Free chapter 路 Read without an account

12

by Binta Umar Abbale 路 Sadauki Omar

SADAUKI!!馃徆

_OMAR馃挮馃憫_


Free pege

12



Hankalin kowa ya koma kan Aysha dake tsiyayar da hawaye shikkenan asirin ta ya Tono ita kuwa me zatayi wa 'yar iskar yarinyar nan ta huce takaicin ta.... Mai marba ya kalli Omar dake sunkuye da kansa a 'kasa yace." Maganar da Safara'u ta fada shin haka take ko ba haka bane menene ya Kai Aysha har inda kake bayan nayi sulhu a tsakanin ku." Omar ya rasa abunda zai ce ganin Ayshar na kuka sai ta bashi tausayi amma saboda yana so aka ja mata kunne yasa yace." Ranka ya dade babu wani Abu da ya sake shiga tsakanin mu tun bayan sulhun da kayi mana a fada yau din ma akasi aka samu ranka ya dad'e ni na amunce na zama bawan nata kamar yanda take bukata mutukar hakan zai sanya ta zauna lafiya dani." Sarki yace." Maganar runguma fa shin da gaske ta rungume ka ko A'a." Omar yayi kasa da kansa kwata-kwata a rayuwarsa shi bai iya karya ba shiyasa yayi kasa da kansa Mai Martaba yace." Tunda naga ka sunkuyar da kanka kasa nasan da gaske hakan ta faru domin nasan kai din mutum ne mai fadin gaskiya Cikin lamuranka.



Nanne ta fara share hawaye tace"Ranka ya dade ina da magana. "! Sarki yace." Bislimillah ." Tace''Duka wannan maganar da ake gaskiya ne Aysha ta aikata abunda ake tuhumarta dashi lokacin data shiga gurina naga alama Allah ya taimake ka gatanan a gabanku Ku tambaye ta idan aure take so to ta futo da miji ayi mata tun kafin ta jawo mana abun kunya.



Baba Waziri ya kalli Aysha ransa a bace yace. " Aysha kin bani kunya wallahi kuma kin zubar da darajarki da kimarki ta d'iya mace kaf! A tarihin masarautar nan babu Wanda ya ta'ba aikata irin wannan aikin saboda haka yanzu ba sai anja wani lokaci ba Sarki zai yanke miki hukuncin da duk ya dace dake..... "Wai yaya zaku Dora mata laifi ita kadai ne na tabbatar da cewar wannan abun Aysha ta bata aikata ba duka sharrin wannan munafukar yar ne da Uwar rokon ta dashi kanshi munafikin Yaron Ina rokon alfarma kafin a yanke mata hukunci a tsaya a tsaurara bunkice kan lamarin." Mai dakin kusurwa ce take wannan maganar sai share hawaye take..... Babu Wanda yace mata komai duka suna sauraron hukuncin da mai Martaba zai yanke.......Gyaran murya yayi yace." Aysha daga nan zuwa kwana goma ki tsayar da mijin aure cikin mane man ki.. Shiru yayi na minti biyu ya cigaba da cewa "Zaki zauna cikin Dakin dake kusa da rumfar dokona tsawon kwanaki bakwai ba tare da kin le'ko waje ba sai dai komai za'a mik'a miki." Duka suka kalli Mai Martaba jin irin hukuncin da ya yanke...... Wani wawakeken daki ne me wata gajeriyar kofa duk wani nau'in abincin dabbobin dake cikin gidan a cikin dakin yake duk kwa'kwar mutum bazai gano karshen sa ba saboda yanda yake da mugun zurfi da fadi kofofi sun kai goma a cikinsa daga ko wane sashen ana iya shiga dakin. Wannan dakin Sarki yake so ta zauna tsawon sati daya..... Da rarrafe ta karasa kusa dashi ta rike k'afarsa tana kuka tana Neman afuwarsa.""" Babu Wanda ya tausaya mata a cikinsu shi kanshi Galadiman yaji dadin hukuncin da Dan uwansa ya yanke kan yarshi idan ya daga kansa ya kalli Omar sai yaji Kamar ya shake shi ya huta saboda yanda yake jin haushin sa...... Kukan da take yana ta'ba masa rai don haka sai ya 'kagu a sallame shi ya bar gurin.... Mai dakin kusurwa ta hakikance sai kuka take Kamar gaske take "Fadin" A gaskiya wannan hukuncin yayi tsauri ranka ya Dade na tabbata ko bawa ne yayi laifi cikin gidanan baza'a tura shi irin wannan dakin ba dakin da ake aje abincin dabbobi Wannan ya nuni da cewar kun mayar min da yarinya Kamar dabba." Waziri yace." Hauwa duk Wannan bata taso ba hukuncin dai an zartar dashi kin San kuma Sarki baya magana biyu, saboda haka magana ta wuce." Hanci ta fyace tace"Shikkenan shi wane irin hukunci za'a dauka a kansa? " da sauri Nanne tace"Meye laifin Omar anan gurin? Hukunci dai mai laifi ta kar'ba Allah yasa ya zama izina a gare ta.....Mai Martaba ya mike da niyar futa Waziri da Galadima suka rufa masa baya..... Aysha ta rarrafa tana kuka ta rirrike k'afafun Nanne tana kuka da fadin"Wallahi Nanne ba da wata manufa na rungume shi ba asalima ban San lokacin da haka ta faru ba."


Don Allah Ku yarda dani wallahi bana jin komai a dangane dashi Asali ma shine Babban Wanda na tsana a duniya makiyi na ne shi na tabbatar dashi aka hada min wannan sharrin.....! Tana wani irin kuka ta k'arashe maganar.


Nanne ta mike ba tare da ta komai ba ta kama hanyar futa ranta duk babu dadi........ Wani irin murmushi ta saki tabi bayanta da harara tana tab'e baki! Ta kalli Ayshar da ta kwanta kasan kafet tana gurshen kuka Cikin zuciyarta tace"Shegiya kadan kika gani naso an yake miki hukuncin da yafi haka na tsane ki Aysha na tsani duk wani d'a dake cikin gidanan sannu a hankali duk sai na lalata muku rayuwa...... Duk a zuciyarta take wannan maganar a zahiri kuwa sakkowa kasa tayi tana kuka ta rungume ta tana fad'in "Ki daina kuka kinji ko nasan Wannan sharrin ba daga gurun kowa ya fito ba sai daga gurin Fulani kina dai gani 'yar dakinta CE ta bada shaida a kanki tana so ki lalace kamar yanda 'yayanta suka lalace saboda haka ki kula da ita ki San irin zaman da zakiyi da ita. Bata kaunar ki ko kadan.".


Aysha na kuka take fadin"Mommah! Nima nasan daga gurinta sharrin ya futo dama tuntuni nasan bata kaunta ko meye ya faru na San da saka hannunta shiyasa na tsane ta gabaki daya bana kaunar ta cikin raina." Kulu tace"Aysha ni zan fada miki sharrin Fulani Mari kiri-kiri ta hanani haihuwa tabi boka tabi malam an daure min mahaifa ko batan wata bantaba yi ba, an d'aura mana aure rana daya ankawo mu rana daya amma saboda tsabar iya asiri ranar da aka kawo ta ta samu ciki shiyasa na dauki alk'awarin salwantar da abunda yake Cikin kuma Allah ya bani iko na 'batar dashi a doron duniya. " !! Mammah ban fahimci maganar ki ba me kika batar."!? Jin tambayar da Ayshar ke mata yasa ta dawo nutsuwarta ta gane tana so ta tona abunda ya faru sama da shekara talatin a masarautar....... Baiyo ce ta shigo da sallama ta durkusa gurin tana gaishe su, Tace"Ranki ya dade Fulani Mari ta aiko ni na kira mata gimbiya Aysha tana son magan....."Kije kice nace inji ni banzan zo ba." Baiyo tace*Allah ya huci zuciyar ki gimbiya Kulu tace"Maza kije ki fadi sa'kon ki." Baiyo ta mike da sauri ta futa.


 Kulu tace"Ko uban me zatayi miki da zata aiko kiran ki munafukar mata mai siffar mutanan kirki a zuciyarta kuwa sharrin ta yafi na shaidan." Tace"Mommah! Ki k'yaleni da ita sai na kirta mata rashin mutumci duk sanda ta sake ta shiga gona ta." Kulu tace"Kinyi min dai-dai irinsu dama haka ake musu."


Omar ne yayi sallama ya shigo Kulu ta watsa masa mugun kallo cikin tsawa tace"Me kuma ya dawo da kai munafiki an hada baki da kai za'a tozarta yarinya."!! Yace." Umarni daga Mai Martaba Aysha ta fito ina jiranta waje domin kaita dakin hatsi." Kulu tace"Au! Kaine ma zaka kaita dakin saboda ka samu d'aurin gindi kayi laifi a dorawa baiwar Allah sannan a had'u da kai gurin hukuncin ta." Omar yana kokarin futa yace." Wannan umarnin mai Martaba ne bana wa." Futa yayi yana tsaki ya tsani matar nan wallahi.


Aysha kam ta rasa ma abunda zatace saboda tsabar bakin ciki da takaici kulu tace"Tashi kije Aysha zan biyo ki da duk abun bukata kar ki damu kullum zan shigo ina debe miki kewaya." 


Hawaye ta share tace"Mommah dare fa ni tsoron dakin nake ji wallahi har da kadangaru da kwadina kunami babu abunda babu." Kulu tayi dariya cikin ranta tace"Shegiya da zanga kunamar ma zan sa miki ita cikin Riga ki ne ai haka nake so ki shiga cikin kunci." A zahiri kam cewa tayi"Ki kwantar da hankali nasan sarki ba zai sanya ki a dakin ba sai an duba lafiyar sa babu abunda zai same ki insha Allah. " Aysha ta mike jikinta duk a sanyaye tace"Mommah ina jiran ki don Allah. "! Kulu tace " Kar ki damu yanzu zan shigo inga lafiyar dakin. "



Yana tsaye waje yana dakon fitowarta ta futo sau daya kawai suka hada ido da juna ko wanne ya dauke kansa Omar yayi gaba ba tare da yace mata komai ba, bayansa tabi tana sak'e-sak'e cikin ranta yanzu take da ta sanin shiga hurumin sa da tasan al'amarin zai juye kanta da batayi ba yanzu kowa yana mata kallon yar iska, wasu zafafan hawaye suka shiga zubo mata..... Daf da zasu shiga kofar ne ta kara sauri har ta taddashi ya sanya mukkuli ya bude dakin da hannu ya nuna mata yana fadin"Bisimilah." Wai ta shiga, taji irin takaici! Had'e fuska tayi sosai tace"Naga kamar kai ma kana yi wani irin kallo kar kayi tunanin da wata manufa na ta'ba jikinka baka kai wannan matsayin ba baka da abunda zaka burge ni dashi abunda ya faru tsakanina da Kai tsautsayi ne da kuma bacin rai! Amma ni ban taba jikin ka da wata manufa ni ba yar iska bace." Murya na rawa take maganar... Shi tausayi ma ta bashi yace." Naji bani da abunda Zan burge ki dama bana so na burge kowa nafi so nayi ta burge kaina ni bawa ne makaskanci dame zan burge ki."!! Tsaki taja ta fara kokarin shiga dakin. Gurin shiga ta buge kanta da sauri ta dawo baya ta manta kofar shiga gajeriya ce sosai sai ta sunkuya sosai...... Yace." Sannu baki ji ciwo ko."!! Ina ruwan ka."! Ta fada tana watsa masa mugun kallo. Hannu ya daga sama yace." Babu ruwana ni dai Shiga in kulle da akwai abunda zanyi. Tace"Wallahi baka isa ka kulle ni cikin dakin nan ba so kuke Ku kasheni ko."?








8/3/2020



BINTA UMAR ABBALE

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.