Free chapter 路 Read without an account
Chapter 5 chapter 5
by autararewa101 路 DR MUHSEEN
DR MUHSEEN
Bismallahi Rahamir Rahim.
PAGE 5锔忊儯
馃摑...................Karan wayar shi da ya ji ne ya dakatar da shi daga abinda yayi niyyar yimata.sakinta yayi yana Mika hannu gaban motarshi shi ya ciro wayar daga jikin charge.hakan Yaba seeyerma damar matsawa gefe tana gyara hijaf dinta tare da mayar da numfashi,ganin sunan Dady na yawo akan screen din wayar yasaka shi tunawa da tunda ya shigo bai shiga part dinsu ba,cikin sanyin jiki ya daga Yana dora yatsar shi saman labban shi alamar kada tayi magana.itako yi tayi kaman bata gane me yake nufi ba tahau kiciniyar bude kofar Amma ta kasa budewa saboda ya saka luck.da sauri ta juyo tana kallonshi jin Yana cewa "Dady bazan samu shigowa ba saida safe,tunda na zo ban zauna ba haryan zu"jin Dady ya ce "to soon Allah ya kaimu"kafin ya katse Kiran Yana bude motar.da sauri ta figi Jakarta ta fice ba tare data Kara Koda kallon shi ba.A zuciyarta kuwa Allah yaisa take jamai da zagi,ita kam ta kasa gano me wannan mutumin yake nufi da ita,kwata-kwata sai ya rinka yimata wasu abubuwa Wanda hankalinta ya kasa dauka.da wannan tunanin ta shiga islamiyyar tasu direct ajinsu ta nufa har ankusa awa daya da fara karatu.shidai malam Husaini baice da ita komai ba ta samu gurin zama akaci gaba da karatu.
Shiko tun bayan ta fita ya dade a bayan motar kanshi jingi ne Yana tunanin halin da mahaifiyar shi take ci na wulakancin mahaifin su da Hajiya mariya ta haddasa masu.ko dazu yaso shiga gidan kodan yaga mahaifin nashi Amma saboda makirar matar nan ya kasa shiga,Wanda a halin yanzu duk tashin hankalin da mutanen estate din suke ciki ita ce sanadi.shiyasa a kullun yake Kara jin tsanar Hajiya mariya.bai ankare ba yaga har karfe goma ta kusa,da sauri ya zagaya mazaunin direver ya tayar da motar da gudu ya Kara cikin estate din.wurin da aka tanada dan aje motoci ya shiga runface mai girman gaske har Kashi biyu a jere,Wanda a kalla za'a iya aje motocin da zasu Kai hamsin.saida ya tabbatar ya dauki wayoyinshi da wasu abubuwan kafin ya rufe motar ya wuce gidan shi mai nomber 26 tazarar dake tsakanin su da Faruk bata da yawa.bayan ya saka key ya bude saida yayi addu'a kafin ya shiga Yana mayar da kofar falon.kayan kallo ya kunna kafin ya wuce bedroom saboda Yana so ya kalli ball kafin ya konta.
Seeyerma sune Basu taso daga islamiyya ba sai karfe goma,tunda suka taho su sakeenah da Bahijja suke tambayarta meyasa ta makara?shiru tayi ta kyale su taki basu amsa,da taga sun dameta ta Kara sauri ta wucesu gidan su Aunty Hajara ta wuce dan tayi alkawarin ita da dawowa sai ranar Monday da yamma.ganin ta kyale su yasa Suma suka shareta suna magana kasa-kasa har suka shige gidan Mama ita Kuma ta karasa gidan Uncle Yusuf.
*WASHE GARI*
Washe gari muhseen tunda ya dawo daga sallar asuba shi ne bai fito ba sai karfe goma na safe cikin Shirin shi na farar black boyel mai kyau da tsada sai faman tashin kanshin turaren uhd yake zubawa.da daidaya ya fara bin gidajen iyayen nashi Yana gaishe da su,Wanda da yawan su kannen mahaifin shi ne da iyalen su.yana gaf da shiga part din Dady wayar shi tayi Kara sosai ya duba ganin wadda take Kiran shi yasaka shi Jan wani siririn tsaki tare da furta"wannan yarinyar ta takurama rayuwata,na rasa me take nema a gurina"har saida Kiran ya katse kafin wani ya Kara shigowa.cikin jin haushi yayi picking ba tare daya ce komai ba.ita ko jin yaki yin magana tayi saurin cewa "Kayi hakuri na kiraka da wuri ko"saida yadan yi shiru kafin ya bata amsa da "ki Bari sai kin koyo sallama kafin ki Kara korana"kit ya katse Kiran ba tare daya Kara bata damar magana ba.sosai zahara'u taji wani bakinciki ya mamaye zuciyar ta."wallahi baka isaba Dr muhseen baka da wata Mata bayan ni,inhar ina numfashi to dole ne ka soni,Koda abinda na mallaka zai Kare saina mallake ka a matsayin mijina"tana sakin wani makirin murmushi mai dauke da ma'ana daban-daban.a daidai wannan lokacin tana konce a changing room dake cikin maternity na asibiji sojoji dake Daura.mirginawa ta karayi tana Kara kankame wayarta a kirjinta.lumshe ido tayi tana Kara tuno da kyakykyawar surar Dr muhseen Wanda tayi Imani da Allah babu macen da zata ganshi ta kushe shi sai maki Allah.tunowa tayi da ranar data fara ganin shi tayi tinanin balarabe ne.tundaga ranar ta kasa samun sukuni musamman data fahimci kusan rabin yan'matan cikin asibitin rububinshi suke yi.sai dai abinda yafi bata mamaki da daure Mata Kai ganin duk cikinsu ba wacce ta isheshi kallo a cikinsu.hasalima idan ba gaisuwa ba ko fannin aiki ya hadaku ba ruwanshi da kowacce.itama dakyar tayi nasarar samo nomber shi a wurin wani abokin shi,dukda tana Shan wulakanci Amma a haka take jurewa harsai ta cimma burinta.lekowar wata Mata ya katse Mata tunaninta jin Karin ruwan data jonama marar lafiya ya kare.cikin mutuwar jiki ta nufi dakin Dan dubata.
Shiko Muhseen mutssssssss ya ja tsaki Yana danna belt na gidan.a zuciyar shi Yana tunanin rashin kamun Kai na wasu matan da sunga namiji kyakykyawa da Yan canjin shi sai su makalemai.ganin an bude kofar yasa ya Kai duban shi Dan ganin ko waye.Hajiya Mariya ce tsaye ta kama kugu cikin kwalliyar leshin ta kashe daurin Dan kwali kaman wata Karamar yarinya.kauda kanshi yayi ya nufi cikin gidan ganin kamar zai turo ta yasa tayi saurin matsawa tana hararar shi.ganin Dadyn nashi baya falon yayima kanshi masauki a Kan kujera.yana Kara jin tsanar matar.zuwa tayi ta wuce shi tana cewa "Aikin banza kiba a kunne rama a takashi,Ni duk yadda mutum ya tsane ni dole ya kalle ni ya kyale ni"ta shige dakin mai gidan nata Alhaji Muhammad.shidai muhseen ko kallonta baiyi ba ballantana ta saka ran zai tankata. saboda shi yunwama yake ji so yake ya karasa gidan Aunty Hajara yayi breakfast acan.jin kamar motsin fitowar mahaifin nashi yasa yayi saurin saukowa kasa.saida ya tabbatar ya zauna kafin ya ce "Dady Ina kwana,mun same ku lafiya"saida mahaifin nashi ya Kara kallon shi sosaikafin ya amsa da "lafiya Lau,ya Aikin naku"
"Aiki alhmdlillah "cewar muhseen.
"Masha Allah,Allah yayi taimako ya tsare ku Baki days"sosai yayi dadin addu'ar mahaifin nashi yayi saurin amsawa da "Amin ya Allah"
"Yanzu soon kazo tun jiya Amma bazaka shigo ba harsai na nemeka"cikin muryar tausayi da dattijantaka.sosai muhseen ya ji tausayin mahaifin nashi,Dan yasan ko a watannin baya da al''amura sukayi ta faruwa marassa dadi yasan bada yin kanshi bane,Dole akwai makircin waccen munafikar matar,Amma koma meye suna addu'ar Allah ya toni asirinta.
Kontar da murya yayi Yana ba mahaifin nashi hakuri,saida yaga ya Dan saki ransa kafin yayimai sallama ya fice daga gidan.Direct gidan Auncle Yusuf yayima tsinke kusan yawanci gidan su a bude yake Dan haka ya kutsa kanshi cikin gidan bakin shi dauke da sallama.ganin Aunty Hajara A kasan kafet tana break yasa ya fadada murmushin shi Yana nufota."A lallai dana sai yanzu ka tuna da ni,nayi tinanin bazaka zo ba"tana goge hannunta da tussue.shima kasan kafet din yayima kanshi masauki Yana dariya"Allah Aunty kiyi hakuri tunda nazo ban zauna ba,jiyama gidan su Lameer naje,kinsanshi da shegen surutu haka ya rike ni sai dare na dawo,yanzu bama wannan ba Aunty kin ji cikina ya fara Kiran ciroma a taimakoman da break kin ji"Yana marairaicewa kaman wani karamin yaro.dariya tayi ta yimasa kafin ta ce "kaga illar gauranci yanzu da kayi aurenka tun kafin ka tashi a bacci ta hadama komai"shidai shiru yayi Yana murmushi.kwala Kiran seeyerma tayi donta kawo mai abinci.itako daidai ta fito daga kitchen da cup a hannunta.jin Kiran Auntyn yasa ta karaso da sauri sai a lokacin ta lura da Wanda yake zaune,cikin razana ta kwalalo idonta waje tana sakin cup din kasa,sai akan ...................
By
AUTAR AREWA.
鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍