Free chapter · Read without an account

2

by Aisha Ahmed Machika · Halin Dana Shiga...

🤳🏻


💘 нalιn dana ѕнιga...💘



© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ



*Arewabooks@Shooly84*





*S͢A͢D͢A͢U͢K͢A͢R͢ WA G͢A͢R͢E͢K͢U*...


*ᴷᴴᴬᴰᴵᶻᴬ ᵁˢᴹᴬᴺ*

*ᴺᴬᴮᴵᴸᴬ ˢᵁᴸᴬᴵᴹᴬᴺ*

*Ɗᴬᴵᵞᵞᴵᴮᴬ ᴵᴰᴿᴵˢ*

*ᴴᴬᵁᵂᴬ ᴬᴸᴵᵞᵁ ᴿᴬᴮᴬᴴ*

*ᶠᴬᵁᶻᴵᵞᵞᴬ ᴰᴬᵁᴰᴬ*




💘 2 💘








  Da daddare muna cin abinci afalo tare da Farida, Mami tayi baƙi suna ɗakinta,wayata tana gefe ta fara tsuwwa na duba naga baƙuwar lamba,ban ɗauka ba naci gaba da cin abincina,Farida tace bai kamata ki ƙyale ba,nace bansan ko waye ba barta kawai, kiran ya yanke...


Lokaci kaɗan aka sake kira Farida tayi saurin ɗauka ta amsa da sallama, naji tace ba ita bace bari abata, ina harararta tasamin wayar a kunne tana dariya, waye? 


Na tambaya muryata adaƙile, yi haƙuri ba abin faɗa bane, na ƙara ɗaure fuska jin muryar namiji, kina saurarena? Na amsa da ummm yi maganarka...


Ya yi ɗan shiru can ya nisa yace " da fatan ba zaki damu ba"?


Nace inba abin damuwar zaka faɗa min ba, ya yi ƴar dariya da faɗin Asiyah kenan yaci gaba da cewa, da yamma muna tare da yayanki Hashim anan ƙofar gidanku na rako abokina wajenshi, kwatsam Allah ya nuna mani ke, wallahi ina ganinki Asiyah zuciyata ta harba nan take na amince wa zuciyata ina sonki so mai ƙarfi...


Yai shiru kaɗan, me kika ce Asiyah? 


Zan iya zuwa mu gana?


Abinda ya ɗanja hankalina gareshi jin muryanshi ba yarinta, haka nan kalamanshi babu wasa, duk da cewa bawai na amunta da kalaman nashi bane sai naji ina son ganin nashi koda kuwa ban bashi fuskar yin wata mu'amula ba.


Kinyi shiru Asiyah me kike gani game dani?


A yanzu dai bani da lokaci...ya tare ni ba lallai sai yau ba, zuwa gobe ma in kina so ina iya zuwa, na ɗan yatsina fuska tamkar agabanshi nake nace sai ka zo ɗin, ban ƙara sauraren shi ba na kashe wayar.


Farida data zuba mun ido cikin mamaki da al'ajabina tace Allah ya kyauta, wannan hasken fatar taki da kyan fuska dana jiki ke ruɗarki kina wulaƙanta bayin Allah, Allah ya rufa asiri da ya yi ki doguwar mace da an bani, ki dai yi ahankali akwai ranar dana sani...



Washe gari na dawo makaranta na iske baƙona yana jirana, muka gaisa amutunce dan sanin abokin ɗan'uwana ne, gani nazo Asiyah, na kalleshi na gane maganarshi, kyakkyawane dan jiya ban wani tsaya na kallesu ba sai yaune na laƙanci kamanninshi.


Wankan tarwaɗa ne yana da dogon hanci da idanuwa masu girma a fuskarshi ya bar gashi ya kewaye fuskar da ƙasan hancinshi.


Ya gari? Na ɗanyi murmushi yana wajanku, ko amma dai da zakiyi adalci sai kice yana wajanku ƴan mata nace uhm kawai..


Nan ya hau zuba yace wannan yace wancan, ni dai da Allah yayini ba mai magana ba jinshi kawai nake ina gyada kai, tsayin lokaci mukai sallama bayan na nuna mashi buƙatata tason shiga gida.


Mun rabu ba tare da samun wani gamsasshen bayani daga gareni ba, ni kaina bansan ame na ɗaukeshi ba, nasan dai araina bana ƙinshi kawai.



Kullum da yamma Nura kan zama abokin hirata, tun bana iya sake mashi muyi magana harta kaiga yawan zuwanshi gareni ya sani soma jinshi ajikina, sai dai ba wai sonshi naji inayi ba, a'a mun dai yi sabone mai ƙarfi har ina rayawa araina zan iya zaman aure dashi in halin hakan ya yiwu.


Amma wani abun mamaki lokacin da shaƙuwa ta ƙara shiga tsakaninmu sai naji na fara sashi araina, ina damuwa dashi ina son kasancewa tare dashi ako yaushe, aƙarshe dai na yarjewa kaina son Nura nake.



Nasha tsiya wajen Anty Lubah, wai yau Allah ya nuna mata gwanina, na kanyi dariya nace ki bari dai kiga in za'a kai labari...



      *******


Na amsa wayar Abdul daga Delta ina bashi labarin Nura, ya yi dariya yace " kice dai shi ya ciri tuta tunda ya samu fada awajenki, nayi ƴar dariya nace harda kai Abdul da faɗin irin haka?


Yace " aiko ni ya kamata na faɗi haka mutane nawa agabana suke nuna suna ra'ayinki kice ke sam ba suyi maki ba?


Wasu ma fa dan tsabar wulaƙanci sai kin basu fuska magana tayi nisa atsakaninku ki ɓullo masu da ire-iren wulaƙancinki, a ƙarshe ki koresu kice bakya yi, nace amma dai kasan duk irin waɗanda kake magana yara ne ko?


To shi wannan ya yake?


Ba laifi yanada ɗan shekaru dan na tabbata kaɗan zaka girmeshi...mts yai tsaki, shi ɗinma nasan ƙarshenta dai yanda kika yiwa waɗancanne, Allah ya taimakeshi kar ahaɗa mishi da...sharri kake son yimin Abdul, na katse layin ina dariya.





Tsakanina da Nura abin sha'awa ni kaina ina mamakin yanda na saki jiki dashi har muna maganar aure, duk da cewa adai-dai wannan lokacin ban shirya aure ba, amma na yadda na amince inna tashi Nura shine zaɓina.





Tsayin zamana da Nura bai taɓa faɗamin yanada mata ba, bai taɓa nuna min wata alama ba da zai sa na gane yana da mata ba, sau tari in muna hira nakan nuna mashi ra'ayina na rashin son kishiya...



Ya kanyi mani dariya yace " ai ajinki ya wuce ahaɗaki da wata ma ace amatsayin kishiya, ni inna aureki shikenan na rufe aure keda zama da kishiya sai dai na *Hurul'aini* (Matan Aljanna) suma in baki so saina roƙi Allah ya barni dake kawai.


Yasha rantse mani baida sha'awar mata biyu, yasha faɗa min ba zai min kishiya ba ni kaɗaice zaɓin shi, ashe abun nashi munafunci ne zalla babu gaskiya aciki.




Mami ta kirani awaya ina makaranta ta bani saƙo inna tashi na biya kasuwa nayo mata siyayya, kasuwar Ceceniya na shiga na ɓata aƙalla awa ɗaya wajen aiken Mami, na kammala na fito daga shagon dana sayi laces idona ya faɗa kan Nura ina fitowa kenan.


Abinda ya ɗan so ya faɗar mani da gaba ganinshi tare da wata mace, tayi shigarta irinta matan aure, wato ta rufe jikinta duka da babban mayafi, atamfa ce jikinta ba zan iya tantance wace iri bace sai dai kalarta bulu ce, mayafinta fari da bulun takalmi ta rataya farar jakka akafaɗarta.


Nura ɗauke da yarinya akafaɗarshi, aƙalla inaga ba zata zarta wata tara zuwa shekara ba, cikin nishaɗi suke tafiya suna hira atsakaninsu, ni ko na bishi da kallon mamaki da tunanin wace wannan ke tare da Nura meye kuma atsakaninsu?


Har zasu gotani ya kula dani atsaye, yai min wani irin kallo irin na mamaki ko tsoron ganina ya tsaya, ya kalli matar da suke tare atsorace kana ya sake kallona, ya gyara fuskarshi ta hanyar yin murmushi tare da kiran sunana.


Malama Asiyah kice a kasuwa haka?


Matar da suke taren ta kalleni nan da nan ta ɓata fuska, nima na ɗaure tawa ina mata kallon tuhuma, Asiyah Nura ya kirani muryanshi a raunane na maida kallona gareshi, yai min nuni da matar da suke tare yaci gaba da magana...



Kinga matata Maryam da nake baki labari sai ƴarmu Fariha ya nuna yarinyar dake hannunshi, yai saurin kallon matar yace ga Asiyah ƙanwar abokina ce.


Kalmomin nashi sukai mugun ɓata min rai da tayar da hankalina.


Wai matarshi ya gabatar min abinda ko amafarki ban taɓa zato ba, ni kuma ya gabatar matani amatsayin ƙanwar abokinshi...


Lallai wannan rainin hankalin ya girmama, a zuciyata na ringa ayyana wanne irin hukunci ya dace naiwa Nura bisa wannan abun?


Ƙamin na yanke shawara sai na shawarci kaina da abu ɗaya.


Na saki jiki muka gaisa da Maryam harna karɓi Babynsu nai mata wasa na yaba da kyan yarinyar, daga bisani nai masu sallama muka rabu ba tare dana bari ko kaɗan ya karanci ɓacin rai akan fuskata ba.



Gidan Anty Lubah na tsaya zuciyata na tafarfasa da ɓacin rai na gaya mata abinda ya faru, itama ta daɗe tana mamaki daga bisa ta nisa tace, "to amma meyasa tun haɗuwarku bai gaya maki yana da mata ba?


Na juya kai Allah kaɗai ya sani, tunanina yaudara ce kawai yake bina da ita, ba wai son gaskiya yake min ba, karkiyi saurin kawo haka aranki, ina ganin akwai dalilin da yasa ya ɓoye maki hakan, mai yiwuwa ma zafin kishin daya kula kinada shine...



Na girgiza kai cike da ɓacin rai, na miƙe ina faɗin zanyi maganin duk abinda yake nufi.



Cikin gidanmu babu wanda na faɗi ma abinda ya faru, sai dai duk sun kula na wuni ne cikin ɓacin rai, da daddare harna fara bacci wayata ta tadani naga Nura ne...


Ɓacin rai ya sake kamani meye zaice dani?


Kamar karna ɗauka sai kuma nayi tunanin na nuna mashi sam ba cikin baƙin cikinshi nake ba, na ɗaga wayar bakina da sallama, ya amsa da faɗin na tadaki bacci ko? Na amsa da eh wallahi ko.


Ya ɗanyi shiru can ya numfasa da faɗin dama Asiyah maganar Maryam ce, nasan abin zai ɓata maki rai kiyi tuanin yaudararki nake sonyi shiyasa na ɓoye maki batunta...


Ko ɗaya karka kawo hakan aranka Nura, na katseshi da faɗin haka, naci gaba da cewa bakamin siffan mayaudara ba shiyasa kome zaka min ba zan baka wancan sunan ba, illa dai na nemi tsari da kai da irin halinka, dan tunda kamin haka na tabbata wataran zaka min abinda yafi hakan...


Wallahi Asiyah ba komi...karka damu kuma ka daina rantsuwa akaina, sai dai inda hali ina son ka mantani zan so ka cire batuna aranka gaba ɗaya cikin rayuwarka...amma dai Asi...na katse maganarshi ta hanyar kashe wayar gaba ɗaya na koma nai kwanciyata.





Na tattara batun Nura na watsar agefe, duk wani shiri da nai na auranshi na rusheshi, ni sai a lokacin ne ma na rinƙa fahimtar ashema ba wani sonshi nake ba, kawai shaƙuwa ce da mukayi tasa na damu dashi.


Shiko anashi ɓangaran yana nan yana naci shi dai nayi haƙuri mu sasanta.


            *******


Bayan rabuwata da Nura nayi tarkacen samari bila adadin ko da yake da yawa ba shiga harkansu nake ba sai dai suyita shirmensu harsu gaji su kyaleni.


Akwai wani Isma'il wanda shi azahirin gaskiya shida gaske son aurena yake, to sai dai ni gaba ɗaya bai kwanta mani ba dan yayi yarinta da yawa.


Koda yake ya girmeni da aƙalla shekaru biyar, to amma ni anawa ra'ayin nakan so ace manemina ya girmeni da aƙalla shekaru goma.


Isma'il akwai naci duk yammaci yana ƙofar gidanmu, wani lokacin nakan shiga harkanshi, wani sa'in kuma haka nake barinshi yaita shawagi tsakanin layinmu inya gaji yaja jikinshi ya tafi...


Rannan dai dana haji yana aikowa kirana na fita na haushi da faɗa, ni kaina bansan faɗan na miye ba, na dai haushi da bala'i ta inda nake shiga bata nan nake fita ba, shiko baice min komai ba harna gaji na juya na shige gida.


Toh tun daga lokacin ban sake jin ɗuriyar Isma'il ba...



Na tsaida hankali wajan karatuna bani da matsalar komai, duk abinda ya shige min duhu ga Abdul da Bashar nan dan alokacin sun kammala nasu karatun har sun samu aiki a nan Kaduna Refinary, wanda Abbanmu yai masu cuku-cukun samu...


Cikin wannan lokacin na rinƙa tara samari aƙalla arana sai nayi taɗi da samari wajan biyar, kuma wanda ya zo yau bashi bane gobe.


Wani abu da ni kaina yake ɗaure min kai da halina shine yanzune zan sami saurayi lumi-lumi muta soyayya wata ɗaya zuwa biyu sai naji ya fita raina na tsaneshi bansan ko ganinshi, tuni zan watsar dashi na kama wani, shima lokaci kaɗan zanyi canji da wani, wani lokacin kuma tuni zanji samarin gaba ɗaya sun isheni naji na tsanesu, irin wannan lokacinne na kan haɗasu gaba daya na koresu.


A lokacin sai najini sakayau nafi jin daɗi nayita rayuwata cikin kwanciyar hankali, to kuma in ankwana biyu naji ina ra'ayin taɗin da kaina zan rinƙa nemo samarin ta waya da tsokana zan fara flashing suko kamar jira suke sai kaga ɗaya bayan ɗaya sun fara dawowa.


       

           ********



Abdul-jabbar kwatsam ya bijiro min da maganar aure daga ganina dashi na farko, ya rako abokinshi wajen Farida ta kirani mu gaisa da Abubakar wanda alokacin ake maganar aurensu ne sai dai ba'a riga an tsaida rana ba.



Kamar wasa Abdul-jabbar ya nuna yana sona, wani abinda ya bani mamaki yanda duk ƴan gidanmu suka amince dashi har Mami, babu mai kusheshi sai dai yaba mashi da son saminshi cikin zuciyata...


Ni kuma gaba ɗaya Abdul-jabbar baya gabana dan a gaskiya ba irin namijin da nike muraɗin aure bane.


Abdul-jabbar kyakkyawa ne yana da ilmin da hankali gashi dai-dai gwargwado Allah ya rufa mashi asiri, amma illarshi ɗaya wajena bashi da tsayi, ni kuma haka Allah ya yini gaskiya bana son gajeran namiji, ni gajera kuma mijina gajere ai akwai sake.



Babu irin artabun da bamayi da Farida kullum cikin yiwa Abdul-jabbar campain take, har takan kaimu da faɗa inna nuna bana sonshi, ita ko Mami ahankali take bina da nasiha, sau tari takan zaunar dani tace niko na rasa illar Abdul-jabbar Asiyah.


Na kanyi ƴar dariya nace nifa Mami bance ga illarshi ba, to me zaisa ba zaki tsaida hankalinki akanshi ba, yaron kirki mai hankali yana ganin mutuncin kowa, baida kwaramniya irinta sauran samarin da kike tarawa.


Na kan zumɓuri baki nace Mami zakuyi min auren dole ne?


In taga nai fushi saita rabuda dani ta bini da addu'ar Allah ya fito maki da miji nagari Asiyah wanda zaki tsaida hankalinki kanshi...



Itama Anty Lubah kullum ƙorafinta ɗaya ne ta rasa ganin illar Abdul-jabbar, na kanyi mata dariya nace Anty Lubah ya zanyi da gajeren namiji?


Ta harareni matsalolinki sunyi yawa Asiyah, ko wanne namiji awajenki yanada illa, nace ba zaki gane bane Anty Lubah nifa har yanzu banga namijin da yayi dai-dai da rayuwata bane, ta kama haɓa tana kallona...


Asiyah ina guje maki abubuwa da yawa cikin rayuwarki, kamar me da me?


Na tambaya, ta taɓe baki wataran zaki zo da kanki kina neman mijin aure ki rasa, ba baki nake maki ba amma irin yawo da hankali da wulaƙancin da kike ma samari yai yawa...


Nayi ɗan yake ina kallon jikina bance mata komai ba sai dai acikin zuciyata ina tunanin abubuwa da yawa.





Abdul-jabbar har kuka yake sanyani agaba yana min akan na yadda na aure shi, ni kuma naita ƴankwanashi da kyararshi da son yakiceshi daga jikina, amma shi a kullum kamar ƙara iza mishi wutar sona ake...






 Machika novels🤳🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.