Free chapter 路 Read without an account

59

by Aisha Ahmed Machika 路 Namijin Goro

馃尡 *59* 馃尡



"Jiki Alhamdulillah dukkanninsu ansamu kansu akwai sauran rai atare dasu, da sauk'i sosai" likita ya amsa.


Aisai kowa ya fara hamdala, Hadiza hada hawayen dad'i tayi.


Wannan asibiti kuwa yau sunga turuwar mutane har saida suka rik'a korasu waje, Hajiya Uwa dama tunda ta iso asibitin take matsanancin kuka tana fad'in "nashiga uku ni d'iyar Iro, ya Allah kana gani, Allah karka kasheman yarona domin bazan iya jure rashinsa ba", nandai suka yita rarrashinta.


Duk wannan ikon Allahn dake faruwa Maijiddah na can gida rimin Gado, hatta Yabi dai dasu Ushe da wasu acikin y'an Uwanta sunyi zuga sun tafi sun hau mota zuwa kano amma banda ita, su Mariya sukayi juyin duk duniyarnan kan Maijiddah ta tashi su tafi amma sam tace bazata je ba, daga k'arshe ma sai tashi tayi tabasu wuri, ta tafi d'akin Khalil ta rufe ta rik'a kuka mai shiga rai.


************


Yaya ya tambayi likita zasu iya shiga su gansu, likita yace eh zasu iya amma kar a rik'a shiga da yawa saboda cinkoso da hayaniya.


Yaya shida Hajiya Uwa ne suka fara shiga, bacci suka tarar yanayi, Hajiya Uwa ta kwantar da kanta bisa k'irjin Khalil ta rik'a kuka tana fad'in "Auta ka yafeman, karka mutu ka barni don girman Allah, ohni ina zansa kaina?" Kuka take sosai, tun ana ganin hawaye har yazam babu.


Yaya ya shafa kansa yace "Allah ya baka lafiya Auta".


Bayan ya gama duba jikin d'an Uwan nasa, sai ya tashi ya lellek'a d'akunan kusa dashi inda sauran masu raunin suke, yagansu suma Alhamdulillah dukkanninsu jikin da sauk'i.


Haka mutane suka yita shiga d'aya bayan d'aya suna duba su, Jamil kam duk bayan mintuna kad'an sai Momy ta kirasa tace ya jikin Khalil, dayake tace zasu taho yace su bari asibitin cike yake, zuwa anjima sai yazo ya d'aukota ya kawota ta ganshi.


Hankalin mutane yayi mummunan tashi yadda duk baku tinani, had'a dani ma nan marubuciyar, haka rayuwa take wai ace duk taron mutanen nan saboda Khalil ne, ikon Allah kenan.


Duk wannan abubuwan da suke faruwa Kamal baya da masaniya akai, domin ko tunda yaba k'asar baya bai sake waiwayar kowa ba.


*******


Bayan su Yabi sun duba Khalil sai suka cema Yawale zasu koma dare nayi, ganin lallai dare yayi gashi ba motar gida zata kaisu ba yasa Yawale ya hana su tafiya, yayi waya can gida rimin gado yace da wani yaronsu yaje nan gidansa yace Maijiddah ta duba cikin wata langa fara mai flowers green nan d'akin Yabi ta d'auko masa wani makulli ta bashi ya kawo masa, data basa ya hawo mota yazo ya kawo masa, ba wani makulli bane wannan illa na gidansa da Marigayi ya basa.


Momy ma ta samu zuwa duba Khalil amma fa har dare be farfad'o ba, Hajiya ko nanan manne wurinsa sallah kad'ai ke d'agata.


Da yaron ya kawo ma Yawale makullin sai ya kira Jamil domin ya kaisu, tare da Yawalen suka tafi domin Jamil besan gidan ba.


Gida ne d'an maikyau, baza'a kirasa babba ba kuma baza'a kirasa k'arami ba, d'an daidai ne, kuma gini ne na kece raini na yayi, amma fa sai tarin k'ura, gidan nada buk'atar aiki na musamman, babu abunda ba'a zubama gidan ba, su gadaje, kujeru, kai komai dai da kuka sani, su Yabi suka karkad'e wurin da zasu kwanta suka samu suka d'an rab'a suka kwanta, abunku da mutanenmu su babu ruwansu.


A Asibiti kam, sai da k'yar aka samu aka kori Hajiya Uwa zuwa gida don mata basu jinyar Maza, Jamil yace shi ze tsaya amma sam Yaya ya hanasa, yace duk su tafi ba damuwa gobe da safe sun dawo.


***


Caaan cikin dare Khalil ya farka, Yaya ya matso kusa dashi da sauri yace "Auta ka tashi ya jikin?"


Kallonsa kawai yake ido waje, bud'ar bakin Khalil sai cewa yayi "Jiddah, kaine Jiddah ta?" Sai kuma ya kwashe da dariya sannan ya cigaba da cewa,

"Ai na fad'a miki, bazaki iya rayuwa babu ni ba, hhhhhh, Uwa baki sona ko? Kinyi ma kanki" Sai kuma ya b'ata rai ya fara shashshekar kuka.


Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, domin ko dukkan alamu sun nuna Khalil ya haukace, k'wak'alwarsa ta samu matsala.


"Auta meyake samunka ne? Nine fa Yaya, nine Yayanka" Yaya ya rik'a fad'in haka cikin tashin hankali.


Maganganun da Khalil keyi ko nace sambatu da sauran iyayyaku, suka k'ara tadama Yaya hankali, babu shiri ya fita kiran likita, kafin su shigo har Khalil ya tsitstsige allurorin da aka tsira masa a hannu, garin k'ok'arin mik'ewa ma har ya fad'i k'asa.


Da sauri likita da Yaya suka k'arasa suka kakkamasa suka maidasa kan gado, Khalil ya rik'a fiffizgewa yana sirutai, akaf cikin surutansa sunan Maijiddah yafi Yawa sai na Hajiya Uwa, likita ya d'auko allurar bacci ya maka masa, take bacci yayi awon gaba dashi, sannan yayi wasu y'an gwaje-gwajen sa, bayan ya gama yace ma Yaya ya samesa office d'insa.


****

"Azahirin gaskiya Alhaji d'an uwanka ya samu matsalar k'wak'walwa sakamakon buguwa da kansa yayi, saidai a shawarce kamata yayi ku d'aukesa ku kaisa asibitin mahaukata domin sanin ainihin abunda ya faru.


Ga AC na bugawa amma wata iriyar zufa Yaya yaji ta zubo masa take a wurin, ya fara firfita da wata takarda daya gani kusa dashi kan table d'in likitan, yana mai nanata kalmar "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un"


****


A can Rimin gado kuwa, idan nace maku Maijiddah ta runtsa to nayi k'arya, domin a daren yau ko b'arawon bacci be samu nasarar sace ta ba, har bacci ya d'auke kaf ilahirin mutanen dake gidan amma ita sam ko alamarsa ma bata ji.


*********************


Washe gari tunda safe Yaya ya kira Jamil, yazo ya samesa asibitin suka fara shirye-shiryen wucewa da Khalil asibitin mahaukata, har kuka saida Jamil yayi, sunata cuku-cukun wucewa dashi Yawale ya iso asibitin, nandai suka fad'a masa abunda ke faruwa, hankalin Yawale ya tashi shima sosai, suka sakasa mota, Likita ya basu referring letter suka wuce.


Wuraren k'arfe takwas Hajiya Uwa, Hadiza da Momy suka iso asibitin, ga uban kayan abinci a hannunsu, suna shiga d'akin suka tarar da babu kowa, wurin likita suka tafi kai tsaye, ya sheda masu ai tun da farar safiya suka wuce.


"Suka wuce ina likita?" Hajiya Uwa ta tambaya idanu waje.


Nanfa likita ya fad'a masu komai, bayan sauraronsa sai Hajiya Uwa ta tafi luuuu zata fad'i k'asa don ji tayi tana ganin jiwa, Hadiza da Momy suka tareta suka zaunar da ita.


Hadiza ta matsa gefe guda ta kira Yaya, ya fad'a mata inda suke, bayan da Hajiya Uwa tad'an huta sai suka kamata suka shiga mota suka kama hanyar asibitin mahaukata.


Duk wanda yaje asibiti duba Khalil saidai ace ai an sallamesu, sukuma sai su wuce gidansu Khalil d'in kai tsaye.


***********


"Matsalar k'wak'walwa shike damun patient d'inku, kuma a iya binciken da mukayi koda ace babu accident, sakamakon wasu k'wayoyi da yake sha masu k'arfi yaso yayi masa illa a k'wak'walwa, abu d'aya ze hana yiyuwar hakan shine idan ya dena sha wannan miyagun k'wayoyi, amma yanzu gaskiya akwai matsala kam" wannan shine abunda likitan mahaukata ya fad'a ma su Yaya.


Yaya yace "to yanzu likita yakenan? Kana ganin akwai yiyuwar ze warke koko sai mun dangana da k'asar waje?"


"Eh to gaskiya kai tsaye bazan iya ce maka eh ko a'a ba, amma koda akwai yiyuwar warkewar tasa to ba yanzu ba, nanda shekaru uku ko sama da haka ma gaskiya albarka, kuma ko wace k'asa zaku fitar dashi inada tabbacin suma abunda zasu fad'a maku kenan, saidai zamu d'orasa kan magunguna masu k'arfi da allurori, kuma irin ciwonsa yana buk'atar ya rik'a kasancewa da wani mafi soyuwa kokuma kusanci dashi"


Tashin hankali ba'a sa masa rana, gaskiya iya kad'uwa yau Yaya ya kad'u, dukda munanan halaye irin na Khalil a da amma kowa yasan Yaya yana sonsa sosai, arayuwarsa be tab'a hangoma Khalil hauka ba sai gashi yau rana tsaka.


Dasu Hadiza suka k'araso Yaya ya fad'a masu duk yadda sukayi da likitan, bud'ar bakin Hajiya Uwa sai cewa tayi "ganinan, ai nice mafi kusanci dashi, ba damuwa insha Allah"


Yaya yace "anya kedai Uwa?"


"Uwa wannan ba maganar kishi, fad'a, son zuciya ko sonkai ake ba, ana magana ne akan lafiyar d'anki, sanin kanki ne kinsan cewa babu wanda ya dace daya rik'a kasancewa tare dashi sama da Jiddah, domin babu abunda yakeso sama da ita ayanzu dai" inji Hadiza.


Hajiya Uwa tayi shiru domin tasan babu sirki ko algush a cikin gaskiyar da Hadiza ta fad'a


****


Taron biki kam ya watse kowa ya kama gabansa, haka can ma wurin su Maijiddah, kowa da kowa ya koma gidansa, Mariya ma ta tafi gida.


**************


Wasa-wasa yau har kwana uku dakai Khalil asibitin Mahaukata amma Maijiddah tak'i zuwa dubasa, anyi-anyi da ita taje amma tak'i zuwa.


Yawale kam yanason kusantar Khalil domin a ganinsa shi Uba ne ga Khalil da sauran y'an uwansa, hakan yasa ya shirya baro k'auye, suzo su tare da Iyalinsa gabaki d'aya tunda daman yanada niyar hakan.


A rana d'aya suka gama komai, ya taho tare da Sada yaron wani k'aninsa domin ya rik'a je masu aike tunda basu da babban d'a namiji.


*****************


Hadiza ta shirya tazo gidansu Maijiddah nan cikin gari, ta rok'eta don Allah taje taga Khalil, tayi iya yinta amma abun yaci tura, a k'arshe sai Maijiddah tace "Aunty Hadiza karki d'auki maganata a matsayin rashin kunya, amma inaso ki bama Hajiya wannan sak'on, kice mata ni Maijiddah nace nida Iyayena ba mayu bane kuma bamu da abunda zamuyi da arzik'inku da take ikirarin zamu cinye, sannan idan har tanaso naje wurin d'anta to sai tazo har gida ta rok'i yafiyar mu nida mahaifiyata, kamar yadda taje har gidanmu can rimin gado kwanaki biyar da suka wuce, tayi mana rashin mutunci, ta zagemu tas sannan ta tsinkama mahaifiyata mari a cikin taron jama'a"


"Wa iyyazubillah, yaushe akayi haka? Innalillahi" inji Hadiza, sai alokacin ta rik'a tinanin fitar Hajiya Uwa dakuma yadda akai suka had'u asibiti bayan accident d'in su Khalil, babu tantama ta tabbatar da Hajiya Uwa ta aikata hakan.


Koda Hadiza ta koma gida, bata canza komai ba acikin abunda Maijiddah ta fad'a mata ba, ta fad'a ma Yaya shima hakan, nan suka taru suka yita yima Hajiya Uwa fad'a.


******


Yawale da Yabi suka yima Maijiddah fad'a da nasiha sosai, Maijiddah ta amince zataje taga Khalil amma sai sunyi mata alk'awarin babu wanda zesan cewa taje, suka amince da Hakan.


Yau da yamma kafin Maijiddah taje ganinsa saida Yawale ya tabbatar kaf y'an gidan su Khalil d'in sunje sun tafi tunda dama bawai zama ake dasu can ba, sannan ya raka Maijiddah suka je asibitin.


Da farko likitan ya hanasu ganinsa wai an rufe sai gobe, da Yawale yace masa wannan itace Maijiddahr da Khalil yake yawan ambato, aisai likita ya barsu suka shiga ba tare da b'ata lokaci ba, amma sai yace ita kad'ai zata shiga wurinsa saboda sun basa magunguna da allurori yanzu haka bacci yake, Yawale dai yace ai ba damuwa ita kad'ai ma idan ta shiga ya wadatar.


Maijiddah na shiga d'akin da yake taji gabanta ya yanke ya fad'i, zuciyarta ta hau bugu a d'ari, kyakkyawar fuskarsa ta hango, idanuwansa a rufe yanata bacci, kamar ya bud'e ido ya kira sunanta *"Jiddah"* yadda ya saba, ta k'arasa ta zauna gefen gadon da yake kwance, hawaye suka fara zarya a fuskarta, saida tayi kuka mai isarta sannan ta fara magana,


"Allah karka hukunta bawannan naka ta wannan hanyar, Allah idan jarabawa ce wannan ka misanya masa da wata mafi sauk'i don tsarkin mulkinka, Khalil ka yarda dani wallahi ban tab'a tausayinka irin yadda naji yanzu ba, inama ace fitar kalmar SO daga fatar baki na ze iya maidomin da hankalinka Khalil, dana furta maka hakan sau babu adadi, don Allah hankalinka ya dawo gareni, nice Jiddahr ka Khalil, ina sonka, na amince inasonka, wallahi inasonka" wani sabon kuka yazo mata, nanfa ta dasa.


Bata iya barin wurinsa ba har saida wani acikin masu kula dasu yazo yace ta fito hakanan.


Saida ta share hawayen fuskarta ta goggoge sannan ta fito (yaro man kaza, wanda take b'oye mawa kar ya gani ai ya gane tayi kukan, tunda ba makaho bane shi), suka fito daga asibitin suka tafi gida.


**********************


Yabi na zaune ita da y'an yaranta a parlour sunata kallo, abunka da ba'a saba ba duk sun tattara hankalin sun maidasa kan TV, aka yita maka sallama basu jiba har saida aka shigo, Yabi na d'aga kai taga Hajiya Uwa ce ai sai ta mik'e gabanta ya fad'i rasss, don tasan ganinta ba alkhairi bane, kafin suce komai Maijiddah ta fito daga d'aki ta shigo parlourn, saiko taci karo da wannan sarautar Allah, ta had'e rai kamar taga takaici.


"Kai ku tashi ku shiga ciki" Yabi ta kora yaran, suka tafi d'akinsu gabaki d'ayansu.


Ga mamakin su Yabi dani kaina sai muka ga Hajiya Uwa takai guiwoyinta k'asa..........

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.