Free chapter · Read without an account

SIRRIN ZUCIYA 4.

by Nusaiba · SIRRIN ZUCIYA

SIRRIN ZUCIYA❤






Na

Nuceeyluv😘




4....



"Ya na ganki duk a turbune fuska ba walwala?"


"Daga can part din nake mana Ammi wlh sun fara kaini bango"


tayi mgnr tana zama kusa da Ammi,


"haba sameera mene abin gaggawa a ciki? Ai karki wani damu dole ma daya daga cikinsu ya aureki"


Sameera ta dan tabe baki tana kallon mahaifiyar tata tace,


"Ammi duk yadda nake qasa da kaina a wajen su sunqi bani yadda sbd Allah inda kara bani ya dace na karbi ragamar part din 'yan uku ba? Ai tanan zamu shaqu har su zabe ni dukda dai nafi son Abutturab, amma suka kawo wata shegiyar yarinya me ido a tsakar ka wai itace me kula da part din Mtwss"


Ammi da mmki tace,


"wata suka samo?"


"Ehmana"


Sameera ta amsa rai a bace, murmushi Ammi tayi tace,


"idan 'yan uku ne da gudu zata fece dan ba kowa zai iya dasu ba, Amma karki damu zamu san yadda zamuyi kinji?"


Sai a lkcin sameera ta saki ranta tace,


"Allah dai ya biya Ammina"


Ammi tace,


"ai Insha Allahu wannan ji da kai da Khadija take da kuma dukiyar su duk sai sun dawo karkashin ikon mu"


Sameera tayi murmushi tana hango tuggun da suke hadawa ita da mahaifiyar ta Ammi.


Hasiba kenan wacce suke kira da Ammi mahaifiyar Sameera da Sameer, green snake under the grass kenan duk cikin matan gidan ta fisu shiru2 idan ka kalleta zakace ko yatsa bazata ciza ba, tanada sanyin hali sosai idan kaga yadda take yada kai da kambama hajia Khadija wato Mummy sai kasha mmki, sosai zaka dauka tafi kowa sonta, shiyasa ma Mummy ba wacce tafi aminta da ita irin Ammi,


ta bata yadda 100% Allah sarki akace rashin sani yafi dare duhu bata san cewa duk cikinsu tafi kowa mata Hassada ba, tana mata Hassada da dukkan ni'imar da Allah yyi mata, bata taba sonta ba koda na misqali zarratin, duk wani so da take nunawa mummy da yaranta fanko ne tanayi ne kawai dan ta wargaza farin cikin familyn,


So take duk abinda hajia khadija ke takama dashi ya dawo karkashin ikon ta, tana bakin cikin ace hajia khadiya ce kan gaba a komai,


tun farkon tashin sameera ta cusa mata wannan akidar sbd tanason cimma burinta ta hanyar ta, Sameera nada rawar kai kwarai gata lange2 kamar a bushe ta fadi, tunda ta taso itama sai takejin wannan kyashin irin na mahaifiyar ta, gashi dai suna dasawa da khairat dukda ta girmeta da 2yrs hakan be hanata jin haushin duk wani kaya mekyau da zata gani gun khairat ba,


shiyasa duk abinda ta gani sai Ammi ta siya mata sbd kyashi, khairat zaton ta duk a cikin so ne shiyasa takejin dadi idan taga irin abinta wajen Sameera, Nan kuwa batasan hassada tasa tayi irinshi ba dan itama ta tsani ace khairat ita kadai ba'a sa da ita ba, Sameera tanaji da kanta sosai yadda kasan itace khairat yadda take nuna isa kamar gidansu, kai har ya wuce ace khairat dan ita bata cika nuna isa kamar sameeran ba,


shiyasa takeson Abutturab sbd yafi 'yan uwansa zafin kai irin mijin da takeso kenan ta fiso a dinga jera ta a high class babys, tanason karya ba kadan ba, batasan shi a jininsa yake ba sannan kai tsaye ba karya yake ba tunda ta ko ina Allah ya basu kyau, dukiya, da kira Masha Allah duk mace me jini a jika dole ta kyasa,


sabanin ita da farin saida aka kara da mai, hips da breast saida ta kara da tabs dukda ta kara ma ba wani sosai ya fito ba yadai fi da datake kamar sillen kara. Baban Sameera kawu Idris da Sameer kaninta duk basu san me suke shirya ba sbd abin ya kasance *SIRRN ZUCIYA*


Wannan kenan,


~~~

Su kuwa bangaren Kawu Yusuf kuwa matarsa Asiya yaranta uku Musa, jibril sai Autar su Humaira itakam anyi aurenta watannin baya, Asiya da suke kira Mami tana da masifa ssai duk abinda akai mata idan be mata dadi ba yanzu zata amayar shi, shiyasa suke gogawa da Hajia khadija dan itama akwai fada sam basa zama inuwa daya, dan kowa kar da kar ne, sau tari xakaga basa shiga sabgar juna dukda suna gida daya, Mami 'yar kasuwa ce kasuwanci shine a gabanta shiyasa sam wani rikicin ma batasan anayi ba, bata iya ruko ba dan haka babu kowa a gabanta, matsala dayace a part din,


kawu Yusuf shine me mummunan hali, duk irin kyautatawar da Alhji Mahmoud zai musu baya gani, shima hasada tayi masa katutu a zuciya yana me bakin cikin ci gaban Alhaji Mahmoud, da son samu ne a ra'ayin sa duk kamfanonin Alhji Mahmoud su kama da wuta kadarar sa ta karye kowama ya huta. Wannan kenan,



•••

Part din kawu bala kuwa matar sa me suna Maimuna ana kiranta da Ummah yaranta biyu ne, duk mata sa'adatu da Halima, Sa'adatu anyi mata aure tare akayi dana humaira, Ita dai Umma barta da makirci Allah ya bata, tanada surutu da hada gulma sau tari wani abin ma idan Mummy da Mami suka kaure suna maida zance itace ke hadasu,


sai ta gama makircin ta ta koma gefe tana sheka dariyar mugunta, haka halinta yake, sannan burinta itama ace halima ta auri daya daga cikin 'yan uku badan komai ba saidan su sami me danshi a nuna 'yarta ace matar wane ce gata a makeken gida shikenan burinta.




****

Tunda suka fara tafiya babu wanda yace komai khairat na gaba fati na bin bayanta, Da wannan damar ta samu zarafin karewa gidan kallo, tun kafin su karasa part din 'yan uku ta fara lura da yanayin gaban wajen da aka kawata da wasu fulawa masu kyau.


Basu wani tafiya ssai ba suka isa gaban part din, key khairat tasa ta bude kafin ta juyo ta kalli fatima tace,


"shigo mana"


shiga fati tayi nan ta fara kallan Aljannar duniya kamar ba parlon Maza ba, wani daddan kamshi ne ya bugi hancin ta ai kuwa ta lumshe ido kafin ta wara su,


khairat tayi gaba wani dan corridor babu nisa sai ga wata kofa, nan ma key tasa ta bude kafin ta waigo still fatima na tsaye tsakiyar parlon,


"Kizo mana kina batamin lkci"


khairat ta fada cikin jin haushi, kallon ta fati tayi taga yarinya ce bazata wuce tsarar ta ba, dan girgiza kai tayi tana cije lips a ranta tace a sannu zan saita muku shaidanun kanku dan naga alama yaran gidan wani tashen balagar tsuntsaye ke tashi a kansu,


tayi mgnr tana karasawa wajen khairat.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.