Free chapter · Read without an account

11

by Na'ima sulaiman Sarauta · ZAIN_ABEED

*🌈ZAIN_ABEED🌈*



_By Nimcyluv sarauta_


Page 11...

End of book1



*Gaba ɗaya Littafin sadaukarwa ce ga ADDA RAMLA MAI DAMBUN ZAMANI🥰😂 Allah yabar ƙauna*


_Special Thanks to_ *Real Smasher BILLYGALADANCI🥰🥰 Aysha Aliyu Garkuwa, My ƙungiya Elegant Online writers😍😍😍*




Ɓata fuska Abeed yyi yana sanya hannunsa tare buge nata, data riƙe masa hannu, ƙasa tayi da kanta idanunta na ɗan cika da hawaye, ganin hakan da tayi ya sanya Abeed ƙara haɗe fuska sosai a ɗan kaushashe yace "Kee..." Shiru tayi taƙi ɗago kanta, tsawa ya daga mata tare da cewa "I'm i your mate?" jikinta na rawa ta kallesa ba tare da tace komai, idanun Sara ya cika da hawaye, ganin hawayen fuskarta yasa Calmy yace "Saaaa.." Sara ta ɗago idanunta ta kallesa kallo ɗaya tayiwa fuskarsa tayi kansa da kanta, Abeed yace "Zo nan Saaaaa" matsawa tayi wajansa domin no matter how scared of him ba zata iya barin wajan ba, shi take kallo a matsayin wanda ta sani kawai, ganin shoulder ɗin su na gogar na juna Abeed ya ɗan ja baya kaɗan yace "Zaki ci?" Gently ta ɗaga masa kanta alamar eh, yace "Ok eat" kasa taɓa komai tayi sai hannunta data miƙa wajan naman, kafin ta ɗauki naman ya buge hannuna yace "ke Mayya ce? Da sai Nana za kici?" Miƙewa tsaye kawai tayi tana ɗan surutai a Zuciyarta, juyawa tayi suka haɗa idanu Abeed, ya ware mata manyan idanunsa da mmkinsa sai yaga ta murguɗa masa baki, with so much surprised ya ware idanunsa, yun ƙurawa yyi kamar zai bita, ta fasa ihu tare da yin part ɗin Amma. Tattausan sajensa ya shafa yana sauke ajjiyar zuciya, felling so much better akan yadda yake ji jiya, fararen ƙafafuwan sa ya miƙe kafin ya ɗauki mug ya haɗa tea ya fara sha a hankali, kaɗan yaci abincin ya miƙe tsaye, walking slowly ya nufi part ɗin su, Sara dake laɓe tana kallon duk abinda yake yana barin wajan ta ƙarasa inda yabar Lunch ɗin ta fara cin naman kamar wani zai ƙwace mata. Abeed na shiga cikin bedroom ɗin su ya samu Zain zaune yana kallon movie, Abeed ya ɗan kallesa sai kuma ya ɗauke kai, ya nufi bathroom, wanka yyi ya fito ya shirya cikin ƙana nan kaya na shan iska, zuwa lokacin Zain ya koma Parlo kai tsaye shima parlon ya koma, Zain ya samu yana waya taɓe baki yyi jin Zain na cewa "Give me some times Du'a, i can't marry serious idan ba tare mukai da Abeed ba, just relax" Diva dake zaune tana jin zuciyarta sam bbu dɗi tace "we're all mature, na fara hqr gsky ace aure sai wani yyi zakai?" Idanunsa ya buɗe yace "hold on, wani fa kika ce? Idan akwai wani bai huce ke ba, Abeed ya fi ƙarfin ki kirasa da wani, i don't force you to love me, dan haka zaki iya neman wani" yana faɗin hakan ya kashe wayar sa, yana jin wani irin haushin Du'a, duk wanda zai taɓa masa Abeed wlh ko waye zai iya karta masa rashin kirki, Abeed idanunsa akan Movien da Zain ke kallon na Sanam teri kasam yace "What noisess" Zain yace "for?" Abeed ya ɗan shafi kansa yace "Bata time ne kallo movie, kalli yarinyar ta mutu fa?" Zain yyi dry tace "And so what dan ta mutu? Have you watching frm the beginning?" Abeed yace "Nop, kawai hauka ne kallo Love movie" ya faɗa yana sauya channel zuwa ta ball, time ɗin ana buga ball Tsakani Madrid da Laliga, Zain yace "Ka gwada soyayya ko bbu yawa, zakai farin ciki koda farin cikin zai zama taƙi ne" Abeed ya gyara zama bayan ya buɗe fridge ya ɗauki chocolate da yawa yace "ba wata Soyayya da take dauwama, nifa da mace Gwamma Chocolate ina respect sunan mace ne kawai" Zain yace "Sure? Zakai bayani one day" Abeed ya lumshe fararan idanunsa yana jin zaƙin chocolate ɗin na ratsa masa ƙwaƙwalwarsa, yana matukar son chocolate, a hankali yace "Bayani, like? How?" Zain yace "Ohhu, lokacin da zaka fara ɗanɗana soyayya da ɗanɗana mace a time ɗin zaka san chocolate ba komai nace, U can live with chocolate, but u can't live without woman" Abeed yace "wahala dai" ya faɗa yana ƙoƙarin saka wata chocolate ɗin abakinsa da sauri Zain ya kwace, Abeed ya buɗe ido sosai domin abin yazo masa unexpected, yana ɓata fuska yace "Malam zan maka rashin kirki bani" Zain yace "Dan Allah yaya kaji dana kwance chocolate ɗin?" Shiru Abeed yyi baice komai ba, ya jima da sanin Zain bashi da kunya, Zain yace "To duk sanda kasan mace, ba zaka so tayi nisa dkai ba ko na 1mnt ne, Abeg my friend take your time ka Gwada ko kissing na mace ne" tashi Abeed yyi ya zauna yace "God forbid, baki na ana wata" ya faɗa yana nuna bakinsa tare da ya motsa fuska, Zain yace "Eh, idan har kai lafiyayye ne" Komawa Abeed yyi ya kwanta, yana jan tsaki Zain yace "Ni yayyanka kake ma tsaki?" Abeed yace "Allah ya sauwaƙe,kowa ya san nina fara shaƙar iskar duniya" Zain yace "wlh ƙarya ne, kai daka maƙale a ciki" pillow Abeed ya ɗauka tare da cilla wa Zain yana kwaɓe fuska..Kiran sallar Magrib ya sanya suka miƙe a tare, Abeed ya ɗan riƙe cikinsa maganar da yyi duk ya sanya ciwon na masa zafi, a haka sukai Alwala Zain ya shige Masjid Abeed kuma ya zauna a ɗakin bai iya zuwa masjid. Wajan 9 na dare suka fito a tare sanye da ƙana nan kaya, wando 3gauther sai vest mai ɗan kama jiki, Abeed ne kawai ya sanya bandana a saman gashinsa, kai tsaye danning area suka nufa, a nan suka samu Amma da Abba, Zain ya jawa Abeed kujera ya zauna kusa da Abba, shi kuma Zain ya zauna kusa da Amma, Zain yace "Barka da sare our sweet parent's" Amma tace "me kuke tun ɗazo kun zauna musun da kuka saba" Zain yyi Murmushi yace "A'a kallo muke" shi dai Abeed bai ce komai ba, sai can yace "Abba barka da dare" Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace "Ywwa sweetheart, ya jiki" yana ɗan kwantar da kansa a kafaɗa tare da kwaɓe fuska yace "Allhmd, Abba zani Australia" da sauri Amma ta kalli Abeed shima ya kalleta sai ba tace komai ba, Abba yace "meyesa?" Abeed yace "Kawai Abba" Mai martaba Abdul-Jabbar Abbas yace "To ba zaka ba" a sanyaye Abeed yace "To Abba" Zain dai shiru yyi ya fara cin abincin shi kuma Abeed ya sunƙi da kansa, so yake yaje yaga wani babban likita acan Australia amma ba zai iya faɗa ba, idanunsa ya ɗaga cikin Sa'a kallonsa ya sauka akan Sara wacce take zuwa wajan, ganin babu wanda ya kula da ita ta miƙe da sauri tare da shan gabanta, sai a lokacin Amma tace "Abincin fa" Yana kare Sara wacce take sanye da wani crazy Jen's ita gwiwa yace "I'm full" kallonsa Amma tayi amma bata hango abinda yake ɓoyewa ba, Abeed ya kalli Sara fuska babu fara'a yace "Muje" maƙale ka faɗa tayi tana murguɗa baki, idan yyi mgn yasan za'a jisa, sai kawai ya kama hannunta tare da shigewa part ɗin data fito, yana zuwa ya kulle ƙofa tare da tura ta da bedroom shi kuma ya jingina da jikin ƙofa, tun daga ƙasa ya fara ƙare mata kallo har zuwa sama, da sauri ya ɗauke idanunsa yace "Ke baki da hankali ko?" Kallonsa tayi ba tace komai ba, juyawa yyi tare da fita ya kulle ƙofar, bayansa tabi da kallo cikin Sanyin murya tace "Abin bauta kabas ka taimake ni" tana nan tsayen taji an buɗe ƙofar ware manyan idanunta tayi ganin ya shigo hannunsa riƙe da bulala, baya ta fara ja tana yarfe hannayenta idanunta ya cika da hawaye, duk inda tayi binta yake baya son raini a rayuwa yaga kuma kamar bata da kunya, har ta ƙarasa jikin bed yana binta, ganin zai kamata ya sanya ta sulale ta gefensa zata gudu yyu saurin kama hannunta, ƙara ta ƙwala, Abeed kam hannun ya riƙe ya dinga tsola mata bulalar tana ihu sai da yyi mata bulala goma, sannan ya zauna gefen bed ɗin tare da daka mata tsawa yace "Shiru, ko nai ball dake" ajjiyar zuciya ta dinga saukewa hannunta tuni yyi ja, sai a lokacin jikinsa yyi sanyi ganin ba wani lafiya gareta ba, ƙilan ma bata san me take masa ba, gently cike da tausayi ya jawota tare da zaunar da ita saman cinyarsa yace "Shiru" kanta ta ɗura a ƙirjinsa tare da cewa "Twin" idanunsa a rufe yace "Saaaaa" ya faɗa yana hura mata iska a hannun wanda yyi jaa sosai, shiru tayi jikinta har lokacin rawa yake, kanta dake ƙirjinsa ta ɗaga idanunta ta sauke a fuskarsa murya na rawa tace "Twin" idanunsa a rufe yana fisgar Numfashinsa dake ƙoƙarin kwacewa yace "Saaaa" ya faɗa yana buɗe ido tare da kallon ta ganin yadda take kallonsa yasa yace "Nine ko?" Fuska ta kwaɓe tare da ɗaga masa kai, yace "Ok ki daina saka wannan kayan" kayan jikinta ta kalla sai ta kallesa, ɓata fuska yyi yace "ɗaga ni" tashi tayi shi kuma ya miƙe tare da nufar wajan deep frizeer bottle of water ya ɗauka, tare da ɓalle wa, a hankali ya manna bakinsa a gorar ruwan yyi bisimillah ya fara karatu, ya jima na karatun kafin ya gama ya rufe ruwan ya jijjiga, juyawa yyi ya ganta tayi rufda ciki, yatsarta a baki tana tsotsa a hankali..ya jima yana kallonta kafin ya ƙarasa wajanta ganin zata faɗo, ajjiye ruwan yyi, tare da sunkuyawa ya ɗauke ta gaba ɗaya ya mayar da ita tsakiyar gadon, zama yyi ya mata addu'a ya shafa mata, kana ya ja mata duvet ya rufe mata jiki baki ɗaya, remote ya ɗauka ya ƙara mata gudun a.cn daga nan ya fita daga part ɗin. Har zai je wajan Naila sai kuma ya shige nasu part ɗin ya sauya kaya zuwa na bacci ya kwanta yana sauke ajjiyar zuciya.


Masarautar Zahel.

Gimbiya Noro ce zaune, akan wani abin zama sai Sairah wacce take zaune itama, can Gimbiya Noro tace "Kinyi sake Sarki Mabus ya ganki yanzu baki da wani madafa" Sairah tace "bani ya gani ba" da mmki Gimbiya Noro tace "waya gani to?" Sairah tace "Sara"... “Sara” Gimbiya Noro ta maimaita kafin tace "wace haka?" Sairah tace "Tare aka haifemu, mu Twins ne ai, ni ban san tana nan Bama ai" Gimbiya Noro tayi shiru can tace "Meya rabaku?" A hankali Sairah ta shiga bawa Gimbiya Noro labarin komai tace "She broke the Promise, ta gudu ta barni banyi tunanin hakan ba, ita nake kallo matsayin uba, uwa ƴan uwa amma taci amanata, me zan mata wanda ya shige na rama abinda tayi min?" Gimbiya Noro tace "me kikai mata" Sairah ta ƙara bawa Gimbiya Noro labarin komai dake faruwa tace "Idan nace nice za'a kashe ni, shiyasa nasa Sara ce ta caka masa wuƙa, tunda har ta iya rabuwa dani danme ni ba zan hakan ba?" Jinjina Kai Gimbiya Noro tayi kafin tace "Shi ke nan, tashi kije" fita tayi tana fita Sarki Mabus na shigowa yace "Kunyi mgn da Ayyana?" Gimbiya Noro tace "Kasan Ayyana wani lokacin sai a hankali, ina tunanin wannan karan zan amshi aikinta kawai" Sarki Mabus yace "Ba zaki iya Aikin da Ayyana take ba, a wajan fashin nan" shiru kawai tayi shi kuma ya juya ya fita, Sairah tafiya take zuwa wajan da Gimbiya Noro ta ɓoye ta, tazo daidai wani sashe taji ana rera wata waƙa mai daɗi, a hankali ta dinga tafiya har ta ƙarasu wani daƙi, tura kanta tayi zaune ta hango wata farar mata ƙyakƙyawa da ita, ta zagaye fuskarta da wani ƙyalle kamar buzuwa, sosai Sairah taji gabanta ya faɗi, Matar waƙa take cikin zazzaƙar muryarta mai daɗi can kuma ta fashe da kuka, Hawaye Sairah taji ya zubu mata na tausayin matar ta jima a wajan kafin ta juya ta nufi nata sashen, a Zuciyarta tana tunanin wacece wannan? Mene ya sanyata kuka har haka?. Sarki Mabus ya kalli Boka yace "Ka tabbatar cewa tana cikin gidan sarautar nan?" Boka yace "Madubin mu baya ƙarya, Tabbas tana cikin gidan sarautar nan, tana cikin Zahel, nasha faɗa maka cewa wannan yarinyar bakai ka kawo ta ba, itace ta kawo kanta zuwanta tsararre ne hakan kuma na nufin abubuwa da dama" Sarki Mabus yace "Mekake tunani da ita?" Boka yace "Zata kuɓuta kafin kuɓutar kuma sai haske ya baibaye Masarautar Zahel" Sarki Mabus yace "Haske?" Boka yace "Abinda na gani ke nan, amma ga shawara, mene ya sanya ba zaka iya hqr da aurenta ba? Domin babu rabon aure tsakanin ku, abinda nake gani cewa wannan rabon a wajan ɗan ka nake ganowa?" Sarki Mabus yace "Kana nufin ɗana SUBASH shine zai aureta..?"


Abeed ne zaune akan kujera watching TV yana kallon labarai a aljazeera, safiyar Juma'a kuma, Naila ce ta shigowa cikin part ɗin tana faɗin "To ga duk kayan ka nan, tunda kai ma ka zama gantalalle rabamu za'ai cinka shanka duk nice shine yanzu ka dawo ko kazo inda nake" Abeed ya Shafi sumar kansa can ciki yace "Sorry matar" Naila tace "A'a ba wani sorry, kasan baka da wacce take sonka kamata sau ashirin ina dama fura ina zubarwa ko Jambar ne ya bani kuɗin ai sai haka, balle bbu ruwansa shi da dama ma cewa zai bani na kawo sa duniya ba, taro da sisi haka nake tarawa na ajjiye saboda bikinka, to wa nake dashi wanda zai taimaka min? Babu kuwa wlh kaji na faɗa maka sai dangin Allah dana ma'aiki, to daman ai dasu muka dagora, jiyan kukan duniya nayi amma ace jeki ci Kanki" Abeed yay ɗan cute smile yace "To Aure Zaki min ke nan?" Baki ta buɗe zatai magana idanunta ya sauka akan Sara wacce take laɓe jikin kujera, da sauri Naila tace "Muhammadur Rasulullah S.a.w, ita kuma wacce haufaffiyar wacce ƙasar ce? Yanzu masifar take a kawo mana aljanu cikin gida a zube?" Da mmki Abeed yake kallon Naila shi bai ma kula da Sara ba, domin rabonsa da ita tun shekaran jiya yace "Aljanu fa?" Naila wacce take zare ido da alama itama mutanan ta ke son motsawa tace "A'a wlh na rantse da Allah babu mai mana ɗiban albarka a nan, uban kuturo yyi kaɗan" domin ita tsakani da Allah ta hango aljanun jikin Sara Miƙewa Abeed yyi bayan ya lura da Sara suna haɗa ido ta zura a guje zuwa part ɗin Amma, yace "Sorry matar kiyi Addu'a" Shiru kawai Naila tayi bayan ta ɗan dawo daidai tace "Daman shofin zani, shine nace bari nazo ka kaini domin bana son naje jama'a su ɗauka ni talaka ce, to Allah na tuba mene haɗi na da wani talaka ba dangin iya balle na baba, Gwamma naje dakai na nunawa uban kowa cewa jikina mawaƙi ne wanda yake nomba ɗaya a duniya" Zain dake shigowa parlon yace "to babu mai kaiki, daga can idan kin tafi kada ki dawo mana gida" Naila dai bata kula Zain ba, daga ƙarshe ma tashi tayi ta fita abinta. Zain yace "JUNAID zai dawo yau, idan muje masallacin juma'a zamu biya airport" nan da nan Abeed ya haɗe fuska yace "Ba zani ba" Zain yace "Meyasa? Kusan shekarunsa goma bayan ƙasar nan baka farin ciki da dawowarsa ne?" Ka faɗa Abeed ya ɗaga tare da Miƙewa, Zain yabi bayansa da kallo....Bayan sakkowa masallaci Abeed na zaune idanunsa akan Sara wacce ta shigo yace "Kee" ta ɗaga idanu ta kallesa yace "Kinci abinci?" Ta ɗaga masa kai yace "zo nan" ta ƙarasa wajansa Murya can ƙasa tace "Gani" hannunsa ya ɗura a cikinta yaji cikin shafal kamar zai haɗe da bayanta yace "Ƙarya kike" tayi ƙasa da kanta yace "Zane maki jiki zannayi ƙazama mara wanka" kwaɓe fuska tayi idanunta na cikowa da hawaye tace "Twin" yace "Daina kirana" tayi shiru yana ƙoƙarin magana yaji Sallamar Zain idanunsa ya ɗaga a hankali, yaga Junaid a bayan Zain yana ɗan sakin tattausan Murmushi, Junaid nada tsayi amma ba fari bane chocolate color ne, ƙyakƙyawa wanda yake kama da Dad Waziri sak, hannun Junaid zube cikin Aljihu idanunsa ƙuri akan Sara hakan yasa Abeed yace "Kee shige ciki" da sauri ta miƙe ta koma part ɗin ta, Junaid kuma ya bita da kallo a ransa yana cewa "What a beautiful young lady...


A can Masarautar Zahel kowa, Sairah ce ke tafiya a hankali ita kanta bata san inda zata ba, a haka ta ƙarasa cikin wani waje mai kama da lambu amma ba lambu bane, jikinta na rawa tayi baya ganin ƴan mata a cikin wani babban keji a kulle su sai ihu suke, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un baya ta fara yi tana ƙoƙarin juyawa taji tayi karo da Mutum juya tayi suka haɗa idanu da SUBASH, Jibgegen saurayi ƙato dashi, fuskarsa babu alamar yasan wani abu imani amma yana da sahihin kyau, hasken Muslunci ne kawai babu a fuskarsa, baki ta buɗe zata kira sunan Allah yayi saurin sanya hannunsa tare da ɗaukar Cak ya nufi wani daƙi, Ihu Sairah take tana Dukansa amma ko a jikinsa, shi tunda yake bai taɓa jin wani abu game da mace ba, amma yana ganin Sairah yaji mazantakarsa ta motsa. Yana zuwa ɗakin ya kwantar da ita tare da cire kayan jikinsa yyi tsirara wani uban ihu Sairah ta ƙwarara lokacin da idanunta ya sauka akan Gaban SUBASH da ya wani irin Miƙewa har rawa yake.....



*Ƙarshen free pages, last free pages* _A nan na kawo ƙarshen free pages, dan girman Allah kada ki karanta min littafi kyauta, ina son litattafan sarauta idan gsky ne ki fitar da ₦500 a baki Zain Abeed, bana Allah ya isa a littafi ba zan fara a wannan ba, kawai nasan haƙƙi na ne🧏🏾‍♀️_


*Zain Abeed it's ₦500 via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank, shaidar biya....*** dan Allah idan baki da banki akwai P.O.S kaca kaca a gari ki bada 50 a tura maki ki tura min 450 ma, ƴan Niger kuyi min Mgn na, na gaya maku yadda zaku biya Nimcyluv lover's You❤️*


_Jama'ar Abu Maleek, mutunan Tsintacciya, masu jiran Kwaila ce, tawagar Sirrin mu duk kuzo mu haɗe a gidan Zain Abeed, muji daɗi tare ai karatu cikin kwanciyar hankali, Bayan na gama Zain Abeed zanyi muku littafin *MIJIN MALAMA* Wanda zai zo kyauta, amma idan har kunci amanata kun fitar min da Zain Abeed na fasa yi a Free_


_Su waye Sara?_

_Su waye Zain Abeed?_

_Waye Junaid?_

_Abeed zai samu lafiya?_

_Wa Sara zata aura, Zain? Abeed? Ko Junaid?_

_Abeed zai auri Riya?_

_Wacece Ayyana?_

_Mene makomar Sairah wajan SUBASH? Waye zai kawo ƙarshen Zahel? Zasu amshi musulunci ko kuma a'a?_


*MU HAƊU A BOOK 2 A NAN NA KAWO ƘARSHEN BOOK 1 DUK MAI SON CI GABA YA BIYA YA KARANTA AKWAI NUMBER JIKI DA ACCT NUMBER, BANA SON KIRA KUMA BANI DA COMPLETE ZAIN ABEED, KO NA GAMA BA ZAN DUCOMENT BA A AREWABOOKS ZAN ƊURA👌🏾*



3:11pm

Sat/may/ 2022

Na'ima Sulaiman sarauta

Nimcyluv

Sarautar marubuta✍🏾

Thank you for choosing Nimcy's library👏🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.