Free chapter · Read without an account
Chapter 19 Chapter 19
ZAMANINMU!!!!!
(Hattara yanmata)
Written story
By
AUTAR AREWA
BISMALLAHI RAHAMANIR RAHIM.
*Abinda musulmi zai ce* *idan ya zo yabon wani* *musulmi*
*_Manzon tsira da* *amincin_ _Allah_ _su_* *_tabbata a gare shi ya ce_* " *_Idan har dayan ku* *ba_ _makawa sai ya* *yabi_ _abokin sa,to ya* *ce:Ina_ _zaton wane* __ *Allah shi_ _ne* *dai makiyayin sa,Mai_ _yi* *masa hisabi,Kuma* *ni_ _bana tsarkake kowa* *ga_ _Allah -- Ina* *zato shi_ _kaza-da-kaza* *ne* ( *idan_* *_har mutum* *yasan hakan_ _dangane* *da wannan_* *_musulmi_* ).
🅿️19
📝 Shigowar doctor yasa kowa koma gefe daya.
"Ina abincin na ba shi, Dan ya sha magani, saboda ana bukatar ya Kara samun hutu" cewar shi Yana kallan gefen da suke.
Momy ce ta fara mikewa dan kaima shi Dady yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa "Farrah ta so ki ba shi".
A hankali ta mike cikin sanyin jiki ta dauko plate din da ta zuba arish a ciki tare da cop, cokalin take zuyawa a hankali.
Shiko hannunta kawai yake kallo yanda take komai cikin sanyi,Amma Yana ga kamar a tsorace take.
Yana wannan tinanin ya ji maganar ta daki kunnan shi.
"Yaya ga shi"tana miko ma shi.
Wurin da su Momy suke ya kalla sai yaga hankalin su baya wurin dan su Abba tuni sun fi ce shida Dady domin su jira fitowar doctor.
A hankali ya mayar da eyes din shi ya rufe tare da Kara jingina kanshi da jikin filo.
Sororo tayi tana kallan shi a ranta ta ce "wannan gay din Dan rainin wayo ne,Yana ji zai yi wani forget da ni".
Ganin haka da Doctor yayi yasa ya cewa su Momy su je waje su jira shi.Ya dawo da hankalin shi kan Yasir Yana cema shi "Tashi zaune sosai ka sha na baka druks idan ba haka ba bazamu yi discharge din ka a gobe ba".
Da sauri ya bude eyes din shi tar sai akan Farrah suka sauka sosai ya tsare ta da kallo yadda rouwn face dinta futo a cikin dogon hijaf din da ta saka.
Sai a sannan ta ankare da yadda ya tsareta da kallo.
Idanunta ta fara janye wa da ga cikin nashi,sakamon yadda taji wata muguwar kasala ta Kara saukoma ta.
Gyaran murya doctor yayi cikin dariya yake cema su "Ni Bari na tafi idan kun gama kallan love din na dawo na baka druks din ko? Tunda kun manta da ni a tsaye "ya karasa maganar Yana duban su.
Sosai ya ji kunya ta kamata ta Kara kauda kanta,A zuciyar ta tana cewa "Allah ya sauwake zuciyata ta rasa Wanda zata so sai wannan mai idanu kwala-kwala iri na Yan chaina,Allah ya sauwake ni Swety Hasan ne kadai a ruhina".
Maganar Doctor ta dawo da ita daga dan lulawar da tayi duniyar tunani.
Matso ki ba shi dan na fahimci abin naku ba mai karewa ne ba.
Jikin gadon ta Kara matsawa tana Mika ma shi cop di alamar ya amsa da hannun shi.
Yasir ya fahimci haka kawai sai ya buda bakin shi alamar anan zata ba shi.
Cikin nutsuwa ta fara ba shi Yana kurba har ya kusan shanyewa duk motsinta Yana Kan idanun shi,duk ji tayi ta takura har ta matsu ta gama ba shi ta fita daga dakin ga doctor ya saka su a gaba Yana kallan su kamar ya samu tv.
Arish ta dauko da wainar kwan zata fara ba shi da cokali mai yatsu cikin murya irin ta marassa lafiya ce "ki bani da hannu bana so da cokali"Yana kara kafeta da eyes din shi masu kashe mata jiki.
Tana jin shi tayi biris da shi ta dauko da cokalin a ranta tana cewa sai ka ce na zama baiwarka dole kake bani comment .
Kin bude bakin yayi Kuma ya Kara yimata kir da eyes din shi.
Duk abinda suke yi doctor Yana jin su,Dan Yana wasu cike- cike a file din shi.
"Ki taimaka madam ki ba shi da hannun Dan naga alamar wanna peshent din namu taurin Kai ne da shi " Yana duban su,Dan sun birge shi sosai daga gani akwai boyayayr soyayya mai zafi a tsakanin su duk da ya hango rashin jituwa .
Bata ce komai ba ta fara ba shi da kyakkyawan hannun ta na dama.
Sosai yake ci har wani lumshe eyes din shi take yi.saida ya ji ya koshi tana kai mai wata lomar ya hada da yatsunta biyu ya taune da karfi Yana sane yayi haka.
Zabura tayi ta kwalla wani uban Kara tana yarfe hannun ta,a kasa ta yada plate din ta hau tsalle da yarfe hannun tuni hawaye sun wanke ma ta fara fuskarta.
Tasowa doctor yayi daga kujerar da yake saboda shi kanshi ya tsorata Kira take"Subahanallahi meya faru"Yana kokarin ruko hannun nata.
Yasir Yana ganin haka da sauri ya diro daga Kan gadon,cikin karfin hali ya turo doctor sai ga shi ya dira a gabanta,Dan shi harga Allah bazai yarda ba a gaban shi wani kato rike mai hannun mata.
Hannun ta yake kokarin komawa su Momy suka shigo jin karar daga dakin ta ke,Daman suna bakin kofar daga waje.
Momy gurin Farrah ta nufa ganin yanda take yarfa hannu.
"Ke meya sameki da wannan daren kike yiwa mutane Kara haka"?tana murza ma ta yatsun.
Farrah ba baka sai kunne,Dan ita kadai tasan irin zugin da take ji a yatsunta kamar zasu cire Dan azaba.
Kanta take juyawa karfe ta rungume Momy tana hawaye masu zafi a zuciyar ta tana cewa "wato duk cutar da yake yi ma ta Bata isheshi ba har sai ya cire mata yatsu Dan idan ya nakasata saita rasa mai auranta ko".
A hankali Momy take shafa bayanta alamar tayi hakuri.
Shiko gogan naka tun shigowar su Momy ya koma Kan gado ya konta tare da rufe eyes din shi ruf,Yana jin duk hayaniyar da suke har suka fita daga room din bai motsa ba.
Doctor ya dauko druks din shi da gorar ruwa na faro Yana cewa "marar jin magana saika ta shi tunda ka kusa cirema diyar mutane yatsu saboda mugunta,wallahi da nasan haka zaka yi bazan ce ta baka abincin ba".
Bude idanun shi yayi Yana cema doctorn "wallahi ji nayi ina na cijeta,Daman ta saba Shan cizona tun tana karamar ta yanzu naga tana neman rainani dqn ta ga ta zama cikakkiyar budurwa shiyasa nayi haka Dan ta tuno ni sosai".
Doctor dariya yayi ya ce "wato ku irin taku salan soyayyar kenan "?.
"Hmmm Kai kadai ka fahimci haka,Amma su iyayen mu sun kasa lura har suke Shirin bada ta ga wani daban" cewar Yasir bayan ya shanye maganin.
"To Yasir konta ka huta insha Allah zuwa gobe zaka koma gida"Yana tattara kayan shi ya wuce office dinshi.
Yasir ko Bacci ha koma tare da damuwa fal a cikin zuciyar shi,duk da a wani bangaren na zuciyar shi bai ji dadin abinda yayi mata ba,Amma hakan yayi Dan yafi so yadda zafin son da yake yimata yake hana shi bacci a Lokutta da yawa,gwamma itama yau ta ji irin zugin da yake ji.
Farrah kuwa ana fita fa ita wata likita da duba hannun nata ba wani rauni a wurin sai 'ja' da yatsun suka yi.
Magani kawai aka bata suka fita waje.
Jabir suka gani a jikin motar Abbah Yana waya.yana ganin sun fito ya katse wayar Yana nufowa inda suke.
"Momy har kun fito"?
"Eh wallahi Jabir dan Allah zoka mayar da mu gida dare kara yi yake,ga farra ta ji rauni w hannu"
Cikin rudewa yake kokarin kama hannun Farrah Yana cewa "meya sameta a hannun".
Farrah tana ganin irin kallan da Ummah take jifarta da shi Hakan yasa tayi saurin nufar wurin motar ta shige tana sauke ajiyar zuciya.
Suma motar suka shiga ya jasu zuwa Barhim cikin su ba Wanda ya Kara magana har ya sauke su Momy da Farrah ya nufi GRA Dan sauke Ummahn tasu.
Whattpad user
@rukyyidrsi
Psl follow and share 👏
BY
AUTAR AREWA