Free chapter · Read without an account

1-2

by Fatima M. Jibril · CAPTAIN UMAR

👨🏻‍✈️CAPTAIN UMAR👨🏻‍✈️

(Sympathy,pure love and Revenge)📒📚

Story and writing

By

Fatima(Zarah)


*🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

*M. W. A* 


'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''

***

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah.Ya Allah yanda ka Bani ikon fara rubuta wannan lafiya kasa na gama shi lafiya.


Typed

*1/01/2021*


Edited

21/06/2021


Page 1⏩2


__________________


Safiyar Monday ce wacce tayi dai dai da 21st December,tsaye na hango wani saurayi a harabar barrack din dake Nigerian Defense Academy wato NDA dake jahar Kaduna,wanda a'kalla baze wuce shekara talatin a duniya ba.Kyakyawane dai dai gwargwado amma ba irin over d'innan ba ,dogone,fari amma irin na 'yan Ethiopia,yana da faffadan 'kirji had'i da daradaran sexy eyes,kanshi cike yake da ba'kin gashi mai she'ki,yana da siririn saje a gefan fuskarsa.


Sanye yake da T-shirt fari da three-quarter na wandan sojoji,fuskarsa a d'aure yaketamau Wanda hakan ze tabbatar maka da cewa shi bamai san Wasa bane ballantana raini.Observing yaran da ake commanding Wanda suke Monster Parade yake yi a harabar gurin.Captain Umar Abdullahi kenan.


Mutun ne Adali,wanda yake da ri'ko da addini duk Kuwa da yanda mafi yawanci sojoji ke playing dirty life acikin barracks,amma shi Allah ya tsareshi da taimakon addu'an iyaye.Mutun ne miskilin gaske na bugawa a jarida,kwata kwata baya son raini komi 'kan'kantarsa haka ma 'karya,duk yanda kuke dashi bayaso 'karya ta shigo cikin Ala'karku.


A rayuwarsa in kaga yayi dariya ya na tare da Mami ne ,ko Ammi,ko Abbansu ko kuma Jabeer wato Babban abokinsa kuma Amininsa wanda suka taso tare tun suna 'kanana, in bakasani ba zakai tunanin cewa brothers from the same family.


Jin tafiyar Mutun na tunkarosa ne yasa shi d'ago akanshi,murmushi ya saki Wanda ya 'karya fito da kyawunsa ,ba kowa bane face Jabeer ,ya na zuwa ya mi'ka masa hannu suka tafa tare da cewa"My guy an tashi lafiya"cikin muryarsa na cikakken namiji yace"lafiya,kai fa?"Jabeer ya saki murmushi sannan yace"lafiya qlau"Umar ya Sauke ajiyar zuciya yace"Okay,'karfe nawa zamu wuce"Cikin takaici Jabeer ya ce ai an yanka ta tashi ,dan yanzu Brigadier yace mun inje in yi compiling files d'innan na wannan case d'in"Umar ya saki fuska yace "kar ka damu kayi sauri zan jira ka ka gama se mu wuce"cikin farin ciki yace"yawwa bari inyi sauri inje inyi kafin a gama parade d'innan"Umar yayi dariya yace "inna shirya zan biyo ta office d'in sai mu wuce"Jabeer yace "nama sa travelling bag d'ina acikin motarka"Umar yace "Okay".Gaba Jabeer yayi yana mai alama da hannu alaman sai ya ganshi.


Sai da aka gama Monster Parade d'in kafin ya wuce Apartment d'inshi domin shirya wa ,bud'ewa yayi ya shiga,straight bedroom din yaje se da ya rage kayan jikanshi sannan ya wuce toilet ,be wuce 20minutes ba ya fito,m ai ya shafa sannan ya bud'e cupboard d'in ya d'akkao kaya ,shiryawa yayi cikin Farar T-shirt da ba'kin trouser,Agogo 'kirar iwatch ya d'aura a tsintsiyar hannunsa,Mayikan Kai ya shafa sannan yayi combing gashin ,tsaf ya fito yayi kyau ba kad'an ba.'Daukar traveling bag d'inshi daka aje a kan gado yayi sannan ya d'auki mukullan motarshi ,fitowa yayi ya kulle apartment d'in sannan ya shiga motarsa yayi office d'in Jabeer.


Sai da yayi sallama aka bashi izinin kamar yadda addini yace sannan ya shiga cikin office d'in,tadda Jabeer yayi yana aiki ba kama hannun yaro,cikin za'kuwa yace"haba Malam ,kai ma mutane sauri mana,wlh na 'kosa naga Mamina"Jabeer yayi d'an dariya sannan yace "toh 'dan Mami ai sauri nake yi,kaga ma har na gama,kawai tashi mu muje".Fitowa sukayi suka shiga mota suka kamo hanyar Zaria.


Umar ne ke driving yayin da Jabeer ke zaune a d'ayan side d'in,Jabeer ne yayi magana da sauri alamun ya tuni da wani sa'ko da yake so taba Umar d'in,yace"dan Allah in kaje gida kace ma Husnah Ina gaisheta kafin na zo anjima da yamma,d an gaskiya nayi missing d'in ta"wani harara Umar yama Jabeer sannan yace"in kana da 'kafa kaje ka fad'amata kayi missing d'in ba wai kace in fad'a mata ba ,dan kasan ni ba sa'an ta bane,k Ina ni ba d'an aiken ka bane,kawai kasa yara su raina ni", Jabeer yayi dariya sannan yace"kasan Allah tana gama secondary zanje gurin Abba da maganan auranmu"cikin takaici Umar yace"ai ga fili ga mai doki ,yanzu ma bata 'baci ba kaje inya so se a d'aura auran ku gobe kaji".


Jabeer ya d'an yi dariya kad'an sannan yace"guy,i can't wait to see aure na da Husnah, dan inaji ranar babu wanda yakai ni sa'an mata a duniya"cikin mamaki Umar ya juyo ya kalli Jabeer sannan duk a ransa yana matu'kar jin dad'in yadda Jabeer ke 'kaunar 'yar tilon 'kanwar tasa,sannan yace "wai da gaske yarinyar nan zaka aura?"gyada Kai kawai yayi kafin yace"ai dole yara su rainaku tunda kuna zuwa kuna musu kalaman soyayya shiyasa suke ganin kafad'ar ku d'aya"yaci gaba da cewa"yarinyar da next year zatai 18 ita wai zaka aura"ya fad'a cikin ta'be baki kamar ya ga wani abin kyama.


Jabeer ya juyo yana fuskantarsa sannan yace"haka na ke son ta mezan yi da tsohuwa?"

Umar yace"ninan daka ganni nafisan yarinya 'yar shekara 26 zuwa 27 wacce zata kulawa dani da bu'katuna ,sannan wacce idanun ta ya bud'e kuma wacce bazan ji kunyan shiga taro da ita ba "


Cikin mamaki Jabeer yace "wai,kace Mama zaka auro mana kenan",tab har naga kalan wacce zaka aura,amma ba komai haka nan zanyi maneji da ita a matsayin matar abokina",cikin jin haushi Umar ya kaimu duka yana cewa"toh mai ruwanka da ita,in ma ka samu damar ganinta toh Ina tunanin sai ta sanadin Husnah,itama dan tana matsayin Matar kace kuma 'kanwata,nasan ba yadda za'a in hana ta ganin mata ta",dariya Jabeer yayi yace"lallai yaro,wuyanka ya isa tana,ba komai nasan Ina zaune za'a zo ana neman shawarata akan auren,in ma ta kama ni za'a bama duk wani hidimar a hannu",harara Umar ya watsa masa yace"hey guy,who?,ni har kana tunani in zanyi aure ire iren ka zasu shige min gaba a biki,haba dai ai sai naji kunya,kuda bakwa jin kunyan soyayya da kananan yara",dariya sosai Jabeer yayi sannan yace"lallai yaro,shikenen can't wait to see that time".


Umar cikin Jin haushi ya kalleshi yace"kaga a bar maganan kar ka 'batamun rai"cikin dariya Jabeer yace"ai dole kace haka tunda kaga an fara maganar da bazaka iya depending kanka ba"...........



More Comment..............

More Typing...................


Edited 


*FATIMA ZARAH*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.