Free chapter 路 Read without an account

PAGE__1

by Muhammad Sani Aliyu 路 SAI DAKE!

馃拵 _page 1_馃拵


*SAI DAKE!*馃珋

    _written by_

*BILLY S FARI馃拵*


漏 *HASKE WRITERS ASSOCIATION*馃挕


_Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhuun馃槏 gaisuwa da fatan alkhairi agareku masoyana abun alfaharina, Ina Mai farincikin sake dawowa da had'uwa daku acikin wannan sabon littafi nawa mai suna *SAI DAKE!*, littafin da zaizo maku da wani irin qayataccen salo mai matuqar burgewa, *SAI DAKE!* littafine da zai ilmantar daku, ya fad'akar daku had'i da kuma nishad'antar daku ta hanyar da ni daku zamu amfana dashi tare da ribantuwa da d'imbin darussan dake ciki, Ina fatar zaku karb'esa hannu biyu kamar dai yanda kuka saba nagode馃馃徎, *SAI DAKE*馃珋 qirqirarren labarine dana zauna na tsara da kaina domin farincikin masoyana, don haka ban yarda wani ko wata su juya min shiba tako wace irin siga har saida izinina, yin hakan kuwa babban kuskure ne da zaisa na qalubalance ki/ka akan haqqina, don ALLAH akula_馃憦馃徎 

    馃拵馃拵馃拵馃拵


Tunda ALLAH ya wayi safiyar yau yake kwance bisa makeken gadonsa na alfarma yana baccinsa hankali kwance ba tare da yayi tunanin akwai wasu abubuwa masu muhimmanci da ALLAH ya haliccesa don su arayuwarsa ba, Sallah itace abu mafi muhimmanci na rayuwar d'an Adam da ALLAH ya haliccemu domin ita kuma ya umurcemu da yinta da kuma kiyayeta kuma ya sanyata wajibi ga kowane mutum musulmi namiji da musulma macce, ya umurci mu bauta masa da ita acikin yanayin Safiya, Rana da kuma Marece, sannan ya sanya mana ita abar kiyayewa acikin dare ga bayinsa masu neman tsira agobe qiyama, yayinda shi wannan saurayi mai suna RA'EES dake kwance tun daren jiya yana shark'ar baccin har zuwa yanzu da qarfe d'aya da rabi na rana (1:30pm) ya soma yi ya d'auketa abar wasa kuma ba abakin komai ba awajensa, matuqar yana abubuwan daya d'aukarwa kansa cewa sune jin dad'in duniya da rayuwarsa to tabbas baya tuna duk wani abu mai muhimmanci da aka haliccesa donsu kamar Sallah.


RA'EES haifaffen d'ane ga fitaccen d'an siyasar nan da yayi qaurin suna ako ina qauye da birni dake cikin garin kebbi mai suna Alhaji sulaiman sadam sada wato (SS Sada) kamar yanda akafi saninsa dashi, wanda yanzu haka shine d'an majalisar dake riqe da wasu yankuna acikin garin, shi mutumne mai matuqar fad'in rai, izza, son kai da kuma isa ganin yanda yasamu wani d'an qaramin cikin cokalin mulki aduniya, sam bayada tausayi ko imani ga duk wanda ya nemi shiga gonarsa balle bibiyar al'amurransa, idan kuma yasa abu agabansa to tabbas sai ya cimma burinsa da muradansa akai hankalinsa ke kwantawa, shiyasa abokanan hamayyarsa ke matuqar shakkunsa tare da girmamasa awani b'angare wanda babu shakka ko tantama kusan rabin halayyarsa ce tayi tasiri arayuwar babban d'an nasa da yake matuqar so fiye da komai aduniya, indai akan Ra'ees ne zai iya aikata komai kuma zai iya b'atawa da kowa, tsakaninsa dashi sun koma tamkar bawa da uban gidansa, ya shimfid'a dukka rayuwarsa washi shiyasa yakeyin duk abunda yaga dama kuma yakeso acikin garin batare da shakku ko tsoron kowa ba, hatta hukumomi manyansu da qanana girmamasa sukeyi kuma sam basa shiga al'amurran rayuwarsa, duk wani ji da kai da mugun hali na mahaifinsa ya gadosa koma nace yana nema ya zarcesa saboda sabon jinin samar taka dake yawo ajikinsa, 


A 'daya b'angaren kuma na rayuwarsa shi da mahaifinsa akwai wata jigo atattare dasu da ako yaushe ke neman ganin ta saita rayuwarsu izuwa kamilalliyar rayuwa mai cike da nagarta da mutuntaka, ba kowa bace wannan jigo face maihaifiyar Ra'ess mai suna hajia Hafsat, macece da duka d'abi'unta da halayyarta sun sha banban dana mijin nata dashi kansa d'an nata Ra'ees, shiyasa duk lokacin da take tufqarta akan yaronta sai ya zamana mahaifinsa ke warwarewa har yake alaqantata da rashin son d'an nasu da son takura masa wanda shi sam baya son haka,


Ra'ees shine babban d'ansu wanda bai dad'e da jimawa da dawowa ba daga qasar Paris bayan kammala karatunsa na master's acan, daga shi sai Aryan da Aryana wud'an da suka kasance 'yan biyu, yanzu haka suma suna qasar UK suna had'a degree d'insu a b'angaren law, sai Musaddeq dake bimasu shima yana a jami'ar sokoto d'an fodiyo saboda shi sam bayada ra'ayin fita waje karatu, sai kuma Easha dake matakin scondry aji hud'u a yanzu da kuma d'an auta sadam (Abbie) da kwata kwata shekarunsa yanzu bazasu wuce bakwai ba, dukkaninsu 'ya'yan hajia hafsat ne data haifa da cikinta wanda kusan haihuwar tayita ne kusa da kusa shiyasa babu wani tserewa sosai tsakaninsu ko a karatu, musamman a tsakanin Ra'ees, Aryan da Aryana da kuma Musaddeq, dukkaninsu tana son abinta kuma tana qoqarin basu tarbiya daidai gwargwadon iyawarta kuma ba laifi suna bi in banda Ra'ees daya zamo mata kwan d'ararre acikinsu.


Fitowarta kenan daga cikin d'aki sanye da hijab bayan ta kammala sallar azahar tana bitar azkar abakinta ta nufo katafaren falon dake laqe da d'akin nata yaji ado da kyawawan kujeru masu matuqar d'aukar hankali kalar dark blue da ratsin ruwan qwai asaman katakon jikinsu sai qyalli sukeyi, hatta labulayen dake jikin qofofi da tagogin falon kansu dark blue ne, kai kusan komai ma dake cikin falon kala d'aya ne wanda tayi matuqar yin kyau fiye da tsammani, a gefe kuma ga wata irin makekiyar tv dake laqe ajikin bangon d'akin daga arewacinsa wacce idan kana kallo zaka d'auka mutanen dake cikinta zasu iya fitowa, duk inda ka kalla a d'akin masha ALLAH an qawatasa sosai yanda daka gani kasan tsarin na manyan masu kud'ine da 'ya'yan banki zuka zauna masu, tako ina qamshi ke tashi tamkar anyi b'arin turarukka.


D'aya daga cikin kujerun dake falon ta nema ta zauna fuskarta d'auke da murmushi tana kallon d'an autan nata dake zaune yana kallo ba tare da yasan shigowarta ba.


Hannuta ta d'ora akansa tace,


"Sannunka Abbie! anya kayi sallah kuwa?" Sai alokacin ya d'ago kai yana kallonta yace, "A'a Momy banyi ba, so nake film d'in nan yaqare, wlh ya had'u sosai"


"Subhanallahi, Abbie da bakinka kake fad'ar hakan? Halama baka tsoron ALLAH yayi fushi da kai kuma ya qonaka ne?"


"Momyyy..." Yafad'a a shagwab'e irin an takurasa d'in nan tayi saurin dakatar dashi had'e da d'aure fuska.


"Zan matuqar sab'a maka idan na koma jin wata kalma tafito daga bakin ka, maza ka tashi kaje ka shiga toilet d'in d'akina kayo arwala katafi zuwa masallaci" tafad'a had'e da kausasa muryarta daga qarshe hannunta riqe da remote d'in tana qoqarin kashe kallon had'e da harararsa.


"Sorry momy.." yafad'a tare da wucewa yana tangalar kai alamun yaji haushin kashe masa kallon da tayi, 



Murmushi kawai tayi had'e da cewa "Ubangiji Allah ya shirya mun kai Abbie yarabaka da wahala"


A gabanta yawuce bayan ya gamo arwala tare da cewa "Momy natafi"


"Adawo lafiya." Ta bashi amsa ataqaice, 


Bayan mintuna goma da fitarsa sai gashi yadawo har lokacin tana nan zaune a inda ya barta tana faman tunane tunane, muryarsa ce data jiyo ta fiddota daga duniyar tunanin data shiga.


"Momy wai yaushe dady zai dawo ne?"


"Har kagamo sallar?" Tabashi amsa tana qoqarin gyara zamanta akan kujerar,


"Eh momy na..." Kafin yaqara cewa wani abun tayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa, "Dady bazai dawo satin nan ba sai wani sati in sha ALLAH, lafiya kake tambaya?"


Kamar qwai ya fashe masa a ciki yazo ya zauna kusa da ita yana fad'in,


"Shiyasa ni bana son dadynah, nafi sonki momy!, kullum ke kike tare damu kina kula damu amma shi dady ko muna son ganinsa baya zama, momy wai ina yake zuwa ne da baya son ya zauna muyi fira da wasa dashi, kullum abokanaina Sai naji suna cewa babansu yayi masu abu, ya siyo masu ya kaisu wani wajen amma ni banda ni, kullum saida wasu su dinga yimun abunda ya kamata ace shine yake yimun, kodai baya so na ne!?"


"Kadena fad'ar hakan Abbie, dadynku na sonka mana, yana wajen aikinsa tare da sauke haqqoqan mutane dake kansa shiyasa hakan ke faruwa, kasanfa nauyin al'ummar dake kansa ba qarami bane kuma dole ya jajirce sosai domin ganin ya saukesa,"



"To Amma momy....."



"A'ah Abbie ya isa haka, daka dawo kaga yayanka a waje ko a masallaci?" Tafad'a tana qoqarin basar da wata tambayar da yake neman jefo mata, shigewa yayi a jikinta sannan yace


"A'a momy ban gansa ba."



"Oya maza tashi kaje d'akinsa ka dubomun shi, idan yana ciki kace masa ina kiransa"


Da gudu Abbie ya tashi ya nufi b'angaren yayan nasa, Yana shiga falon yayi tsaye yana dudduba ta Inda zai hangosa, ganin baya nan yasa kai tsaye ya shige cikin uwar d'akinsa, hangosa yayi kwance bisa gadon a duqunqune cikin wani lallausan bargo fari da yasha adon jajayen fulawowi ajikinsa, a hankali Abbie ya taka zuwan bakin gadon yana fad'in.


"Yaya, Yaya, yaya!" Sau kusan sau uku ya kirasa amma bai tanka saba kuma yana jinsa, ana hud'unne d'aya sake kiransa ya amsa masa cikin wata iriyar muryar dake nuna baccin bai ishesa ba yace "Ehmmm"



"Yaya Ra'ees wai kazo inji momy tana kiranka."


Nanma qyalesa yayi bai tanka saba ya cigaba da jero hammarsa tacikin bargon saboda wata irin azababbar yunwar da yakeji amma nauyin baccin yasa ya kasa tashi.


Ganin haka yasa Abbie ya hau kan gadon yana qoqarin janye bargon Ra'ess yayi saurin riqewa had'e da cewa


"Kaje kace Ina zuwa."



"To ka tashi mana Yaya, anfayi sallahr azahar a masallaci." Da yake a nan masallacin dake jikin katafaren qofar gidan nasu suke yin sallolinsu, ai kuwa a fusace Ra'ess ya daka masa tsawa yana fad'in,


"Yaushe nafara wasa dakai Abbie, zaka wuce ne ko sai na tashi na b'allaka gida biyu, banza kawai mai kan kwakwa" ya qarasa maganar yana sake jan bargon tare da duqunqunewa aciki,


Cikin jin haushin kiransa da mai kan kwakwa da Ra'ees yayi Abbie ya sauko kan gadon yana qunquni ya nufi qofa kamar zai fita, 'Dan d'ago murya Ra'ees yayi yanda zai jisa yace.


"Karufe mun qofar d'aki na.."


Bai qarasa rufe baki ba Abbie da ashe ya dawo cikin d'akin kawai ya jisa a saman jikinsa, kafin yayi wani yunquri ya ji bakinsa daidai kunnensa da qarfi yana fad'in.


"Yayaaaa....katashi momy na kiraaaaaa."


Wani irin juyi Ra'ees yayi sai ga Abbie dake qoqarin guduwa a hannunsa, turasa yayi cikin bargon had'e da matsesa jikinsa yana sakar masa soquna a kai,


"Wato na zama abokin wasanka ni zaka renawa wayo ko, to bari yau na fasa wannan kan kwakwan naka naga wanda zakayi rashin ji dashi gobe"


Cikin wata iriyar wahalalliyar murya Abbie ya saki qara da kai masa cizo a hannu saboda azabar matsa da soqunan da yake yimasa yayi saurin sakinsa yana fad'in.



"Wash! Ni ka ciza."


Daidai lokacin momy dake zaune taji sautin qarar Abbie da sauri ta isa sashen had'e da turo qofar d'akin, a yanda ta riski d'akin a hargitse da kuma breakfast d'insa da aka kawo masa har lokacin na ajiye agefe alamun ba'a tab'a ba, gashi ta hangosa kwance cikin bargo kamar yanda ta barshi da asuba, hakan ya tabbatar mata da tabbas d'azu data tadashi sake komawa yayi yai kwanciyarsa,



Ciki b'acin rai taqarasa shigowa cikin d'akin tana fad'in, "Ra'ees! Kar kacemun kaine akwance har yanzu! Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun, wannan wace iriyar rayuwace haka!"


A hankali ya shiga yane bargon dake lullub'e a fuskarsa, kyakkyawar fuskarsa ce tafara bayyana dake zagaye da gashi baqi qirin wato sidebars, yanayin cikar gashin yasa bazaka iya cewa ya kwanta a fuskarsa ba amma kana gani kasan ba kad'an yake samun gyara ba, matsa kaitan idanuwansa farare qal da suka surka da jaja jaja saboda baccin daya sha ya bud'e yazuba akan fuskar mahaifiyar tasa yayin daya fara motsa d'an qaramin bakinsa da yayi jajur tamkar wanda aka shafawa janbaki yana magana a hankali tare da had'e hannayensa biyu sama Yana sakin wata irin doguwar miqa.


"Oh my God!, Sorry momy wlh baccin ne yayimun nauyi banma san rana tayi haka ba." Ya qarasa maganar yana sake danna kan Abbie da hawaye suka jiqa masa fuska sharkat acikin bargon.


Da sauri ta qaraso bakin gadon ta yaye bargon ta riqo hannun Abbie ta sauko dashi kan gadon tana duban Ra'ees cike da mamaki da takaici, 


"Ra'ess dama ashe kaine kecin zalin yaron nan dana jiyo ihunsa!?"


Sinne kai yayi qasa had'e dasa yatsa yana sosa bayan kunnensa.


"Shikenan ka kyauta, nagode kaji ko?, Hop ka daiyi sallahr azahar?." Tafad'a tana kallon cikin idanuwansa da son gasgata abun da take zargi."


Yana qoqarin saukowa daga kan gadon ya amsa mata da "No momy banyi ba, yanzu nake son had'awa da asuba nayi duka"


"What!" Momy tafad'a tare da cewa Abbie yaje sashenta tana zuwa, Yana fita tarufe ido tayita zazzaga masa fad'a ranta duk ab'ace.


Cikin wata irin tafiyar dake nuna sam bayada wani qwari ajikinsa ya nufo Inda take da zimmar tab'ata tayi saurin ja da baya tana yimasa mugun kallon don ko tantama babu tasan akwai abun da yasha, tana wannan tunanin taji hannuwansa a saman kafad'arta yana fad'in,


"Momy sorry don ALLAH kisaki ranki ba wani abu bane, yanzunnan zan rankasu duka"



Wani irin wawan mari ta d'aukesa har sau biyu hawaye na zubo mata a fuska sannan tasa hannayenta ta ture nasa dake kan kafad'unta.



"Tir da halinka Ra'ees har yaushe ne zaka girma kasan haqqoqan ALLAH dake kanka?, Kasani kaifa ba qaramin yaro bane tuni aka manta da anbude maka naka littafi, duk abunda kayi za'a rubuta aciki mai kyau ko marar kyau, haka kuma ALLAH zai tambayeka kuma yayi maka hukunci akansu, aljannah da wuta duka suna jiranka kuma dole a d'aya zaka shiga, meyasa kazab'i yin wasa akan abudda aka halicceka don ka kuma za'a fara yimaka hisabi da ita?, Ra'ees meyasa ka zab'awa kanka wannan rayuwar bacin ba ita na d'oraka akaiba?, Meye laifina na zamowa mahaifiyarka daka zab'awa kanka rayuwar da duniya zata zageni na haihuwarkan da nayi?." 



"Momy." Yafad'a kansa aduqe ya dafe kuncinsa da hannu, duk rashin jinsa da rashin mutunci babu abunda ya tsana duniya sama da b'acin ran mahaifiyarsa, hakan yasa yakejin wani irin qunci azuciyarsa ganin yanda b'acin rai yasa take zubar da qwalla.


Zubewa yayi a gabanta qasan guiwowinsa yana bata haquri tayi saurin ficewa daga d'ikin batare data sauraresa ba.


Yajima wajen a duqe idanuwansa sunyi jajir kafin ya miqe ya Shuri gefen gadon da qafa Yana fad'in, "shet!"


Toilet ya fad'a ya fara watso ruwa yayo arwala, lokar kayansa ya bud'e ya ciro jallabiya sannan ya saka ya tada Sallah, Sai da ya tabbatar ya ranka sallolin sannan yafito ya nufi sashen momy, zaune ya iskota tan d'aurewa Easha kanta data Gama tsifa takasa d'aurewa fuskarnan tata babu walwal ko kad'an musamman da suka had'a idanuwa dashi, 


"Ina wuni Yaya Ra'ees." Easha tafad'a tare da miqewa tabar falon, har takusa fita taji sautin muryarsa da batasa ran zaya amsa tab'a yace.


"Lpy klw Easha, don ALLAH like ki gyaramun d'akina."


"To" ta amsa masa da ita ataqaice tare da qrasa ficewarta tana gunguni.


Shi kuwa agaban momy ya zube yana gaisheta ta d'auke masa kai kamar bataji ba ya shiga bata haquri kamar zaiyi kuka amma tayi biris dashi, da taga zai dameta Sai ta miqe zata bar wajen yayi saurin riqe mata hannu, "pls momy don girman ALLAH kiyi haquri na tuba bazan qara ba!"


Tajima tsaye tana kallonsa kafin ta koma kan kujerar ta zauna, gaba d'aya mamakin rayuwar d'an nata takeyi da yanda rauninsa baya b'oyuwa a duk lokacin da yaga b'acin ranta.




*ALLAH KA JIQAN IYAYENMU*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.