Free chapter · Read without an account

SIRRIN ZUCIYA 1.

by Nusaiba · SIRRIN ZUCIYA

SIRRIN ZUCIYA




Na


Nuceeyluv😘








1....



***Cikin sauri take tafe tana haska er torchlight dinta, dakyar ma take kawowa sbd ta fara bada matsala, dan tsuka tayi tana zance ita kadai haka kurum Hajjo ta aiko ni da tsohon daren nan wai asai mata robb kai sha'anin tsoffi ma sai a hankali tayi mgnr tana bubbuga fitilar sbd daukewar da tayi ga duhu ya mamaye wajen.



•

"Oya bani key din motar" aka fada da dan tsawa, a rude yarinyar ta daina buga fitilar ta koma bayan bishiyar da take hango mutanen ciki dishi2 a hankali ta dora hannu akai "na shiga uku ni fatima" Tayi mgnr tana dora hannu a baki sbd karsu hango ta, sake gwale ido tayi ta hango mutum biyu ne daya a kwance an turmushe shi dayan kuma yana kai masa naushi iya karfin sa ya bashi key din wajen sa, mgnr yake sauri2 yana waige da alama na kwancen fashin motar za'ai masa. Fatima na daga nesa ta kalli gefen ta wani katon icce ta gani gefen ta, dakyar ta cirashi sama kafin ta sadada ta rimawa wanda yake tmbyr key din ji kke timmm... A razane kuwa ya saki na kwancen kafin yyi wani hanzari ta sake rima masa a keya, cikin wahala da tsananin tsoro ya dago yana kallon me dukan nasa, Rudewa yyi a zaton sa ma Aljana ce yadda ta kafe shi da manyan idonta ba bata lkci kuwa ya fece a guje.



Sai a lkcn ta magantu cikin dakiya tace, "dan banza masu fashi akan hanya, kaikuma sallobiyo saika tashi ai"



tayi mgnr tana jawo na kwancen, cikin yanayi na maye ya miko mata hannun sa, gyalanta ta tattare ta kamo hannun nasa zaton ta zai taho bata debe tsammani ba taji tayi luu zata fada jikinsa cikin dauriya ta dafe hannayen ta gefen kasa kirjinta na bugawa, yyinda na kwancen ya zubawa halittar kirjin nata ido yana lumshe ido da alama mayen be sake shi ba. A dan tsorace ta mike daga kansa sbd tsantsan kyawun data gani tattare dashi, Blue eyes dinsa shi yafi bata tsoro anya ba aljani bane? Wayyo ta fada da karfi tana me tattarar robb da torchlight dinta ta fece da gudu.




****

"About a months kenan har yanzu ban sake haduwa da ita ba, pls *HAIDAR* ku tayani neman ta."



"You see? saida nace ka daina shan giyar nan amma kaki Yanzu wa gari ya waya *ABUTURAB?* "


"look bro matsalar nan asan yadda za'a shawo kanta pls *HAIDAR* kuma ma tun daga ranar na daina shan giyar ka sani."


Abuturab ya amshe zancen da hade hannun sa.



"Tun dazu nakejin kunata mgn, wani ya shigo dakin shima, yauwa gwara da kazo *ALIYU* wannan dan taurin ne yaje ya hadu da aljana garin shaye2 giyar sa wai ita yakeso."



"Idan baza'a samar da solution ba pls a daina maida zance"


*ABUTURAB* Yyi mgnr yana bata rai,



"ohk ya zamu mu gane yarinyar idan munason tayaka neman ta?"


*ALIYU* yyi mgnr yana kallon sa,


"Good Question bro, bari muga"


yasa hannu alamar tunani, duk yadda yaso kwatanto fuskar ta lkcin data *TAIMAKE SHI* kasawa yyi, ihunta kawai xai iya tunawa sai kuma Hoton tawada 'yar karama akan kirjin ta lkcn data sunkuyo er fitilar dake wajenta ta dallare su kamar kawowar wuta hakan ya samu zarafin kare ma luntsuma-luntsuman fresh Nonon ta kallo inda ya hango er karamar tawaha a tsakanin breast dinta, haryau ya kasa samun nutsuwa sbd ko yaushe kirjin ke masa gizo, yanaso ya shafasu, yanaso ya tsotse su, yasan ko tantanma bayayi zasuyi dadin latsawa.



"Oh God!"



Ya dafe kansa,



"Yadai?"



*HAIDAR* ya tmby, cikin damuwa ya sanar musu shaidar dazai iya ganeta,


*ALIYU* yace,


"kaifa karamin dan iska ne, wanne shege ne zai ta kallon kirjin mace har a gano ta? Mtwss idan zaka zubda makaman yaki ka karbi ta gida toh, kasan Daddy Tsaf ba kanwar lasa bane idan ka kasa kawo mata nan da 3mthns zai hadaka da duk wacce yaso a hada da bikinmu kuma dole ka karba."



"kaga nifa bance ku kalli kirjin mata ba, beside ma bazanso wani ya kallar min kirjin mata ba, zan nemeta da kaina, kuma mgnr a hadani da wata God Forbid"



Dariya *HAIDAR* yyi sbd hango karfin halin *ABUTURAB* baya ga haka ma duk cikinsu ya fisu taurin hali da miskilanci gsky wacce yake nema *RUWA A JALLO* Ba karamin dacen shi tayi ba, kawar da tunanin yyi yace,


"fatan Alkhairi bro"


*ALIYU* Ma murmushi yyi yna buga kafadar sa yace,


"All the best"


kala bece musu ba saima hade fuska da yyi da alama sunma maidashi mahaukaci.



•••••

Juyi take tana sake rintse idonta, gajiya tayi da kwanciyar ta mike zaune dirshan kan gado har yanzu tunani ne fal ranta, Meyasa take jinsa a ranta? Meyasa koyaushe ta rintse ido shi take gani? Meyasa blue eyes dinsa kullum yake mata gizo a cikin kwanyar tunanin ta? Duk sanda ta rufe ido sai ta ganshi tarr cikin halin maye tsantsar kyawun fuskar sa ita ke daga mata hankali harta fara tunanin anya ba gamo tayi ba? Kai ita bata taba ganin me blue eyes a wajajen su ba anya ma mutum ne? Sau tari ta kanyi tunanin meyasa ta gudu bata tsaya ta karasa taimakon data fara yi masa ba? Shin bayan tafiyar ta a wanne hali ya kasance? Why na barshi? Why??? Tayi mgnr tana dukan kanta hankalin ta a tashe.


"Ke lpyr ki kuwa Fatima?"


A firgice fati ta dago tana kallon Hajjo, hajjo tace,


"mgn nake"


fatima ta girgiza kai tace,


"ba komai hajjona"


"Ke 'yar nan ba kalau ba na lura kwana biyun nan bakya cikin hayyacin ki anya babu wata a qasa?"


Hajjo tayi mgnr tana zama, Murmushin karfin hali fatima tayi tace,


"ba komai fa."


"Ke ni kakarki ce dan haka fadamin meye matsalar ki kinji jikalle?"


Murmushi Fatima tayi tana me tattaro karyar da zata zugawa kakar tata dan batason fada mata yanzu bare ta daga mata hankali.


"Tunanin makaranta nake hajjo, inason ci gaba babu hali aikin yaki samuwa shiyasa kikaga na damu."


Hajjo jikinta yyi sanyi Tabbas fatima na cikin wata irin rayuwa meban tausayi, Murmushi fatima tayi tana me dafa hajjo tace,


"shiyasa fa naki fada miki dan banaso ki shiga damuwa"


dan nisawa hajjo tayi tace,


"ba matsala Insha Allahu komai yazo karshe dazu Innar sumayya tazo min da Albishirin din samun aikin ki a gidan Alhaji Mahmoud Mustapha mai canji, tace babarsu tana neman yarinya me hankali da zata kula mata da yaranta guda uku, me tsafta, da Gaskiya dan batason aci amanarta toh Alhamdulillah nasan bazaki bani kunya ba shiyasa nace ba matsala dandai renon yara uku ka basu abinci da kula dasu ai ba matsala bane."



Tunda ta fara mgnr Fatima ta wangale baki tana kallon hajjo, saida taji takai karshe tace,


"Hajjo Nanny zan koma?"


Hajjo tace,


"meye kuma Nanny?"


Fatima tace,


"me renon yara mana"


Hajjo ta kama hannun fatima dan taga alama zata botsare gashi dakyar ma aka samu aikin cikin lallashi tace,


"Fatima kodan karatun ki saiki duba ga saukar ku ta kusa idan babu kudi dame zamuyi bikin saukar? Bayan haka kawarki sumayya itama fa a gidan take aiki kwanan baya Innarta ta samar mata wanke2 kinga kinada 'yar uwa a kusa kuma a gari daya muke kullum zaku dawo gida."


Dan numfasawa fatima tayi Tace,


"shikenan Allah ya kaimu"


"yauwa koke fa jikalle."



*ASALIN LABARIN*



****

Babban gidane wanda ya tara bangarori dayawa, amma aka dunqele waje daya ana iya cewa gidan Alhaji Mahmoud Mustapha mai canji, Matar sa daya hajiya Khadija, sai yaransa 'yan uku duk Maza ne bazasu wuce 30yrs ba da kuma karamar kanwar su Khairat itama duka 18yrs take, dake dukka iyayen sun kwankwadi boko sun koshi sai ya kasance daga kan Auta khairat suka tsaida haihuwar, Mahafinsu jinsin fulani ne farin dogon mutum me cikar haiba uwa uba ga mutunci da sanin darajar mutane shiyasa duk abinda Allah ya tara masa be rufe masa ido ba sam, amma fa yanada zafi sosai,


sosai ya jawo 'yan uwansa jikinsa wato kannen sa uku, kawu Balare, kawu Yusuf, kawu Idris, dukkansu kannen sa ne saidai Uba daya ne ya hadasu dan shi kadai mamarsa ta haifa ta rasu, suna son junan su sosai hakan yasa zumunci me karfi ya kullu tsakanin su, Kawu bala yanada yara biyu duk Mata wato Sa'datu da halima, sai kawu Yusuf yaransa shima uku ne Humaira sai Musa da Jibril, Kawu Idris yanada yarinya daya Sameera sai namiji Sameeer, Dukkansu a hade suke cikin gidan Alhaji Mahmoud mai canji, Kuma kowa yaransa karatu yake sannan gida irin wannan ba'a rasa gutsiri tsoma da en zagon kasa,


Mummy nada fada dan tanaji da kanta sosai dan kuwa ba karya Allah ya bata kyau dangin Shuwa Arab ce, Shiyasa 'yan uku suka tsatso kyau ta kowanne bangare.



'Yan Uku, Wato *ALIYU, HAIDAR, ABUTURAB,* Shine cikakken sunan en ukun Mummy, Aliyu shine babbansu, Yana da zafi kwarai, dan kuwa bayason Raini dan yana kama girman sa sosai saidai Allah ya zuba masa tausayi duk zafin Ransa Akwai tausayi a gareshi, sai Haidar Yanada zafi shima yanzu zaka masa abu ya bata masa rai Amma zuwa Anjima zai manta, Yanada Raha wani lkcin idan yaso wani lkcin kuma ya hade fuska sosai tamkar wani Boss shiyasa wani lkcin en gidan suke ganinsa kamar wani me Aljanu, Abuturab, Autansu kenan, dan rigimar Mummy da Daddy, Duk wani zafi na Aliyu ya hado shi harma yaso ya fishi zafi, haka nan saurin fushi na Haidar yanada shi saidai wannan Rahar babu ita, wani irin murdadden hali gareshi sam baka gane ina yasa gabansa, dayawa en gidan suna kiran sa da Saraki dan wani abun da yake sai kace ya hada dangi da jinin Sarauta.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.