Free chapter · Read without an account

5-6

by Fatima Sunusi Rabi'u · ZURU...!

*ZURU...!*

_*Warmth of love and compassion.*_😢❤️



    _UMMU AFFAN_🤏

  


_Littafina na kuɗi ne, biya ki/ka karanta cikin aminci. It's via Fatima Rabiu Sunusi 0037219728 Stanbic bank N300. Evidence of payment *** ko kuma a ɗauki photon katin MTN a turo, normal group N300 VIP group N500 Ƴan uwa mutanen Niger zasu turo da 500f ta numberta ***._


_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._



DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN ƘAI.



*FREE PAGE 5-6*



Duk kan ƴan uwan Alhaji Salisu Sada da na Hajiya Asma'u sun san da zaman Ameen, kuma dukansu suna ƙaunarsa, sai ƴan bani na iya da ba za a rasa ba.

Idan yazo gida ba wani daɗewa ya ke ba kasancewar aikinsa, domin har ƙasashen waje Daddy yake turasa akan harkokin kasuwancinshi.

Wannan karon ma satinsa guda ya koma cike da tausayin Naanah.


NAANAH POV.


Mun fara jarabawarmu ta kammala ƙaramar secondary wato (JSCE) cikin azumi ne amma Umma ba ta tausaya min, duk kan aikin azumi nice ke yi dana dawo skul ban da wani lokaci sai na aikin gida.

Ina duƙe ina wankin waken da zan soya ƙosai an jima Abba ya shugo, dawowarsa sallar la'asar,. "Sannu da zuwa Abba" Na faɗa cikin ladabi. Ya ce"yawwa Naanah, sannu da aiki" Gefen tabarma ya zauna kusa da inda nake aiki. Ya ce"Naanah yaushe ne zaku kammala jarabawar?" na ce"Abba sauran kwana biyar ana sauran kwana uku sallah" ya ce"To Naanah Allah ya nuna mana, ya kuma ba da nasara" Na amsa da ameen.

 Zuwa cZAn na ce"Abba kana dai sane da saukarmu bayan sallah ko?" Murmushi ya yi ya ce"Kai Naanah kin sa saukar nan a ranki, Yayanku ma ya turo kuɗin shahadar na biya miki" Na ce"To Abba! Allah ya saka da alkhairu, sai kuma ɗayar maganar," "Ta me?" Ya tambaye ni. Turo baki gaba nayi cikin shagwaɓa "Kai Abba ba dai ka man ta da maganar ankon mu ba? Dariya ya yi ya ce"Naanah iyayen rikici, kin san Yayanku ya ce zai yi komi ni ya hutar dani" Zumɓuro baki nayi "Kai Abba ka san Yah Ameen da mantuwa" Eye! baya saya miki waya ba, sai ki din ga tuna mashi" Cike da yarinta nace "E! fa kuma haka ne Abba" gabaɗaya muka sa ka dariya, cike da nishali da farinciki irin na ƴa da mahaifinta.

 Umma ce ta fito daga parlour, taja tsaki mtsuuww, ta galla min harara take na dawo hayyacina. Ta ce"Aikin banza harara a duhu, ayi dai mugani idan tusa zata hura wuta."

  Abba ya kalleta ganin yadda tayi masa tsaye a kai. Ya ce"lafiyarki Ƙalau?" "Lafiya!" Ta ba shi amsa a tsiwace. Kafin ta juyo kaina "Kee!!" Ta ce min, daman mafi akasari tafi kirana da ke. Juyowa nayi ina kallonta. Ta ce"Mayya da shegen manyan idanuwan ki kamar na aljanu, kurwata kurr da ke.

  Da sauri na sadda kaina ƙasa "Kiyi haƙuri" Na ce cikin sanyi. "Yar kaza-kazan nan, ai daman haka kike da anyi magana kice ayi haƙuri kamar kin fi kowa sanin Allah a fuska musa a zuciya fir auna"

 Sake sadda kaina ƙasa nayi. Ta ce "Zan fita ne, kan in dawo ki tabbatar kin kammala komi na buɗa baki, sauran kuma kiyi abinci da yawa ko kiyi kaɗan yazo bai isa ba sakarya shashasha" Ture ni tayi tai gaba ko tambayar Abba ba tayi ba, daman duk in zata fita bata tambayarshi.

 Tashi nayi ina kakkaɓe jikina Abba ya kalleni cikin raunin murya ya ce"Naanah kicigaba da haƙuri wata rana sai labari, nima dai kina kallo hakuri na ke da ita" Ajiyar zuciya kawai naja naci gaba da aikina.

  A raina ina tunanin irin wannan hali na Umma. Abba yana matukar bani tausayi wani lokacin sai dai ina tunani da mamakin me yasa bai taka mata burki idan tayi wani abun ko da yake gaskiya yana bakin ƙokarinsa, ina ga gajiya yayi yanzu.

Koma dai menene addu'a ta kullum ita ce Allah ya shiryata.


A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, mun kammala jarabawarmu lafiya har Allah ya kawomu gobe sallah ranar wuni nayi aiki kamar me na gaji sosai.

Washe gari sallah da wuri na tashi na shirya cikin wata atamfa riga da siket sosai ta amsheni kamar dama ajikina aka tsarata, nayi make-up ɗina simple sosai nayi kyau Yayah Ameen ne ya aiko mana da kayan sallah kala biyar-biyar masu ƙyau da tsada. Ƙawata Zainab na biya mawa muka wuce salar idi, sai ya bani ta ke, wai nayi ƙyau, bayan an idar muka dawo gida cike da murnar sallah.

Abba da Yah Ameen suka shugo sun dawo sallar idi ne, Yah Ameen yana cikin wata ɗanyar shadda da akayiwa ɗinkin da samari ke yayi, gaskiya yayi kyau ainun.


AMEEN POV.


  Tun da ya shugo idanunsa na kan ƙanwar tasa da yake matukar ƙauna a zuciyarsa, kusa da ni ya samu ya zauna, sannan ya raɗa min a kunne. "Gaskiya kin yi ƙyau ƙanwata sosai" Murmushi nayi har sai da dimple ɗina suka lotsa, ni ma a hankali yadda shi ɗaya kawai zai ji na ce"Ai Yayah ka fini ƙyau ka ga yadda ka haɗu kuwa" Ido ya ɗan kura min na wani lokaci sannan ya ce"Ke kanki kin san ba zaki haɗa ni da ke ba, ke me ƙira irin ta indiawa" Dariya t nayi sosai har Abba nacewa "Yau kuma me yasami Naanahr Abba ta ke irin wannan dariyar?" na ce"Abba kamanta yau take sallah dole inyi farin ciki" ya ce"Haka ne" Sannan ya mai da hankalinshi gurin abin da ya ke yi.

Ta ƙara cewa nayi a hankali. "Yah Ameen ai gwamma kai kasan da Abba ka ke kama, su Aunty Rahma kuma da Umma ni kuwa da wa nake kama?" Na gaya hakan cikin damuwa. Ya ɗanyi shuru na wani lokaci sannan ya ce"Ai ke ma da Abba kike kama ko baki taɓa jin wan da ya ce muna kama ba?"

Na san wasa ya ke min sai kawai nayi murmushi ba tare da na ce kuma cewa komi ba. Ashe duk abun da muke Umma na kallonmu abin da muke cewa ne ka wai ba taji. Ta ce"Waiku ƙus-ƙus ɗin me kuke?" Yah Ameen ya ce"Umma ba komai" Sai kuma ba ta ce komi ba.

  Bayan sun fita ne Umma ta kama min kunne taja sosai. Zafin da naji yasa na saki ƴar ƙara ta ce"Wallahi kin ji ni, in har baki fita idona na rufe ba sai na saɓa miki, sau nawa ina gargaɗinki da ki dena shigewa yaron nan? Me yasa ba kiji halinki ya ke irin na mayu ne? Eye! To ina sanar dake wannan yaron yafi ƙarfinki kurwarmu kurrr da ke me baƙin hali.


Na ce"Dan Allah Umma kiyi haƙuri bazan ƙara ba" Ta ƙara jan kunnen tare da sakinsa, kuka na saka saboda zafin da naji yana min, ta buga min tsawa. "Ta shi ki fita can waje kiyi kukanki ba zakiyi mana shi anan ba" Tashi nayi na ɗauki mayafina nayi waje, kai tsaye gidansu Zainab na nufa.

Ina shiga harabar gidan naga motoci da yawa, duk da cewa in nazo gidan ina ganin motoci a ajiye amma na yau sun fi yawa, sai nayi tunanin ko dan sallah ne kila ƴan uwa sukazo gaishe su. Ina shiga parlour cike yake da ƴan uwansu, gaishe su nayi suka amsa cikin fara'a da sakin fuska. Zainab ta taso ta kama hannuna tana cewa "Naanah zo ki gaishe da Yayana Marwan ya dawo daga karatunsa" Da yake tana bani labarin Yayanta Marwan dake karatun likita a kasar Egypt, sai faman jana take har gabansa sannan ta ajeni kusa dashi ita ma ta zauna. Ta ce"Yah Marwan ga Naanah wacce nake baka labarinta a waya aminiyata" Ɗago kansa yayi daidai da ɗago nawa kan muka kalli juna lokaci guda, take naji gabana ya buga kamar yadda naga alamar shima abinda naji yaji, gaisheshi nayi ya amsa a hankali, ganin yayi min banza na juya gurin Hajiya nace"Hajiya ina wuni anyi sallah lafiya?" Ta amsa min tana me fara'a, da ya ke haka yaranta ke kiranta da Hajiya nima hakan nake kiranta.

  Na zauna kusa da Zainab anata hira kamar nima daman ƴar gidan ce, na lura da kallon da Yah Marwan ke min hakan yasa na kasa sakewa, na ɗago ido kenan sai kawai muka haɗa ido dashi na kallesa sosai, baƙi ne shi duk da a zaune yake zaka iya ga ne yana da tsayi ba laifi kyakkyawa ne, fatar jikinsa daga gani kasan akwai hutu, sanye yake cikin ƙananun kaya dogon wando da t-shirt.

Ganin ba zan iya jure kallonsa ba yasa nayi ƙasa da kaina ina wasa da ya tsun hannayena...

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.