Free chapter · Read without an account
page 3
by Aysharhshariff · ABDUL MANI
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇 *ABDUL MANI*🍇
🍇 *TYCOON*
story & written
By
@ashoush_💞
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
```MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUNM WANI ABU SAI ROYAL STAR'S WRITER'S✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) / 💪💪💪
UP-UP-UP BEST WRITER'S EVER💖 ```
*ALƘALAMINMU ƳANCIN*
*PAID BOOK*
Wannan littafin na kud'ine ba kyauta ba ,idan ta account ne zaku biya #300 idan katin waya ne #200 zaku biya kudin ku ta wannan account din 3182414331 Sharif Aisha Ismail ,zaku turo shaidar biyanku ta wannan lambar *** ko ka kati a layin ,banda VTU
PAID BOOK
🍇 _Abdoul maneou_🍇
FREE PAGE 5to6
_____________Fitowa mukayi daga cikin ɗakin Iya muka sameta a waje
"zamu je mu dawo" adawo lafiya ta mana muka wuce lokacin da nazo fita daga gidan sai da na fara leƙawa waje saboda kar Fatime bala'i ta maƙale a ƙofa muna fita da riƙe mu ba shiri, da na leƙa na tabbata ba kowa, sannan na fito ina cewa Ma'u ke fito ba kowa fa,
muka kama hanyar gidansu Feenarh a hanya sai tsalle_tsallenmu mukeyi har muka isa k'ofar gidansu,
bulo na ɗauka na wurga cikin gidan nasu ,na kuma daukan wani na daki ƙofar gidan dashi,.
saiga Feenarh tafito da sauri"ke wai meyake damunki??" duk sanda kika zo da jifa ne zan gane kin iso?" tafaɗa tana tambayata
kallon tara saura kwata nayi mata sannan nace " so kike na shigo wannan mugun yayan naki ya dake ni ko?"nima na bata amsa ina tambayarta
"gaskiya yayanki akwai mugun hali gareshi" ina bata fuska nafaɗa dan har zuciyata yayanta mugune ,kallo na tayi bataji daɗin abunda nace ba, na kalleta nima nace nafaɗa,nikam
kuzo mutafi majalisar cin amana muyi shawara achan cewar Ma'u
tafiya mukayi Chan wani waje da ake cewa majalisar cin amana muka shige wata 'yar bukka mu ka zazzauna a ƙasa Feenarh ta kalleni tohm yanzu mai za'ayi ,
gira d'aya na daga nache" oho"
Ma'u tayi saurin kallona "gaskiya ke dai ƴar iskace ya ma za'ayi wai kice mana oho"
Feenarh ta ƙarbi zancen da cewa "nikam ina ga kawai zanje nabawa Fatime bala'i haƙuri kawai in yaso ta daken a wuce gun inb......"kan bala'i idan kin isa shegiya nake ,kuce bani bace jikar A'i "
na katse wa Feenarh maganarta ina ta hura hanci ni a dole ta ɓata min rai
"dallah kutashi mutafi anfasa sulhun ,dan halak kafasa" na fita a fusace amma sai nayi turuss saboda ganin Fatime a gabana tana kallona bata rai nayi zan wuce ta jawo rigata kiiiii tadawo dani baya ta na cewa "ke dawo nan "
"ba ruwanki dani ban shiga harkarki ba"nafaɗa mata haka,
wata dariyar rainin hankali ta shek'e da ita "wallahi yau kwananki yak'are domin kuwa sai na ci ubanki la'ada waje" tafada tana kara finciko rigata,
karar gudu naji daga bayana ina juya naga su Ma'u ne suka arce suka barni,,
"lallai yau ku taro wa kanku masifa" nafada araina ina k'wafa
sauƙar bulala naji ajiki na ina d'ago wa naga Fatime tana niyyar kaimin wani gashi yara sun fara taruwa ,kamar ni uwar daba za'a kama a daka a hanya ,
fincikewa nayi zan tafi tak'ara jan rigata
berettt rigata ta ɓarke
"kutt idan kin isa Allah ya tsinemin"
na fada raina a bace nayi kanta da duka ta ko ina nake dukanta, dan zuciyata ta ɓaci duk wani fitsarata bana son ataba mutunci na ,
kwarfo ƙafarta nayi saboda naga yadda yaya ado yakeyi mana nida safiya,
wanwar tafaɗi akasa sai da na mata dukan da ko tashi bazata iya ba sannan nayi tafiyata,
ina ayyana irin bala'in dasu Ma'u suka saka kansu a ciki
gida nakoma abuna na samu Baffa a ƙofar gida na gaida shi sannan nayi cikin gida
a tsakar gida na samu Fadwa tana ta wasa daukanta nayi ina mata wasa mukayi cikin ɗaki..
🍇🍇
ABUJA
MAITAMA ESTATE
cikin bacci Maan yake jin wani abu mai laushi yana tab'a masa jiki
yasan ba kowa bace Angelina ce ƙara gyara kwanciyar sa yayi ya juya mata baya ,ita ma da taga haka sai ta hau kansa tafara tattakashi rabuwa yayi da ita ,farcenta,
ta ni tsama sa acikin duvet ɗin nasa
"auuchhh " yafaɗa ya na mik'ewa zaune jawo ta yayi jikinsa yana shafa gashin jikinta
"what do you need"? ( mekike buƙata) yafaɗa yana cigaba da shafata, daga ƙarshe ya sauƙo daga kan gadon ya had'a mata madara yabata "oyya maza kizo Kisha madara"
ya wuce bathroom brush yayi sannan yafaɗa bathtub yayi wankansa tsaff sannan yafito as usual kamar yadda yasa ba shirin sa
baƙar armless yasaka agaban rigan ansaka dolce gabbana da short nica,
sai da yabata lokaci sosai wajen gyaran sumarsa sannan yasaka bandana akansa yaɗauko angelina suka fito.
a parlo ya sami yan gidan gaba-ɗaya kowa ya hallara amma har yanzu bai ga Fannarh ba,
zuwa yayi ya rungume Daddy yana cewa "good morning Dad"
"morning son" Daddy yafad'a yana shafa kansa,bata fuska yayi a shagwabe yace Daddy kaina yana nuna masa gyaran gashinsa,
kallon sa Daddy yayi sannan ya girgiza kai
"Allah ya shirye ka" dubi abunda kake kamar wani Fannarh, bangaren Ammurh yakoma ita ma yagaida sannan ya mik'a wa Umair hannu suka gaisa.
cikin nutsuwa Ammurh ta zuba wa Daddy abinci a plate sannan ta sawa kowa, ta koma ta zauna suka fara ci tare da bismillah babu wanda yayi magana,
Daddy ne yafara kammalawa yakoma main parlon ya zauna ,
sai Maan ya tashi Ammurh ta kalleshi badai harka k'oshi ba cikinsa yashafa yana lumshe mata ido,murmushi tayi tana ɗauke kai, sannan ya koma inda Daddy yake,
kallonsa Daddy ya nacewa bari nayi maka ta mutanen mamanka "akbirni" (bani labari)
Daddy yafad'a
" to alhamdulillah komai yana tafiya yadda yakamata "
shima companyn abubuwa suna tafiya normal saboda jiya ma nayi magana da manager ɗin ,yace bawata matsala
"amma abinciken da akayi on 23rd July akwai wani ƙauye a Jigawa da za'abuɗe Companyn ƙarafuna a wajen "
"bayan haka ma akwai wani ƙofar gida a cikin ƙauyen da akace suna tonon ruwa ansamu petrolleim a ƙofar gidan ". Daddy wannan aikin ka ne yakamata kaje ka gano yadda abubuwan suke tafiya"
"amma ni yanzu akwai wani zane da nayi yau nakeson zuwa naga wajen sai afara aikin buɗe wajen shima" Maan yafaɗa yana mik'ewa tsaye,
" son idan ka fita kaje ka gaida Abbanku shima jiya da daddare yadawo Daddy yafad'a yana hau rawa sama,
"okay Dad"
kiss ya manna wa Ammurh a chick dinta sannan yafita yana tafiyarsa ta jaruman maza
koda yafita side ɗin su Abban Sarina ya nufa kai tsaye yashiga parlon tare da sallama, a dining area ya samesu suna breakfast suma,ga Sarina zaune a kusa da Mami ko kayan baccinta bata cire ba,tana ganin Maan ya shigo tafara mik'a tana gantsare ƙirji ɗauke kai yayi daga kanta ƙasa_ƙasa yace "ƴar iska" sannan yaja tsaki
fasawa zuwa dining area din yayi ya zauna a parlo Abba da ya hango shi yace "a'a Babana bismillah taho mana" shafa sumar kanshi yayi "a'a Abba ina jira ka gama ne ai"
"Babana zo mana" Abba yafad'a yana yafito shi da hannu,
tashi yayi yaƙarasa kusan Abba yana miƙa masa hannu suka gaisa
"ya aiki Baba"?
"alhamdulillah Abba ,andawo lafiya??"
"lafiya kalau alhamdulillah Baban Babansa" Abba yafad'a yana murmushi"
"bismillah Abba yafad'a
"a'a Abba yanzu nagama breakfast "yafaɗa yana duba wrist watched ɗin hannunsa , Abba zan fita shine na leƙo mugaisa"
kallon Mami da take ta had'e rai yayi ,tab'e bakinsa yayi sannan yace" Mami barka da safiya" yana ɗauke kallonsa akanta,
"lafiya ,ashe kadawo kuma"? bai amsataba yace "Abba sai anjima yafita ko kallon Sarina baiyi ba ,dan ya lura yarinyar kanta yana rawa,
da sassarfa yafito a parlon yana ɗan sauri wanda idan ka kalleshi zakayi zaton tsabar girman kai ko ƙud'i yake sashi haka '
wajen motarsa yanufa (land cruiser) ƙirar Toyota ash babbar mota ce kamar jeep , guard dinsa gaba ɗaya suka dashi suka shiga mota suka bishi, abaya convoy sukayi as usual duk inda suka bi ana binsu da kallo dan manyan motoci ne duk wanda kagani yahauta to ƙusa ne, na Nigeria
a dai dai central bank of Nigeria yayi packing, wayarsa ya ɗauko ya danna kira chan ƙasan mak'oshinsa yace na iso sannan ya ƙatse ƙiran within 3 minutes sai ga wani saurayi ƙyakykyawakamar Maan din yafito da suites a jikinsa , yana ganin motar yagane dan yasan Maan yana son irin wa,ƴannan motocin, zagaya wa yayi front seat ya zauna yana miƙa masa hannu "Maan nee!!! Maaan nee !! "
yafad'a yana dariya musabaha sukayi,
"mutum na mutane kashigo kenan "? idon Maan akan titi yace "eh" achan ƙasan mak'oshinsa,dan shima Fahad akwai magana kamar Mus'ab
wuse 2 ya nufa achan yakeson buɗe sabon companyn motarsa,
"ina Mus'ab ɗin?" Maan ya cillowa Fahad tambaya
"nayi magana dashi d'azu yace mu samesa a wajen" girgiza kai kawai yayi,lokacin da suka iso direct cikin filin wajen suka shiga ,ga ma'aikata sai kai da kawowa suke ana ta aiki,daga wani ɓangare wani dogon saurayi kamar Maan din shima yafito hannunsa cikin aljihunsa gurinsu yaƙaraso ya miƙa musu hannu suka gaggaisa,kamar minti huɗu baya ,yakashe wayan yana kallon Maan
"mutum na mutane shi ma yafada yana k'ara miƙa masa hannu,hararasa Maan din yayi sannan ya ɗauke kai
"malam ni dai kawai muje kanuna mana yafaɗa a gajarce dan yasan Mus'ab da surutu tsiya,tafiya suka fara yi ana nunawa Maan yanayin yadda aikin yake tafiya shikuma hannunsa zube cikin aljihun wandonsa yana kallon komai da komai bayan angama nuna masa suka fito domin su koma gida ,Musabaha suka kuma yi da Mus'ab yana kara maimaita masa inshaallahu yau zai shigo yagaida Ammurh,
mota suka shiga shida Fahad suka wuce guess house din Maan din,
Maan yad'auko sketch board dinsa ya cigaba da zane_zanensa, chan sukayi sallar zuhr daga bisani suka fito Maan yaraka Fahad har gida amma bai shiga ba
"ina gaida Mamma" cewar Maan to "zataji Fahad ya amsa sannan yashiga tangamemen gidansu..
🍇🍇MAAN🍇🍇
sunan Maan yasamo asaline daga abokansa Fahad da kuma Mus'ab sai wata Gundo friend dinsu ce tun suna primary lokacin da ake musu bayani akan human body kuma ga Abdul_Mani Ulfat basu iya faɗan sunan Mani ba, sai suke ce masa Maan har sunan ya bishi,
har bayan su gama makaranta tare suke har lokacin da suka je Oxford University a England sannan ne kowa ya kama course dinsa inda Maan yake karantan BIT,shikuma Fahad BSc Computer ya karanta,shikuma Mus'ab artichect duk sun riga Maan gamawa sai suka dawo gida ,koda Maan yaga ma karatu sai ya koma ɓangaren artists&architecture yayi masters ,Bai tsaya ba har sai da yasamu transfer daganan zuwa NETHERLAND achan yaƙara karantar business sosai, yayi PhD akai sai suka riƙe shi achan tare da bashi chief manager a wani companyn royal dutch shell a matsayin professional designer a Rotterdam, har yaƙara samun matsayi avue entertainment alterations and redevelopment a matsayin architect yana da certificate daban_daban a ɓangaren shiysa yayi zamansa a amsterdam yatara dukiya da baisan adadin ta ba..
🍇🍇
KAUYEN JAAKA
maƙogoro na har ƙaiƙayi yakeyi saboda tsabar masifa datake cin cikina ina ta mita" wallahi idan naka ma su Ma'u mai kwatarsu sai Allah a hannu na" Inna tace ta kalle ni mai yafaru"? tana riƙe hannu na "ke daga ina kike haka rigarki duk a barke?"
"Ban mata ƙarya ba nace "faɗa mukayi da Fatime shine ta tsaga min"
Innarmu tana da sanyin hali kama hannuna tayi ta zaunar dani kusa da ita..........
oumu khalil✍🏻