Free chapter · Read without an account

10

by Na'ima sulaiman Sarauta · ZAIN_ABEED


Jin numfashinta na sauka a hankali ta cikin wayar tana sakin nishi kaɗan, ya sanya Abeed lumshe gajiyayyun fararan idanunsa wanda suke cike da bacci, hakan kuma yasa gaba ɗaya ya fasa faɗin sunan nata kamar yadda yay niyya, ajiye wayar yay zuciyarsa gaba ɗaya tayi masa nauyi abubuwa da yawa suna neman gagararsa, taɓe bakinsa yyi kafin yaja numfashi ya jima a wajan kafin ya miƙe zuwa toilet, shower ya sakarwa kansa ba tare daya bari ruwan ya taɓa wajan ciwon ba, yana gamawa yyi alwala tare da sauya kaya zuwa baƙar jallabiya, raka'atul fajr yayi kana yyi sallar Subhi, baccin daya jima baiyi ba shine ya fara fisgar idanunsa, akan pra mat ɗin ya kwanta, not too long bacci yay gaba dashi. Wajan ƙarfe 10 na safe, aka turo ƙofar room ɗin da Abeed yake ciki, Riya wacce taci ado sosai tana sanye da wata Abaya Ash color, tayi kyau sosai kasancewar ta itama fara ce irin farin buzayen nan, hannunta riƙe da basket na breakfast. Muryarta cike da farin ciki tace "Good mrng My singer" Tun shigowar ta Abeed yasan cewa ita ce, shima fitowarsa ke nan daga cikin toilet,gaba ɗaya zaman hospital ɗin ya damesa gida yake son tafiya, Murmushi Riya tayi ganin bai amsata ba sai ma rufe idanunsa da yyi, wajansa ta ƙarasa tare da zama gefen bed ɗin tana ɗan kwaɓe fuska tace "Sorry my dia, wlh bana iya bacci musamman da naji abinda ya sameka, how are you feeling now? Hope da sauƙi ko?" Banza yyi mata Bawai dan baiji mene take cewa ba, Riya ta ɗauka bacci yake a hankali ta sanya hannunta taja dugun hancinsa tace "U looks so unique my dear" ta faɗa tana sumbatar goshinsa, Abeed bashi da lokacin ta duk da hakan bai hana shi faɗin “Mayya” ba a cikin zuciyarsa. Wayar Riya ta ɗauki ringing ganin sunan wata best friend ɗinta tayi answering tare da faɗin. "Hello, I've been calling you,amma baki ɗaga ba" daga can ɓangaren Nusy tace "Nayi busy ne, so ykk ya jikin mayan naki?" Riya ta ɓata rai tace "Stop calling him da wannan sunan, jiki da sauƙi bacci ma yake, Dad yace aure na da Abeed kamar nayi an gama, wlh ina cikin farin ciki Nusy ina son Abeed ina matuƙar ƙaunar sa, ban san yaya zanyi ya soni ba" Nusy tayi dry tace "Kina matsayin mace,amma ki kasa jawo hankalin namiji, musamman Abeed da yyi rayuwa cikin turawa, wlh idanunsa a buɗe yake yasan komai na mace domin ƙarya ne ace bai taɓa sanin ya mace take ba" Riya ta juya ta kalli Abeed taga bacci yake sosai, a hankali kamar zatai kuka tace "Nusy zan iya yarda dake, amma ba lallai hakan ya kasance ba, halin Abeed daban yake,na tabbatar da Zain nace ina so na tuni an shige wajan, i luv him I luv him I can't marry someone else.." shiru Nusy tayi kafin tace "take it easy dear, amma ki gwada Abeed ɗin mana, ba namijin da baya shiga tarkwan mace" Riya taja numfashi tace "To me zan mata? I'll try my best ganin ya soni amma nida banza duk ɗaya muke a wajansa, ni burina na ganni matsayin matarsa ta aure" Abeed dake sauraran conversation ɗin nasu a ransa yace "Tab..." A fili kuma ƙara narkewa yay yana jan numfashi cike da nutsuwa, Nusy tace "ke da waye a wajan?" Riya ta juya tace "Ni ɗaya" Nusy tace "Ok shifa?" Riya tace "breakfast na kawo masa, na samesa yana bacci" shiru Nusy tayi can tace "Kin tabbata bacci yake?" Riya tace "Sure, he's sleeping" Murmushi Nusy tace "wake him up" ware ido Riya tayi da mmki tace "Like? Ban son abinda zai zubar min da mutunci Nusaiba" Nusy tace "Kin daɗe kina zubarwa da kanki mutunci ai, sai dai kada a kuma, Abeg dear wake him up shine damarki a yanzu" Riya tace "Ok, bari na tashe sa" da sauri Nusy tace "hold on,kin fahimci me nake nufi" Riya ta girgiza kai alamar "a'a" Nusy tace "Ki tashe da hot kisses Maahh" zare ido Riya tayi tace "ke kina hauka, wlh yana iya ɓalla ni zuciya garesa" Nusy tace "be classes Madam, shiyasa kike mai da kanki middle class a idanunsa, shifa singer ne, idanunsa a buɗe yake ƙilan ma yana so kamar aji yake ja maki, duk fa wani mawaƙi haka soke suna da son mata" Riya tai shiru tana tunanin abinda Nusy take faɗa mata, domin duk show ɗin da Abeed zai kusan a ƙasar waje yake abune mai wahala ai invited nasa a 9ja yaje, tana tunanin abinda Nusy ta faɗa shine daidai, numfashi taja tace "Ban ɗauka hk abin yake ba, amma wlh ko kaina ne ina iya bawa Abeed idan har hakan zai sanya ya soni" Nusy tayi dry sosai tace "Diploma holder amma kin zama Middle class what noisess" Riya tace "lemme try, I'll get back to you" Nusy tace "ok" kashe wayar sukai baki ɗaya, daga can ɓangaren Nusy tayi dry tace "Shegiya mahaukaciya, wlh ba zan taɓa bari ki auri Abeed ba, kin fini kyau, kuɗi, ilimi nasaba ina matuƙar kishi da hakan" taja tsaki tana kwanciya. Bayan gama wayar Riya ta kalli Abeed kwarjinin sa ya ƙara fitowa, ga wani haiba daya ƙara, matsawa tayi kusa dashi tsoro duk ya cika mata zuciya, hannunta ta ɗura saman kansa tace "Wake up dear" shiru taji alamar bacci yake, Abeed kuma zuba ido yay yaga gudun ruwanta zata iya abinda banzar ƙawar tace mata ko yaya? Idanunta ya sauka kan laɓɓansa masu kyau, a hankali ta manna fuskarta akan nashi fuskar tana ƙoƙarin ɗura bakinta taga ya buɗe idanu, diriri cewa tayi bakinta na rawa tace "So.. Sorry it was a mistake" Abeed ya tsora mata shanyayyun idanunsa, yana ƙare mata kallo, ga mmkinta sai taga ya matso da fuskarta tare da ɗura kanta saman ƙirjinsa, Murya can ƙasa yace "Kinji bugun zuciyata?" ɗaga masa tayi yace "Owk, a duk sanda ƙirjina yay haka akwai abinda nke buƙata, very important haka zaki iya bani?" Da sauri Riya tace "Why not" ta faɗa tana ƙoƙarin rungome sa yace "heyyy get down" ya faɗa fuska ba yabo ba fallasa, janye jikinta tayi daga nasa, shi kuma ya miƙe zaune yana ɓata fuska sosai, kafin can yace "look at into my eyes Riyaa" yadda ya faɗi sunan nata yana jaa ya sanya Riya jin wani dɗi, domin bai taɓa faɗar sunanta ba, kallonsa tayi can kuma ta ɗauke kanta domin ba zata jure kallon ƙwayar idanunsa ba, yana shafa fuskarsa sosai zuwa gemunsa yace "Ke mahaukaciya ce?" Da sauri Riya ta kallesa kalmar tayi mata zafi ta girgiza masa kai tace "A'a" yace "ok Jakar ina ce ke? Nasan Dad Waziri ya baki tarbiyya,ohyaa gaya min maza nawa kika bi" zare ido tayi murya na rawa tace "A'a ban taɓa bin maza ba" Abeed ya lumshe idanunsa ya buɗe kafin yaja tsaki yace "Ohh lalatani da zaki yanzu fa? Kike ƙoƙarin yimin fyaɗe, Look Riya mace da daraja aka santa, a haka kike son na aureki, dan Allah ki fita a harkata wlh ba zan iya aurenki ba ni tsoro kike bani, lalatani zaki a banza" Hawaye tuni ya gama wanke fuskar Riya, cikin kuka tace "Saboda ina sonka? Ka sani idan har baka auren ba wlh nice sanadin ɓata sunan zuri'armu, wlh sai na bar muku abin faɗa" ka faɗa ya ɗaga irin ke kika sani ɗin nan, deep down na zuciyarsa yana tausayin ta, baya ƙaunar ganin hawaye a fuskar mace, da yana da ikon auren Riya daya aureta, amma babu Aure a lissafin ƙadsararsa,baya son auren ko wacce yarinya bare ya mutu ya barta da takaba tun tana ƙarama rufe idanunsa yay zuciyarsa nayi masa zafi da ƙona, gaba ɗaya baya jin daɗin zuciyarsa, sai a lokacin ya tuna cewa ba iya Sara ya gani a ɗakin ba, wacce yarinya ce mai tsananin kama da Sara? Ganin bashi da wata amsa yasa ya miƙe tsaye yana taɓe fuska.


Da yamma Amma na zaune tare da Zain suna magana a hankali kafin yace "Amma mene yasa zaku biyewa maganar Naila? Ita yanzu me zata ɗorar akan soyayya da zaman takewar aure" Amma tace "Waye zai iya da rigimar Naila, tunda tace sai anyi auren Abeed da Riya kasan babu makawa sai anyi" Zain yace "I'll talk to her" shiru Amma tayi can kuma tace "Sara taƙi cin komai, hatta Rubutun da aka yi mata taƙi sha ina jin tsorar yanayinta" Zain yace "Tana ina?" Amma tace "she's in the bedroom" Miƙewa yyi yana faɗin "ɗazo naje hospital zuwa 5pm Abeed zai dawo gida" Amma daba wani shaƙuwa sosai tsakaninta da Abeed ɗin tace "Allah ya kaimu" yace "kin masa sannu da jiki Amma?" Tace "Allah ya bashi lafiya" kallonta kawai yyi sai kuma ya nufi part ɗin da Sara ke ciki....Sara na kwance akan bed tana sanye da wando VGOLD palazzo trousers da riga Silhouette tayi lamo akan bed ɗin idanunta a buɗe ta ƙanƙame pillow, A hankali Zain ya turo ƙofar tare da tsayawa a door way yana ƙare ma Sara, ya jima yana kallonta kafin ya ɗan saki Murmushi yace "Mamana" da sauri Sara ta rufe idanunta tana ɗan tura baki, ƙarasa shigowa ciki yyi tare da tsayawa a kanta yana kallon yadda take bacci domin ya ɗauka bcci take, kanta ya shafa yace "sorry Mamana Allah zai baki lafiya" yana faɗin hakan ya fita zuwa waje, ganin bai ga Amma ba ya sanya ya nufi part ɗin Naila, tsaye yyi saboda jin muryar Riya na kuka tana cewa "Naila ki taimakamin Kice Abeed ya aure ni, zan mutu Naila" Naila tace "Idan kin mutu Allah ya tsine, aure kuma kamar anyi an gama ina cewa nina haifi ubansa, duba nan kiga wanann nonon nawa dashi na shayar dashi" ta faɗa tana ƙoƙarin ɗaga rigar ta kafin tace "Yoo Allah na tuba daidai nuna tsaraici bashi da kyau ne, na haifi Jafaru na haifi Uban ita Rariya take kowa, Allah na tuba ba gwada mahaifiyar ki bama, ita uwar tawayen ba dangin iya balle na baba fa, kawai taimakon musulunci ne kin sanni akwai tausayi da imani har kuka nake dan tausayi" Riya na ƙara narkewa jikin Naila tace "Ba kince zaki ma Uncle AY Mgna ba?" Naila tace "meye kuma AY Allah na tuba, wannan da bashi da cikakken hankali, wajan Mai martaba zani dakai na, na daina jiran wannan ison na Jakadiya Abar" Murmushi Riya tayi tace "Naila kina son ki rasani" Naila tace "A'a wlh ko a mafarki bani nace zaki auresa ba? Allah na tuba ida bai min biyayya ba ai sai bakina ya kamasa maza tashi kije" Riya ta miƙe tsaye tare da fita, ganin Zain a bakin ƙofa yasa tayi Murmushi tace "Our big lawyer" ya ɗan kalleta yace "Sis" ya faɗi hakan yana shiga ciki, taɓe baki tayi tare da yin gaba, Zain ya ƙarasa shiga ciki kallonsa Naila tayi ganin fuskarsa a ɗaure yasa ta fashe da kuka tace "Wlh inaga aljanu sun shafi yarinyar nan, banda haka mace ba aji ba komai, Allah na tuba mahaukaciya ce ni da zan ɗauki lafiyayyan yaro na bata shi, kalleta fa idanunta a tsakar ka" Zain yace "Drama Queen" tace "me kace?" Yace "cewa nayi bake kika haɗa auren ba?" Tace "Inji Ubanwa? To mai ƙarya a ƙona shi a wuta wlh" shiru kawai yyi mata can kuma ya miƙe tare da fita ya nufi hospital... Lokacin daya isa asibitin ya samu Abeed zaune cikin wasu Racing jersey da Camouflage-print cargo trousers, sai wata red ɗin P.cap daya sanya, farar ƙafarsa sanye cikin Mon mule slippers, jikinsa ne ya cewa Biyuninsa ne ya iso, hakan ya sanya ya ɗaga kansa a hankali suka haɗa ido, har zai magana sai yyi shiru, kafin suce Komai Dr Adyan ya shigo hannunsa riƙe da file da wata injection, ɓata fuska Abeed yyi sosai, Zain yace "Dr da alama allura zakai masa ko" Dr Adyan yace "ba kaga yadda yake muzurai ba, sai an shiga cikin mutane a dinga ɗagawa amma ana tsoran allura" Abeed yyi musu banza, ganin da gske Dr Adyan so yake yyi masa injection ɗin ya sanya ya miƙe tsaye, tare da nufar ƙofa a hankali hannunsa zube cikin Aljihu, Dry sukai tare dashi da Zain, Dr Adyan yace "Our singer nace kada ka manta mgnar mu, domin zanyi tafiya ƙaro karatu amma gobe nake tunanin zan shigo sai mu yi mgn" Abeed murya can ƙasa yace "Talkative" yana faɗin hakan sukai waje, Bayan Zain ya amsar masa maganinsa. A hankali Zain ke jan motar sbd yanayin jikin Abeed har suka ƙarasa Masarauta, Abeed ne ya fito yunwa yake ji sosai cikin dauriya yake takawa, Zain ya biyo bayansa da sauri suka jera Zain ɗin nayi masa sannu, A Parlo suka samu Abba da Amma, Abeed ya zauna ƙasan carpet yana lumshe idanunsa, Amma ganin yadda ya zauna kusa da ita yasa ta miƙe tare da faɗin "Bari a kawo maku abinci" Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace "how was your body Shalelen Naila?" Abeed na buɗe ido yace "Allhamdulillah Abba, barka da yamma" Abba yace "Yana da kyau ka samu hutu fa" Zain yace "Abba babu inda zashi ai" Abba ya jinjina kai tare da cewa "Allah ya ƙara sauƙi" ya faɗa tare da miƙewa ya nufi part ɗin sa, domin ya tashi daga fada, Zain yace "Amma kawo abincin nan" tace "ok" a nan carpet ta jera musu kana tayi part ɗin Abba, babu ruwan Amma sa sarauta ita kema yaranta abinci haka ma Mai martaba, Zain yace "bari na sauya kaya" Abeed ya jinjina kai, har ya rufe idanunsa sai kuma ya buɗe saboda ganin Sara tsaye bakin ƙofa ta tsora masa ido, yanayinta kawai ya gani ya gane cewa abinci take buƙata, bata fuska yyi tare da haɗe rai Murya can ƙasa yace "Come" kamar jira take tace "Twin" juyawa yyi yaga bbu kowa a parlon, a gabansa Sara ta tsaya ya shiga ƙare mata kallo can yace "juya" bata fahimci me yake nufi ba hakan yasa ta ɗan zaro idanunta waje kamar yadda taga yyi, hannunsu ya saka kamar mai tsoran taɓa abu ya ɗan riƙe belet ɗin wandon ta ya juyar da ita, tsaki yaja ganin yadda kayan ya kama jikinta gashi kanta baku ɗan kwali daman ita kai duk gayyar aljanu, zame hannunsu yyi yace "sit down" shiru tayi masa, a ɗan ƙufule ya ja hannunta ta zauna ƙasa, sukai very close da juna, baya ya matsa ya kalli abinda take kallo, soyayyan naman da yake ta ƙamshi take kallo a hankali yace "Mayya" ganin yyi mata banza tace "Twin" ta faɗa tana nuna masa naman, ya kalleta can ya miƙa hannu tare da ɗaukan naman yace "Haaa" shiru tayi masa domin bata fahimta ba, gently ya sanya tattausan Farin hannunsa tare da tallafo haɓatar, yace "Buɗe" bakinta buɗe ya ɗan kallon fararen haƙoranta a hankali kuma ya sanya mata naman a baki, Murmushi tayi ta amsa ta fara ci ganin zai ajjiye hannunsa tayi saurin riƙe hannunsa tare da cewa "Twin.....




Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.