Free chapter · Read without an account

BABI NA DAYA

by Fatima Eshak · QAUNA CE

*QAUNA CE*


*UMM ASGHAR*


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*


   


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


INA KUKE MAKARANTA??


INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️


 SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B


INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.


1- *QAUNA CE* 

   NA UMM ASGHAR 


2- *RUKUQI*

  NA FEEDHOM 


3- *WANI SO*

   NA ZEE YABOUR 


4- *SO DA ALAKA*

    NA UMMI AISHA 


5- *MUGUN GANI*

  NA SADIYA NASIR DAN


6- *ABDUL_HAMEED*

   NA NANA DISO


7- *MUKULLIN ZUCIYA*

    NA MAMAN KHADY


DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA


(1000) DUBU DAYA KACAL


KAI KA KAI....!

TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU...


1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍  

*DAGA CHEF RAHMA NA LELE*


2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA

*DAGA AYUSHER MUH'D*


3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI

*DAGA HAJJA CE 👈*


MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN.


_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_

2083371244

ZENITH BANK 

AISHA M. SALIS


*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*

+447894142004


IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*

*** da Shaidar biya duk ta ciki


 _GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU 550F TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_

+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.

MUN GODE.


_HAKA ZALIKA KOFA A BUDE TAKE GAME BUKATAR 'DAYA DAGA CIKIN TOP 10, AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 ONLY_


*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*


_Wannan garabasar tamai rabo ce💃🏻💃🏻 sa kud'i kad'an ki debi hani'an😍😂_


FREE PAGE 1.



Sallama nayi a kofar ofishin headmaster ďinmu. Daga ciki aka amsa mini tare da bani izinin shiga. Su biyu na tarar a office din, ga alama dai bako yayi don baya daga cikin malamanmu. 


Durkusawa nayi har kasa na gaishesu sannan nace "Mallam Bilkisu tace kana nemana". Sai da ya qarasa rubutun dana iske shi yana yi kafin ya amsa mini da "eh naji shiru ne, kowa yana zuwa karbar jarabawar shi ke kuma naji shiru duk da makarantu uku kika samu, ina so ne naji wacce kike so, ko kuma kin fi son day akan boarding ďin?"


A take idanuna suka yi rau-rau alamun son zubar da hawaye, bayan hannuna nasa na goge, cikin muryar kuka nace "Mallam Baba ba zai bar ni nayi karatun nan ba, day ďin ma yaki yace wai nayi hakuri baya da kuďin da zai yi mini wannan ďawainiyar, gara na cigaba da islamiyya zuwa lokacin da zai aurar dani".


Sakon text yake dubawa a cikin wayarshi don haka bai maida hankali akan zancen da abokinshi ke yi da dalibarshi ba amma jin maganar aure ta shigo ciki bai san lokacin da ya dago yana karewa yarinyar kallo ba har ma bai san sa'adda furucin ya subuce daga bakinshi ba don shi ba mutum bane mai shiga abinda bai shafe shi ba.


"What? Aure a wannan 'yar karamar yarinyar, me yasa mutanenmu ke da son kassara rayuwar 'ya'yansu ne? Wannan yarinyar ai bata wuce raino ba itama amma a haka za'a ďauka a bawa wani kato ya lalata mata rayuwa." Bakon Mallam Isah ne yayi wannan maganar cikin bacin rai. 


"Mtsew..." Mallam Isa yayi tsaki yace "kai ma dai ka faďa, idan bai yi mata aure baďi ba to nan da shekaru biyu masu zuwa tana ďakin aurenta. Abin takaicin ma shine yarinyar tana da kwakwalwa sosai, itace daliba mafi kokari a duk fadin makarantar nan, sosai makaranta ke ji da ita.


Bana so ace rayuwarta ta dakushe, zan so ace al'umma sun amfana da tarin baiwar da Allah yayi mata, to amma abin dubawar iyayenta masu karamin karfi ne sosai, primary ďin ma da kyar ta gama da taimakon Allah da taimakona, amma yanzu ni kaina na gajiya, abubuwa sun yi mini yawa, ga iyalina da tsohon ciki gashi nima karatun nake son komawa".


"Abubuwan da ya kamata kenan gwamnatin mu ta dinga dubawa tana taimakawa, karatu ne yanzu nema yake yafi karfin dan talaka sai mutum yana da hali, don ma mu nan Jigawa abin da dan sauki".


Shiru ne ya ziyarci office din na wasu mintuna, zuwa can bakon Mallam ya miko mini wani littafi dake hannunshi inaga a office din ya dauka yace "karanta mini wannan littafin naji".


Karba nayi na duba bangon littafin. 'THE SUGAR GIRL' na gani a rubuce a jikin bangon kenan sunan littafin kenan.


Na fara karantawa tiryan-tiryan suna sauraro na duk da turancin nawa akwai gyara a ciki haka nan kuma gabana sai faman faduwa yake don kar suga gazawata.


Sai da na karanta shafi daya har na juya zuwa shafin gaba sannan yace "ya isa haka nan". Dakatar da karatun nayi na mika mishi littafin.


"To me kika fahimta a ciki?" ya tambaye ni. Nan nayi mishi bayanin dan abinda na fahimta.


Shiru yayi yana kallona tamkar mai tuna wani abu kafin yace "gaskiya Isa ya kamata a tallafawa yarinyar nan domin Allah kadai yasan abinda ya ajiye a cikin kwakwalwarta".


Mallam Isa yace "abinda ke damuna kenan don ma baka binciketa sauran darussan ba, ka dan duba lissafi ka gani".


Nan ma ya rubuta lissafi a takarda ya miko mini, a take kuwa na amsa na maida mishi.


"Wonderful" yace yana murmushi. "Ya zame mini dole na taimakeki don ina son yaro mai hazaka, ina fata ba zaki bani kunya ba".


Ban iya amsawa ba duk da dadin da naji a cikin raina sai dai ina tantamar idan Baba zai amince da taimakon da yake son yi mini ba don ya kasance mutum ne shi mai gudun zuciya da tsantseni, kwata-kwata baya da kwadayin abin wasu.


Ya maida dubanshi ga Mallam Isa yace "muje naga mahaifin nata ko?"


"Sai dai kayi hakuri har a tashi don lokaci ya kusa, ke Zainab wuce gida zanzo naga Baban naki". Tashi nayi tare da yi musu sallama na fita.



Karfe biyu da rabi na rana nayi shirin tafiya makarantar islamiyya, sai da nayi sallama dasu Innata da Baba kafin na wuce.


Ina fitowa wata bakar mota mai matukar kyau da sheki don sai daukar ido take yi a cikin rana tayi parking a kofar gidanmu.


Sau daya na kalli motar na kauda kai duk kuwa da yadda kyaun motar ya dauki hankalina, nazo wucewa ta gefen motar naji an kira sunana daga ciki.


Ja nayi na tsaya ba tare da na karasa jikin motar ba don ban shaida muryar wanda ya kiranin ba.


Mallam Isa ne da bakonshi suka fito daga cikin motar. Karasawa nayi ina yi musu sallama tare da russunawa na gaishe su.


Mallam yace "Zainab kin gan mu sai yanzu ko?" Na daga kai. Yaci gaba da "Mallam din na gida dai ko?"


Nace " eh, yana nan, yau bai fita ba don yace kanshi nayi mishi ciwo". Yace " ayya, Allah ya sauwake. Shiga kice mishi muna sallama".


Na juya zuwa gida. Ina shiga Inna tace ke kuma lafiya kika dawo? Ko dama baki tafi ba?"


Nace "eh, na hadu da Mallam Isa a waje shine yace nayi mishi sallama da Baba".


Tashi yayi daga kishingidar da yayi akan tabarma yace " kice su shigo Mallam Isa ai dan gida ne".



Na fita na sanar musu sannan muka juya zuwa cikin gidan a tare.


Inna ta shimfida musu tabarma kusa da shimfidar Baban. Bayan sun zauna Inna ta gaishesu ta tashi ni kuwa ina daga gefe ina jiran naji me zasu ce.



Bayan sun gaisa da Baba ne Baban yana murmushi yake cewa "mutuniyar ta kai karata hala?"


Mallam Isa yace "a'a Mallam, ai Zainab nada hankali baza ta aikata wani abu makamancin wannan ba, nine dai na nemeta domin ganin kowa na zuwa karbar jarrabawa ita kuma shiru, to bayan tazo na nemi shawararta kan makarantar da take so shine take sanar dani kace ta hakura".


Baba yayi gyaran murya yace " haka ne Mallam Isa. Ka dai san tsarin rayuwar tamu bamu ajiye ba ba kuma mu bawa wani ajiya ba, 'yar sana'ar tawa da ita ne muke samu muyi cefane da sauran bukatu, to yaushe za'a je batun makaranta.


Itama jeka ka dawon ai aiki ce, bayan kudin makaranta da na littattafai dole za'a dinga neman na abinci, shine nace kawai tayi hakuri ta samu abinda ta samu a islamiyyar idan Allah ya kawo mata miji sai ayi mata aure".


Mallam Isa yace " Mallam wannan abokina ne (ya nuna bakonshi), sunan shi Ismael, tare muka yi makarantar secondary, zumunci sosai muke yi da shi. Dan birnin Kano ne, yanzu yazo gani na ne muna tare da shi Zainab ta sameni kan neman da nake yi mata.


To yaji komai game da hazakarta har ma yayi mata dan gwaji, don haka yace shi zai taimaka tayi karatun idan har ka amince".


Baba yayi shiru kamar ba zai yi magana ba ga alama dai jinjina zancen yake yi, zuwa can dai ya bude baki yace "a wane dalili Mallam Sama'ila zaka dauki nauyi irin wannan ka dorawa kanka, a wane dalili?" Ya sake maimaitawa.



Gyara zaman shi Ismael din yayi kafin yace "Mallam ina so ne na taimaketa saboda Allah da kuma kasancewarta na diya mace, domin ance idan ka ilmantar da diya mace guda daya tamkar ka ilmantar da al'umma ne, yarinyar na da wata irin baiwa da bai dace a barta ta tafi a haka nan ba. 


Don Allah Mallam kayi hakuri ka barni na samu wannan ladan, zan dauki nauyin komai, ko naira biyar ba zaka kashe ba a harkar karatunta".




Baba ya nisa yace " naji batunka Sama'ila na kuma gode Allah yayi muku albarka ya kareku daga sharrin makiya da mahassada, amma ku bani kwana biyu zuwa uku kafin na yanke shawara".


Mallam Isa yace " haka ne Mallam, shi Ismael yau zai koma Kano amma duk abinda kenan zan kira shi a waya na sanar mishi".


Suka yi mana sallama suka fita. Ni kam har na fara murna ina jin alamun samun nasara tunda nasan Babana yana son karatun nawa don dai bashi da yadda zai yi ne.


Inna ce ta fito daga daki da ta shige tun bayan zuwan su Mallam Isa "ni kuwa Mallam sai nake ganin da ka yarda ya dauki nauyin karatun nata mana, tunda kaga babu abinda Zaynu take so irin karatun kuma yace domin Allah zai taimaka, kila Allah ne ya dube mu ya turo mana mataimaki".


" Haka ne, mutumin bai yi mini kama da mutanen banza ba kuma Mallam Isa ba zai taba kawo wanda zai cutar damu ba, amma duk da haka zanyi shawara da 'yan uwana zan kuma yi istikhara don neman zabin Allah shine ma dalilin da yasa nace su bani kwana biyu nayi shawara, duk abinda Allah ya hukunta shi za'a yi".


Inna tace "to Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi".


Bayan kwana biyu Baba yayi shawara da kannenshi Kawu Sa'idu da Kawu Sani, duka kuma sun amince da barin Ismael ya dauki nauyin karatuna, to shima Baban tun bayan da ya mika al'amarin ga Ubangiji yaji ya samu nutsuwar zuciya ya yarda Ismael din da zuciya daya yake son taimaka mini don haka da kanshi ya samu Mallam Isa yace mishi sun amince da karatun nawa.


A ranar Mallam Isa ya kira Ismael ya shaida mishi, shi kuma yace yana zuwa a karshen sati.


Ranar asabar ina wanke-wanke ne naji dirin mota a kofar gidanmu. Ina tunanin waye kuma yazo na jiyo sallamar Mallam Isa.


Dauraye hannayena nayi na janyo hijabi na daga kan igiyar shanya na saka na fita.



Shida Ismael ne sun jingina da bangon kofar gidanmu. Nayi musu barka da zuwa na gaishesu.


Mallam ya tambayeni "ko Mallam din na gida?" Nace "a'a yaje dubiya asibiti amma ina ganin ya kusa dawowa don kuwa ya dan jima da fita".


Komawa nayi cikin gidan na shaidawa Inna batun zuwansu, tabarma ta bani na shimfida musu a soro na koma na cigaba da wanke-wanke na.


Sun yi kusan mintuna sha biyar kafin Baba ya dawo. Zama yayi suka gaisa yana basu hakurin rashin samun shi a gida da suka yi.


Mallam Isa yace "munzo ne game da shirin makarantar Zainab, wacce kake so ta tafi? Kasan makarantun uku ta samu".


Baba yayi murmushi "wannan kuma ai shawararku ce Mallam Isa, ku zaba mata duk inda kuka ga ta dace, ni ai dan yin addu'a ne" 



Muskutawa Ismael yayi yace "Isa kai kafi mu sanin makarantun nan, kai a ganinka wacce ce tafi?"



Mallam Isa yace "ina ganin taje Guri junior science ce, makarantar na da kyau kwarai da gaske".



Ismael ya sake cewa "shike nan, sai muje yanzu a yanki yadin uniform a dinka mata ayi duk wasu shiri da ya kamata daga nan zuwa gobe don In Sha Allahu ranar litinin zata tafi makaranta kada ayi mata nisa a karatu".



A ranar suka sayi uniform matar Mallam Isa ta dinka kala biyu ne da house wear shima guda biyu.


Ranar lahadi suka kawo mini duka sayayyar makarantar tun daga kan katifa, akwati, bokiti, hatta da sleepers sai da ya sayo mini, bayan tulin kayan provision da ya jibgo mini. 


Sayayya dai irnta 'ya'yan gata ita Ismael yayi mini ya kuma bawa Inna dubu goma wai a sayo mini mai dasu yaji da kuli-kuli da sauran kayan da bai saya ba.


Inna harda hawayen murna tayi, tayi ta saka musu albarka.



*UMMASGHAR*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol