Free chapter · Read without an account
14
💘 нalιn dana ѕнιga...💘
~Labarin gaske ne~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
*Arewabooks@shooly84*
*_Not edited_*
💘 *14* 💘
Muhammad ya shigemin rayuwa ya cusa kanshi gareni tun ina ƙi ina basar dashi da nuna mishi tsana har dai nasake na fara sauraron shi musamman dana kula da duk irin tsana da wulaƙancin da nake mishi baya fishi in zai zo yau na zagi Uwashi na zagi Ubanshi ba zai hana mishi dawowa gobe ba kai har marin shi na taɓa yi na kutuntuma mishi ashar amma ko a jikinshi, wannan bai hana kiran wayata ba cikin dare, washe gari da farar safiya wayarshi ce ta tasheni, da yamma yana ƙofar gidanmu kaini wani lokacin nacin shi da rashin zuciyarshi har mamaki suke bani.
Abinda ya rinƙa jan hankalina gareshi muryar da yake mafani da ita wajen yi min magana, muryar da yake amfani da ita ce as Ibaraheem..
Koya yai min magana da ita nakan natsu na maida hankali na gaba ɗaya zuwa gareshi, sai da ya kaiga inya kira muna magana ko alama bana son muyi sallama balle na daina jin dadaɗar muryar dana ƙwallafa rai akanta.
Na dawo makaranta abinci kawai naci na tafi gidan Anti Lubah, muna fira wayar Muhammad ta shigo, wayar na hannunta ta miƙo tana faɗin gafa mera dil.. naki, na ƙarba ina dariya na ce ba dai Real one ɗin ba..
Na amsa wayar da sallama bai amsa mani ba sai cewa yayi I love you Asi, nai shiru kamar koda yaushe kalmar ta shigeni yadda ya dace na maida martani sai dai matsalar wannan Muhammad ne bawai wanda nake tsammani ba Ibraheem.
Baki ce komai ba Asi? Ya katse shirun da mukayi yaci gaba da cewa wai menen aibuna Asiyah?
Abu da yawa na faÉ—a ahankali, yace waike ba kiyin afuwane?
Nai guntun murmushi na ce da banayi dako gaisuwa bata haɗamu ba balle ta kaiga musayar magana, nasan da wannan amma ni matsalata dake kin kasa sakin jiki dani, kamar ya kenan? Na tambayeshi, nasha faɗa miki ina ƙaunarki amma ban taɓa jin martanin kalmar daga gareki ba.
Na ɗan rintse ido na ce abinda kawai kake son ji daga gareni kenan? Ƙwarai ya faɗa.
Nai ƙasa da murya tare da tausasata kwarai na ce ina sonka Ibraheem...
Dukan da Anti Lubah taimin ya hanani jin farkon maganar shi sai ƙarshen inda naji , haba Asiyah Muhammad ne fa, na yatsina fuska na ce na sani...zai sake magana na katseshi kayi haƙuri ina tare da Anti Lubah ka nemeni anjima, banjira daga gareshi ba na kashe wayar.
Na kalli Anti Lubah dake bayanin wulaƙanci dai bai da kyau, na ce wai kema ganinki wulaƙanci nake mishi? Na girgiza kai na ce da zan mishi wulaƙanci wallahi ko'a hanya muka haɗu ba zai nuna ya sanni ba...
Da daddare ina É—akina ina duba testbook saboda akwai gwajin da zamuyi washe gari, wayar Muhammad ta shigo na amsa da sallama...yai saurin tare maganar da zanyi da cewa na damu dake sosai Asi ina sonki da yawa.
Nai ƴar dariya na ce na daɗe ina sanar da kai ina ƙaunarka Ibraheem, yai tsaki yace Muhammad ne fa, nima nai tsakin na ce na sani, yai shiru lokaci kaɗan ya nisa yace wai me yake damunki ne Asiyah?
Kai zan tambaya Muhammad, toni dai dan Allah ki daina kirana Ibraheem, akan me? Na tambaye shi, hakanan dan bana son sunan, nayi dariya ƙasa-ƙasa na ce to sai ka kyaleni in baka son na kiraka dashi, danni harshena da zuciyata sunan shi kawai suka sani, shi suka aminta dashi danya zamo makusancinsu abokin rayuwarsu.
Yai shiru kafin ya furta naji amma dan Allah ki daure ki furta kina sona ko sau É—aya ne, na ce amma nasha faÉ—in haka ko?.
Aike Ibraheem kike cewa ni kuma Muhammad ne, ni kuma anan banga wani banbanci ba, tunda Muhammad É—in shiya sanar dani shi ne Ibraheem, kaga kau dan ance ana son Ibraheem awajen shi zai zan Muhammad É—in akace.
Haka ne ko Asiyah?
Ya tambayeni na ce um, ya ce to na gode da wannan ɗinma amma nayi alƙawarin ahankali zan hana bakinki da zuciyarki raya sunan Ibraheem, nai dariya na ce dako ka taimaka min sosai Muhammad...
Munyi sallama na kwanta ina nazari, zuwa lokacin nan na farajin Muhammad ajikina koba komai nacin shi yana birgeni, kuma wani abu dana ringa nazari akai shine tunda ba Ibraheem mezai hana shi na mallaka mishi ƙaunar da nakejin inaiwa Ibraheem ɗin tunda tun farko duk wasu kalamai naso da ƙauna da nake tsammani ina faɗawa Ibraheem shi ɗin nake faɗawa, ashe kenan ba laifi bane danna maye gurbin wancan Gaibun da shi.
Amma fa duk da haka dare da rana, safe da marece tunanin ainihin wancan Ibraheem É—in da son shi n anan manne azuciyata, inaji ajikina watan-wataran Ibraheem koshi waye duk inda yake indai akwai zai zo gareni...text É—inshi daya shigo shiya kashe tunanin dana tsunduma ciki, na É—auka ina karantawa..
*_Ina son ki da yawa Asiyah amma ke wayonki yai yawa, kin gane ko uhm I love you.._*
Nai murmushi na sake karantawa, rana ta farko dana tsinci laɓɓana suna furta kalmar ina son ka Muhmamad, amma acan cikin zuciyata sai naji wani abu ya sokeni wanda ya kaine ga faɗuwar gaba, kota maye oho!.
_____________________
Al'amura sunci gaba da tafiya tsakanina da Muhammad mun zama abu ɗaya, ƙauna so ba irin wanda bama nuna ma junanmu, sai dai wata masifar na kasa cire Ibraheem azuciyata, tsawon lokacin da aka ɗauka gari bai taɓa wayewa ba, ba tare da sonshi da ƙaunarshi atare dani ba, dare bai taɓayi ba nazo kwanciya kewarshi bata addabeni ba.
Tsawon lokacin da aka ɗauka yaci ace ko sunan Ibraheem na mance azuciyata amma maimakon hakan kulluyaumin kamar son nashi ake ƙara cusamin.
Kaini wannan abu ganinshi nake ya zamemin jaraba son wanda in akwai shima a duniya ƙila wa ƙala ne.
A ɓangaren Abdul kuwa ya sami ciwo kaina mun shirya muna harkokinmu kamar da, sai dai har zuwa lokacin ina jin zafin shi a raina ainun, hatta shi Muhammad ɗin wani lokacin in ƙaunar Ibraheem mai zafi ta bijiro min sai naji gaba ɗaya na tsaneshi naƙi shi naƙi ganin shi, sai da ƙyar yake samu ya ciwo kaina mu dai daita.
Cikin irin wannan lokacin na kammala karatuna, amma Abbanmu ya matsa mani akan sai na koma University nayi karatu mai zurfi, matsawar da yayi ne yasa na amsa mashi da to kawai, danni ba son ci gaban nake ba wanda nayi ya isheni.
Batun Ibraheem kuma na tattara maganarshi na jingineta gefe, gaba ɗaya na rufe babinshi da kowa ko ƙanƙani bana son wano ya tada min ita, na riga na dangana na haƙura na baiwa zuciyata haƙuri kuma domin zuwa yanzu na tabbata da akwaishi da ya zo inda nake ko kuma ya nemeni.
Sai dai fa ko dai-dai da rana ɗaya ban taɓa daina son shi da begenshi ba, ina tsananin ƙaunarshi araina rashin nashi yasani gaba ɗaya na danne son nashi,.na maida hankalina gaba ɗaya wajen ayyukan gida da karance-karance sai kuma ɗan lokacin da nike baiwa Muhammad.
Wanda shi dama abinda yake so kenan na cire maganar Ibraheem da son shi araina, ƙaunar da nai mishi na tattara ta maidata kanshi wanda ko ƙanƙani hakan ba zai taɓa yiwuwa ba..
Son Ibraheem daban yake awajena, dan shikam da akwaishi nayi niyyar bayar da kaina agareshi, amma wani abu da nakeji game da Muhammad, sam bana iya auren shi, dan azuciyata bana mashi irin son da zaka so auren mutum.
Bayan wannan Muhammad ya yi min yaro bai da yawan shekarun da nake so ace mijin da zan aura ya kaisu.
_____________________
Shi kuma Abbah lokacin da nake hanƙoron komawa makaranta shi kuma ya fito da wata maganar data rikitani wai na fito da miji aure zaimin, maganar kamar wasa sai gata ta fara girma.
Da zarar yai tafiya ya dawo zaice to Asiyah ya maganarmu, nakan langwaɓe na ce Abbah kaifa kace makaranta zan koma, ya daka min tsawa yace makarantar anfasa in kinyi aure in mijinki ya yarda kyaci gaba..
In naga ya ɗauki zancen da zafi nikam sai nasa mishi kuka, kukana yakan ɗaga hankalin shi danko ni na zamo abar so agareshi, to da zarar na fara kukan sai yabar maganar ya fara rarrashina yakance shikenan ya isa amma fa kamin na dawo tafiya ki turomin maneminki, nakance to na gode Abbah amma ka ƙara min haƙuri dai.
*Allah mai iko*
Ranar Juma'a ranar data zamo ranar tarihi agareni, ranar da ba zan taɓa mancewe da ita cikin kundin tarihina ba, ranar data zam mai ɗauke da abubuwan mamaki acikinta wanda suka haɗa farin ciki da baƙin ciki.
Misalin takwas na dare muna zaune falon Mami muna shirya kayan lefen Hashim da za'akai cikin satin nan, afalon mun kasance da Mami shi Hashim É—in Abdul da Bashir, Abbas ya fita dasu Rabi'a siyen ice-cream, kuma aranar Abbanmu yai tafiya wanda bai tafinba sai da ya gama zageni akan maganar aure, har yana jadda min lallai nafito mijin aure kamin ya dawo dan yana son ahaÉ—a bikina dana Hashim, wanda alokacin duka bikin Hashim É—in baifi sati uku ba..
Wannan dalilin yasa na yini cikin ɓacin rai, ko alokacin da ake shirin kayan ma zaune kawai nake nakiyin kome dan har alokacin aƙufule nake.
Wayata na caji agefen Mami da Abdul ta soma kuka, Mami ta ciro ta miƙawa Abdul ya miƙo mani na karɓa na duba lambar ban santa ba na amsa da sallama, daga can ɗaya ɓangaren aka amsa sallamar daga nan akai shiru ba'a sake magana ba.
Nima da ban san mai maganar ba naja bakina na tsuƙe, wajen second talatin cikin shiru can ya nisa yace bakice komai ba, na ce uhm ban san mai maganar bane, a'a da gaske baki sanni ba Asiyah lallai na kwafsa da yawa, amma dai yanzu canki waye zai kiraki ahalin yanzu?.
Sai naji muryar taimin kama data wani saurayina Kabir, kullum shima cikin kiran wayata yake, banyi ƙasa da gwiwwa ba na ce Kabir ko?
Akai shiru da jan numfashi, can ya nisa ya ce ashe yawa garemu, gaskiya yanzun nan kinsani damuwa, na damu na ce wai waye ne?
A'a kiyi haƙuri ki bar saurin hasala, duk da haka dai ki canka ni bazan bayyana maki kaina ba, ta hanyar ganeni zaisa nasan wane irin matsayine nake dashi awajenki.
Nayi dariya na ce bana son wasa Muhammad maye na mum wasa ta hanyar canza murya, kana man yawo da hankali, akai É—an tsaki akace ba Muhammad bane, na ce Ahmad ko?
Nura, shima bashi bane, lallai na yadda yawa garemu to amma acikinmu waye aka mallakawa zuciyar?
Nai ɗan dum da alamar tunani waye yake neman rikitamin tunani...banga.laifinki ba dan baki ganeni ba Asiyah, wannan zan iya cewa laifina ne mama duk da haka na damu musamman kan sunayen samarinki da kika rinƙa jero minsu naji zafi irin na kishi har tsakiyar kaina.
Dan haka bari na daure na fahimtar dake koni waye ina fatan zaki maraba ki murna da jina...bakice komai ba, uhm na nisa da faÉ—in ina jinka, ba kina jina ba tukuicin me zaki bani?
Tukun naji ko waye inya so saina san wane irin tukuici ya dace da kai, yai sansanyar dariya yaja murya ya furta mai sonki ne *IBRAHEEM*....
Machika novels