Free chapter · Read without an account
E8
by Diamond deejarty · SHU'UMA
*SHU'UMA*
_Yar mutan zazzau Naanarh M Sha'aban_
*Sadaukarwa ga Yaayana d'an baiwa*
_Nagode sosai da comments d'inku na ji dad'i, wanda na gani da Wanda ban gani ba duk Ina godiya, One Love♥️_
*ROYAL STAR WRITERS ASSOCIATION*
Ku sauke Arewabooks a playstore masu iPhone ku shiga ta website, idan na gama posting d'in book 1 chan zamu koma book 2.
Website
Arewabooks.com
Follow me
http://arewabooks.com/u/shaabandaughter01
Book 1
E8
Suna Isa gidan, gaba d'aya sojojin suka zagaye gidan kowannansu hannunsa rik'e da bindiga, Captain Sani ne ya k'arasa k'ofar gidan ya shiga sallama, Habu ne ya fito yana zazzaga masifa "Wai wad'anne irin mutane ne na had'u da su a unguwar nan kullum sai an zo min maula" Tsayawa yayi cak ganin yana zuro kansa waje sojoji suka damk'eshi.
"Ina matarka?" Wani daga cikin sojojin yayi magana yana zare masa ido, kallo d'aya za ka yi masa kasan babu imani ko kad'an a fuskarsa, gashi bak'i ne wulik idanuwansa jajur, gashi k'ato, Habu cikin rawar baki yace "tana cikin Amman dan Allah yallab'ai mai mu ka yi muku haka da zafi, karku manta ni d'an gidan Alhaji Sule ne fa, zaku iya shiga babbar matsala idan ku ka ce zaku kamani, idan wani abu ku ke so, ku fad'a sai na ba ku dan ku Allah ya hore mana arzik'i" Wani irin gigitaccen wari wannan sojan ya d'aukeshi dashi, wanda sai da Habu ya dawo baya ganin komai sai duhu na 'yan wasu dak'ik'u, kafin ya gama farfad'owa daga hayyacinsa Commissioner ya d'ora masa da na sa, dukan tsiya yayi masa, musamman ma fuskarsa ta sha bugu dan har sai da bakinsa da hancinsa suka fara zubar da jini, ya daddage ya gwara kansa da tayals d'in k'ofar gidan wani irin ihu Habu ya saki, duk wannan dukan da yake sha Sojojin nan guda uku suna rik'e dashi.
"Ka ga alamar mu d'in irin wad'annan mutanan ne masu karb'ar cin hanci, kamar yadda ka yi laifi dole ka fuskanci hukunci dan ko ubannaka ne yayi laifi cin ubansa zan yi sai ya fuskanci zazzafan hukuncina"
Wasu sojoji mata commissioner ya kalla ba tare da ya kira sunayensu ba yace su shiga su fito masa da matar Habun, suka shiga gidan ko mintina biyu ba su yi da shiga ba, suka fito tare da Asabe, kai tsaye bayan mota suka nufa da ita suka jefata, dan Habu ma sun riga da sun sakashi, Asabe tana ganin Habu jini yana ta zuba ta ko ina ta zaro ido, tabbas tana jin ana cewa soja ba imani, Amman bata yarda ba sai yau, dan kuwa har fuskar Habu ta fara sauyawa, (ni kuwa nace ai hakan yayi min daidai wallahi😂)Cikin mintina goma sha biyar suka k'arasa barikin sojoji, inda suna zuwa suka zubesu cikin wani d'aki mai bala'in duhu, suka kulle k'ofar.
°°°° °°°° °°°°
Abba suna dawowa gida Khadija ta mik'e ta nufi gurinsu tana tambayar "Abba ya na ga kun d'aukoshi, Dan Allah ka yi min bayani"
Abba yace "kwantar da hankalinki yana lafiya Malam Ado yayi masa addu'o'i har ya basa ruwan addu'a ya sha shine yana sha ya kwanta wannan baccin" ajiyar zuciya ta sauke sosai, "Alhamdulillah Allah nagode maka, Abba to a kai shi d'akina tunda d'akinshi duk ya hargitsashi sai na gyara masa yanzu" Abba yace "to bari mu kai shi chan d'in" Muhammadu driver ya kama Nazeer suka shige d'akin Khadija suka kwantar dashi kan gado, Khadija ta shiga murmushi ko banza dai ta fara koyawa Nazeer hankali kuma ta nuna masa cewa ita d'in ta ci dubu duk inda yake tunaninta ta huce nan, zama tayi kan cinyar Mummy tana dariya "Mummy Yaaya ya ji sauk'i" Mummy ta shafi fuskarta tace "eh Khadija ya ji sauk'i kuka ya k'are" Fitowar Abba ne yasa Khadija ta sauka daga kan cinyar Mummy zama yayi yana cewa "wash yau mun sha fama" Khadija tace "sannu Abba'' Mummy tace "Sannu Abban yara" Abba yace "yauwa bari na huta sai mu tafi" Abba yayi magana yana kallon Muhammadu yace "nagode Muhammadu ka jiramu a waje yanzu zamu fito ku tafi" Muhammadu yace "to Alhaji bakomai" yayi maganar tare da ficewa, hira suka yi ta 'yan mintina suka tashi suka yi wa Khadija sallama suka fita duk da yadda Khadija ta so ta rakasu, Abba yace "ta zauna ta huta ba sai ta rakasu ba" haka ta hak'ura ta zauna akan kujera tana kallo.
Wacece Khadija Shu'uma? Kuma wanene Nazeer?
Da mahaifin Nazeer Alhaji Adam Kamshi, da mahaifin Khadija Malam D'alhat Kamshi uwarsu d'aya ubansu d'aya, 'yan asalin garin K'aura goge ne, su biyu iyayensu suka haifa mahaifin Nazeer shine babba sannan mahaifin Khadija, Allah ya sakawa Adam son yin karatun nasara wannan shine dalilin da yasa ya nemi wata makaranta a garin Kaduna ya fara tun daga sakandare, babu irin yadda bai yi da d'an uwansa D'alhat akan shima ya zo ya fara, Amman sam D'alhat yace baya ra'ayi ya fi son yayi aurensa, haka Adam ya hak'ura Amman ba dan ya so ba, dan ya fi son kullum ya ganshi tare da d'an uwansa, a lokacin da Adam ya kai aji biyar a sakandari aka saka ranar D'alhat wata hud'u shi da 'yar gidan mai gari Ladidi, murna gurin Adam ba'a magana, ranar wuni sukayi suna waya da d'an uwansa yana tsokanarsa, haka dai suka rabu kowannansu yana kewar d'an uwansa, hausawa sun ce rana bata k'arya a kwana a tashi ba wuya a gurin mai sama, yau sauran kwana uku a d'aura auren D'alhat, Adam tun ana sauran kwana ashiri ya dawo k'auyen K'aura goge, komai na bikin Adam ne yake yi tamkar shine angon.
Washegarin ranar da za'a d'aura aure, Baffa ya zaunar da su Adam a cikin bukkarsa, shuru ne ya d'an shiga na wani lokaci kafin yace "Adam kai ne babban d'ana zan so ace yau Allah ya nuna min aurenka kafin k'asa ta rufe min idanuwana, wannan dalilin ne yasa na yanke shawarar had'aka aure da Safara'u d'iyar abokina Saminu, insha Allahu gobe za'a d'aura auren tare da na d'an uwanka".
Anan zan dasa aya.........✍️
*#Comments*
*#Share*
*#Book 1*
*_(