Free chapter · Read without an account

Chapter25-26

by Firdausi Rabi'u Abubakar · GIDAN BALARABE

🪴 *GIDAN BALARABE* 🪴

        By 

🪴 *MAMAN NABEELA* 🪴

 _TAURARUWAR MOONLIGHT✨_ 


***


 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION* 


 *DEDICATED TO MY LOVELY MOMAH* 

 *ALLAH YA ƘARA LAFIYA DA NISAN KWANA AMEEN* 🥰



🅿️2️⃣5️⃣↔️2️⃣6️⃣




 .......Yace ko Wannensu ya Zaɓi abinda yake So nan Suka fara ɗauka Sunyi Siyaya ba ta kaɗan ba,Sannan Suka fito Ma'aikatan gurin na ɗauke da kayan Boots ya buɗe Suka Zuba Sannan aka Zuba Wasu cikin Motar Saboda boots ɗin ya cika.


Shiga Motar Suka yi Suka nufi Wani haɗaɗen guri Me ɗan karen kyau'gurin Sai da kayan Maƙolashi ne,irin so Meatpie,cake,ice creem,Shawarma da Sauransu.

bayan Sun Shiga gurin nan ya basu Umarnin ko Wa ya faɗi abinda yake So nan Suka faɗa,aka Kawo Musu cikin Ledoji Masu ɗauke da tambarin Wajen,

Mota Suka Shiga Suka nufi hanyar gida Lokacin ƙarfe tara ta Wuce.


Balarabe ƙara gudun Motarshi yayi dan Allah Allah yake ya kuma gida ya Samu ya kira Sahibar ruhinsa Adu'a yake a ransa Allah dai yasa kar tayi barci dan shi dai baya jin Zai iya barci ba tare da ya ji Muryarta ba,

Ƙarasuwarsa ƙofar gidansa yasa ya danna horn,Yawale Me gidi da Sauri ya Wangale ƙofar yana Me ja da baya,danna hancin Motarsa yayi cikin gidan in da ya dai dai ta perking ɗin Motarsa fituwa Suka yi 

Aiyman Ma buɗewa yayi Shi da Meme Suka fito Nimrah da tayi barci Aiyman yace da Mahaifiyarsa "Mum Nimrah tayi barci!"

"toh" Asiya ta faɗa tana ɗaukarta nufar cikin gidan Suka yi inda BALARABE Shi kuma yasa aka ɗauki kayan da Suke cikin Motar ana Kaisu ƙofar falonsu bayan an gama kwashi Wa rufe Motarsa yayi ya nufi cikin gidan Aiyman da Meme ya tarar a falo nan yace So ƙarasa Shigo da kayan da Suke ƙofar falon Wanda ya riga ya ɗauko Masu nauyin Waɗan da ba zasu iya ɗauka ba,cewa Suka yi "toh"nan Suka Shigo dasu

Suka kaisu inda ya dace.


BALARABE ɓangarensa ya nufa ya rage kayan jikinsa Barthroom ya Shiga ya Watsa ruwa Sannan ya fito Shafe jikinsa yayi da Maya mayansa Sannan ya ɗauko Wani lalausan Wando ya Saka haɗe da rigarsa mara nauyi feshe jikinsa da turare yayi Sannan ya jawo Laptop ɗinsa tsakiyar gadon da Wayoyinsa Kwacinya yayi ruf da ciki yana latsa laptop ɗinsa jawo Wayarsa yayi yana lalubo Number Sahibar ruhinsa danna kira yayi yana fatan Allah yasa ba tayi barci ba...


**********

Khadija tunda aka yi Sallar Magriba ciwan Mara ya Sako ta gaba Wanda dama duk Sanda Za tayi Al'ada tufa ba ƙaramar Woya take Sha ba Wasu lokotan Ma Sai an kaita asbiti'toh yau Ma tunda ta fara ciwan da Mgariba har ƙarfe tara tana fama Wanda Sai da Ummy ta kira Wata likita Maƙociyasu tayi Mata alurai Sannan ta Samu barci ya ɗauke ta.



I'man dake gefenta tasha kuka na tausayin ƴar'uwartata tana Me adu'ar Allah ya yayi Mata Wannnan larurar dan ita ba ta Shan Wuya kamar ita idan Za tayi al'adar,Ummy tayi tayi ta tashi ta ci abinci amma Saboda rashin lafiyar Yayarta ta taƙe ta ci komai Wanda dama haka Suke in ɗaya bashi da lafiya toh fa ɗayan Ma Sai kaganshi kamar Shima bashi da ita,


Tana zaune gefen Yayarta ta Wayar Ummy dake hanunta ta fara ringing dubawa tayi ganin ansa A.A yasa ta tsaya tana tunanin Wayi kuma Me Wannan Sunan har Wayar ta katsi bata ɗauka ba.


BALARABE jin ta katsi yasa ya ƙara kira yana jin Wata iriyar faɗuwar gaba lokaci ɗaya Wadda ya rasa ta Menene?


I'man jin an ƙara kira yasa ta ɗauka tana karawa a kunenta haɗe da yin Sallama.


BALARABE jin an ɗauka yaji anyi Sallama kuma kamar ba Muryar Khadija ba yasa ya amasa Sallamar yana cewa"uhm har kin fara barci ne!"


I'man ƙwalalo idanu tayi tace"Lah'kaii ne dama?"

jin Murya kamar ta ƙanwarta yasa yace"ƙanwata nine yakike!"

"Lafiya lau"I'man ta bashi amsa tana Sakin Murmushi 

"Masha'Allahu,ina Antyn ki dan Allah temaka ki bata Wayar"

"Ba tada lafiya tun ɗazu Sai da a kayi Mata alura tayi barci"

ta faɗa tan guge ƙwallar idanonta.

BALARABE be San lokacin daya tashi Zaune ba a kan gadon yana faɗin "Subhanallahi Me ya Same ta da Sauƙe Sosai ko?"


"eh da Sauƙe"

"toh baki faɗa min Me yake damunta ba!"

Balarabe ya kuma tambaya


I'man cikin kunya tace "ciwon Mara"

"toh dan Allah in ta farka kice na kira ina kuma yi Mata Sannu,ki faɗa Mata gobe zanzo kinji ƙanwata"

"toh'Zan faɗa Mata"

Sallama yayi Mata yana ajiye Wayar ture computer dake gabansa yayi yana Me jin Wani iri a jikinsa,

"Sallamu alaikum"Asiya ta faɗa tana Shigowa cikin ɗakin amsa Sallamar yayi Yana Me gyara kwanciyarsa.....



WASHI GARI


Khadija ta tashi jikin da Sauƙe ba kamar jiya ba amma Ummy hana ta Zuwa Makaranta tayi tace I'man in taje ta faɗa tace ba tada lafiya zuwa gobe in jikin ya ƙara Sauƙe ta je,I'man dake Shirin Makaranta ganin Ummy ta fita yasa tace da Khadija dake kwance"jiya fa an kiraki'da number A.A kuma yace nace yana yi Miki Sannu kuma yau Zaizo"

Saurin kallonta Khadija tayi tana cewa"faɗa Masa kikayi bani da lafiya ko?"

"eh tambaya ta yayi kinji yanda ya ɗaga hankalisa kuwa Shiyasa na faɗa Masa gaskiya"

"toh kin kyauta"

"ah tunda Masoyinki Zaizo ai dule kice na kyauta"I'man ta faɗa tana ɗaukar jakarta ta fita tana dariya...


BALARABE gari na Waye Wa office ya tafi dake litinince Sai da ya ɗanyi ayuka da dama Sannan ya baro office ɗin gida ya dawo inda ya Sake Wanka ya ɗauko Wani haɗaɗen yadi Me Masifar tsada Wankan turare yayi Sannan ya ɗauko hula Wadda ta Shiga da kayan ya Saka takalmi CoverShose ya ɗauko yasa Sai agogon daya ɗaura a tsintsiyar hanunsa,kyau iya kyau BALARABE yayi ɗaukar Makolin Motarsa ƙirar marsindi yayi ya Sauko ƙasa Asiya da fitowarta kenan daga ɓangarenta Wanda ita batasan Ma ya dawo ba kallonshi take idanonta kamar Zasu faɗo ganin irin tsantsan kyawun da yayi,har ya ƙarso gurin da take ba tare da ta farga ba Maganarsa ta dawo da ita daga Shagalar da tayi"uhm Wannan kallon fa Uwar gidan A.A!"

Murmushi ta Saki tan cewa "yaushi ka dawo gaskiya kayi kyau, amma Wannan kwaliyar kamar zaka ɗaurin aure fa!"

Murmushi yayi daya ƙara Masa kyau yace"uhm dubiya zani ko Zaki je?"

"a'a Sai ka dawo amma dubiya kawai kayiwa Wannan kwalli...yar?"

Wani irin kallo daya jefa Mata yasa ta ƙarasa Maganar a rarabe,tana ƙasa da kanta.

"tabbas Asiya ki naso Mu ci gaba da Samun Matsala 

tsakanina dake toh ki Sani nine gaba dake ba kece gaba da ni ba da har Zaki ringa tuhumata,tabbas in baki gyara halinki ba Wallahi Yarinya ƙarama Sai ta fiki Sanin yadda ake tafe da Miji kullum girma kike amma hankalinki yana yin Wani gurin Allah ya ganar dake"

fita yayi ba tare da ya kuma Magana ba yana Me takaicin halin Asiya.


Mota ya faɗa yayi Mata key ya nufi gete yana Zuba horn Wangale gete ɗin a kayi nan ya harba Motarsa kan titi yana Me kunna karatun Alƙur'ani Sauraron karatun yake Wanda yake jin zuciyarsa na yin Sanyi har ya fara bin karatun.


Wayarsa ya ɗauko yana lalubar Number Khadija kira yayi bata daɗe tana ringing ba aka ɗaga Khadija da ta ɗaga Wayar cewa tayi"Assalamu alaikum"

Jin ita ta ɗaga Wayar ajiyar zuciya ya Saki yana cewa"Amin Wa'alaikissalam,Barka da Warhaka ya jikin?"

"Da Sauƙe"Khadija ta faɗa cike da kunya 

"ganinan a hanayar gidanko ina fatan Ƙanwata ta faɗa Miki Saƙo na"

"eh ta faɗa Allah ya kawo ka lafiya"

"Amin Amin Sai na ƙaraso"

"ok Allah ya kawo ka lafiya "Khadija ta kuma faɗa

kashi Wayar yayi yana Sai ta tracking na Number So Khadija bayan ya tsaya ya siyi kayan dubiya, Nan ya fara binduk inda ya nuna Masa.


 *DUBAI*


Jirgin ƙarfe biyu ne Zai tashi Zuwa Nigeria Wanda harda Laila cikin Waɗɗan da ke dakon Lokacin tashin jirgin,Mahaifiyarta ta kira ta Shaida Mata jirginsu na gab da tashi'Sannan ta Shaida Wa Mahaifiyarta ta tura ƙanwarta Aliya tasa Masu aiki So tayata ta gyara Mata Pert ɗin ta.

Bayan Sun gama Wayar,Wayar Me gidanta ta kira Wanda Sai da tayi Misscall Kusan biyar baya ɗagawa SMS ta tura Masa tana Shaida Masa tana hanya,Sannan ta kashi Wayar Sakamakon Sanarwar da aka fara ta kuwa ya kimtsa jirgi Zai tashi'nan jirginsu ya ɗaga Sai Nigeria....



Asiya bayan Fitar Mijin ta ba daɗewa tana Zaune a falo Sai jin Shigowar Mutane tayi babu ko Sallama,Suna ta taunar cingom ƙas ƙass ƙasss'ɗagowa tayi tana dubansu ko kallon inda take basuyi ba Balle tasa ran gaisuwa Suka Wuce Suka nufi Sashin Laila Suna Zuwa Suka Saka Makullin da yake hanunsu Suka Murɗa amma ƙofa taƙe budewa.

dawo Wa Suka yi Falon Wanda Sai a lokacin Suka kula Asiya Suka ce"Barka da gida!" 

Ɗaguwa Asiya tayi tayi Musu Wani Kallon Shiƙeƙe Sannan tace"Barka"

"Dan Allah Makullin Sashin Anty Laila zaki temaka Mana dashi!"

"toh fa Sai yanzu kuka San dani a gidan, ai Sai ko Nemi Me gidan ya bako ba ni ba"ta faɗa tana tashi ta bar Musu Wajen ta Shige Pert ɗin ta.

"Lalai Matar nan ta Mugun rai na Mana hankali,toh yanzu ina Zamu Samu Me gidan ya buɗe Mana?"

Alisha ƙawar Aliya ta faɗa

"hum'ai Wallahi ni Wannan Matar Mugun haushinta nake ji tsabar ta raina Mu Wai Mu nemi Me gidan ya bamu!toh dama ni ina da abin yi Kawai dan Momcy tace nazu Wallahi nazu,dan haka Zo Mu Wuce kawai Nasan Me zan faɗa Wa Momcyn"


***********


Khadija tunda ya faɗa Mata ya tahu Nan ta Shaidawa Mahaifiyarta dake Zaune bayan ta gama Wayar,Ummy cewa tayi "Allah ya kawo Shi lafiya"

Nan Khadija ta tashi ta gyara jikinta ta Saka Wata doguwar rigar Material Blue black Wadda ta hau farar fatarta tayi Mata ɗan karen kyau,dama ita ba Ma'abuciyar kwalliya bace powder kawai ta Shafa Sai Lip gloss da kwalli data Saka a idanonta,tayi Matuƙar kyau Sosai.



BALARABE yana Isa cikin layinsu Khadija Dai dai ta perking ɗinsa yayi' daga gefe Sanan ya kira Waya ya faɗa Mata ya Iso,


Tana Zaune kusa da Ummy dake Mata bayanin Wanda Mahaifinta yace tayi Mata bayaninsa' ya kira yake faɗa Mata ya ƙarasu, Nan take Mata bayanin ai Shine Yazo yanzu,


UMMY Murmushinsu na Manya tayi tana cewa" Ashi dama kun gama dai dai ta kanku tunda gashi har ya Samu Number Waya" ta faɗa tana dariya.


Ummy Wallahi ba ni na bashi Number ba I'man ce, kuma yanzu Ma ita ta faɗa Masa bani da lafiya"Khadija ta faɗa tana ɓoye kanta tsakan kanin ƙafafunta.


Ummy ce tace "toh ai kin bar baƙon a Waje karya gaji da tsayuwa, Nasir je ka Shigo dashi Soro ke kuma ki kai tabarma kafin ya Shigo dashi!"

Ummy ta faɗa tana tashi daga gurin.



 Khadija tabarma ta kai Soron ta Shimfiɗa daga gefe dake Soron irin ƙatun nane  Kuma Wa cikin gidan tayi inda ta kuma ɗauko darduma ta Shimfiɗa daga gefen taburmar.



Nasir Leƙawa Waje yayi dan yaga Wazai Shigo dashi,

Wata dalleliyar Mota yaga Wani kyakyawan BALARABE ya fito daga ciki ya juya ya kuma juyawa yaga ba kuwa dai Sai Shi nufar inda yake yayi yana cewa"Assalamu alaikum Barka da Zuwa,dan Allah ko kaine baƙon Anty Khadija?"


Murmushi BALARABE yayi yana amsa Sallamar da yayi Masa haɗe da cewa"Barkan ka dai Abokina eh ni ne!"


Nasir faɗa ɗa fara'arsa yayi dan tunaninshi Ma Mutumin baya jin hausa Sai yaje ya Mayar Masa da tambar da yayi Masa.

Cikin fara'a Nasir yace "toh Bissmillah ka Shigo daga ciki"

Nan BALARABE ya rufe Mutarsa ya bi bayan Nasir da ya Wuce gaba.


A Soron ya nuna Masa gurin Zama yana Cewa"ka Zauna bari nayi Mata Magana"

da toh'Balarabe ya amsa, yana yaba tsabtar Masu gidan dan Suron tsab yake babu dati ba yana.


Cikin gidan Nasir ya kuma inda yayi Wa Khadija Magana cewar ya Shigo dashi" 


Da toh' ta amsa tana ɗaukan Jug ta ɗebi ruwan randa ta nufi Soron.

"Assalamu alaikum"ta faɗa tana Shiga cikin Soron,

Ɗaguwa yayi daga danna Wayarsa da yake yana Me kafe ta da idanonsa Masu yanayi dana Me jin barci,cikin Wani Salo da yasa Khadija jin Kunya ta Sunkwai da kanta tana A jiye Ruwan a gabansa.



Ƙarfin halin tataro kalamansa yayi Gurin faɗin "Amin Wa'alaikumussalam Barka da fitowa Gimbiya Khadija"cikin ƙasa da Murya tace"Gimbiya kuma"Ba tare da tayi Zaton yaji ba taji yace"uhm kin Ma fi gimbiya indai a Zociyar da ta kamu da tsananin Son ki ne! ya jikin naki ina fatan da Sauƙe Sosai!"

Kunya kalamansa Suka bata yadda yake Magana tamkar Sun daɗe da Sanin juna yasa taji ya daɗa Burge ta Cewa tayi "Naji Sauƙe Sosai"ta faɗa tana Wasa da yatsun hanunta.


"da gaske!toh Allah ya ƙara Lafiya"

"Amin ina Baby?"

"uhm tana lafiya"


"Ba kasha ruwan ba!"Khadija ta faɗa tana Kallonshi ganin ita yake kallo ko ƙeftawa babu yasa ta janyi idanonta daga kansa.

"kinyi kyau Sosai"ta tsinci Muryarsa yana faɗa.

ɗaukar ruwan ya ɗan kurɓa Sannan yace gaba da cewa"Khadija nasan Zuwa yanzu kin fara gane Manufa ta gareki,toh inaso ki bani dama Wadda zan kasance jagora a rayuwarki,Na turo an tambayar Min Mahaifinki Wanda ya Shaida Cewar Be yi Miki Miji ba' ya bani dama nazu Mu dai dai ta,toh gani da ƙoƙon barar Soyayyar ki a taimaka Wa Wannan Bawan Allahn a bani dama"ya faɗa yana kallonta.


Ɓoye kanta tayi cikin hijabi ba tare data faɗi kumai ba,ganin abin da tayi yasa Shi Sakin Murmushin Nasara yana cewa "uhm baki ce kumai ba!"

"Allah ya zaɓa abinda yake alkairi"

Khadija ta faɗa kanta cikin hijabi.

"Amin Suma Amin kina nufin kin bani dama kenan?"

BALARABE ya faɗa.

Ɗaga kanta tayi alamun eh'

"a'a da baki Zaki faɗa min dan na tabbatar ba Mafarki nake ba"

BALARABE ya faɗa yana Sakin Murmushi.

"eh"

cike da farin ciki BALARABE yace"Alhamdulilah"

Nan Suka ci gaba da hira kamar Sun daɗe ita dai Khadija cike da Kunya haka take hirar cikin hirar yake bata labarin ko Shi Waye da kuma Adadin Matansa da ƴaƴansa,yace gaba da cewa"kar kiji nace Matana biyu abun ya baki tsuro,ki chanja Shawara ina fatan ko Zauna lafiya ke daso,dan ina jin labaran Wasu Matan basa Son Me Mata toh ni dai a taimaka a So ni"ya faɗa yana Me Sakin Murmushi yana kallonta.



"ai ko Wanne bawa baya kauce Wa Ƙaddararsa in Allah yayi Me Mata Zaka aura ba Makawa Sai ka aureshi Allah ya bamu haƙurin Zama da juna"

Khadija ta faɗa.

tunda ta fara Maganar yake binta da kallo dumin ta Matuƙar burgeshi,Wanda daga lafuzanta ya fahimci ita ɗin tana aiki da ilimin da Allah ya bata.

Cewa yayi "Amin ya rabbi amma fa gaskiya kalamanki Sun burgeni,ina gudiya ga Allah daya haɗa ni dake Allah yasa ke ɗin ki kasance haske a rayuwata,Allah kuma yasa ke zaki cika Min gidana da ƴaƴa Masu hali irin naki"BALARABE ya faɗa yana dariya ganin ta cusa kanta cikin hijabi.

Duba Wayarsa yayi ganin duhun Magriba ya kawo kai yana cewa" kiyi Min iso gurin Ummah Mu gaisa dan Wuce Wa Zanyi"

"toh" Khadija ta faɗa tana tashi'Shima tashi yayi.

Cikin gidan ta nufa nan ta Shaidawa Ummy Zasu gaisa dashi,Ummy hijab taja Sannan tace ta faɗa Masa ya Shigo"

Kuma Wa Khadija tayi tayi Masa iso ya Shigo cikin gidan Nan ya tsuguna har ƙasa ya gaida Ummy inda ta amsa tana tambayarsa Mutan gida, nan ya amsa kansa a ƙasa yayi Mata Sallama Sannan ya fita 

Khadija rakashi tayi har gurin da yayi perking ɗin Motarsa.


Buɗe Motar yayi ya ɗauko Ledar dayayi Mata ta kayan dubiya,ya Miƙa Mata yana Cewa "gashi ba yawa Allah ya ƙara lafiya,yasa kaffarane"

"kaiii har da ɗawainiya haka toh na gude Allah ya ƙara buɗi"Khadija ta faɗa ba tare da ta karɓa ba.


Mahaifinta daya dawo daga kasuwa ne yazu Wuce Wa Nan Khadija ta faɗa Wa BALARABE ga Mahaifinta Su gaisa cikin ladabi haɗi da girmamawa yace"Barka da yama Abba"

"Barkanka dai Ɗannan ko kaine Wanda Alhaji Mujahid yayi Mini bayani?"

"eh ni ne Abba"

"toh Masha'Allahu Allah ya taimaka,ka gaida Mahaifin naka"


"Amin Abba zaiji insha'Allahu"

Nan baban Khadija ya Shiga gida.

Miƙa Mata ledar ya ƙarayi Sannan ta karɓa tana gudiya.

Mota ya Shiga ya zauna yayi Mata key yana cewa"Sai Munyi Waya"Murmushi Khadija tayi tana kaɗa kai inda Shima Murmushin yayi yana me barin layin,juyawa Khadija tayi ta nufi gidansu.......


LAILA


Jirginsu na Sauka a airport Bayan ta Sauko daga Jirgin Hango Mahaifiyarta tayi tsayi gurin perking ɗin Motoci, ƙarasa Wa tayi inda take ta rungume ta tana faɗin "I Miss you Momcyna"

"Miss you to My Daughter" 

Sannan Suka Shiga Mota Suoa nufi gidan Mahaifiyarta ta.



Suna zuwa Wanka tayi ta ci abinci Sannan tace da Mahaifiyarta"Momcy Bana ƙarasa gida kinga dare yayi gobe zan dawo Sai Muyi Maganar"

"toh Allah ya kaimu,amma fa Aliya ta faɗa Min basu Share Miki Sashinki ba,Wai Key ɗin yaƙe buɗewa'kuma Sun tanbaya basu Sami Wani ba!"

daka tawa tayi daga yafa Mayafin da take tace "Momcy ban gane ba tana nufin an Chanza Min Makulli ko Me?"

ta faɗa cike da Mamaki.

"Idan kinje dai Zaki ji'ai da alama ya fara gajiya da Wannan halin naki na yawun ƙasashi,dama nasha faɗa miki duk randa ya gaji ba Zai yadda da hakan ba"

"haba Momcy ya zaki ringa faɗar haka ni nasan Wannan Munafukar ce........."



 *SHARE & COMENTS* 🙏🙏🙏






 *MAMAN* *NABEELA CE...✍️

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.