Free chapter · Read without an account

Chapter 13-14

by Firdausi Rabi'u Abubakar · GIDAN BALARABE

*🪴GIDAN BALARABE🪴* 

         BY

 *🪴MAMAN NABEELA🪴* 


  *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION* 





💃🔥💃🔥💃🔥💃🔥💃🔥💃🔥💃💃 **SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!"*



*INA MASOYAN, KUMA MAKARANTAR LITTAFAN FATIMA MRS AHFAT? KAMAR SU*


K'ANINA NE


MIJIN YARINYA


ITA CE RAYUWATA


MAIRO'YAR KAUYE


NADAMAR ZUCI


DOCTOR KABIR

💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃TOH *ALBISHIRINKU, DOMIN NAZO MUKU DA SABON SALON LITTAFIN NA ME TAKEN SANADIN KUNCI NA, LOVE AND ROMANCE, LITTAFI NE DAKE DAUKE DA DARUSAN RAYUWA SOSAI ACIKINSA, TARE DA NISHADAN TARWA DA FADAKARWA ILMANTARWA"*


NI MRS AHFAT ASHIRYE NAKE TSAB DON BAKU DADDADAN LABARI MAI CITTA GAREKU💃💃💃💃💃💃💃💃


PAID BOOK NE AKAN FARASHI MAI SAUKI......


NORMAL GROUP 300 ONLY


VIP GROUP 500 ONLY


SPECIAL GROUP 800 ONLY


*ME KUKE JIRA MAZA KUYI SAURIN BIYAN KUDUN KU TA WANAN ASUSUN, 0431560118 FADIMATU BABANGIDA GT BANK*...


EVIDENCE OF PAYMENT ***


KARKU BARI A BAKU LABARI, WANAN SALON SA NA DABAN NE MASOYA


*MRS AHFAT* ✍️




 *DEDICATED TO GIDAN BALARABE FAN'S* *SAN SO MARA ALGUS* 🥰🥰🥰🥰🥰


🅿️1️⃣3️⃣↔️1️⃣4️⃣



Kamar ɗan jarida yabi ya dame ta da tambaya "kiyi haƙuri fa in na taƙura miki da tambayoyi'Wata ƙyela su amfane mu gaba ɗaya!"ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba "su amfane mu gaba ɗaya " ta mai maita maganar a ranta tana me nazarin toh'amfanin me zasuyi Wani sashi na zuciyarta yace "ko dai sonki yake!"da sauri ta ture tunanin tana cewa Wane ni ai kowace ƙwarya da abokin burminta ina ƴar talaka ya za'ayi ma Wannan kyakyawan BALARABEN me kuɗin yace yana sona, ko dan wasu ana cewa basa kin talaka'maganarsa ta dawo da ita daga tunanin da take,



"Wane layi zamu shiga!"ta tsinci muryarsa me daɗin sauraro yana tambayarta,"layin M.D KWANGILA gida na biyu"Khadija ta bashi amsa, murmushi yayi yana karya kwanar layin dan ya gane gidan da take faɗa




gidan Alhaji Mujahid kwangila ne wanda suke bawa duk Wani aikin gine-gine idan zasuyi,yanzu haka ma shi suka bawa kwangilar gina Wani company a Sharaɗa Wanda suke da Babban company a Lagos.


 

Perker Motar yayi a ƙofar gidan,Mame dake baya buɗewa tayi tana fita mane da waya a kune'tana rufewa Meme dake baya tuni tayi barci,Nimrah ma dake hanun Khadija barci tayi itama 


Khadija ƙoƙarin bude Motar tayi sai taji ta a rufe juyowa tayi nan idanonsu suka haɗo dan Shima kallonta yake kallon da batasan da Wanne suna zata kirashi ba ƙasa tayi da kanta dan baza ta iya jurar kallon idanonshi ba.




Mame jin bata fito ba yasa tayi cikin gida dan dama ta kula da kamar Bistynta tayi Babban kamu lol.



Jin beyi magana ba yasa cikin tura baki da maganar ta me kamar Shagwaɓa tace"ka buɗe min in tafi"ta faɗa tana daɗa tura baki gaba



Balarabe da Salon yadda tayi masa maganar yake neman jifa shi Wani yanayi'Saurin ɗauke idanonshi yayi daga kanta yana me ƙoƙarin sai ta muryarsa kar ta bayyana halin da yake ciki yace"ai kece baki sallameni ba" surin ɗaguwa Khadija tayi tana me mamakin kalaminsa "Sallamar me!" ta faɗa a ranta 


Cikin daɗa Shagwaɓe fuska kamar zatayi kuka dan ya takura mata da yawa dan ya samu ma ta ɗan kulashi, tace"toh' ni Sallamar me zanyi ma!"



Ba tare da yayi magana ba tamfatsitsiyar Wayarsa ya miƙa mata dan shima yawan magana ba ɗabi'arsa bace amma ya ya'iya zuciyar sa ke masa tilas har bakinsa ke furtawa,


Ɗagu kanta tayi ganin ya miƙo mata Waya,alamun tana neman ƙarin bayani'ɗayan hanunsa yasa a cikin sumar kansa ya yamutsata yana cewa"Number ki!"


Batare da ta karɓa ba tace"bani da Waya"ɗaya daga cikin Wayoyinsa ya ɗauko ya miƙa mata yana cewa"ga Wannan ki riƙe in ba damuwa"girgiza kai tayi tana cewa"a'a Ummy faɗa zata yimin,ka buɗe min na tafi........maganar ce ta maƙale ganin I'man ta fito tana nufu gurin da Motar take 



Ɗaguwa yayi jin tayi shiru ba tare da ta ƙarasa maganar ta ba'inda take bi da kallo ya kalla ganin Wata Wadda suke matuƙar kama na tahuwa,kallonta ya ƙara yi yana cewa"ƙanwarki ce?"


"Uhm"Khadija ta faɗa ba tare da ta daina kallon I'man da ta ƙaraso gurin Motar ba jin ya cire lock ɗin Motar yasa tayi Saurin buɗewa tana fita ta kwantar da Nimrah a kan kujirar Motar,


I'man kallonta tayi tana me cewa"Anty Khadija kin kuwa duba lukaci harfa Ummy ta fara kira tana cewa mun..........Maganar ta kasa karasawa ganin Wani kyakyawan matashi ya buɗe Motar ya fito, a ranta tana yaba kyaun da Allah yayi mai,tana cewa"ah' dule ki maƙale ki kasa tahuwa yau Allah ya haɗa ki da wanda ya iya sace zuciyarki da alama" tana sakin Murmushi ƙasa-ƙasa





Zagayo wa inda suke tsayi yayi yana me sakarwa I'man murmushin sa me ƙara masa kyau,I'man gaishi shi tayi cikin sakin fuska yace"lafiya lau ƙanwar mu,kinga Shiru bata Shigo ba kika biyo sawu?"


I'man cewa tayi"eh"tana sunkwi da kai'dumin wallahi BALARABEN nan da ya tsaya kusa da Yayar tata gani tayi sunyi wani bala'in dacewa da juna,kai Allah yasa karta kureshi'ta faɗa a ranta. 




"ƙanwar mu ko zaki taimaka ki samin Number Yayarki!" Balarabe ya faɗa yana miƙawa I'man Wayar dan shi be yarda ba tada Waya ba gani yake shine kawai baza ta bawa ba sai ta jamai aji.



"Ba tada Waya amma kawo na saka maka lambar Ummyn mu" miƙa mata Wayar yayi ƙirar I'phone Wadda da gani bada kuɗi kaɗan a ka siyita ba,

number ta sa masa ta miƙa masa tana cewa"gashi"karɓa yayi yana cewa"ƙanwarmu na gude susai da fatan zaki taya ni campain gurin Yayarki"



Dariya I'man tayi tana cewa"Insha'Allah Sai dai bansan Sunan Yayan nawa ba!"



 Murmushi yayi yana me jindaɗin tambayar da tayi yace"ABDULL-SAMAD ABDALLAH Shine sunana ina fatan baza ki manta Sunan Yayan naki ba"ya faɗa yana murmushi,Haɗi da sauke ajiyar zuciya Saboda Surutun da yake tayi'dan har kansa ya fara yi masa kamar zeyi ciwo Saboda Shidai haka Allah yayi shi bashida yawan magana




 "Insha'Allah" I'man ta faɗa "Mun guɗe"Khadija tace tana jan Hanun I'man Murmushi yayi yana me Buɗe Mota ya Shiga'dan Shifa Yarinyar tana mugun burgeshi,Kuma ya fuskanci itama ba tada yawan magana Susai tsayawa yayi yana kallonsu har suka Shiga Gidan Sannan ya yiwa Motarsa key ya nufi layin da gidansa yake,danshi gidansa ba'a cikin Layin yake ba.


Khadija Suna Shiga cikin gidan Suka Shiga falo bakinsu ɗauke da Sallama,ganin Anty Kubra a falon yasa ta saurin sunkwi da kai tana cewa"Anty Barka da gida" ganin yadda take ta Sunne kai yasa Anty Kubra yin dariya tana cewa"Barkanki dai kun dawo lafiya'ina Sabon Ɗan nawa ko ya tafi!"Anty Kubra ta faɗa tana Murmushi, Khadija ƙasa ta ƙarayi da kanta tana Wasa da yatsun hanunta tace"Anty Bafa Saurayi na bane,kawai hanya ya rage mana"



Dariya Anty Kubra ta kuma yi tace"toh'naji nima ai ba cewa nayi Saurayinki bane'tambayarki nayi Sabon Ɗana ya tafi kinga ai shi Ɗa na kuwa ne!"


Murmushi Khadija tayi tace"eh'ya tafi" 

"toh'kuzo kuyi Shirin tafiya dan Yaya Hauwa tun ɗazu ta fara kiran Waya tana tambaya kun tahu'Adnan yace zai maida ko kuyi maza ko kimtsa"



"toh Anty ina Mame?" Khadija ta tambaya"tana Sama ɗakinta"Anty Kubrah ta bata amsa.


Tashi tayi ta nufi ɗakin Mame,I'man kuma ta Shiga kicin kiran Saudat dake gurin Hama me aikin Anty Kubra.


Khadija na shiga ɗakin Mame tana fituwa daga banɗaki nan ta hau tsukanar ta tana cewa"a'a kaga Masoya harkun gama Shan Soyayyar,Wadda tasa kuka manta dani a bayan Mota" Mame ta faɗa tana sakin dariya'harararta Khadija tayi tana cewa"uhm'har kince haka,ke da tunda muka hau Motar nan kike Waya kina Wani kashi Murya ina fa kule dake"dariya Mame tayi tana cewa"ah'kinga laifina nida Masoyin nawa ba haɗuwa muke dashi ba kinga ai ɗule a Waya musha Soyayyar mu"ta faɗa tana dariya "Allah ya shiryi ki,kinga ni banɗaki zan shiga na fito mu tafi gida'Khadija ta faɗa tana shiga banɗaki. 


Bayan sun Shirya suka yiwa Anty Kubra Sallama'Anty Kubra ta basu Wata ƙatuwar leda me ɗauke da irin kayan da take Order ta basu suka yi mata gudiya.

Mame ma turaren da aka basu a gidan su Huda ta ɗau guda ɗaya ta basu tace suyi amfani dashi,I'man ce ta karɓa sannan suka sauko ƙasa'Suna saukowa Adnan na shiguwa yake tambayarsu in sun shirya su fito Suka ce "toh'suna nufar ƙofar fita........


 

 *BALARABE* 


Ya na yin parking ɗin Motarshi,ya fito Yawale me gadi na yi mishi Barka da dawowa hannu ya ɗaga masa yana amsawa da tambayarsa "ya aiki!", "Alhamdulilah" ya ba sa amsa ya na cike da farin cikin yau Uban gidansa ya Shigo ya na ta Murmushi da alama ya gamu da abinda ya sa shi farin ciki, dan shi dai a iya zamansa a gidan ya fahimci Me gidansa be yi sa'ar Mata ba, ga dukiya iya dukiya ya na da ita Amma Allah ya jarrabeshi da Mata Wanda Wani Tallakan ma Wanda ke fama da matsin rayuwa ya fi shi samun kwanciyar hankali."Allah ya kawo maka mafita ya baka Macen ƙwarai", Yawale ya faɗa a ransa yana kumawa bakin aikinsa.



Zagayawa ya yi ya buɗe Motar ya tashi Meme da ke barci, ta sauko, Sannan ya ɗauki Nimrah da ita ma ta farka yanzo su ka nufi cikin gidan.


Falon ya tura bakinsa ɗauke da Sallama, Baba Larai da ke zaune a falon ce ta amsa ta na yi musu Barka da dawowa, zama yayi kan kujerar falon ya ɗora Nimrah kan cinyarsa.


Asiya ce ta fito daga kicin hanunta ɗauke da flaks ta a jiye a dinning ta ƙarsu cikin falon tana cewa, "Abban Aiyman Barka da dawowa, ya ka baro mutan gidan!"



"Barka lafiya lau suna gaishe ku" miƙa mata Nimrah ya yi yace"kar ki bar ta ta kuma barci Magriba ta kawo kai", toh' ta amsa ta na karɓar ta.



Tashi ya yi ya nufi Sama falonsa ya tura yana ambaton sunan Allah ƙamshi falon ke ta yi alamun yau ya samu gyara fess da shi ko ina sai ƙyalli yake Murmushi ya yi Wanda ya kasance iya laɓɓansa ya na nufar Wani coridor tura ɗakin ya yi Wanda shima ya samu gyara sosai yaji daɗin yadda yau ta gyara masa ɗakin dan shi baya son komai ace masu aiki ne za su yi yafi son Abinci, gyaran Ɗaki duk ya kasance Matarsa ita za ta yi ba tasa Wata ta yi ba. rage kayan jikinsa ya yi ya nufi banɗaki ya jima a ciki Sannan ya fito jikinsa sanyi da rigar Wanka hanunsa ɗauke da towel yana tsane ruwan kansa jin an fara kiran Sallah yasa shi cikin Sauri ya ɗauko Jallabiya white ya saka tare da hular tashi ka fiya nace, turare ya fesa a jikinsa jin an buɗe ƙofa ya sa shi kallon ƙofar ta cikin mirow Asiya ce ta shigo ta zauna gefen gado tana cewa"Abban Aiyman na ga ban ga Aiyman ba a chan ku ka bar shi !"





"eh" ya bata amsa idanunta ne ya kai kan Wani kati ɗauka tayi tana dubawa taga I.D card ne na Mace nan Wani kishi ya taso mata amma sanin dawa ta ke tare yasa ta dake tana cewa"kayar da I.D card" ta na mika masa karɓa yayi yana dubawa Murmushi ya yi tuna I.D card ɗin lokacin da zata faɗi daya taro ta ya faɗo daga jakarta ita kuma ba ta sani ba bayan ta hau sama ya gani ya ɗauka Aljihu ya turashi yana me sakin Murmushi ya na hargitsa Sumar kansa ya faɗa duniyar tunaninta , ya ma manta da Asiya dakee zaune tana ta Kallonshi. 




Wani tunani ne ya faɗo zuciyarsa cikin hanzari ya ce "Uhm haka za'a yi " yana nufar ƙofa' Asiya da ta saki baki da hanci tana kallonsa ta ce "Abban Aiyman me za'ayi?na ji kana cewa haka za'a yi"dan ita tunaninta kar dai ko hulɗa da Mata ya fara shiyasa ta dakatar da shi cike da tashin hankali tana tambayarsa .




"Ba komai sai alkairi ki taya ni da Addu'a" ya faɗa.ya na fita ya ji ana ƙoƙarin tada Sallah.



Jiki a sabule haka ta tashi ta nufi ɗakinta ta na tunani me Abban Aiyman ya ke Shiryawa dan ita hankalinta ya kasa kwanciya tunda taga I.D card ɗinan ɗakinta ta shiga tana shiga Nimrah ta Shigo tana cewa"Mom ki ce da Abbuhh ya kaini gidan Anty me ƙyau", zaro idanonta ta yi Waɗɗanda su ke ba manya ba tana cewa"na shiga uku ni Asiya wacece kuma Anty me kyau?" "Mom gidan Ammy su ka zo yau ita da ƙawarta Mom kin gan ta tana da irin abun Abbuhh na nan" ta faɗa tana nuna kumatunta tsuma jikin Asiya ya fara nan ta fara zarya takai ta kawo tana Adu'ar Allah dai yasa ba buduruwarsa ba ce ta samu 

 Waccan ta bar gari yanzu kuma Wata ta kunno kai cikin rayuwarsu.




*****************



Khadija bayan sun kuma gida su ka baje kayan da Anty Kubrah ta ba su nan Ummy ta yi ta yiwa ƴar'uwarta Addu'a tana yaba yadda ba ta gajiya da yi musu alkhairi, kayan su ka kai ɗaki Sannan suka zauna suna taɓa hira.



Ummy tace "khadija bakwanan anyi ta kiranki a waya fa, Nasir ya ɗaga ya ce bakya nan" "toh" Khadija ta ce tana faɗawa duniyar tunaninshi "ko kaicma kana tunanina" ta faɗa a ranta Murmushi ta saki tuno moment ɗinsu na ɗazu da za ta faɗi kamar Wani film murmushi ta daɗa sake, Ummy da ke lura da ita tace "lafiya dai kike ta Murmushi haka"






Iman dake gefe ta tuntsire da dariya tana kallon Khadija ta ce da Ummu "Wallahi Ummy yau tunda ta dawo daga raka Meme unguwar da ta ce zata raka ta take cikin nishaɗi, tunda mu ka taho zamu dawo ma sai Murmushi ta ke " ta kai maganar tana tashi ganin hararar da Khadija ke aika mata dan zatonta faɗawa Ummy Mutumin ɗazo za ta yi, ita dai ba ta ce komai ba sai cewa da tayi Ummy "Yaya Khalel yau ya kira!"



"eh ya bugo mun jima ɗazu mu na magana da shi ya ce nan da sati uku za su dawo", cikin farin ciki su ka fara murnar Yayansu zai dawo bayan kwashi shekaru ba su Sashi a idanonsu ba.



***************


....Ana idar da Sallah gida ya dawo, Asiya cikin ƙarfin hali ta zuba masa abinci ta na kallon yadda ya ke ta fara'a cikinta na daɗa ɗurar ruwa kar dai Saboda Wannan yarinyar ya ke cikin Wannan farincikin, ta faɗa a ranta ta na Sak'e-sak'e daban-daban. bayan ya ci abincin tashi ya yi yana cewa "zan ɗan fita bazan jima ba zan dawo"






"Toh Allah ya kiyayi hanya"ta faɗa tana ƙoƙarin maida ƙwallar da ke neman zubuwa domin ya tabbata zarginta ya zama gaskiya,"na shiga uku ni Asiya.....................







 *SHIN* *INA BALARABE ZAI JE❔* 




 *SHIN* *WANENE MA BALARABE❔* 



 *WACECE KHADIJA ❔* 




 *KU BIYO NI DOMIN JIN TUSHEN LABARIN...?* 



 


 *SHARE & COMENTS* 


  *MAMAN* *NABEELA CE....* ✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.