Free chapter 路 Read without an account

14

by Binta Umar Abbale 路 Sadauki Omar

SADAUKI!!馃徆

_OMAR馃挮馃憫_





_*Ga masu bukatar karanta littafin zasu tura #300 ta wannan accont din.....0542382124 Binta Umar GT bank.... Idan kuma katin waya zaka tura sai ka tuntu'be ni ta wannan numbars .....***.....*** Insha Allah zan fada maka yanda zaka biya kudin... Mutanan Nijar Idan kuna bukata zaku tura dala Dari ta wannan numbars....90899076 _88137740 Katin Airtal ko Orange Dala Dari itace a madadin Dari uku kudin Najeria.*_




Free pege


14



'Kara shigewa jikinsa take yana kara janyewa domin gudun abunda ka iya kaiwa ya kawo duk sanda zata kusanta jikinta da nashi ya Kanji duk wani karsashi gami da jarumtar sa na Neman guduwa kasala da sha'awa subi su dabaibaiye shi, jikinsa a Dan sanyaye yake kokarin jawo ta amma taki sakin shi rike shi taki sakeyi tana goga masa k'irjinta dake mutukar kashe masa jiki.


Ya jawo ta da karfin gaske ta tsaya gabansa tana zazzare ido hade da waiwayaewa bayan ta....... Hanya fita ya kama, a guje tabi shi ta rirrike shi tana wani irin kuka gwanin tausayi k'irjinta sai bugawa yake. Tausayi ta bashi yasa yaja hannunta suka zauna kan wani buhu dake cike da abincin dabbobi ko da suka zauna din sai shiga jikinsa take tana rirrike hannunsa tana waige-waige kana ganinta kasan a furgice take...... A hankali nutsuwa ta soma zuwa jikinta ta saki hannunsa a hankali tana sauke ajiyar zuciya tace"Don girman Allah kar ka barni anan gurin ka taimaka min kaji."!! Cikin wata irin siga ta fadi maganar yaji wani irin bakon yanayi na shiga jikinsa idonsa ya tsura mata tayi saurin kauda kanta kunyar abunda tayi masa a baya take ji yau gashi tana Neman taimakon sa..... Cikin dakakkiyar murya yace." Kin san dai bazan saki aikina nazo nayi ta gadinki ba ko."!? Aysha tayi shuru tana jin fad'uwar gaba addu'a take Allah yasa kar ya botsare mata. Ya cigaba da cewa "Kiyi hakuri ki zauna nan in da na zaunar dake Insha Allah babu wani kwaro da zai zo kusa dake zan baki fitila ta kiga haske, Idan bacci ya kamaki ki kwanta kan buhun ina tsaye a waje har wayewar gari Idan jin ji motsin wani Abu ki hasko min fitila zan zo."



"Uhumm! Ni dai ba inda zakaje kawai ka zauna tunda dama ai bani kadai nayi laifin ba." Yanda take magana k'asa-k'asa Cikin shagwaba yaja hankalin sa sosai ya tsirawa bakinta ido yana kallo


Aysha tayi saurin dauke kanta tana marairaice fuska kanta ta d'ora kafadarsa tana lumshe idonta. Omar ya rasa yanda zaiyi yarinyar na so ta saka shi tsaka mai wuya zaman sa tare da ita daki daya zai janyo masa matsala babba a kankin kansa yana fargabar kusancinsu domin dumin jikinta na rikita shi mutuka gefe guda kuma yana fargabar wani ya gansu a tare ga aikin tsaron gida da yasa kansa...... Wata jarumta ce ta zo masa lokaci guda ya ingije ta saura kadan ta fadi, ta bude idonta da yake da alamun bacci Tana kallonsa tana marairaice wa ganin ya mike tsaye ne yasa ta mike da sauri zata rik'o hannunsa ya daka mata wata razananniyar tsawa! Hannu ya daga mata cikin fushi yace." Kika kuskura kika kara sanya hannun ki a jikina sai nayi mugun bata miki rai."!! Aysha ta tsira masa ido ya cigaba da cewa"Ke ko kunyar da'kumar mutane baka ji kina so ki jefani wani hali ki jefa kanki idan zaki dangana ki dangana ki kwanta kan buhunan na fada miki babu abunda zai same ki kin tsaya taurin ka. Kina so in zauna tare dake wani sharrin ya sake biyo wa baya kome." ? Aysha taji zuciyarta nayi mata zafi ganin sai wani buga mata tsawa yake yana hantarar ta tana ganin kome tayi masa tunda ta bashi hakuri sai ya hakura ba sai ya fada mata magana ba."

 Hanyar futa ya nufa tace"Kaje din Idan ka tafi sai me? Aikin banza kawai an hada ka da Allah da Annabi kamar ba musulmi ba komai zai faru dani na hak'ura idan ma mutuwa nayi sai Ku zuba ruwa a 'kasa kusha."! Juyo wa yayi Dan kalleta ya juya yana girgiza kansa mamakin rashin kunyar yarinyar yake tabbas Aysha baza ta taba sanjawa ba ya rasa me yasa ta raina shi kofar ya bude ya futa ya mai da ita ya rufe. Aysha ta fashe da kuka cike da tausayin kanta ta kwanta kan buhun harawa 'kayoyi sai soke ta suke ga wani irin saura dake bin jikinta yana wani irin kuka Mara dadin ji.



Omar kuwa futa yayi ya cigaba da shawagi a harabar gidan kamar yanda ya saba raba dare yanayi wajejen k'arfe uku ya koma dakin yana bude kofar ya ganta kwance kasan kofar tana bacci.... Cike da tausayi yayi nufin daukar ta sai kuma ya fasa ya juya ya rufe kofar amma bai sanya mukuli ba tsaye yayi bakin kofar yana sak'e-sak'e minti goma ya sake komawa dakin yanzu ta tashi zaune sai buge-buge take tana kashe sauro Fitilar ya dauka yana haskata.... Ta mike tana jin wani irin jiri na dibarta yunwa da fargaba yasa ta tafi luuuuu! Zata fadi da sauri ya taro ta ta fado jikinsa...... Kokarin kwace jikinta take don har yanzu da sauran haushin sa a tare da ita ya rike hannunta yana Dan murzawa kadan baya so yayi magana saboda dare yaja hannunta suka zauna kan buhun ta dinga dauke kai tana kokarin kwace hannunta tace"Sakar min hannuna yanzu kuma meye ya dawo da kai wallahi ban taba tsammanin baka da imani ba sai yau na tsane ka."!! Ba tare da ya saki hannun ba yace." Yanzu ma ba wani Abu bane na shigo dubaki ne kuma in fada miki wata magana kafin in futa." A hankali yake magana saboda yanayi na dare


Shiru tayi tana sauraron sa yace." Ina so ki kula da duk wani nau'in kayan ci ruwa ko abinci ko kayan marmari da Mai dakin kusurwa zata baki ko ta aiko a baki komenen Kar kici matar bata kaunar ki kullum kokarin ta taga bayan........."Dakata Omar."!! Ta katse shi cikin bacin rai! Shi kam kasake yayi yana sauraron ta tunda yake da ita bata taba kiransa da anihin sunan sa ba sai yau *Omar!* kamar a bakinta aka rada sunanan.



"Mommah! Na kake kokarin yiwa 'kazafi da sharri Kamar ni ka kalli 'k'wayar idona kace wai Mommah! Bata kauna ta zata kasheni."!! Kai ta dafe tana fadin" Innalillahi! Alamun maganar da yayi mata ta bata mamaki! Fuska a murtuke take kallonsa cike da bada umarni tace"Karka kara zuwa gurina da magana makamanciyar wannan!Mommah! Na bazata cuce ni ba har abada matar da ko kuda bata so ya sauka a kaina shine zaka zo kace zata kashe ni Mtssssw..........!


 Bakin ya buge da bayan hannunsa yana kallonta da yanayi na bacin rai yace." Ba tun yau ba kike min wannan halayyar taki ta tsaki wai me kika mayar dani ne? Sa'an ki ne ni."!!? Ya fada ransa a bace!


Hannu tasa ta dafe bakinta tana kallonsa cike da mamaki! Yau bawa makaskanci ne yake kai hannunsa jikinta da nufin duka lallai in da ranka kasha kallo."


Yace." Idan muna magana dake karki sake nuna ni da hannu duk sanda kika sake sai na karya shi I Dan bai karye ba sai na targad'a shi."!!!Aysha tayi fiki-fiki da ido tana kallonsa tsoron sa take ji Yanzu Dan ja da baya tayi..... Ya cigaba da cewa"Na fada din Kulu bata sonki bata kaunar ki sai me?." Aysha tayi shuru tana sauraron sa, rai a daure yace." Shashasha kawai ana nuna miki gabas kina kallon kudu to ki kiyaye wallahi Wannan matar fuska biyu gareta gaban idonta kike mutum bayan idonki sai Allah tsakanina dake gaskiya ce ba wani abun ba da har kike kokarin tsokane min ido saboda an fada miki gaskiya idan kinji maganar Dana fada miki ki ceci kanki idan kuma bakiji ba kije kiyi tayi...... "Idan na kijin maganar ka me zai biyo baya."!? Tafad'a tana mik'ewa daga Kusa dashi (saboda tsaro) ta cigaba da cewa" Na farko dai baka haife ni ba da har zaka fada min magana naji sannan cikin ku babu Wanda ya shiga halin damuwar da Mommah ta shiga lokacin da sarki ya yanke min wannan hukuncin, hatta da mahaifiya ta bata nuna damuwar ta kan lamarin ba kai ma baka damu ba Duk da Kaine silar faruwan komai Kaine me kulleni a daki ina hadaka da Allah da Annabi kana ji baka saurare ni ba shine Yanzu zakace naji maganar ka? To bari kaji yau ko Guba Mommah ta bani hannu da hannu tace inci zanci saboda na yarda da kaunar da take min, Kufa!"? Daga kai har wad'an da suka kawo ni duniya ba su nuna damuwar su akai na ba saboda haka bani da ma'kiya sama daku."!!!! Tsaf! Yake kallonta yana mamakin kuruciyar ta a fili girgiza kansa yayi ya kama hanya zai futa, tsaki taja sai tayi saurin rufe bakinta da hannunta tana addu'ar Allah yasa baiji tana tsoron mari don na dazu ya shige ta sosai karfin hali kurrum take.


Bude kofar ya futa ya mayar da mukkulin ya kulle yana joyowa sukayi arangama da Yarima Faisal ya shigo cikin gidan cikin mota Omar ya bashi hanya domun sa samu damar shigewa da motar Yarima Faisal ya bude motar ya futo yana tangadi kana ganinsa kasan a buge yake." Da hannu yake nuna Omar din yana sambatu "Kyai! Kai! Ina fada maka ka kiyayi had'uwata da kai wallahi sai na koya maka hankali!!! Shin me kayeyi dakin ka futo kana zare ido shin ka shiga ka cigaba da 'kwakule ta ne ko me!? Kai!! Wallahi sai na kashe ka in dai akan Aysha ne! Matata ce faaaa."!!! Omar ya dinga kallonsa yana mamakin tangadin yake Sam yaki ya tsaya guri guda sai zagaye gurin yake yana nunnuna Shi.....Hanya ya kama zai bar gurin yana masifar jin takaicin yanda Suka Mai da kansu shida Dan uwansa Abbas yana jin tausayin mai Martaba matuka saboda rashin nagartattun 'Yaya macecen ce kawai mai hankali Karima tayi aure harda yaranta uku...... Faisal yayi yunkurin rik'o rigarsa bakinsa a jirkice yake fadin"Kai! Wato ka raina ni ko ina magana kana tafiya."! Omar ya janye rigar sa take Ya fadi a gurin Amma duk da haka bai daina yunk'urin kamo Omar din ba. Sambatu kawai yake zangawa har bacci ya dauke shi a gurin.









9/3/2020



BINTA UMAR ABBALE

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.