Free chapter 路 Read without an account

Chapter 8 chapter 8

by autararewa101 路 DR MUHSEEN

DR MUHSEEN





Bismallahi Rahamir Rahim.





PAGE 8锔忊儯




馃摑....................Cikin mutuwar jiki ya ci gaba da maimaita kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un,har zuwa tsawon wani lokaci bai gusa daga inda yake ba saida ya yayi addu'o'i sosai domin shidai tunda ya bude yaga kamar mutum zaune bisa kujerar falon nashi.Amma cikin ikon Allah da karfin addu'a ya daina ganin mutumin.ba tare da yayi kasa a gyuwa ba ya shiga gidan da kafar dama Yana ci gaba da neman tsari daga sharrin abinda ya gani.



A katsina kuwa a lokacin da ya bude dakin shi yayi daidai da farkawar Seeyerma daga nannauyan baccin daya dauketa.bakinta dauke da Addu'a ta juya ganinta konce kan gado yasa tayi

saurin ta shi tasan tuno abinda ya faru Amma ta kasa.shigowar Aunty Hajara yasa tayi saurin Kai dubanta bakin kofar tana girgiza kanta.



Da sauri Aunty Hajara ta karaso bakin gadon tana yimata sannu.

Ita dai bata amsa ba,sai gyada kanta da tayi.


Ganin hawaye nabin saman kumatunta yasa Aunty Hajara tayi saurin kamo hannunta tana cewa "sorry Seeyerma taso mu je kiyi Alwala, lokacin salla yayi,kiyi hakuri ki yawaita addu'a,zo mu je kafin Uncle din ki ya amso maki magunguna sai ki fara amfani da su"tana kokarin mikar da ita tsaye.saida ta kaita har cikin toilet ta hada Mata ruwan wanka kafin kafin ta fito tana jin alhinin faruwar wannan abin al'ajabi.



Seeyarma ta dade sosai tana wankan kafin ta dauro alwala ta fito.kayanta ta gani Aunty Hajara ta ajemata a bisa gadon.ko mai bata tsaya shafawa ba turare kawai ta murza a jikinta kafin ta saka doguwar rigar ta atamfa.bayan ta shimfida prayermate ta saka dogon hijaf tare da kabbara salla.cikin nutsuwa ta biya sallolin da aka biyota.ta Jima ta addu'o'i ga iyayenta da neman sauki a rayuwar ta.abinda yafi dauremata Kai shi ne yadda aka fara bibiyar rayuwar ta,sannan tun daga lokacin da taga ya Muhseen Amma ba da ainahin sufar shi ta ganshi ba shi ne abinda ya tsorata ta.Aunty Hajara ce ta Kara shigowa hannunwanta dauke da babban tray sai kayan abinci da aka jera a saman shi.

Kusa da ita ta aje tana umartar ta da ta ci abincin yanzu zata amso Mata maganin ta sha.tana juyawa zuwa part din Uncle Yusuf.



Cikin sanyi ta cire hijaf din jikinta ta fara zuba abincin.kadan taci faten doyar ta ji ta koshi.shiru tayi hannuwanta bisa kumatunta tana ci gaba da tunaninta.


"Mhammadu kayiwa Allah ka maido da matarka,ni bazan yimaka Baki ba akan zaman ka da Mariya,Amma bazan gaji da jaddadama ba Mariya ba matar kirki ce ba,bawai Ina zarginta ba,Amma ni da ahalina a kullun Muna addu'ar Allah ya toni asirin duk Wanda yake da saka hannu a cikin rudanin da muke fuskanta."cewar Kaka da take zaune bisa abin sallah kanta jingi ne jikin doguwar kujera.kallon shi ta Kara yi a karo na biyu ganin yadda kolla take zuba daga idon shi.ajiyar zuciya ta Kara saukewa ganin kalamanta sun fara ratsa jikin shi.tabbas an fara samun ci gaba idan lokuttan baya ne ko saurarenta bazai yi ba.

"Kayi hakuri muhammadu kowane bawa da irin kaddarar shi,Amma hakuri shi ne ke maganin komai"

Shi dai ko uffan baice ba,sai faman sharar kolla yake yi.shiru sukayi dukan su,har tsawon wani lokaci kafin ya mike jin mahaifiyar tasu bata ce komai ba.harya fice tana kallon shi kafin ta girgiza kanta tana tunanin wasu lokutta da suka shude.




Dr muhseen ne ya fito daga part din shi ya nufi cikin area asibintin dan duba masu jinya.yayi nisa sosai da tafiya ,saboda akwai tazara mai Dan nisa daga dakunan su zuwa cikin asibitin.zuciyar shi cunkushe take da tunani iri-iri,jin Karan wayar shi ya saka saurin laluba ajjihun farar jallabiyar da take jikin shi,ganin sunan Ummeey akan secreen din wayar yasa ya Kara jin faduwar gaba,Dan yasan zata tambaye shi jikin Seeyerma ne.saida ya Bari ta katse kafin ya danna calling nomber,wata Yar inuwa ya nufa Yana tsayawa.

Cikin sallama ta daga wayar jin muryar Dan nata abin soyuwa a gareta.cikin yaren larabci take tambayar shi jikin Seeyerma,cikin sanyi yake cemata da sauki, Anan yayi Mata bayanin matsalar.

Sosai taji tausayin yarinyar Dan tasan tabbas magautan su a cikin estate din suke,Anan ta Kara bashi shawarwari tare da Kara kontar mai da hankali.kafin suka yi sallama.ya katse Kiran,ya karasa cikin asibitin .Dan Muhseen Al'adar shi kenan,inhar Yana nan to sai ya ziyarci masu jinyar.


Faruk ne yake kokarin bude part din,Amma jin kamar ana magana a gefen part din yasa ya juyo da sauri,cikin sanda ya nufi wurin Yana Kara kasa kunnen shi,jin irin kalaman da suke fitowa daga bakin wacce take tsaye.da sauri ya koma Yana labewa ganin kamar zata juyo.ji yayi tana Kara cewa.


"Idan har kayi sake daga ni har Kai zamu fada wata zazzafar rijiya wadda zurfi da kwazazza fan da suke cikinta zasu hallaka mu"nisawa tayi tana cigaba da cewa "kaga Alhaji na gaji da gafara sa Banga kaho ba,tsawon shekaru Muna faman turin mota Amma tana neman tashi ta bademu da kura,ko kasan abinda zaka yi da mu,ko ni na dauki mataki da hannuna"banji amsa da aka Bata ba tayi saurin juyowa cike da mamaki Faruka ya Kara bude idanuwan shi dan tabbatar da wacce ya gani......................










By




AUTAR AREWA.






鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍鉁嶏笍

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.