Free chapter · Read without an account
BABI NA UKU
by Fatima Eshak · QAUNA CE
*QAUNA CE*
*UMM ASGHAR*
©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
FREE PAGE 3.
Haka nayi hutuna cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Naje Aujara wurin Yaya Indo nayi mata kwanaki biyar sannan na dawo na cigaba da hutuna a gida.
Yaya Engnr bai zo ba sai da hutunmu ya qare ana saura kwana hudu mu koma.
Shi kadai yazo a dalilin Mallam Isa baya nan. Har cikin gida ya shigo suka gaisa da Inna duk da cewar Baba baya nan yana gidan gona.
Sun yi hira sosai har nake mamakin dama yana magana haka? Ni kullum fuska a dinke nake ganinshi sai na dauka baya magana ashe ba haka bane. Ga alama kuma sunyi sabo da Inna.
Bayan Inna ta tashi ne ya kallo ni yace
"'yan makaranta ya hutun? koda yake ma ai ya qare sai shirin komawa ko?"
Na daga kaina alamun amsawa.
"Isa ya fada mini sakamakonki, kinyi qoqari sosai, sai dai ina so ki qara dagewa next term ki kawo mini first position kinji?"
Nace " In Sha Allahu".
Yace na kawo mishi school bag dita yaga ayyukan da aka yi mana a school din.
Tashi nayi naje na dauko school bag din na kawo mishi.
Ya fiddo da duka books din nawa yana dubawa tare da yi mini wasu 'yan tambayoyi ni kuma ina bashi amsa.
Har lokacin dawowar Baba yayi yana gidan. Baba yana yi mishi Barka da zuwa shima yana yi mishi.
Bayan sun gaisa Baba ke tambayar shi "ya wajen su Alhaji da mutanen gidan duka?"
Engnr ya amsa "suna nan lafiya, sun ma ce a gaisheku. Alhaji yace na fada maka yaji dadin maganin nan don haka idan akwai wani a qara mishi zai baiwa abokinshi".
"Babu matsala, ai ba yau zaka koma ba ko?"
"Eh sai gobe idan na gama shiryawa Zainab kayan tafiya makaranta".
Baba yace "Ismael da ka bari tunda yanzu Alhamdulillah ina samu sai nayi mata, dawainiyar ai sai tayi maka yawa".
Tun Baba bai ida maganarshi ba ya fara girgiza kai yace "a'a Baba, wannan alqawari ne da na dauka cewa ko kwabonka baza ka kashe ba a harkar karatun Zainab don Allah ka bari na cika shi. Fatana dai ayi tayi mana addu'a".
Baba yace "wannan ai na kullum ne Ismael, Allah dai yayi muku albarka ya kareku daga sharrin dukkan wani mai sharri ya shiryar daku ya hadaku da abokan rayuwa nagari".
" Ameen Baba Ameen" ya amsa cikin jin dadin addu'ar da Baba yayi mishi.
Washegari Yaya Engnr sai da ya gama yi mini dukkan sayyayar kayan makaranta don har pocket money sai da ya bani kafin yayi mana sallama ya tafi bayan Baba da Inna sun cika shi da tsarabar fura da nono da kifi sai kayan miya da Inna ta bayar ya kaiwa mahaifiyar shi.
Ranar lahadi muka koma makaranta. Sosai na dage da karatu don ina so na cika alqawarin da nayi wa Mallam Isa da Yaya Engnr na cewar zan dage na samu first position a wannan hutun.
A wannan visiting din Yaya Engnr ne yazo mini shi da Mallam Isah. Kaya sosai suka kawo mini ba 'yan kadan ba duk da ko rabin kayana ban cinye ba.
A rayuwa babu abinda zance wa Yaya Engnr sai dai nayi ta binshi da addu'ar fatan alkhairi da gamawa da duniya lafiya don ya tallafi rayuwata a lokacin da burikana suke daf da tarwatsewa.
Lokacin da muka yi exams sai gani na dauko first position dita.
Da kwarin gwiwa na isa gida don nasan nayi abin a yaba mini. Ban bari yamma tayi ba na iske Mallam Isah a school na kai mishi result dina.
Shima yayi farin ciki kwarai da sakamakon nawa. A take ya kira Yaya Engnr ya shaida mishi shine ma ya nemi da ya bani wayar.
Na karba na gaishe shi cikin tsantsar ladabi da girmamawa. Sosai ya tayani murna sai kuma yace "sai bangaren Islamiyya banji kince komai ba, ko su ba kya maida hankali kamar na bokon ne?"
"Shima ina yi don yanzu haka izu na arba'in kuma idan mun zo hutu ma ina zuwa islamiyya sannan Baba ma yana koya mini a gida".
Yace "that's very good, nasan kina da qoqari dama duk da haka kada ki saka wasa a harkar karatunki kinji ki kuma dage da addu'a ki dayaita Allah In Sha Allah babu abinda zai gagareki".
Muka yi sallama na miqawa Mallam Isah wayarshi
*****************
Rayuwa dai tana tafiya mana babu laifi cikin rufin asirin Allah. Bani da matsalar komai a harkar karatuna, haka ma a gida Baba yana cikin rufin asiri saboda yana samu a kula da gidan gonar da yake yi.
A dalilin karatuna Baba ya zama kamar danuwa a wajen mahaifin Ismael don zumunci suke yi sosai tamkar tun da can sun san juna. Allah kenan Al-Hakimu gwanin hikima mai tsara yadda yaso a daidai lokacin da yaso.
Lokacin da muka yi jarrabawar placement mun dawo gida ne Inna take shaida mini ai sauran kwanaki takwas bikin Engnr don wajen ranar laraba muma zamu wuce Kanon wajen bikin.
Nayi murna kuwa kwarai da gaske don tunda nake a rayuwata ban taba zuwa Kano ba sai gashi ta dalilin Yaya Engnr yau nima zanje Kano.
Ni da Inna da kuma Asiya matar Mallam Isah muka isa Kano a ranar laraba da rana fatae-fatse. 'Gandun Albasa' shine sunan unguwar da naji Asiya tace wa dan adaidaita sahun da ya daukomu daga tasha.
Ni dai na baza idanu ina basu haqqinsu don ban cuci kaina ba na bude idanu sai kallon gari nake yi. Lallai 'Kano ta Dabo tumbin giwa' ashe mu bamu san me duniyar take ciki ba, Kano ai qare kallonka ce.
A gaban wani babban gida mai katuwar kofar gate muka tsaya. Asiya ta biya mai adaidaita kudinshi sannan muka sauka.
Mu dai bin bayanta kawai muke yi, wai sai na samu kaina da faduwar gaba ina tunanin ko dai Asiya sayar damu zata yi. Da sauri da kori shaidan daga zuciyata jin zai fara kawo mini tunani marar kyau.
A karkashin wata rumfa muka iske wani dattijo ya kishingida akan carpet ya tokare jikinshi da pillow, inaga dai shine mahaifin Yaya Engnr tare dashi akwai wani saurayi a durkushe a gabanshi suna magana, inaga dai qanin Engnr ne don naga suna yanayi.
Durkusawa muka yi muka gaisheshi. Cikin fara'a ya amsa mana yace "a'a mutanen Jahun har kun iso? Yasu Mallam din?"
Inna tace "yace a gaisheku sai tanar daurin aure zasu zo".
Alhajin yace " madalla, 'yan makaranta anzo hutu ne? Ko ba Zainabun bace? Kin san ban taba zuwa na sameta a gida ba".
Inna tace "eh itace wancan satin suka dawo".
"Madalla, ai ina jin labarin qoqarin ki wajen Ismael, aci gaba da kula Allah ya taimaka ya bada sa'a".
"Ameen" su Inna suka amsa ni dai kaina a sunkuye.
"Kai Suleiman kaisu wurin Hajiya Babba kayi mata bayani Zainab sin Ismael ce dasu Innarta".
A dakin Hajiya Babba sai maraba take yi mana tana yi mana sannu, kai gaskiya mutanen ba daga nan ba wajen karrama baqo. Nan da nan an cika mana gaba da kala-kalan abinci.
Ni kam na kasa sakewa yadda naga ana ta zuwa gaishemu, kuma duk wanda yazo sai ya nuna ni ace "wannan ce Zainab din Engnr?"
Hajiya tace "itace Zainabu Abu mai tagwayen suna".
Bayan mun ci abinci Hajiyar da kanta ta kaimu wani daki inda aka saukemu muka yi sallah.
Ina ji Inna da Aunty Asiya suna hirar karamcin mutanen ni kuwa tunani nake yi wane irin matsayi haka Yaya Engnr ya bamu ni da mahaifana? Ga kuma wani sabon suna wai Zainab din Engnr, har a bakin Alhaji kuwa.
Hajiya ce tayi sallama tare da wata mace wacce naga suna kama da Yaya Engnr da kuma Hajiyar.
Matar ta gaisa dasu Inna nima na gaisheta. Hajiya tace "Yayar Ismael ce itace babba, akwai kuma kanwarta ita a Abuja take aure muna saka rai da zuwanta zuwa anjima.
Inna tace "Allah Sarki, sannu, duk ya yaran naku?"
"Lafiya lau, ai duk tare muke suna can a dakin Hajiyar Jamila".
Ta tashi zata fita ta kirani "zo Zainab ga yaran can ko kin fi sakewa".
Tashi nayi nabi bayanta inda muka bar Hajiyar tare dasu Inna suna hira kamar sun dade da sanin juna.
Muna fita parlour ta zauna akan kujera tare da nuna mini kusa da ita wai na zauna, sai dai ban iya zama akan kujerar ba sai na zauna daga qaaa wajen kafafunta.
"Sunana Binta, ina da yarinya kamar ki, ai zaki zauna a gidana ko anjima sai mu tafi tare ko kuwa kin fi son zama anan wurin Hajiya?"
Murmushi nayi kawai ba tare da amsa mata ba.
'Yammata ne da zamu iya yin sa'anni suka shigo. Kallinsu tayi tace "yauwa Rufaida, Jamila ga nan Zainab ku dinga yin komai tare kafin ta tafi".
Daya daga cikin 'yammatan ce ta zauna kusa dani tare da ruqe hannayena a cikin nata tace "to Umma, amma dai da ita zamu tafi gida ko ta dinga kwana acan?"
Jamila tayi zaraf tace "a'a wallahi bayan ga inda tazo zaki wani ce ta tafi gidanku, anan zamu yi zamanmu ko Zainab?"
Ni dai murmushi kawai nake yi don yaran sun burgeni.
Yaya Binta (kamr yadda naji Jamila ta kirata) tace "to in haka ne duk ku tattara ku tafi can court road din mana tunda nan din ma cika zai yi kuma ma ai dare ne kawai zai maida mu can anan din dai za'a dinga yini".
Rufaida ta kalli Jamila tace "haka kuwa za'a yi ko Aunty Jammy" ta hada da kai mata dukan wasa.
"Yarinyar nan kin rainani wallahi, nifa uwakice amma kike yi mini tsaurin ido".
Dariya Rufaida tasa tace "ah karamar uwa ba". Yaya Binta tayi dariya ta qarasawa Rufaida da "madaukar zunubi, tunda kun fara halin naku ku tafi can dakinku kuyi acan nima wajensu Inna zani naji hirarsu tana dadi".
*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪
*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*
INA KUKE MAKARANTA??
INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️
SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....
TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B
INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.
1- *QAUNA CE*
NA UMM ASGHAR
2- *RUKUQI*
NA FEEDHOM
3- *WANI SO*
NA ZEE YABOUR
4- *SO DA ALAKA*
NA UMMI AISHA
5- *MUGUN GANI*
NA SADIYA NASIR DAN
6- *ABDUL_HAMEED*
NA NANA DISO
7- *MUKULLIN ZUCIYA*
NA MAMAN KHADY
DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA
(1000) DUBU DAYA KACAL
KAI KA KAI....!
TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU...
1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍
*DAGA CHEF RAHMA NA LELE*
2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA
*DAGA AYUSHER MUH'D*
3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI
*DAGA HAJJA CE 👈*
MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN.
_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_
2083371244
ZENITH BANK
AISHA M. SALIS
*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*
+447894142004
IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*
*** da Shaidar biya duk ta ciki
MUN GODE.
_HAKA ZALIKA KOFA A BUDE TAKE GAME BUKATAR 'DAYA DAGA CIKIN TOP 10, AKAN FARASHI MAI SAUKI 200 ONLY_
*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*
_Wannan garabasar tamai rabo ce💃🏻💃🏻 sa kud'i kad'an ki debi hani'an😍😂_
*UMMASGHAR*