Free chapter · Read without an account
chapter 20
by Zainab Yerima · MURADIN RAI
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*MURADIN RAI*🦋🦋🦋🦋🦋🦋
_*Dedicated to MARDIYYA LUMANA*
_Afrahabdul my best wattpady, wannan page din nakine, naji dadin sake ganin ki❤️🥰_
By: *ZEETY*💞
*wattpad @Zeety-AZ*
karku manta ina sauraron votes dinku a wattpad 👆🏻
20📚
Tunda aka kama hanya mardiyya batada aiki sai kuka har aka isa, tasha mamaki lokacin data fito a mota, har zata wuce ta hango motan Abbas, ta mayar idonta ne, amma ga mamakin ta shi ta shi ta hango aciki, sosai zuciyar ta ta buga, driver ne yace mata hajiya mu karisa ko, gaba yayi tana biye dashi a baya.
gida ne me madaidaicin kyau, saboda a ƙauyen ma irin gidajen goggo kaɗan ne, da sallama suka shiga, wata tsohuwa suka samu akan kujera a tsakiyar gida wa driver ta ansawa da fara’ar ta, ko kallon inda mardiyya take batayi ba, ɗakin dazai kwana ta nuna mishi tana cewa ai tun dazun ku nake jira saboda sabir (sunan Abban mardiyya kenan) yacemin kun kusa isowa, eh wallahi don ai tafiyan dare ne banson inyi gudu nafison in taho a hankali shiyasa mukayi dare, hakan ma ba laifi ai gudun bashida amfani…
Kayan hannu shi ya nuna mata yace wannan kayan mardiyya ne ina zan kai mata, wani ɗan akurkin ɗaki ta nuna mishi tace kasa mata anan.
Saida tagama dashi sannan ta dawo kan mardiyya, ɓata rai tayi kamar ba ita bace tagama dariya yanzu… harara ta zabgawa Mardiyya wanda tasata sunkuyar da kai ba shiri.
Munafukar banza sunkayar dakan me zakiyi, bayan kin gama nunawa duniya rashin kunyan ki…. Ai mu zuba nida ke saina seta miki hankali kuma a ƙauyen nan zan nema miki miji keda zaman birni kam kunyi bankwana kodon ma yabzu kam a birni ma babu wanda zai kwashi tamba ɗaɗɗiya.
Hawaye ne masu zafi sukafara bin fuskar ta, tsabar kukan da tayi yau ji take kamar kanta zaifashe.
Ga ɗakin ki nan maza ki shiga ki ɓacewa ganina…
sum sum ta wuce kamar wacce kwai yafashewa aciki.
Goggo itace mahaifiyar Abban mardiyya, masifeffiyar mata ce, duk da tanada daɗin zama, dama can babu wani shiri tsakanin ta da mardiyya, tunda ta tashi ko irin wasan jika da kakan nan bata mata… tsanan ta ga mardiyya yasamo asali ne tundaga kan mahaifiyar ta saboda lokacin auren su da Abba goggo taso ya auri yar kawarta amma fir yaƙi wannan dalilin yasa ta tsani maman mardiyya kuma ko da ta rasu ma baisa zuciyar goggo ya huce ba, saita maida tsanar nata akan mardiyya…
Koda ta shiga ɗakin kuka ta fashe dashi, saida taji zazzaɓi ya rufa mata sannan ta tsagaita, fitowa tayi taje bayin tsakar gida saboda ɗakin da aka sata ba toilet aciki.
Ruwa takama sannan tayi alwala, ko da tazo salloli tafarayi… tana idarwa wani yunwa ne taji yana murɗa mata ciki, dubawa tayi taga babu abinci gashi tana tsoron zuwa kitchen kar goggo tajita, tunowa tayi da ta tattaro su chocolate ɗinta dasauri taje ta buɗe akwatin ta, cimar tuwo ta musu har saida taji sun cika mata ciki.
Abbas ne ya faɗo mata, kirjin ta ta dafe tace kaddai a mota zai kwana? Watakila ma baici abinci ba? Yazanyi insan halin da yake ciki? Gashi babu ko waya ko a hannu ta… kai da gwiwa ta haɗa, tanajin aranta duk abunda yasamu Abbas itace sanadi.
Tunda sukaga shigansu Abbas yace tunda munga gidan datake, muje mu nemi masauki kafun musan abunyi, wani suka samu yana tafiya suka mishi sallama sannan suka tambaye shi inda zasu samu lodge, kwatanta musu yayi suka mishi godiya sannan suka kama hanya.
Da dare ya harun yasamu baban su ya sheda mishi gaskiya yafasa auren mardiyya… take ran baban su yabaci, yace haruna wannan wane irin maganan banza ne? nizaka maida mutumin banza, kasan bakason ta kasani a ciki…
Shuru harun yayi bai iya cewa komai ba.
Jeka kiramin maman ku, harda zainab tazo don itace wakiliyar mardiyya a gidan nan.
Tashi yayi jikin shi babu ƙwari, wani ɓangare na zuciyar shi yanajin bazai iya zama da mardiyya ba, wani bangaren kuma yanajin bazai rayuwa babu ita ba, kwata kwata zuciyar shi babu daɗi, yanaji aranshi mardiyya tana ɗaya daga cikin jarrabawan rayuwar shi.
Tare suka dawo dukansu, kowa ya zauna sannan baban su yace kinsan abunda yake faruwa tsakanin haruna da mardiyya? Cikin yanayin rashin fahimtar abunda yake faruwa tace ban sani ba, wani abunne yafaru?
Hmmm gashi nan yagaya miki da bakin shi..
Zeezee takalla sai wulli wulli takeyi da ido kamar marar gaskiya sannan ta maida dubanta ga harun tace inajinka babana meyake faruwa?
Baban su yakalla sannan ya sunkuyar da kanshi yace maa dama akan maganan mu da mardiyya ne…..
sai kuma yayi shuru, cikin tsawa maa tace meye hakan kasamu a gaba kana janjanin magana kamar wani yaro…
zeezee kam tuni hawaye yafara wanke mata fuska, haushin harun ne fal a ranta, tanajin fa zata iya tsanan shi akan wannan case din.
Inajinka idan kuma bazakayi magana ba sai mu watse…
Dama na janye maganan auren mu ne…
meye? Kanada hankali kuwa? Meyafaru? Meye dalilin ka?
Baban sune yace yauwa yanzu kika iso daidai wajen dazai mana bayani… shuru yayi yana tunanin anya kuwa zai iya faɗa musu asalin abunda yafaru, ko bakomai bai kamata ya tona mata asiri ba, amma kuma yaya zaiyi, idan bai faɗa ba laifin duka kanshi zai dawo…
Saida maa tasake kufula sannan ya kwashe duka abunda yafaru yagaya musu….
Shuru kowa yayi sai can baban su yace nifa kaina yakasa ɗaukan abunda kakeson faɗa saboda mardiyya tarbiyan muce, duk da bamu muka haifeta amma munsan yanayin tarbiyan ta don anan suka girma tsakanin nan gidan da gidan su,
aima Alhaji ba wannan ba, meye shedan shi akan labarin da yake faɗa? Wayan shi ya ciro ya nuna musu video maa kam jikinta duk yayi sanyi, baban su ne yace wannan ai hidiman kayan na’ura ne watakila haɗawa akayi da fuskarta domin a ɓata mata suna…
haba Alhaji kana ganin abu da idon ka kace haɗawa akayi, gaskiya mardiyya ta ban kunya.
Karkiyi saurin yanke hukunci wataran kizo kiji kunya, nidai haruna kabuɗe kunnen ka kajini, dama wani lokaci mutun baya samun maƙiya sai maganan auren shi yatashi, zan baka shawara dakar kayanke hukunci cikin gaggawa katsaya ka saurari meye zuciyar ka zatace ma, kuma meye zai sake biyo baya acikin gari, karkazo kayi aikin dana sani.
Taran shi maa tayi dacewa gaskiya Alhaji bazaiyu ba, abunda ya faru ya riga da yafaru kawai kaje kagayawa baban ta yafasa ni bazan bari haruna ya aureta ba….
Sai lokacin zeezee tasamu daman yin magana cikin kuka tace wallahi maa sharri ne, karkiwa mardiyya haka, ta ɗaukeki kamar uwa, idan har kika yadda da wannan abun nima duk randa haka yafaru dani zaki yadda kenan…
Ke da Allah rufe mana baki, banason shashanci, idan kika kuskura ki ka aikata makamancin haka wallahi yankaki zanyi…
Ya isa haka, kedai yanzu kin goyi bayan ɗanki ko? Toh shikenan zanyi yadda kukeso, amma kusani duk abunda zaije yadawo ni babu hannu na aciki, zo nan mama na kidaina kuka kinji nima ko kaɗan ban yadda ba kuma Allah na tare da ita kinji, kifa kanta tayi a kafan baban su, shi kuma yana shafa kanta, harun kam fita sukayi da maa.
Haka farida tayita sa ido har ƙarfe sha ɗaya amma shuru babu labarin ya Abbas fargaban kar yabar gidan ne yahanata bacci, duk yadda taso bacci ya ɗauketa abun ya gagara, bata taɓa tunanin tana mishi so me tsanani ba sai wannan lokacin, inya daina kulata yaya zatayi? Ballema tayi tunanin auren shi… zuciyar ta take ta buga, yanzu me zatayi wanda zaisa ya aureta, zabura tayi ta mike tafara safa da marwa a ɗakin, har asuba yayi bata samu mafita guda ɗaya ba.
Tunda suka samu ɗaki, suna shiga nabil kam yanayin salloli bacci ya kwaɗeshi agun ko abinci bai ci ba tsabar gajiya.
Abbas kam dayagama duk abunda zaiyi saida yakwanta yaji bacci ya kauracewa idon shi, tunanin yadda zaiyi ya ɓullowa lamarin mardiyya yafarayi… toma me zaiyi? Babu wanda zai yadda dashi matukar baiyi proving innocent dinsu ba, ta ina zaifara?
Dole farida ce zata fallasa komai da bakinta, amma yaya za’ayi yasata tayi hakan… huci yayi sannan yatashi yafara sintiri a ɗakin, shi yanzu ko ƙaunar ganin farida bayayi, ballema yadda take bibiyan shi da sharri… baisan metake nema agun shi ba… kodai zaiyi mata soyayyar karya ne? kai ina bazaiyu ba hakan zai iya sashi acikin wani hali, duk abunda zata faɗa akan shi mutane zasu iya yadda… tunda yake bai taɓa ganin sheɗanin mutun irin farida ba.
A wannan daren dai babu wanda yayi bacci me daɗi acikin duka wayanda abun yashafa.
Asuban fari goggo taje tana bugawa mardiyya ƙofa kamar zata ɓalla shi, a firgice ta tashi, tana buɗewa tace mata a gidana ko kafuri ne yazo sai yayi sallah , sai ki tashi lokaci yayi idan kinyi sallah kuma ki jawo ruwa a rizabuwa ki cikamin randan tsakar gida, kiyi shara kiyi wanke wanke duka inason ki gamasu kafun rana ya fito, zakiga tuwo a kitchen ki dumama ki dafawa driver ɗan wake ki dama mana kunun tsamiya, ban yadda kici komai acikin abunda zaki haɗa ba sai dumame idan kuma kikaci zan gane, sannan in sheda miki na kori duka masu aikin gidan nan daga yau ke zakinayi komai.
Tana kaiwa aya tasa kai tawuce side ɗinta, mardiyya kam binta da kallo kawai tayi tana tunanin anya kuwa dagaske ta haɗa jini da matar nan, meyasa ta tsaneta dayawa haka.
Zeezee tun safe take tunanin ta ina zata ɓullowa lamarin gashi batada numban Abbas, balle taji daga gareshi, karshe dai yanke shawaran zuwa gidan su farida tayi ko zata sameshi sannan kuma ko zata gane wani abu daga gurin farida.
Kafun karfe tara mardiyya tagama komai don driver su kam ma har ya kama hanyar kano, haka goggo tazo tanata dube dube a kitchen ko mardiyya taci wani abu bayan dumame, saida tagama dube duben ta sannan tace mata gacan kayan wanki nafito miki da su amma kafun nan, kije ki gyaramin daki na tukunna.
Sallama akayi jin muryan wanda yayi sallamar shiya tsinkawa mardiyya zuciya… don ko a mafarki taji tasan waye ne, fitowa goggo tayi tana ansawa itama bayanta ta biyo.
Da fara’a goggo tace mishi a ah samarin bautan kasane yau a gidan namu, Allah yasa dai ba masu karɓan kuɗin wuta bane…
murmushi yayi tareda cire face cap ɗin nysc dake kanshi, yace a’ah kaka wannan me zuwa cin ɗumame ne, dariya tayi sosai tace ai indai ɗumame ne kasamu harda manshanu ma zansa ma…
haka kawai goggo taji yakwanta mata arai, dan saurin ya shiga ranta.
Juyawa tayi tacewa mardiyya kin tsaya kina kallon mu maza ki kawo mishi tabarma sannan ki zubo mishi ɗumame ki kawo mishi da man shanu da yajin daddawa, kuma ki hanzarta banason nawa..
Dasauri yace a ah kaka wasa nakeyi nakoshi, wani kujera yaja yana cewa nan ma ya isheni.
Baza ayi haka ba, je ki kawo mishi… kitchen tawuce yabita da kallo ganin yadda ta lalace a rana ɗaya kawai.
Zama goggo tayi suka gaisa sannan tace ɗan samari meke tafe dakai?
Gyara zaman shi yayi sannan yace ina wucewa ne kawai jikina yabani inada kaka anan gidan shine na shigo domin gaida kaka ta, dariya goggo tayi sannan tace Allah ya haɗani da ja’irin jika, nidai addu’a ta Allah yasa ba kuɗi kazo karɓa ba, ko kaɗan bazan karɓi kuɗi a wajen kakata ba.
Kayan karyawa mardiyya takawo mishi ta ajiye, binta yaketayi da kallo itama data ajiye saida taɗaga ido takalleshi…
Haka suka cigaba da taɗi da goggo ita kam ciki tawuce tagyarawa goggo ɗakinta, shikam tuntuni yagama cin abinci kawai yana jira mardiyya ta fito ne yasake ganinta.
Har ya hakura zai tafi saboda kar goggo tagano shi saigashi tafito.
cikin masifa goggo tace maza kizo kiyi wankin nan kafun rana yayi ki ɗaura abincin rana..
Dasauri yace kaka ki bari zan miki, a ah kabarta tayi batada wani abunyi banda ayukan gida… a’ah kaka to ainima inason insamu ladanki, haka sukayita ja karshe dai harta hakura tabar mishi… amma duk da haka cewa tayi mardiyya bazatayi zaman banza ba don haka tazo ko ɗauraya tana mishi, tashiga ɗaki tabarsu, kallon juna suka fara bako kyafta ido……
*ZEETY DELIGHT*💖