Free chapter · Read without an account
Chapter 2 chapter 2
by autararewa101 · SUDESS
🌈🌈 *SUDESS*🌈🌈
*Written story*
*By*
*AUTAR AREWA*
_Ina yima masoyana_ _albishir ga duk wanda bai_ _samu krnt Book ɗin_ _DR MUHSEEN ba, to_ _ya_ _garzaya Wattpad_ _domin samun_ _nishaɗi,But wannan Book_ _ɗin da nake yi mai_ _suna SUDESS_ _na_ _kuɗi_ _ne_ .
*Paid Book ne akan farashi mai sauki ₦500 kacal 👌 za ki sha krt cikin kwanciyar hankali,ta wannan Account 3125654602 Rukayya Idris first Bank,ki turo shaidar biyan ta wann Nomber ***,ko hoton katin MTN pls banda VTU 🥰🥰 Idan kinsan ba siya zaki yi ba kada mu ɓatawa juna time*.
*Bismallahi Rahamir Rahim*.
*Free page* 2️⃣
📝.................Yana kokarin buɗe fuskarta da yalwataccen gashinta ya rufe.Da sauri Salisu driver ya ce "Sir muyi kokarin Kaita asibiti kada ta rasa ranta".
Da sauri SUDESS ya ɗauke ta cak ya nufi bayan motar,Salisu ya buɗe ya kwantar da ita,bayyi tunanin jinin dake zuba a jikinta ba haka ya zauna ya ɗora kanta bisa cinyar shi,dan gaba ɗaya a ruɗe yake sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi,dan shi mutum ne mai tsananin tausayi.Jin sun fita daga unguwar yasa hankalin shi ya fara dawowa jikin shi,kallan fuskarta yayi yaga har yanzu babu alamar numfashi a tare da ita.Muryar Salisu ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula.
"Sir wane Hospital zamu kaita?"
Cikin sanyi jiki ya amsa da "pls salisu Ina ganin idan mun je Hospital to dole zasu ce mu zo da ɗan sanda,Ni kuma bana san abin yayi nisa tunda bisa tsautsayi ne hakan ya faru" Ya idar da maganar yana duban agogon dake ɗauke a tsintsiyar hannun shi,ganin har karfe goma ta kusa ya yi saurin ɗaukar wayar shi tare da dialing wata Nomber.sai gaf da zata katse kafin aka yi picking.Ko gaisuwa bai tsaya yi ba ya ce "Pls Doctor Mujaheed kana gari ne?".Ban ji amsar da aka bashi ba ya kara cewa "To dan Allah yanzu ka same ni a gidana,na shigo ne yau,to wata yarinya ce Salisu ya kaɗeta"katse call ɗin ya yi yana cewa "Tnx U Doctor".
Duk maganar da suke yi Salisu yana ji hakan yasa ya kara gudun motar yana ɗaukar hanyar da zata sada shi da unguwar GRA inda gidan ogan nashi yake.
Suna karasowa bakin gate saiga motar Doctor Mujaheed ta shigo layin.Kusan a tare suka shiga bayan gate man ya buɗe masu.Ba tare da jinkiri ba SUDESS ya kara saɓarta zuwa cikin babban falon nashi da yake cike da kayan alatu na zamani su Salisu da Doctor Mujaheed suna biye da shi a baya.wani karamin bedroom ya shiga,ya shimfiɗeta saman bed kafin Doctor Mujaheed ya fara dubata cikin kwarewa da sanin makamar aiki.Ganin haka yasa SUDESS wucewa room ɗin shi,saman bed ya aje phones ɗin shi da watch kafin ya nufi toilet ya sakarma kanshi shower,ajiyar zuciya yake saukewa jin yadda ruwan yake ratsa kofofin jikin shi.
Karfe 10:30 Doctor Mujaheed ya gama dubata,bayan ya ɗaura mata drip ya zuba allurai a cikin ruwan,sauran magungunan da ya rubuta yaba Salisu takardar ya je Farida chemist center ya siyo,dayake ba nisa nan cikin kwaɗo ne a cikin short time ya dawo,shiko gogan tun bayan fitowar shi da ga toilet ya ɗauko wata farar jallabiya cikin wheredrop ya zira tare da feshe jikin shi da Arabia Uhud masu sanyin kamashi,kafin ya nufo ɗakin da yarinyar take kwance.sosai ya ji daɗin ganin komai ya tafi yadda yake so.Tare suka fito da Doctor Mujaheed ya rako shi har bakin motar shi,inda ya kara yimai bayanin sai an kula da ita sosai,Allah ya taimaka kanta bai bugu ba sai raunikan da ta samu,amma insha Allah zata warware.
Sallama suka yi yayimai godiya da cewar zai ga alart gobe insha Allah.Daga haka ya koma ciki. A falo ya tadda Salisu saida ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon kafin ya dubi Salisu yana cewa "Pls ka je Hotels ɗin nan ka tahoman da kayana,kayi signing daman sunanka ne a rubuce" da "Ok sir" salisu ya amsa kafin ya fice daga gidan.
SUDESS ya daɗe zaune a wurin yana saka da warwara,sai a time ɗin ya ji wata yunwa tana tasomai.mikewa yayi yana shafa cikin shi,lekawa yayi ɗakin da take kwance ganin bata farka ba yasa ya wuce bedroom ɗin shi.
Kwanciya ya yi yana jingina bayanshi da allon gadon kafin ya ɗauko phones ɗin shi, Misscall ya gani masu yawa,haka ya fara dubawa ganin Misscall ɗin Momy da *AUTAH* yasa yayi dialling Nomber Momy yana kara wayar a kunnen shi.
A Abuja kuwa daidai wannan lokacin Momy ce zaune a falo ita da mai gidanta wato Alhaji *MUSA MASANAWA* ta kawomai kayan marmari,kallan news yake yi jefi-jefi suna taɓa hira akan abinda ya shafi iyalan nasu,anan ne Alhaji Musa ya ce ta kiramai SUDESS ya ji ya isa lafiya,tunda ya tafi basuyi waya ba.kiran da tayi mai baya kusa da wayan,sai yanzu ya kirata.
Da sauri ta yi picking call ɗin ganin Nomber SUDESS.
"Assalamu Alaikum Momy barka da dare,afuwan Momy ban kira ku ba,Wallahi ban zauna ba sai yanzu".
Saida ta amsa sallamar kafin ta ce "Ayya sannu my son,ka zama mai juriya ka ji,shi neman halak sai an jajir ce".
Sosai yake jin daɗin yadda Momy take karamai karfin guywa a lamurran shi hakan yasa yake yin komai with compidens.
Sun daɗe suna waya kafin ta mikama Dadyn shi suka gaisa,saida ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce "Am,,mm Momy Ina AUTAH naga Misscall ɗinta,amma na kira wayan bata shiga"Ya karasa maganar yana sosa kanshi alamar ya ji nauyin tambayar.
"Ta yi bacci tun ɗazu,tana part ɗinsu". Daga haka dai suka katse call ɗin.Text yayima Salisu akan ya tsaya ya siyomasu abinci kafin ya taho.
Sai around 11 kafin yayi shirin kwanciya bayan ya kaima peshent ɗin shi abinci.ya kwanta bayan ya duba chart.Wuraren karfe biyu na dare ya koma ɗakinta ganin drip ɗin ya kare ya ciremata.A hankali yarinyar ta fara girgiza kanta tare da kokarin motsa hannunta.Ganin tana motsa bakinta alamar tana san yin magana,yasa yayi saurin kara kunnenshi.Baya jin me take cewa saboda Muryar ta bata fita.A hankali ta buɗe eyes ɗinta akan shi,ganin ta farka ya furta "Sannu ta shi ki yi brosh ki ci abinci"ita dai binshi take yi da ido dan bata jin me yake cewa.
Kokarin tashi ta fara ganin haka ya ya kamata ta zauna.
Suffarta yake kallo ganin kama take yi da ƴaƴan larabawa.Ganin irin kallan da yake jifanta da shi yasa tayi saurin yin kasa da kanta tana kallan ɗan karamin yatsanta saboda ciwo.A rashi yayi tunanin bari yayimata mgn da yaren turanci kota fahimci abinda yake nufi.
Cikin ikon Allah yana yimata yaren turanci ta fahimci abinda yake nufi,ganin ta sauko da ga bed ɗin ya nuna mata toilet.saida ya ga ta shiga kafin ya fice daga ɗakin.
*Washe gari*
Kiran sallar farko akan kunnen shi,haka yasa ya fito danya duba ko tana lpy.Lokacin daya fito falon babu haske sai yayi amfani da wayar shi ya haska.tura kofar ya yi ya jita a buɗe ya shiga.Light ya kunna ɗakin ya gauraye da haske,ganin bata kan bed ɗin yasa ya ja ya yi tsaye yana tunanin ina ta nufa.Bakin kofar toilet ya matsa yana Kara kunnenshi ko zai ji karan ruwa,jin shiru babu alama yayi saurin tura kofar yana tunanin a ranshi ina yarinyar nan ta nufa.Ihun data kwallah yasa yayi saurin kallan cikin toilet ɗin dan tantancema kunnen shi inda sautin ya fito,Saurin runtse idanuwan shi yayi saboda irin abinda idonshi ya haskomai, ɓammmmmmmm ya yi saurin janyo kofar yana jin gaba ɗayan tsikar jikin shi ta tashi.
*By*
*AUTAR AREWA*
✍️✍️✍️✍️✍️