyu amma har hud'u, tom Allah ya kaimu lfy. Ita kuwa Ameera gaba d'aya Abun ya zama mata biyu, ga har yanzu an'ki a sanar mata da abun da ke samun Anty Zainab, saide a ce Mata kawai dai bata da lafiya, hakanne yasa ta ce gurin Dr Lurwan zataje ta tambayeshi gaskiyar lamarin.
*KABIR* kallon d'an uwan nasa yayi Wanda a cikin wata shida ya lalace ya bar asalin fuskar sa ta Najib ya koma kamar wani abun tsoro, kai in ba kamasa sani me kyubane bazaka iya ganeshibs. ya ce "Yanzu Najib haka ka koma? Najib wanda tinda a ka kawoshi wannan gidan kullum sai ya tsinewa shaye-shaye da kuma neman mata, in ya tina cewar wai 'kanwarsa yayiwa fyad'e har ta mutu kuma a ka kawoshi gidannan sai yaji duk ya tsani kansa.
Kabir ya ce "Najib saninn kankane kaine abokin shawarta kaida Mommy bayan ku bani da kowa, to amma wannan abun bana son Mommy ta ji shine yasa nazo gurin ka domin kaban shawara? Najib ya ce "Ina jinka.
Kabir ya ce "Wallahi wata karuwa ce... Take Kabir ya baiwa Najib labarin komai da yafaru tsakanin sa da Nusaiba, ya karasa da cewa...."Wallahi nayi-nayi a kan na cire sonta a zuciyata amma na kasa kuma ni Wallhi inada kishi bazan iya auran macen da wani ya mata cikiba.
Najib ya ce "Kana sonta?
Kabir ya ce "Yes sosaima.
"To ka aureta domin kuwa na lura da labarin da kaban cewar bayan kowa ya gujeku ita kuma ta ce tana son ku, kuma a lokacin batada cin, please dan Allah kar ka gujeta kaje kaji a'salin abun da... "Kafin ya 'karasa gandiroban dake kula da su ya ce "lokacin ku ya yi, haka Kabir ya bashi abun da ya kawo masa sannan ya bar gidan birsin d'in cike da jin tau sayin d'an uwan nasa.
*AMEERA* Sai da gyar ta samu Dr Lurwan ya sanar mata da ciwon Anty Zainab, ai kuwa lokacin da taji wani irin ihuu! Tayi tana mai zabgawa Allah salati tin daga A har Z, sai ta fara tinani. Itafa dama tinda take da anty Zainab bata ta'ba jinta da saurayi ba, dukda kuwa iri kyan da Allah ya mata ga iya d'aukar wanka, sai Habib wanda shima ba wani dad'ewa sukayiba, to Ashe abun da yasa kenann, take taji bata son ganin anty Zainab d'in ma, ta ce "Kai Allha dai ya rabamu da masu irin fuska biyunnan, yanzu wazaiyi tinanin abun da Anty Zainab keyi kenann!!!.
Zaune ya ke agaban Mommy domin sanar mata da komai, in dai ta yarda to shima zai zai ha'kura ya aureta domin kuwa yana sonta sosai, ta riga da tazama wani sahi daga jikin sa.
Ya ce "Mommy a kan batun Nusaiba ne.
"Ok ina jinka.
Sai kuma ya rasa mai zaice mata, sai kawai ya ce "Mommy Nusaiba fa tana da ciki? Ya ci gaba da cewa...Wai ashema karuwa ce ita da 'kawar tata abun da yasa kenann kikaga naja baya da zancen. Sai ya d'ago kai domin ganinn yanayin fuskar mommy d'in...📝
*Wai shin menene ciwon Anty Zainab ne??🤔🤔*
*Please dan Allah kimin subscribe a YouTube channel d'in na a sama please 👆.*
Comment🙏
My FAN'S 👍
One hause 🥰
Love all ♥️♥️
By S REZA ✍️