Free chapter · Read without an account

CHAPTER 14

by Aisha Adam · WATA KISSAR..(Sai Mata)

✨✨✨✨

    *WATA KISSAR...... *

         ✨✨✨✨✨


           ( *Sai Mata* )


      


             


*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞


( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)


/***


P.W.A✍️


*_A SHORT LOVE STORY_*


*Story and written by*


'''AISHA HUMAIRA

(Daddy's girl)

The experience writer of ABDUL JALAL'''


Na sadaukar da wannan littafin ga Ɗaukacin masoya na, wanda nasani da wanda ban sani ba


Watpad @ Ayshercool7724


What's app ***


Gmail ***


   


ELEGANT ONLINE WRITER'S 


        


      


          


            Page 14


Ammar be kai dare ba yau tun azahar ya dawo gida, amma yana zuwa ya tarar da Mufeeda a falo kwance akan kujera, da ƙyar ta iya amsa masa sallamar sa ya kalleta yace

"ya dai?" tace

"bakomai ya naga ka dawo da wuri yau?"

"kince in dena kaiwa dare, na dawo da wuri kuma kina tambaya ta"


Ɗan murmushi tayi tace "ai ban san zaka dawo yanzu ba, ban girki ba"


"haka kike zama da yunwa in ba na nan, salon Ace bana baki Abinci?"


"Ai bana jin yunwa ne, kuma ga cornflakes can, idan naci ya isheni, Abincin yafi daɗi idan ina ci ina kallon ka"


Murmushi yayi yace "yanzu me zaki ban, ina jin Yunwa"


"ina da miya, bari inje kitchen ɗin in gani"


Ammar ya lura da ita kaman jikin ta babu ƙwari, a hankali take komai, ta dafo masa Abinci ta kawo masa, ta koma kan kujera ta kwanta.


Ammar yace "wai meke damunki ne?"


"Ciki nane yake min ciwo fa"


"Shine kike ta faman haɗe rai haka, wannan ciye ciyen naki ma ya isa su saki ciwon cikin ai"


Shiru tayi masa ta lumshe idon ta, ya kalle ta yace

"ki sakko kici Abinci seki sha magani"


Girgiza masa kai tayi alamar A'a,.

Ammar yaci Abincin sa ya ƙoshi, ya ture Kwanukan gefe, ya ɗakko wayarsa yana game, a tunanin sa Mufeeda ba dagaske take ba.


Can ta ɗan fara juyi tana riƙe cikin ta, tana numfarfashi.


Ya kalleta yace "idan banɗaki zaki shiga ki tashi ki tafi mana"


Haushi ne ya kamata, tana fama da kanta amma yana mata wata maganar daban, a hasale tace 

"Idan banɗakin zani ai na sani, ko na taɓa fitsari a falo ne? In haka kake gudu seka dinga samun pampers kar in ɓata maka guri tunda dama ni Jaririya ce"


Mamaki ne ya kama Ammar, ko da wasa be taɓa tunanin Mufeeda zata gaya masa baƙar magana ba.


Ƙara riƙe cikin ta tayi tana rintse ido, Ammar binta yake da ido kawai, miƙewa tayi tana durƙusawa ta tafi ɗakin ta.


Ɗan taɓe baki yayi ya ci gaba da danna wayarsa, idon sane ya sauka a inda Mufeeda ta tashi, tayi staining na jini a gurin, ɗan zare ido yayi, dama Mufeeda ta isa fara period ne? 🙄 


Miƙewa yayi ya samo ruwa da Omo ya goge gurin, da yake bada yawane inda ta ɓata ɗin ba, shi da farko ya ɗauka kawai rigima take ji, se yanzu ya tabattar bata jin daɗi ne. 


Ya bita ɗakin dan ganin halin da take ciki, yana shiga ɗakin nata ya tarar ta cire kayan jikin ta, daga ita se underwear hatta ribbon ɗin kanta ta cire shi, gashin ta a wargatse tana durƙushe a gaban gado, ta tattaro bedsheet ɗin kan gadon ta tada kai dashi tana kuka, ga fanka se gudu take amma ita ta haɗa gumi sosai se kace me naƙuda. 


Daidaita nutsuwar sa yayi, ya ƙarasa da sauri ya ɗago ta, ya ƙare mata kallo, Mufeeda ba farace tas ba amma chocolate ce me haske, fatar ta tana da matukar ɗaukar ido se sheƙi take, ga wannan sassanyan ƙamshin da take me kashe masa jiki


A hankali yace " sannu ban zaci abun ya kai haka ba, daure kisa kayan ki se muje Asibiti" 


Ɗan ƙura masa ido tayi sannan ta ƙara kwanciya a jikin sa tace

"bazan iya tafiya yanzu ba, ka bari ya lafamin, kuma ma daka ƙyaleni ze dena fa" 

"No gara muje Asibitin dai" 

Ɗan lumshe ido tareda yamutsa fuska alamar tana jin jiki, a hankali kaman me raɗa tace

"bari ya ɗan lafamin, yanzu ina jin ciwon sosai" 


"shikenan sannu" 

Bata iya amsawa ba se lumshe ido da tayi, a hankali Ammar ya kai hannun sa kan gashin ta yana shafawa, zuciyar Ammar ta shiga bugawa da ƙarfi tana raya masa abubuwa da dama akan Mufeeda, Amma wani ɓangaren na zuciyar sa na ƙoƙarin kawar masa da tunanin da yake. 


Ɗan yamutsa fuska ta kuma yi tana miƙe ƙafafuwan ta tace

"Yaya Ammar Ciwo" 

Ya riƙe hannayen ta yace "Sannu ze dena Insha Allah" 


Gaba ɗaya tausayi take bashi, yana tuna wani littafi daya taɓa karantawa me suna (MATA A LOKACIN HAILA) 


Mata na shiga mawuyacin hali a wannan lokacin, wani yanayi ne wanda inba wanda yake jinin ba baze gane ba, sukan shiga halin takura, yawan ƙunci, kasala tashin zuciya, yawan faɗa da saurin fusata, kwaɗayi kaman masu ƙaramin ciki, yawan kuka ko san kaɗaici da dai sauran su, ga uwa uba Wannan ciwon da wasu matan kan yi, ciwo ne me wahala matuƙa wata duk lokacin da za tayi seta kwanta rashin lafiya sosai, ciwon mara me haɗe da ciwon ciki da gudawa, ko kuma ciwon baya da ƙafafuwa, wasu kuma hada amai da zazzabi ƙuraje su fito su ɓata musu fuska, wannan ma ya ishesu shiga damuwa, wata idan tana wannan ciwon kaman zararriya haka take, wata harta gama Al'ada bata san saka kaya, se dai marasa nauyi, wata kuma komai sanyi zata dinga kwanciya a guri me sanyi ko cin abu me matukar sanyi, da dai sauran su. 

 Dan haka yake da mahimmanci miji kokuma wanda yake tare da Mace ya gane idan mace tana irin wannan yanayin ayi mata uzuri, ba kowane lokaci mata suke wani abun suna sane ba, sedai dan kusan gaba ɗaya rayuwar su cikin yanayi ne na hormones da suke sauyasu lokacin al'ada, lokacin da suke da ƙaramin ciki ko kuma idan cikin ya tsufa. 


Kallon ta ya ci gaba daya, bacci ne yayi gaba da ita, dan haka Ammar yasa mata filo ya kwantar da ita ya fita. 


Se la'asar sannan ta farka, ta shiga tayi wanka ta samu ta saka kaya a jikin ta, ta gyara gadon ta ta nemi guri ta zauna. 


Ammar ya dawo ɗakin yaga har tayi wanka ta canza kaya, ya kalle ta yace "ya jikin?" 

"Da sauƙi Alhamdilillah" 

"Saka hijjabinki kizo mu tafi" 


Kaman tace masa A'a amma ta fasa saboda yanzu seya ɓata rai, haka ta saka hijjabi ta fito. 


A hankali take tafiyar, Ammar ya riƙo ta suka fito zuwa cikin a daidai ta sahunsa, Matan layin da yake sana'ar su ce leƙen ƙofar gida suna gulma, suna ganin Ammar ya riƙo Mufeeda sun fito gaba ɗaya hankalin su ya koma kansu, yasa Mufeeda a babur ɗin ya zagaya ya zauna a mazaunin direba ya kunna suka tafi. 


Suna tafiya matan layin suka dasa gulmar su, wasu suna itace matar gidan, wasu suna ba ita bace ba sedai ko baƙuwa suka yi ko 'yar uwassa ce, da yake basu san itace matar gidan ba. 


Wani Clinic na kuɗi ya kaita, suna zuwa ta samu guri ta zauna Ammar yaje aka buɗe mata file, sannan suka shiga gurin ganin likita. 


Suka gaisa da Likitan, ya kalle su yace "to kai ta kawo ko kai ka kawo ta" 


Ammar yace "itace ba lafiya" 


Likitan ya kalleta yace "meya ke damun ki ne?" 


Kallon Ammar tayi tai shiru, Ammar yace "kiyi magana mana" 

"Ciki nane yake min ciwo" 


Ammar yace "ba ciki ba dai mara ko?" 

Kunya ce ta kamata tai shiru tare da sunkuyar da kai. 


Likitan yai murmushi yace "Nagane, menstrual cramp ne, yaushe kika fara?" 


"haka yake min idan zanyi" 


"Yaushe kika fara menstruation?" 


"four years back" 


Ba Likitan ba har Ammar seda ya kalleta Ammar yace "are you sure?" 


"Very sure" ta bashi amsa


Likitan yace

"Ok hakan ba wani abun damuwa bane, mata suna shiga wannan yanayin idan suna Al'ada, sedai a kula da ita da abubuwan da zata ci, Sannan idan ta samu ma nemi a mata Aure, idan akayi musu Aure in akayi sa'a wasu yana raguwa koma su rabu dashi baki ɗaya" 


Ita dai Mufeeda ba tace komai ba.

Likitan yace

"tsakanin magani da Allura wanne kike so?"

Kafin tayi magana Ammar yace "Allura zaka rubuta mata"

Zare ido tayi tace "Haba Yaya Ammar wallahi bana son Allura, dan Allah kar ayimin"

"Likita rubuta mata Allura, Allura tafi quick Action, in ba haka ba muka koma gida zuwa zata yi ta cigaba da lanƙwashewa"

Mufeeda tuni ta fara kuka, liktan yace "We have to respect her autonomy, tunda magani take so a rubuta mata"

Ammar yace "No Allura zaka rubuta mata"

Haka likitan ya rubuta mata Allura da sauran magungunan, ya kalle Mufeeda yace

"Sorry Baby Allura ba zafi fa, Wannan Yayan naki yace se an miki Allura"


Basu kuma kulashi ba, Ammar ya sunkuya dai dai kunnenta yace mata "gobe ma ki ƙara min rashin kunya koki gayamin baƙar magana, ina sane nace a miki Allura" zumɓura baki tayi suka fito daga OPD ɗin, Ammar yace ta zauna ya siyo maganin, ta zauna tana jiran sa.


Bayan ya siyo maganin ne yaci karo da Faruk, suka gaisa Faruk yace "Ahh mutumina me kake anan?"


"Mufeeda ce bata jin daɗi na kawo ta A duba ta"


"Allah sarki, nima nazo in duba wasu patients ɗina ne da na yiwa CS jiya, muje semu gaisa tunda kuka tare ko leƙoku ban kuma yi ba"


Suka tafi tare suna hira, Faruk yaga Mufeeda ta ƙara ƙiba, dukda kuka take amma tayi wani fresh da ita, Faruk yace "Madam har yanzu ba'a dena rikici ba? Hala laulayi ne?"


Ammar yace "Haihuwa zata yi ba laulayi ba"


Ganin irin kallon da Faruk ke mata yasa Mufeeda tace "Na gaji Mu tafi"


Ammar yace "to Faruk se anjima se munyi waya" ya kama hannun Mufeeda suka tafi Injection room.


Fafur Mufeeda taƙi shiga Nurses suyi mata allurar, Ammar ya fara ƙulewa ya janyo ta zuwa cikin gurin, kuka take sosai kamar wadda za'a yanka.


Ammar yace "haba Autar Baba sonake ki warke da wuri shiyasa nace ayi miki allurar ai, hug me you won't feel the pain"


Ya buɗe mata hannayen sa, a hankali ta ƙarasa ta kwanta a jikin sa, ya riƙe ta, Nurse ɗin tace

"Ikon Allah, dan Allah ƙanwarka ce ko matar ka?" da yake babbar mace ce dan haka Ammar ya bata amsa

"Mata ta ce"


"gaskiya ran haihuwa da kallo, Allura kawai tana wannan abun, Allah ya ƙara maka haƙuri ɗan nan, kana fama da shagwaba" murmushi kawai Ammar yayi.


A hakan ma da ƙyar ta tsaya aka yi, Hawaye sharkaf fuskarta, maimakon da'aka gama ta tashi sema ƙara narke masa da tayi a jiki tana kuka.

Ammar yace 

"ya isa haka harfa an gama, Insha Allah yanzu zaki dena jin ciwon"


"Wallahi Allurar da zafi sosai"


"to ai zafin kaɗan ne akan ciwon da kike ciki"

Nan ta shiga zabga shagwaɓarta, ƙarshe nurse ɗin se fita tayi tabar musu room ɗin.


Ammar yace "ki tashi mu tafi kinji an fara kiran sallar magariba"


Noƙe masa kafaɗa tayi,

"idan munje gida zan baki biscuit ai zaki ci ko Jariri ya ta?"

Murmushi tayi masa tana lumshe ido, a hankali ta miƙe ta biyo shi suka fito, suka hau babur ɗin su zuwa gida. 


Da sukaje gida Mufeeda tace ita ba zata iya tafiya ba, ƙafar ta ta sage jikin ta babu ƙwari, ƙarshe seda Ammar ya ɗauke ta ya kaita har kan gadon ta a ranta tace

"tunda kasa akamin Allura se kayi jinya kaima" 


Ammar yaje yayi salla, ya dafo mata tea ya kawo mata, ta karɓa ta sha sannan ya miƙo mata ledar pharmacy yace

"gashi nan pampers ɗin da kika ce in sai miki ne" ta kalle shi tace 

"Pampers kuma?" 

"Eh mana ko kin manta ne?" 

Karɓar ledar tayi ta duba, pad ce guda uku da sababbin pants guda biyar, wata kunyace ta kama ta, banda abun Ammar panties ɗinta kona lefe bata taɓa ba amma ya sai wasu. Sunkuyar da kai tayi taƙi ɗagowa su haɗa ido. 


Yace "zanje masallaci idan nayi sallar isha'i zan ɗan za gaya, kinga yau ban samu nayi aiki ba yadda yakamata" 


"Shikenan amma karka yi dare sosai dan Allah" 

Jinjina mata kai yayi, ya miƙe ya fita. 


Bayan ya idar da Sallar isha'ine Aminu ya kira shi yace "yana so su haɗu za suje gidan Jabir" 


Haka kuwa akayi a gidan Jabir suka haɗu, Jabir yayi farincikin zuwan su, Yace

"Kai Ammar Mufeeda ta ɓoye ka, ko a hanya sam bama haɗuwa, ga yadda kayi kumatu" 

Yaita zolayar Ammar sannan yai musu iso zuwa cikin gidan, falon sa ya kaisu suka zauna suka dinga hira, Can Ammar yace


"Jabir abar hirar nan muyi abunda ya kawo mu? Ina matar gidan ne?"

Jabir yace 

"tana gidan ɗakin ta"


"a gaskiya naji wani labari dabe min daɗi ba game da auren ka, Jabir ya'akayi haka ta faru?"


Jabir yace "bari Ammar ai nayi zaɓen tumun dare dana san haka Auren yake da banyi ba, wallahi mata basu da mutunci nayi dana sanin Auren Saima"


Ammar yace "Dana sanin mene?"


"Yarinyar nan sam bata da Mutunci bata ganin girma na, bata da tarbiyya Sam, ban isa in gaya mata taji ba, wallahi badan ina tsoron abunda iyayena zasu ce ba da tuni na sake ta"


Aminu zeyi Magana sega Saima ta fito, tana ganin su ta faɗaɗa murmushin ta tace

"Manyan Baƙi aini har nayi fushi, sau ɗaya kuka zo mana tun bayan bikin mu, Ammar ina Amaryar?"


"tana gida, idan ma baku zoba zan kawo ta Insha Allah"

Saima tace

"Insha Allah ai zanzo har gida mu gaisa, Jabir baka gayamin sunzo ba ai be kamata abar baƙi babu ko ruwan sha ba, bari in baku ruwa"


Ta wuce ta nufi kitchen, Jabir yaja wani uban tsaki yace

"Munafukar Banza"

Aminu yace "Subhanallah, haba Jabir a gaban mu kake kiran ta Munafuka"


"mece idan ba Munafukar ba, danta ganku take nuna ita ta Allah ce, Amma tafi sheɗan iya rashin mutunci"


Saima ta dawo da lemuka da ruwa faranti da kofuna, ta ajiye Musu a gaban su.

Saima ta kalli Su Ammar idon ta fal Hawaye tace

"Aminu wallahi Abokin ku Azzalumi ne, dan Allah ku gaya masa idan mutum ya auri mace baya na nufin ya auro baiwa bane, Jabir Jahili ne besan darajar ɗan Adam ba"

Miƙewa Jabir yayi yana zare ido, ya fara narko mata Ashar, Saima tace


"Wallahi ba iyaye na ba sedai naka"


Da sauri Aminu ya miƙe ya riƙe jabir yace "Jabir meye haka? Matarka ta Aure kake wa wannan mummuna ashar agaban abokan ka?"


Saima tace "baka ga komai ba a gurin sa, dana san haka yake wallahi bazan Aure shi ba, mutanen kirki suka fito suna sona na liƙe nabi soyayya nace seshi, amma bayan Auren mu, shine kullum cikin chatting da 'yan mata, ba dare ba rana lokacin da nake buƙatar lokacin sa lokacin ne yake chatting, idan nayi magana seya ce wai na taɓa ganin anyi campaign bayan zaɓe? Da ina haƙuri ina ƙyale shi, Amma Ba damar inyi masa laifi se ya fara zagarmin iyaye, wallahi baka isa ba iyaye basu fi iyaye ba kakuma zagarmin iyaye sena zagi naka iyayen "


Ammar yace 

"Saima yi haƙuri ki koma ɗaki, zamuyi magana da Jabir "


Haka ta wuce ɗaki tana kuka, Aminu yace

"gaskiya Jabir kaine mafarin samar da matsala a cikin gidan ka, ta yaya zaka dinga ce mata ba'a campaign bayan zaɓe, hakan fa na nuna bata da wani mahimmanci a gurin ka, haba dan Allah Jabir kaman ba wayayye ba kaima fa kana da ƙanne mata baza kaso ayi musu haka ba, kuma wallahi in gaya maka kaida ta ƙara ganin mutuncin ka har gaban abada sedai tayi pretending, amma a matsayin ka na namiji daga lokacin da ka buɗe baki ka zage ta ka zagi iyayen ta mutuncin ka ya zube a idon ta musamman idan ta buɗe baki ta rama, Jabir meye Amfanin hulɗa da 'yan matan daba Auren su zakai ba bayan ga matarka ta halal a gefen ka? Kawai ka zauna fadi banza faɗi wofi a haka har sheɗan ya kawo muku wani tunani na daban" 


Ammar shiru Yayi yana tunani, ya tuna Yadda Jabir yake Soyayya da Saima kaman babu wata mace da tai Saura a duniya sama da ita. 

Ammar yace

"tabbas Jabir kana da laifi, ba kowane ze iya jure ka zagi iyayen sa yai maka shiru ba duk mutuncin ka da yake gani, karka manta da haƙoran ta bayan iyayen ta sun gama ɗawainiya da ita ka ganta ka aura, babu yadda zata iya jure cin zarafin su gaskiya, kaman yadda bamu da juriya da jarumta irin na iyayen mu haka suma matan basu da haƙuri da biyayya kaman na iyayen mu duk sedai muyi haƙuri da juna, amma batun chatting da 'yan mata lokacin da matarka ke buƙatar lokacin ka, to tabbas idan me raunin Imani ce hakan zesa itama ta fara tunanin fara chatting da wasu mazan"


Suka dinga yiwa Jabir Nasiha, zasu tafi ne Saima ta fito idon ta jawur saboda kuka ta miƙawa Ammar turaren wuta, da humra tace

"Ammar gashi ka kaiwa Amarya a bata haƙuri, Insha Allah ina nan tafe mu gaisa, Kaikuma Aminu se Fiddausi ta haihu ma haɗu" 


Ammar yace "to mungode zan gaya mata Insha Allah, sannan Adinga haƙuri ana kai zuciya nesa saima, a unguwar mu babu wanda be san Soyayyar ku da Jabir ba, be kamata ace daga yin Auren ku hakan tana faruwa ba" 


Murmushi me ciwo Saima tayi tace "Ammar kenan, Soyayyar nan duk a baki ce ya nunamin, kudai ina muku fatan Alkhairi ku gaida gida" ta juya ɗakin ta tana sharce hawaye. 


Ammar yake tunanin ita kuwa wani irin pain take ji a zuciyar ta har take wannan kukan haka. Su kayi wa Jabir sallama suka tafi, seda Ammar da Aminu suka ƙara tattaunawa akan batun, Ammar yace 


"gaskiya Aminu lamarin rayuwar nan akwai ban tsoro, shiyasa naita gudun yin Aure a baya" 


"Ammar kenan, ai abun dace ne, kaga ni babu wata babbar matsala da nake fuskanta tsakanina da fiddausi se tarkacen ƙawaye da yawon maƙota, sune babbar matsalar ta, nayi nayi ta dena taƙi, Amma ta wani ɓangaren idan na duba alkhairan ta se in share ta kawai inyi haƙuri tunda nima haƙuri take dani"


Suka gama taɗinsu sannan Ammar ya nufi gida, ya ɗan tsaya a hanya yaiwa Mufeeda siyayya, sannan ya tafi gida, tunani yake tayi ya gano me Mufeeda take yi wanda baya so, amma ya kasa ganowa se yai tunanin ko dan Yarinya ce, ko kuma tana jin tsoro nane yasa bata min wasu abubuwan? Ko dan bamu daɗe tare ba? A'a wannan Yarinyar da tana jin tsorona da bata tunkareni ta kalli tsabar idona tace tana sona ba wata zuciyar ta bashi amsa. 


Da wannan tunane tunanen yaje gida, se daya duba agogonsa yaga sha ɗaya na dare. 

Aikuwa yana shiga tana falo a zaune tana rarraba ido, tana ganin sa ta miƙe

"Yaya Ammar ina ka tsaya haka? Har na fara tsorata ko wani abun ne ya same ka" 

"Sarkin tsoro, ba abunda ya sameni gani na dawo" 

"gaskiya ka daɗe sosai" 

"Ai gani na dawo dai, ya jikin naki?" 

"Naji sauƙi Alhamdilillah" 

"Haka ake so, ungo gashi nan ki samu Kisha, tunda yau baki ci Abun kirki ba" 

Ƙatuwar Jarkar yoghurt ce a ciki, 

Murmushi tayi tace "Masha Allah, Nagode sosai mijina Allah ya baka Aljanna maɗaukakiya, Yasa ka gama da duniya lafiya" 

"Ameen" 

Ta ɗakko kofi ta zubawa Ammar ta bashi yace shi baya sha, ita dai ta sha ya sata a gaba ta sha sosai sannan ta ajiye sauran. 

Ta kalle shi tace "Mijina meke damunka ne? Naga kaman akwai damuwa tare da kai" 

Kallon ta yayi da mamaki ya akai ta gane yana da damuwa. 


Ya maze yace "gajiya ce ni babu wata damuwa dake raina" 


"idan gajiya ce kawai take damun ka ina ganewa, yau yanayi ya nunamin bayan gajiya akwai damuwa" 


Miƙewa yayi yace "jeki kwanta seda Safe" 


Bayan sa tabi da kallo daga bisani ta miƙe ta tafi ɗakin ta, yau ta sha baccin rana, saboda rashin lafiyar ta, dan haka ta kasa bacci, tana ta tunanin meke damun Ammar? "dole inyi wani abu kar ya kwana da damuwa. 


Ta ɗakko wayar ta tura masa saƙo 

"My love, hau online kaga wani abu" 


Ya tura mata "me kike baki Bacci ba?"


"Nakasa baccin ne, ka hau ka gani"


Ya buɗe data ɗinsa ya shiga what's App, hoton ta ta tura masa, tayi wa gashin kanta ado, ga wata body hook ce a jikin ta pink, leɓen ta raɗau da jambaki se shining yake, ta ɗan turo baki ta lanƙwasa wuya, a haka ta ɗau hoton ta ɗora waƙa me daɗi akan hoton.


Ammar na buɗe hoton besan lokacin da ga tura mata

"Wow Masha Allah"

Wani murmushi tayi tana daga kwance ta tashi zaune, ta tura masa

"Nayi kyau?"


"Ba laifi kin kusa yin kyau, dama kin girma ne da se yafi kyau"


Sosai Mufeeda tayi dariya, baze ce tayi kyau ba sedai ya kushe ta.


Ta tura masa

"Mijin baby wani jambaki yafi min kyau?"


"kowanne" ya bata Amsa.


"shikenan gobe idan na saka zaka ce nayi kyau?"


"ba tabbas dan ba wani kyau kike ba idan kin saka, seki koma kaman 'yar ƙauye" ya rubuta yana murmushi.


Emoji ɗin haɗe rai ta tura masa tare da "nice mummuna ko? Sena gayawa Umma kana cemin mummuna"


"Ke ki kwanta dare yayi fa"


"to My love, you do your task very well today ka kula da Jaririyar ka, nagode sosai Allah ya ƙara Arziki, da naso inyi fushi saboda kasa anmin Allura, amma bazan iya ba nagode sosai da kulawar ka miji nagari, Allah ya barmin kai har ƙarshen rayuwa ta"


"Me a daidaita sahun kike so har ƙarshen rayuwar ki?"


"Ko sana'ar da kake bata kai ta a daidaita sahu ba, ai halal kake nema, kuma ni ba sana'arka ce a gabana ba, kai nake so Ammar ɗina"


Tayi mai voice message kaman me raɗa take cewa "I love you my Ammar have a nice dreams"


Shiru Ammar yayi yana jujjuya wayar a hannun sa yana kuma duba chatting ɗin sa da Mufeeda.

Murmushi yayi ya kwanta wani daddaɗan bacci yayi awon gaba da shi.


(to su Yaya Ammar ko an faller ne🙄🙄🙄)


Ina godiya da ƙauna da kulawar ku.

Ƙofata a buɗe take, domin gyara sharhi, ko kuma shawara nagode sosai 😍 😍 😍 and please don't forget to vote and Comment 

Ayshercool

*** 


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.