Free chapter · Read without an account
21
🤳🏻
💘 нalιn dana ѕнιga...💘
~Labarin gaske ne~
© ᴬYˢᴴᴬ ᴹᴬᶜᴴᴵᴷᴬ
*Arewabooks@shooly84*
*_Not edited_*
💘 *21* 💘
Na sami littafina 40 leaves nai zaune arashin aikinyi na soma rubuta tarihin rayuwata, tun ina ɗaukar abin wasa dan inna ɗau littafi nai rubutu bana ƙara dubashi sai bayan wasu kwanaki wato in idea ta zo min na rubuta abinda ya samu ina ajiyewa sai kuma wani lokacin.
Abu kamar wasa nakai ƙarshen 40 leaves amma labarin nawa bai ƙare ba, gani da tarin idea buhu-buhu hakan yasa na samo wani na ɗora shima kamar ɗan'uwanshi da shiririta sai gani nakai ƙarshen shi, ga labari akwai saura musamman akan tsakanina da Ibraheem, dan haka ne dana tashi sai na samo 80 leaves na ɗora akai.
A'a ashe ni Asiyah zan iya zama marubuciya, dan koni ina mamakin kaina musamman inna karanta sai naji tamkar bani na rubuta ba anan na yadda da magana Anti Lubah data ce *abin sa kaine*...
Ban taɓa gaya mata ina rubutu ba kawai ganina tayi da littafi na miƙa mata ba tare da nayi magana ba, ta karɓa tana tambayar na meye?
Nace ki duba inkin karanta daga baya mayi magana, banko zauna ba na juya na fice nabarta tafara dubawa.
Cikin dare ta dameni da waya tambayata take wai ina sauran labarin, na kyalkyale da dariya nace ya dai Anti Lubah ya yi daɗi, tace fiye da yadda kike zato Asiyah, shiyasa na matsu naji ƙarshen shi, na sakeyin dariya nace ki ɗanyi min haƙuri nakai ƙarshe saina baki kikaranta gaba ɗaya, har zuwa yaushe kenam zaki gama?
Nace sai lokacin da Ibraheem ya bayyana, tai dariya da faɗin Allah ya nuna mana lokacin..
Ina kwance da rana ina son yin bacci alokacin bamu dade da gama waya da Ibraheem ba inda yake ceman zai zo nan da sati ɗaya, na tambaye shi game da ƴan'uwanshi yace komai ya warware sai fahimtar juna wannan kuma sai a hankali.
Abdul ya leƙo ta windon ɗakina yace kina bacci ne? Na juya mashi kai bance komai ba, to zo mana kiɗan rakani nan baya, na kalleshi da faɗin da ranar nan Abdul? Aiba nisa zamuyi ba gidansu Muhmamad ne, kamar naƙi binshi sai kuma can zuciyata taraya min naje mana.
Na tashi naja ƙaramin mayafi na rufe kaina alokacin shiya bar wurin sai nabi bayanshi muka haɗu awaje, muna tafe muna hira wadda hirar tamu bata wuce ta Ibraheem har muka isa, da yake ɗakin shi shi ne na farko inka shiga gidan, hakan yasa muna shiga muka soma jiyo hayaniya da alama ɗakin a cike yake, Abdul ma yace ɗakin yau ba dama in munje sai ki tsaya daga ƙofa na shiga na karɓo abinda zan karɓa nace to muƙarasa.
Kalmar data samu tsayawa cak ni da shi ta fitone daga bakin Muhmamad inda mukaji yana cewa"kunsan girman Allah wallahi ni bason Asiyah nake ba, Allah ya sani abu ɗaya nake kwaɗayin samu awajenta wanda da zarar na mallake shi shike nan tsakanina da ita sai dai hange daga nesa..".
Ni da Abdul muka kalli juna, daga cikin ɗakin kuma aka tambayi Muhmamad ɗin da cewa kai da duk tsayin lokacin dakuka ɗauka baka sami komai ba daga jikinta?
Yace ina ai shegen wayo gareta kofa hannunta bata yarda na riƙe dukko lokacin da tsautsayi ya kaini ga hakan sai munyi bala'i kai akwai lokacin dana so nayi kissing ɗinta, amma kafin na ida nufina ta ɗago wallahi barina tayi awajen tai tafiyarta...aikaine mara wayon mutumina, wata muryar ta kuma faɗa, yaci gaba wallahi ba'a halicci yarinyar da zan ɗau lokaci mai tsawo irin haka da ita ba tare dana ɗanɗani wata zuma daga jikinta, ballanta ace ina tare da yarinyar dana san tabbas ba auranta zanyi ba, kai haba akwaifa hanyoyi da dabaru abokina, kasan wani shawara da zan baka, aka tambayi Muhammad ba muji abinda yace wancan yaci gaba da cewa"kasan yanda zakayi ka kawota dakinka ka gane so sai kayi amfani da irin maganin nan na bacci mai saurin bugarwa ka watsa mata cikin fura ko yoghurt tunda kace ita mayyarsuce, ka bata tasha tana sha malam shikenan ta tashi aiki aiki wallahi ina baka shawara kai mata kaca-kaca karka saurara mata malam...
Ihu suka ɗauka irin an kawo shawara mai daɗi, muryar Muhmamad yace ka kawo shawara Bukar kai ina ma kai ma kana wajen ranar daka lashi ladar kawo shawara, ko..suka tafa da bushewa da dariya, muryar Muhammad ta kuma tashi da faɗin aikin kaɗe Asiyah zan maidaki fango sai wancen mayen ya kwashi ragowa..
Kai tsaye Abdul ya tura ƙofar ta buɗe, su shida ne harda Muhammad ɗin suka zubowa ƙofar ido ganin Abdul da yadda fuskarshi take yasa suka fahimci yaji hirar tasu hakan yasa wasunsu kaɗuwa marasa kunya irinsu Muhammad aka dake, ya taso yana cewa Abdul yaa Baabah yaushe ka shigo garin ne?
Ya ɗan matsa tare dayi mashi nuni dani dake tsaye baya ina cikin mamaki da kaɗuwar abinda kunnuwa suka gama ji , Abdul yace gata nan na kawo muku ita basai kunsha wahalar zuwa ku taho da ita ba..
Suka kalli juna Muhammad ya dake yace ka gane ko dama wata Baby ce muke magana bawai wannan Asiyan ba...marin da Abdul y awatsa mashi ne ya sashi rufe baki ba shiri da kama baki, nan da nan Abdul ya tashi da masifa da surfa ashar yana kaima Muhammad naushi ana riƙeshi kai ban taɓa zaton ya iya masifa ba sai wannan karon.
Nima suka zo suna bani haƙuri ko kallansu ban sakeyi ba nabar musu gidan su, wannan shi ne ƙarshen mu'amulata da Muhammad wanda ko'a hanya muka gamu bana nuna ko alamar na taɓa sanin shi.
Shi kuma Hussain rabon da na ganshi harna manta dan gaba ɗayama ƙishin-ƙishin na rinƙa ji wai zaiyi aure, sam bai dameni ba dan dama can ni ba son shi nake ba.
A yanzu Ibraheem shi ne kawai agabana babban burina lokacin aurenmu yayi mu mallaki juna.
Koda yake satin daya ce zai zo harya wuce da wani satin bai zo ba wannan kuma yana da nasaba da ciwon da mahiafiyar shi ta kwanta gashi shi kaɗai ne ɗanta dole shi ne mai tsayawa ya bada kulawarshi akanta.
***
*Kamar Wasa.....*
Kwanan mu tara Yola nida Mami dasu Ruƙayya, randa muka dawo da marece Abdul ya kawoma Mami yarinyar da zai aura, Kubrah kyakkyawar yarinya akwai hankali da natsuwa kowa ya yaba da ita an kuma yabama Abdul da iya zaɓe, aranar ne Abbah kecemin to saura ke Asiyah, kinga dai Abbas da Bashir ga Abdul duk sun kawo matayensu dan haka kema ki kawo miji danna gaji da zamanki haka.
Akwai ɗan taƙaitaccen lokaci da zan baki inhar kika haura lokacin nan na rantse miki da Allah zan haɗaki da duk wanda na samu koda kuwa malami ne...nayi dariya nace insha Allah Abbah bazan ko kai lokacin da ka ɗiba ba dan nima mijina yana hannu lokaci kawai muke jira mu gabatar dashi.
Mami ta harareni da fadin marar kunyar yarinya, Abbah yai dariya yace barta ina son hali irin nata ta faɗi abinda shi ne ra'ayinta..
Washe gari da yamma muna tare ni da Abdul a ƙofar gida muna hira wadda dukkanta akan Ibraheem ne, Abubakar wani saurayine anan maƙotanmu suke, muna mutunci dashi sosai, shi ne ya iso wajenmu suka gaisa da Abdul ya dawo gefena ya zauna ya soma jana da hira, tsam Abdul ya miƙe yacemin bari nayi ƙasa na dawo, da ka na amsa mashi saboda dariyar da nake sakamakon labarin da Abubakar yake bani.
Har magrib muna tare, na miƙe ina mashi sallama zan shiga dai dai lokacin Abdul ya dawo ya wuce cikin gidan, Abubakar ya yi dariya yace ina mamakin Abdul da yake kishin duk wani namijin da zai raɓeki, na buɗe ido akanshi nace kana nufin me anan?
Ina nufin Abdul yana da zafin kishi akanki sai dai cikin al'amarinshi nakasa gane inda ya dosa, shi dai har yau bai fito yace yana sonki ba, kuma ya tsani ganin ko wane namiji na raɓarki koda kuwa abokin hulɗane ba saurayi ba, amma abinda ban gane ba shin Abdul ya taɓa gaya maka yana sona ne?
Yai sauri faɗin a'a bance ba, yanayin da yai maganar kawai zaisa kasan akwai wata aƙasa, nace Abubakar bakin ka da magana, yai dariya ba'a bakina ba ki dai jira kiji a wani bakin..
Machika novel