Free chapter · Read without an account

BABI NA GOMA SHA DAYA

by Fatima Eshak · QAUNA CE

*QAUNA CE*


*UMM ASGHAR*


©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION.*


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


FREE PAGE 11.



A ranar da nayi kwanaki uku a Kano a ranar na rubuta jarrabawar post utme. Driver gidan ne ya kai ni sai Suleiman da muka je tare ya raka ni tunda ba sanin wurin nayi ba.


A yammacin ranar Yaya Engnr yasa Suleiman ya maidani gida, duk da mutanen gidan sun so na qara kwanaki nice naqi tunda dai nayi abinda ya kawo ni zaman me kuma zan yi.


Cikin hukuncin Allah jarrabawar mu ta fito na kuma yi dace na samu 70 points don haka Medicine din da na nema shi suka bani.


Ranar da Yaya Engnr ya kira Baba ya shaida mishi har kuka nayi don farin ciki don ban yi zaton zan samu ba saboda jarrabawar ta dan bani wahala.


Tun daga ranar Baba yake tanadin tafiya ta Kano don yace ko da Ismael ya dauki nauyin karatu na shima zai yi nashi qoqarin don ba zai yiwu ya sakar mishi dukkan hidima ta ba.


Ita ma Inna tayi tanadin kayan miya masu kyau irin su daddawa, kubewa, kuka, yakuwa busashiya haka da zan kaiwa su Hajiya Babba tsaraba tunda Yaya Engnr yace ba zan zauna a hostel ba a gidansu zan zauna mu dinga tafiya makaranta tare da Jamila.


Dubu goma haka Baba ya bani yace na riqe na dinga yin buqatuna na makaranta ba komai sai na tambayi Yaya Engnr ba.


Sosai na yaba da qoqarin Baba tunda na san fitar dubu goma daga wajen shi a wannan marrar ba abu ne mai sauqi ba.


Inna Baba yace ta shirya ta raka ni don ba zai yiwu ace sai an jira Ismael yazo ya daukeni ba, a cewar shi dama ya kamata na koyi tafiya da kaina tunda ba zai yiwu ace duk lokacin da zan tafi ko zan dawo sai Ismael yasa an kai ni ba.


Da wurwuri muka shirya muka tafi saboda Inna ba kwana zata yi ba.


Ba karamar murna suka yi ba da zuwan mu duk kuwa da ban wani jima da zuwa ba.


A uwar dakinta Hajiya Babba ta sauke Inna, sai hidima take yi da ita, ta kawo wannan ta ajiye ta koma ta dauko wani ta ajiye. Tun Inna tana ce mata "ya isa haka Hajiya" har dai tayi shiru ta zubawa sarautar Allah idanu ganin ba dainawa zata yi ba.


Sai da ta zauna sannan suka samu gaisawa sosai, daga nan kuma suka barke da hira.


Anan ne ma Innar ke cewa "Hajiya ga nan Zaynu, don Allah duk abinda kuka ga tayi ba daidai ba a tsawatar mata. Na barta ga Allah na barta a hannunki Hajiya, ki kula mini da ita kamar yadda zaki kula da yaran wajenki".


Kamo hannayenta Hajiya tayi ta riqe a cikin nata tace "ai ko baki fada ba Innar Zaynu wannan dole ne, ita amana ai daya ce da kuma na kowa ne bare ma yadda nake jin 'ya'yan cikina haka nake jin Zaynu a cikin raina, kada ki samu damuwa, In Sha Allah lafiya lau zata yi karatunta ta gama ba tare da wata mishkila ba".


"Nagode kwarai da karamci Hajiya, Allah ya saka muku da alkhairi ya dawwamar da farin ciki a rayuwarku. Shi kuwa Ismael babu abinda zamu ce mishi sai dai fatan gamawa da duniya lafiya, tun haduwar mu da shi ba rayuwar Zaynu kadai ya inganta ba har ma da tamu iyayenta. Allah ya saka mishi da alkhairi ya bashi masu yi mishi shima".


"Ameen Inna Ameen nagode" Hajiyar ta fada cikin jin dadin yabon da Ismael yake samu, har kullum tana alfahari da kasancewarta mahaifiyarshi saboda mutum ne shi mai tausayi da taimakon na qasa da shi, sam abun hannunshi bai rufe mishi idanu ba, shi yasa kuwa kullum cikin sake samun budin rayuwa yake.


Ni dama tunda muka gaisa da mutanen gidan Jamila ta janye ni dakinta, bamu fito ba sai da muka ji Inna zata tafi.


Sai kuma a sannan naji kewar gida ta kamani, idanuna suka cika da kwalla ya wasan nan sai gani ina zubar da hawaye, gefen hijabi na na sanya ina sharewa amma duk da haka wasu hawayen ke zuba kamar an bude famfo.


A haka dai muka yi sallama da Inna ta tafi ni kuma na koma parlour Hajiya Babba na zauna ina kuka.


Hajiyar ce ta shigo tana cewa "haba ke kuwa Zaynu sai kace yau kika fara barin gida da sunan karatu, aka kaiki makarantar kwana ma tun kina 'yar qanqanuwarki kika zauna bare nan da kike a gida. Wannan kukan naki ai sai ya dagawa Innarki hankali ta kasa samun nutsuwa da barin ki anan din. Maza share hawayenki ki shiga cikin 'yan uwanki ku cigaba da harkokinku, da nan gidan da can Jahun duk daya ne kin ji. Kada na qara gani kina zubar da hawaye".


Da kyar na samu na tsaida kukan. Tashi nayi na koma wajen Jamila, tana ganina kuwa ta fara tsokanata wai "iyye iyye, kaga 'yar lelen Inna mai kuka shagwaba don wannan kukan naki da gani na shagwaba ne", tun ina shareta har ban san lokacin da na fara dariya ba daga nan kuma muka cigaba da hira.


A ranar da nayi kwana biyu muka shirya da Jamila zamu gidan Yaya Engnr mu gaishesu.


Kafin mu tafi Hajiya Babba ta tsaida mu tace bari ta dauko tsarabarsu da muka kawo musu mu tafi musu dashi.


Kifi ne da nono ta dauko tana cewa "nasan dai gidan Ismael ba tuwo suke yi ba shi yasa ma ban debo musu daddawa da su kukar ba. Wannan din ma don nasan yana so ne tunda naga yana saya".


"To Hajiya ba sai ta iya girkin ba ma bare har a yi tuwo a gidan, cook ne fa da su shi yake girkin abincin gidan. Bata da wani aiki daga ci sai sha sai kwanciya, kuma wallahi yana son tuwon tunda idan yazo nan yaga anyi tuwo baya tafiya sai yaci kawai dai yi mishi ne baza ayi ba". 


"A'a to ba shi yace yaji ya gani ba Jamila, tunda irin rayuwar da ya zabawa kanshi kenan ai sai yaje yayi tayi ni dai nawa ido".


Daga yadda tayi maganar zaka san ranta a bace yake da al'amuran gidan Ismael, tana kawar da kai ne kawai don kada ta zamto mai yawan sa ido a harkokin gidanshi.


Suleiman ne zai kai mu. Tunda muka shiga motar yake yi wa Jamila masifa wai ta hada shi da Hajiya tasa dole ya kaimu bayan tasan ba zuwa gidan nan yake yi ba.


"Kuma wallahi idan kuka shiga kuka zauna tafiyata zan yi na bar ku sai dai Yaya Ismael yasa a maidaku don ni dai ba shiga zan yi ba" yace yayin da yayi parking a kofar gidan.


Saukowa muka yi daga motar ni ina riqe da kwalin kifi Jamila kuma ta dauko jarkar nonon muka durfafi babbar kofar shiga gidan.


Kwankwasawa Jamila tayi daga ciki aka amsa da "waye anan?"


Jamila tace "qannen mai gidan ne".


Da sauri mai gadin yazo ya bude karamar kofar dake jikin gate din yana yi mana sannu da zuwa.


Tunda muka shiga nake kallon harabar gidan ina jinjina tsaruwar shi, sai naga kamar an qara qawata gidan ne.


A babbar kofar da zata sada mutum da cikin gidan muka tsaya Jamila ta danna qararrawa.


Kamar ba za a bude ba don mun dan jima a tsaye a wurin kafin wani saurayi yazo ya bude kofar, ga alama dai yaron gida ne don gashi nan sanye da kaya irin na aiki a jikin shi.


Sai da ya qare mana kallo tun daga sama har qasa kafin yace "kun kuwa sanar da Madam zaku zo don dai bata ce mini zata yi baqi ba".


A qufule Jamila tace "idan kuma ba haka ba fa? Sai mu koma kenan ko yaya? Dallah Mallam matsa ka bamu waje mu wuce bamu da lokacin tsayawa batawa a wurinka".


Tayi kanshi kamar zata bangajeshi don haka yayi sauri ya matsa ya bata wuri.


"Taho mu tafi Zaynu" tace tana mai shigewa cikin gidan.


Ni dai ina biye da ita a baya kamar raqumi da akala ina mamakin jin ba a shiga gidan sai an sanar da masu gidan za a zo tukunna. 


Muna zama a parlour da ya kasance na matar gidan yaron gidan yazo ya dauki waya ya kara a kunne bayan yayi 'yan danne-danne.


Ina ji yana sanar da wanda ya amsa wayar daga daya bangaren cewa baqi ne aka yi gamu a parlour madam na qasa, bayan ya gama wayar ne ya dauki remote ya kunna tv sannan ya qara karfin ac ya wuce.


Ni dai tunda muka shigo nake kallon wurin nan ina qarewa dukiyar da aka zuba a ciki kallo ina mamaki.


Hira muke yi jifa-jifa ni da Jamila. Ganin shirun yayi yawa nace da Jamila "ko dai tafiya zamu yi ne ga alama fa masu gidan basu tashi ba".


"Bari na kira Yaya Engnr na sanar dashi zuwan mu don inaga wancan yaron matar gidan ya fadawa shi yasa har yanzu ba a waiwaye mu ba. Ai dama haka take yi idan tayi baqi sai tafi awa bata sauko ba shi yasa babu mai son zuwa gidan nan".


Cikin bacci yaji wayarshi na ringing. Tsaki yayi ya kai hannu ya dauko wayar daga kan bedside table ya amsa tare da kai ta kunnenshi ba tare da ya duba sunan mai kiran ba.


"Hello Yaya, ina kwana" aka ce bayan ya kanga wayar a kunnenshi. Dago wayar yayi ya kalli sunan mai kiran don bai gane muryar mai magana ba.


"Oh Jamila, lafiya lau" ya amsa bayan ya maida wayar kunnenshi.


"Yaya gamu a qasa mun zo tun dazu har yanzu Aunty Badi'a bata sauko ba".


"Kun zo ina kenan?"


"Gidanka fa Yaya, gamu a qasa tun dazu muka zo"


"Ok, gani nan saukowa".


Cire Badi'a yayi daga jikinshi ya kwantar da ita akan pillow ya nufi bathroom.


Tubewa kawai yayi ya fara wanka, ko kadan baccin nan bai ishe shi ba ko don baya samun hutu sai a irin wannan lokacin na weekend shi yasa yake kashe wayarshi don kada a dameshi.


Yana cikin wankan yaji qarar bude kofa. Juyawa yayi yaga Badi'a ce ta shigo.


Cire kayanta tayi tayi joining dinshi a cikin bath din ta karbi soson hannunshi ta hau saba jikinshi tana wankeshi, a taqaice dai tare suka yi wankan don haka suka dan bata time kafin su gama.


A gurguje ya shirya cikin qananun kaya wandon jeans faded black sai polo shirt kalar maroon. Turarenshi na 212 ya fesa a jikinshi sannan ya fita.


Ni dai tsabar gajiya da nayi da zama har ban san lokacin da na fara bacci ba, sai jin muryar Yaya Engnr nayi yana cewa "kuyi haquri fa mun barku kuna ta jira, wayarku ce ta tashe mu daga bacci".


Dama dai baccin nawa ba wai yayi nisa ba ne don haka na tashi na gyara zama na.


Zama yayi akan kujera single sitter ya dauki remote ya canja channel zuwa CNN.


A tare muka gaishe shi, a taqaice ya amsa. Sai kuma ya juyo ya kalleni yace "ke da Zainab ne ashe, yaushe kika zo babu labari ni da nake cewa zan samu time gobe naje na taho da ke".


Murmushi nayi nace "yau kwanana biyu Yaya, Baba ne yace mu taho kawai ba sai an jiraka ba shine Inna ta rako ni".


Murmushin yayi shima yace "Baba kenan, ai da ya sani da bai wahalar da Inna ba don dama gobe nake da niyyar zuwa na taho dake. Yasu Baban da Inna duk lafiya suke?"


Nace "lafiyarsu lau Alhamdulillah".


"Masha Allah. Yanzu sai karatu ko? Kuma kun zama 'yam matan jami'a".


Murmushi muka yi.


Yace "sai kun qara zage damtse don wannan karatun ba irin wanda kuka gama bane ko yaya kuka samu matsala sai yayi affecting result din ku a gaba ba ma dai irin karatunku Zainab dole ne kiyi passing duka courses din ki a wadannan shekarun farkon babu batun carry over, it's either kiyi changing department ko ki haqura da karatun gaba daya don haka sai kin dage".


Nace "In Sha Allah Yaya, nagode".


Mun dan jima muna hira kafin muka ce mishi zamu koma. Jamila ce ta nuna mishi kayan da muka kawo.


Yaji dadi kuwa kwarai da gaske yayi ta godiya kamar wanda muka kawo mishi wasu kayan gabas ba nono da kifi ba.


Driver yasa ya maida mu. Bai ce mu tsaya mu gaida matar gidan ba muma kuma bamu nemi yin hakan ba tunda dai ai tasan mun zo amma har muka qari zaman mu muka tashi tafiya bata sauko ba.



  

*SABON SALO SABUWAR TAFIYA.....*💪


*TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B*


INA KUKE MAKARANTA??


INA KUKE MASOYA? INA KUKE MAKARANTA LITTATTAFAN HASKE WRITERS??? KU MARMATSO 🗣️


SABON SALON Namu NA DABAN NE, SABON TAKUN NAMU MAI KAYATARWA NE MAI FADAKARWA MAI ILIMANTARWA MAI GIGITARWA ABANGARAN SOYAYYA, ZAKU KOYI SALO DABAN DABAN DA ILIMI TA BANGARE DA DAMA, SOYAYYAH MAI GIGITA ZUCIYA MAI SAKA NUTSUWA....


TOP 10 TAKUN HASKE BATCH B


INDA ZAKI KWASHI GARABASAR KARATUN LITTATTAFAI MASU 'DINBIN FADAKARWA DA SAKA NISHA'DI HAR GUDA BAKWAI.


1- *KAUNA CE* 

NA UMM ASGHAR 


2- *RUKUQI*

NA FEEDHOM 


3- *WANI SO*

NA ZEE YABOUR 


4- *SO DA ALAKA*

NA UMMI AISHA 


5- *MUGUN GANI*

NA SADIYA NASIR DAN


6- *ABDUL_HAMEED*

NA NANA DISO


7- *MUKULLIN ZUCIYA*

NA MAMAN KHADY


Daya 200 

biyu 400, 

guda uku 500

Guda hudu 700 

Guda biyar 750 

Shida 800 bakwai 1000 da programs


DOMIN MALLAKAR NAKI ZAKI BIYA


(1000) DUBU DAYA KACAL


KAI KA KAI....!

TIRQASHI, DUKA FA WANNAN GARA'BASAR ZA'A BAKU ITA AKAN N1000 KACAL, GA KUMA SHIRYE-SHIRYE HAR GUDA UKU DA ZAMU KOYAR DOMIN YABAWA, JINJINAWA DA KUMA FARANTAWA AGAREKU MASOYAN MU...


1- SHIRIN KOYAR DA GIRKE-GIRKE DOMIN ZUZUTA MAIGIDA😍 

*DAGA CHEF RAHMA NA LELE*


2-SHIRIN KOYAR DA YANDA ZAKI TSAFTACE JIKINKI, DA YANDA ZAKI ZAMO CIKIN KAMSHI A KODA YAUSHE WANDA ZAKI HAD'A DA KANKI ACIKIN GIDANKI DOMIN MAQALEWA A ZUCIYAR MAIGIDA

*DAGA AYUSHER MUH'D*


3-SHIRIN KOYOR DA YANDA ZAKI IYA HADA KAYAN NI'IMA A JIKINKI CIKIN SAUKI DOMIN GYARAN GIDAN AURENKI DA ZAMOWA FITILAR GIDANKI

*DAGA HAJJA CE 👈*


MASHAA ALLAH DUKA FA AKAN NAIRARKI *DUBU DAYA* KACAL ZAKI KASANCE ACIKIN GROUP DINNAN


_GAMASU BUQATAR WANNAN GARAB'ASAR TAMU ZAKU IYA TURA KU'DINKU (N1000)TA WANNAN ACCOUNT👇🏼_

2083371244

ZENITH BANK 

AISHA M. SALIS


*SHEDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR👇🏼*

+447894142004


IDAN KUMA KATIN WAYA NE, ZAKU TURA TA *WANNAN LAMBAR👇🏼*

*** da Shaidar biya duk ta ciki


_GA MUTANENMU NA QASAR NIGER🇳🇪 ZAKU IYA TURA KUDINKU TA NITA, AMANA, ALI'ZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR👇🏼_

+227 96 91 36 36 RAHINA daga niamey.

MUN GODE.


*TOP TEN TAKUN HASKE BATCH B 2022*


_Wannan garabasar tamai rabo ce💃🏻💃🏻 sa kud'i kad'an ki debi hani'an😍😂_


*UMMASGHAR*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol