Free chapter · Read without an account

3

by NANA HAFSATU · KAI MIN HALACCI🥰

_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_*............_KAI MIN HALACCI!_*

   💕

 

_*NA_*

 

_*©️NANA HAFSAT_*

 _*(MISS XOXO)_*

 

®️_*HASKE WRITERS ASSO💡_*

 

   *_SHAFI NA UKU_*

 

 

Ganin yadda Shamsu ya zuba mata na mujiya yasa Aliya k'arasawa wajan da yake zaune, yana ganin tahowar ta yayi saurin kawar da kai yana kallon wani wajan daban. Dariya yaji tana yi masa a wajan kansa amman bai tanka mata ba itama juyawa tayi ta shige gidan Talatuwa, cikin d'aga murya take yi musu sallama har sai da ya jiyo shi da yake zaune kofar gida, bawai yau bane ganin sa na farko akanta ba, amman yau shine farkon ganinsa da ita har yaji zuciyarsa ta motsa wanda bai san dalilin hakan ba kodan yasan gidan da tazo ne?, ga wani mugun kwarjini da yaji tayi masa a yau dan ta ‘kara girma akan lokacin da ya santa, ya sosa tsakiyar rantal din kansa tare da d'aga kafad'a alamar rashin damuwa yaci gaba da sana'arsa. 

 

Cikin gidan kuwa tana shiga Talatuwa ta dafe kirji tana zaro ido, a duniya taki jinin Aliya tazo mata gida saboda shegen yawonta, wani lokacin idan tabar gidan sai kayi tunanin sace ta aka yi domin sai dare take dawowa, daka ganta da sassafe kuma ta fita bayan babu wani ciwon hauka ko shafar aljanu a jikinta, kawai tsabar fitina ce da rashin son zama guri guda. Cikin takaici domin sam Talatuwa ba taji dad'in ganinta ba duk surutunta sai Aliya ta ‘kure ta, bata san lokacin da tace da ita.

 

“Aliya zuwa kika yi?” Aliya tana shirin d'aukar goron gwaggo dake kan ice tace.

 

“Zuwa nayi gwaggo Talatu, ko baki yi farin cikin gani na ba kakata ta kaina?”

 

Murmushin yake Talatuwa tayi tana kallan Aliya, ko tace ba tayi farin ciki ba tasan ba komawa zata yi ba dan haka ba taga amfanin cewa eh ba, aikinta taci gaba da yi kafin tace.

 

“Ina su Adama?” Aliya na zama a kan tabarma tace.

 

“Suna can a ‘kauye, ai wallahi inna Adama ta tsaneni gwaggo, kinga yadda ta koroni kuwa wai harda cewa na tafi can inda aka haifi uwata dangin jaraba, wallahi gwaggo so nayi nak'i tahowa tunda ai can d'in ma akwai jini na a gidan, da suka kama suka wani koreni.”

 

Gwaggo Talatuwa ta yatsina fuska tasan kila wani abun ne ya faru shi yasa suka koreta, amman haka kurum Adama ba zata ce Aliya ta taho nan ba har da uban kaya, yadda Adama keji da Aliya saboda abin arzikin da ake kai musu sanadin ta, kasan cewar kyakyawa ce samarin birni idan suka ganta sai sun yaba da halittar fuskarta saboda akwai hanci ga gashin gira da na ido sai dai akwai ‘kauyanci da rashin kunya domin bata ganin girman duk wanda zai yi mata magana ta nasiha ko kayi mata hannunka mai sanda.

 

“Toh Allah ya kyauta.”

 

“Amin gwaggo ina Fa'iza take ne?'” Gwaggo Talatuwa tace.

 

“Tana makaranta kinsan yanzu karatun nasu yayi zafi tace min jarabawa zasu yi ta fita daga primary, kullum cikin karatu take yarinyar nan ko hutawa bata yi ita a dole sai ta zama likita wai.”

 

Dai-dai sannan Fa'iza ta shigo gidan da murnar ta, duk juyawa suka yi suna kallanta taje ta rungume Aliya cikin murnar ganinta dan Shamsu ya shaida mata tazo, raken da ke hannun Fa'iza Aliya ta ‘kwace tana cewa.

 

“Wannan kuma fa Fa'iza, na gutsira?” Fa'iza na k'ok'arin zama tace,

 

“Takice daman aka ce na kawo miki.”

 

“Inji waye?”

 

“Inji Shamsu mai raken dake nan k'ofar gidan, na d'auka siya ki kai kika ce ya aiko miki da ita idan ya yanka?”

 

Girgiza kai Aliya tayi alamun ba siya tayi ba ta fara gatsawa tare da da cewa Fa'iza.

 

“Jeki d'akko wuka na gutsirar miki.”

 

“A'a ni na koshi kisha lafiya.”

 

Fa'iza ta fad'a tana mik'ewa ta shiga d'aki yayin da Aliya ta kanne ido d'aya tana kallon Gwaggo Talatuwa tace.

 

“Kefa gwaggo zaki sha na yankar miki?” Gwaggo ta wani yatsina fuska tana rufe randar ruwan sanyinta tace.

 

“Bana sha sai da kika fara gutsira sannan zaki wani ce zan sha? shi da ya aiko miki da ita ai naga albarkaci na ne tunda ni ya sani ba ke ba, maimakon ki bani kamar yadda aka kawo miki ba tare da an tambayeki ba.” Dariya Aliya tayi, ta kara gabzar bari d’aya tana lumshe idanu, kafin tace. 

 

“Kaji gwaggo nafa san bakya shan rake, tsokanarki kawai nayi amman dubi yadda kika cika gidan da mitarki, ni daman bance na sanshi ba amman dai mai raken nan akwai jarabar iya kallon mata gwaggo.”

 

“Kinga Aliya bana san jan magana daga zuwanki yanzu, ta ya kika san cewar Shamsu nada kallan mata? Ki kuka da kanki wannan karan ba zan lamunci shiriritarki ba na gaya miki.”

 

Farfar tayi da kwayar idanunta tare da tashi tabi bayan Fa'iza da kayanta.

 

Bayan wasu kwanaki cinikin rake ya ragu, gashi ba'a samu. Sana’a ta fara ja da baya hakan yasa Shamsu sake tunanin abin yi tunda babu laifi ya tara kud'i, zaune ya samu Umma a d'aki tana ninke kayanta ya zauna cikin sanyin jiki, duk tana kallansa ba tun yau ba yana cikin damuwa sannan taga ya dena shigo da rake mai yawa sai dai sanda biyu uku zuwa hud'u. Ajiye ninkin tayi tana fuskantarsa cikin nuna alhini da ganin yanayinsa tace mishi.

 

“Shamsu ya dai naga kamar baka jin dad'i?” Sai da yaja numfashi tare da langab'ar da kai sannan yace.

 

“Umma yanzu rake babu kasuwa, gashi lokacin ta ya fara wucewa shine na fara tunanin sake wata sana'ar.”

 

Jan numfashi Umma tayi sannan ta gyara zaman ta tare da matsar da kayan dake gefenta tace dashi.

 

“Haka ne Shamsu, nima na gani wallahi shiru kawai nayi maka dan karka zargi wani abun, amman yanzu tunda da kanka ka gano hakan yanzu wace irin sana'a kake son kayi?” Sai da yaja numfashi sannan yace.

 

“Umma da 'yar tireda zan bud'e na fara siyarda alawa, biscuit, sugar, Maggie, gishiri da dai sauran abubuwan da ba zasu min wahala ba saboda bana san zaman banza wallahi.”

 

“Haka ne Shamsu ai zaman banza ga matashin namiji mai isasshiyar lafiya bai taso ba, saboda ragwantaka ce zaman banza.”

 

Dad'i yaji da yaga Umma ta karb'i maganarsa da muhimmanci, cikin ‘kankanin lokaci Shamsu ya fara sai da kayan buk'ata a nan inda ya saida rake yake zaune yana dorasu akan tebur, duk sanda Aliya ta fito daga gidan gwaggo Talatuwa sai taje gurin sa daga 'yar hira zata kwashi alawoyi da biscuit gashi baya iya hanata ya kasa tantance dalilin da yasa bakinsa yake nauyi wajan yi mata magana wata rana shi yake d'iba ma ya bata, ana haka wata rana da daddare yana zaune shida Kamal domin yanzu duk su Kabeer sun yi nisa ko wanne karatu yake yi babu kama hannun yaro kamal ne yanzu shima kuma hutu yake yi shi yasa suka kasance tare yanzu.

 

Aliya ce tazo zata shiga cikin gida wajan karfe goma sha d'aya lokacin duk an dad'e barin wajen tebur d'in Shamsu sauran shi kad'ai, shima ya fara nannad'e kayansa amman jiran dawowarta yake yi saboda zai yi mata magana, zai fallasa mata sirrin zuciyar sa wanda kullum da ita yake kwana yana tashi ya riga ya tabbatar kaunar yarinyar yake yi gashi lokacin shekarunsa ashirin da biyu yayin da ita kuma a kalla take da shekaru goma sha biyu.

 

“Aliyah tsaya kiji dan Allah.” Cak ta tsaya tare da kallansa tana tsuke fuska saboda a gajiye take yau.

 

“Aliya daga ina kike haka?kinsan karfe nawa yanzu?”

 

Takaici ya rufe ta ko ina ruwansa da ita, amman dan karta b'ata masa rai ya dena bata alayoyi yasa tace.

 

“Wallahi ina gidan su Husna muna kallo.”

 

“Amman sai yanzu kika dawo ke ko tsoro bakya ji.” Kuma kallansa tayi haushi kamar ta buge sa amman ta daure dan ba ta son yabar yi mata abin arzikin da ya saba.

 

“Na dena toh Shamsu a gaida Umma.'” Tayi maganar tana shirin shiga gida ya kuma tsayar da ita.

 

“Aliya kina sona? Ni dai gaskiya ina sonki har cikin zuciyata.” Wani irin kallo tayi masa ta cikin hasken wutar lantarkin dake kunne a kofar gidan yaga yanayin fuskarta, kugu ta rike tare da cewa.

 

“Ni kake so Shamsu? lallai ma, dubeka fa dame kwad'o yafi gaya?”

 

Shamsu ya gyara tsayuwa tare da dafa bango da hannunsa guda d'aya, iska sai d'aga hannun rigarsa take yi kasan cewar dama d'inkin 'yar shara ne, kallanta yayi tsab sannan yace.

 

“Akwai wani kalubale ne tsakanin nida ke da aure ko soyayya ta yiwa shamaki?” Dariya tayi tare da ce masa.

 

“Yo gani nayi duka-duka jarinka nawa yake, sannan kaima yaro ne fa gaka makocin mu, ko ‘kwakkwarar tusa nayi sai ka jiyo a gidan ku, gaskiya ban iya yin soyayya da kai ni ina da saurayina ma yayan Husna idan ka san shi, idan kuma baka ganesa ba toh yaya Sahal nake nufi kuma shi nake so domin shi d'an gayu ne gidan su na 'yan gayu ne, kaga ni sai da safe kaje ka nemi su Dije 'yar gidan malam Rayya ai itama macace kuma makociyarka.''

 

Tana kaiwa nan ta shige gida mamaki da haushi suka kama Shamsu, yanzu wannan 'yar yarinyar ce take gasa masa wannan uwayen maganganun, lallai wannan idan ta k'ara girma ba karamar uwar iyayi za'a yi ba, yanzu Sahal take so kenan saboda su suna da kud'i kuma bama anan yake karatunsa ba yana habuja (Abuja) wannan ne dalilin da yasa Aliya ba zata yi soyayya dashi ba, tabbas zai yi amfani da kalmar nan ta cewar zuciya nason mai kyautata mata, zai ci gaba da yi mata alkairi yana kuma lallashinta har ta yadda da ‘kaunar da yake yi mata.

 

Da kyar ya iya d'aga kafa ya d'ibi sauran kayansa ya shiga cikin gida, da kyar ya samu bacci saboda tsabar tunanin abinda da Aliya tayi masa, shi kansa yana mamakin yadda yake jinta a zuciyarsa gabaki d'aya ta shigesa ba tare da sassauci ko rahama ba. Kwana biyu ya kulla kayan kwalam da makulashe ya bawa Fa'iza ta bata, ana bata ta karb'e ko 'yar aiken guda d'aya-d'aya ta bata kuma harda cewa sai ta gode mata haka Fa'iza tayi mata godiya ita kuma ta b'oye sauran.

 

Washe gari ya rubuta mata wasika ya bawa Fa'iza ta bata, lokacin ba ta nan sai da daddare da ta dawo sannan Fa'iza ta bata sakkon, karb'a tayi kasan cewar tayi primary secondary school ne bata yi ba wadda ake saka ran zata yi anan gidan gwaggo Talatuwa dan har an yiwa Abban su Shamsu magana akan dan Allah ya samowa Aliya makarantar jeka ka dawo wato (day school), bud'e wasikar tayi bayan ta karo fitilar dake ajiye kusa da gwaggo.

 

_''Assalamu alaikum gimbiyata Aliya, hak'ik'a so sahihi ne, so tabbas ne, so guba ne mai zaki da likitoci suka kasa magance maka, tabbas Aliya na had'iyi gubar sonki I lobiyu.''_

 

Wata irin shegiyar dariya ta yi wadda tasa gwaggo Talatuwa dake gefenta sanya hannu ta mangareta, cikin fushi tace da ita.

 

“Wai Aliya dan Allah baki da hankali ne, wannan wace irin dariya ce irin ta mugunta?” Sai da ta sake karantawa still tana dariya kafin ta cewa gwaggo.

 

“Wallahi gwaggo Shamsun nan bashi da hankali, wai fa ni yake so shine yanzu harda rubuto min wasika Fa'iza karb'i ki karanta kiji.”

 

Tayi maganar tana kuma tuntsurewa da dariya yayin da Fa'iza ta karb'i takardar tana dubawa, fuskarta babu walwala domin ita tana son Shamsu hankalinsa da nutsuwarsa tayi mata gashi akwai barkwanci ashe shi Aliya yake so hak'ik'a so beyi mata adalci ba, tana gama karantawa ta ajiyewa Aliya wasikar a gabanta ita kuma ta kwanta tare da cusa kanta cikin zanin da take lullub'a hawaye suna zirarowa daga ida cikin idanunta dan ta tabbatar so bai mata HALACCI ba, ashe Shamsu son Aliya yake shi yasa yake yawan yi mata kyauta, toh mai yasa ta zamo 'yar aikensa koda tana zaune a gida zai kirata ya bata sakko yace ta bawa Aliya wannan wace irin kaddara ce.?

 

Gwaggo Talatuwa rik'e da baki take kallan Aliya jin yadda take cewa Shamsu bashi da hankali kawai dan yace yana sonta, cikin Shiga matuk'ar mamaki tace mata.

 

“Yanzu ke dan baki da mutunci Shamsun kike cewa marar hankali dan kin samu yace yana sonki? ke wai wace irin sakaryar yarinya ce ne Aliya, na rasa wane hali kika biyo domin mahaifiyar ki ba haka nai renonta ba yarinya ce mai hankali da nutsuwa yadda kika ga Fa'iza, ni anya ma ba Fa'iza bace 'yar marigayiya Murjanatu? Saboda rana d'aya aka haifeku kuma a asibiti d'aya ta yiyu canzawa aka yi wallahi, kinga duk wannan d'abi'un nata irin sune na mahaifiyar ki sannan ke kuma d'abi'unki shigen iri d'aya ne da Sulaiman kawun ki wato mahaifin Fa'iza, shi yasa nake kokwantan idan ba canje aka yi ba, dandai kawai kamaninki d'aya da Murjanatu banda haka da abinda nake tunani ya tabbata.”

 

Turo baki tayi tana hararar gwaggo cikin duhu, cike da jin haushin kalamanta Aliya tace.

 

“Toh wai gwaggo ko kinfi son Shamsu dani ne naga sai yabansa kike ni kuma kina b'atani.?”

 

“Ban sani ba ja'irar yarinya kawai.”

 

Kai ta jijiga tare da juyawa ta kwanta itama nan ta bar gwaggo sai masifa take yi mata, yayin da ita kuma ta d'auki alwashin yiwa Shamsu rashin mutunci gobe, Saboda duk shi yaja gwaggo take ta yi mata wannan bankad'ar. Fa'iza kuwa tana jinsu duk abinda yake faruwa sai dai yadda take a kwance ba zaka tab'a tunanin cewar idanunta biyu ba dan ko kwakwaran motsi ba tayi sai hawaye da zuke zuba kan abinda tayi matashi dashi(pillow).

 

Da sassafe kuwa suna tashi wajan karfe takwas Aliya ta fita k'ofar gida ranta a matukar had'e ta nufi wajan Shamsu, yana ganinta yasha jinin jikinsa, dan yasan tabbas kuwa tayi ta gaya masa wata bak'ar maganar. Aikuwa tana zuwa ta kallesa gashi su Kabeer sunzo gurinsa ga customers suna ta siyayya a gurinsa, taje tana nishi kamar wadda taci gudu tana cewa.

 

“Shamsu bana san wulak'anci ka dena min abinda ka aiko Fa'iza dashi jiya, nace maka ina da wanda nake so ni ka kyaleni sai kace ni kad'ai ce mace a duniyar nan?”

 

“Shikenan kiyi hakuri.”

 

Ya fad'a yana kullawa wata yarinya sukari da tazo siya, harara ta dankara masa sannan ta juya zata shiga gida Kabeer yace.

 

“Shamsu ba dai wannan kwailar kake so ba? har kake cewa damu kayi babban kamu.” Aikuwa ta waigo ta kallesa tare da bud'e baki cikin haushi tace.

 

“Nice kwailar? Toh wallahi Allah ya isa daman kirjin mata kuke kallo? Idan ba haka ba taya kayi kasan bani da n...”

 

Bata karasa ba taji muryar malam Rayya, juyawa tayi ta kallesa taga yana yi mata dakuwa hakan yasa ta murgud'a baki tare da jan tsaki dan ba taso malam Rayya dakatar da ita ba da sai da zagi uwar Kabeer, tace masa kila babarsa kafin tayi aure ba ta kaita ba amman a haka kuma babansa ya aure ta tasan yasha gurgura kafin su fito, amman ta barwa anjima indai ta fito ta ganshi babu abinda zai hanata gaya masa.

 

“Gaskiya wannan yarinyar bata da kunya Shamsu kuma a haka kake sonta?” Cewar Khaleel yana shan burodi da shayi (tea and bread).

 

Zama Shamsu yaje yayi a kusa da su yana karkad'e hannunsa yace,

 

“Wallahi a haka nake mayatar sonta, ni kaina kuna ganin yadda tazo ta gaya min magana saboda na aika mata cewar ina kaunarta, toh amman gaskiya a hakan nake kuma kara jin zazzafar kaunarta.”

 

“Amman dai gaskiya kai d'an k......”

 

 

 

 

 


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol