Free chapter · Read without an account
Chapter29-30
🪴 *GIDAN BALARABE* 🪴
By
🪴 *MAMAN NABEELA* 🪴
_TAURARUWAR MOONLIGHT✨_
***
*MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*
*DEDICATED TO MY LOVELY MOMAH*
*ALLAH YA ƘARA LAFIYA DA NISAN KWANA*
🅿️2️⃣9️⃣↔️3️⃣0️⃣
......."Son ɗin da kansa yake faɗar haka?amma be kyauta ba yanzu ki kwanta zuwa Safiya Zan kirashi naji Menene dalilin faruwar hakan?"Ammy ta faɗa tana tashi tsayi"kinci abinci!"
"eh"
"toh kiyi Wanka ki kwanta kinji Zaizo ya Sameni ne!"
"toh" ta faɗa tana tashi ta Shiga banɗaki.
Ammy Wata Sabuwar rigar barci ta ɗauko Mata ta ajiye gefen gado Sannan ta nufi Ɗakin Me gidanta dake ta Zabga Mata kira ta Waya.
Tura ƙofar tayi Sannan ta Shiga bakinta ɗauke da Sallama Zama tayi gefen Me gidan nata nan take bashi Labarin abinda yasa bata Zo da Wuri ba,cikin nazari da tunani irin na Babban Mutum yace"ta faɗa Miki Me ya haɗaso?"
"a'a yadda take faɗa dai kamar bata yi Masa kumai ba,amma Sai dai Mujira gobe in Allah ya kaimu yazu Muji ta bakinsa"
Ammy ta faɗa.
"uhm Allah ya kaimu goben" Abby ya faɗa
"Amin"Ammy ta kuma faɗe..
WASHI GARI
BALARABE yana tashi Shirin office yayi bayan ya karya Shi da yara Suka nufi Mota.
Bayan ya Sauke yaran offece ya nufa,yana Zuwa Meating Suka Shiga basu fitu ba Sai gurin ƙarfe goma'Wayarsa da ke Silent ya ɗauko nan yaga kiran Abby kusan biyar Sai Saƙo da ya turo Masa guda ɗaya duba Saƙon ya fara yi kamar haka;
( _Baffa duk inda kake kazu gida ka Sameni ina Son ganinka.)_
Ɗaguwa yayi ya dubi P.A ɗinsa dake kusa dashi ya Miƙa Masa Wasu takardo yace"ka Shigar dasu office,idan Dr joshua ya ƙarasu kace Masa ya jirani Zan ɗan fita bazan daɗe ba Insha'Allahu Zan dawo"
"toh" P.A ɗin nasa ya faɗa yana nufar offece.
Mota Ya nufa yana Shiga ya bata Wuta ya ɗauki hanayar RIJIYAR ZAKI.
Ko daya isa yana yin peking Sashin Abby ya nufa Sallama yayi nan Abby ya bashi izinin Shiga,yana Shiga ya nufi gefen ƙafafun ABBY ya zauna yana gaishi Shi,amsawa Abby yayi cikin Sakin Fuska ɗaukar Waya yayi yanna kira "kizu ke da yarinyar nan yanzu" Balarabe Ɗaguwa yayi cikin tsananin Mamaki,kar dai Yarinyar nan gurin Iyayensa tazo ta kawo ƙararshi?
Sallamar Ammy ce ta dawo dashi daga tunanin da yake amsa Sallamar Su kayi nan Ammy ta Shigo Laila na biye da ita Zama Ammy tai gefen kujera Laila dake Sanye da Hijabin Huda ita kuma ta Zauna kan Carpet.
Gaida Abby tayi Sannan ta gaida Balarabe da tunda ta shigo Wani Mugun Wari ya Ziyarci hancinshi cikin dauriya yace "Lafiya"a takaice yana yin gefe da fuskarshi.
Abby ne yace"Baffa abinda yasa na kiraka ba Wani abu bane face jiya Matarka ta zo da Wata Magana ta faɗawa Mahaifiyarka,ita kuma ta faɗa min toh'inason naji gaskiyar Menene ya ke faruwa?"Abby ya faɗa yana duban Balarabe.
Shuru yayi Sai Wata Uwar Zufa da yake haɗawa Saboda Warin da yake ji ya fara fin ƙarfin hancinshi cikin dauriya ya Kwashi abinda ya faro jiya ya faɗawa Abby gama faɗarsa ke da Wuya Sai amai Shaaa ya fara Kelayashi kamar zai amayar da kayan cikinshi Ammy da Abby cikin tashin hankali Su kayi kan ɗan naso Abby ne ya kamashi yayi ɗakinsa dashi ya haɗa Masa ruwa yace ya gyara jikinsa.
Ammy falon ta gyara tana tunanin tabbas akwai Lauje cikin naɗi tunda da ai ba haka yake ji game da Lailar ba tabbas dulle ta riƙe Laila har Tsahun Wasu lokuta dumin ta Sa ayi Mata rubutu,idan har tabar Ɗanta ya ci gaba da zama da ita a haka ba ƙaramar Matsala hakan zai haifar ba dumin Shi zai chutu.
Laila kuwa tunda taga abinda ya faru take kuka Shan Shana jikinta ta ringayi ko Zata ji Warin da yake faɗa amma ba abinda ta ji Sai ƙamshi,Maganar Ammy ta dawo da ita da take cewa"Laila kuma ɗaki na kinji idan nazu Za muyi Magana"
"toh"ta amsa ta tashi ta fita tana Share hawayi.
Balarabe bayan ya fito ruwa Abby ya bashi yasha Sannan ya ke tambayarshi ya dena jin aman ko?
da eh ya amsa Ammy ce ta Shigo cikin ɗakin tana tambayarsa idan yana jin Wani abu ya faɗa! yace ya dena ji"
Nan Ammy ta zauna Suka tsaida Matsayar Laila zata zauna a gurinta dumin ta fara Sawa ana yi Mata rubutu,inda Ammy tace ya kwantar da hankalinsa Zata kira Mahaifiyarta So tatauna kan batun dena tafiye tafeyin da yace bayaso.
AFTER ONE WEAK
Cikin Sati ɗayan da Suka Wuce abubuwa da yawa Sun faro ciki harda fara Samun lafiyar Laila,inda Malamin da yake yi Mata rubutu ya Shaidawa Ammy jinnu aka tura Mata Waɗanda zasu ringa Sawa Mijinta yaji Wari duk Sanda tazu gurin da yake' Nan a ka gano basu ka ɗai bane a jikinta harda Waɗɗanda aka turosu So Sa ta ringa neman Mata Wanda So Suka faɗa yayin da Malamin ke Mata ruƙiyya amma fur Suka ƙe faɗin Wanda ya turuso inda akayi Nasarar cire Masu Sa ta Warin inda Masu Sata neman Mata kuma dake taurin kai garesu Suka gudo bayan Sun Shaida Lokacin aikin da aka turuso be ƙare ba.
Mahaifiyar Laila lokacin da tasamu labari kuka ta ringa yi da idanonta tana yiwa ƴarta ta fatan Samun lafiya.
Cikin Satin kuma Khadija da Balarabe Soyayyarsu tayi Mugun ƙarfin da ɗaya in beji ɗaya ba yakan Shiga Wani yana yi Soyayya Suke gudanarwa Me tsabta.
inda cikin Satin aka tsaida ranar aurensu bayan candy da Sati biyu farin ciki gurin Masoyan ba'a Magana.
Ɓangaren Asiya kuwa cike take da farin cikin Nasarar aikin da Buka yayi Mata Wanda ta kashi Maƙodan kuɗi kwana biyu da yin aikin kuma aiki ya Lalace inda ta Samu labarin Laila ta Warke,Wanda yasa ta ringa kuka Saboda ɗonbin kuɗin da ta kashi.
Khadija yau Yayansu ke dawo Wa Wanda yasa Suke ta Shirye-Shirye Anty Kubra Ma ta zo gidan ita ta ringa bada Kuɗaɗen da ake Shirya Masa abin tarba, ƙarfe uku Saura kwata,Adnan ya tafi tarushi inda ƙarfe uku dai dai jirginsu zai Sauka.
*AMINU KANO INTERNATIONAL AIPORT*
Ƙarfe 3 dai dai jirginsu ya Sauka inda filin jirgin ya cika dam ƙam dan harda Me girma Gwamna gurin tararsu Saukowa Suka farayi cikin Shigar farar Tshit da jar hula Sai farin jens gaban rigar ansa KWANKWASIYA Saukowa Su kayi cikin nutsuwa Suna Masu farin cikin dawo Warsu ƙasarsu cike da tarin Nassara,bayan Sun gama Saukowa Gurin Me girma Gwamna Suka nufa daya Miƙe tsayi yana yi Musu barka da dawo Wa Shima Sanyi yake cikin ɗanyar Shadda fara Sul Sai jar hula a kansa,zuwa Suka ringayi Suna Miƙa gaisuwa cikin Sakin fuska da ƙaunar tallaka yake amsawa yana rungumarsu.
Bayan an gama gaishi gashi Umarni ya basu da Kowanensu ya je gida ya huta zuwa dare So zu gidan Gwamnati dumin akwai Liyafar da aka Shirya Musu.
Dama kusan duk anzu ɗaukarsu kowa nufar Motar da aka zo ɗaukarshi yayi Nana Suka Shiga,Khalil Ma tuni ya hangu Adnan nan ya nufi Motarshi inda Adnan ya taho da Sauri yana rungumeshi cike da farin ciki Mota Suka Shiga Suka nufi gida.
"MAN gaskiya india ta karɓe ka kaga yadda ka ƙara girma da kyau kuwa!"
Adnan ya faɗa yana cigaba da tuƙa Motar.
Dariya Khalil yayi Wadda ta daɗa bayyana tsan tsar kamar da yake da Khadija Sannan "haba dai har na kai ka kaga yadda ka ƙara chanzawa kuwa banda nayi Maka farin Sani ai da bazan gane ka ba"Khalil ya faɗa yana dariya .
"kai Man kai fa chanza da yawa ji hausar taka Ma fa da alama Sai mun kuma kuya Ma"Adnan ya faɗa cike da zulaya.
"uhm ai tunda ina tare da My Mame ba nida Matsala ta ringa kuyan idan har da gaske kake!"
Dariya Adnan ya kece da ita yana cewa"ah kaga Masoya,toh ai Sai kazu kayi ƙoƙari a haɗa dana Khadija Muyi Mu Miƙa ko dan ni dai Ba yanzu ba"
"kamar ka Sani kuwa Ai dana huta Zanyi Maganar dan da zafi zafi ake dukan ƙarfe"
dariya Adnan ya kuma kecewa da ita yana cewa"gaskiya Bro nayi kewarka ba kaɗan ba"
"nima haka"
Ƙarasuwa Su kayi ƙofar gidan Suna yin perking So Khadija Suka fito da Sauri jin tsayuwar Mota Khalil na fituwa Khadija ta rungumeshi tana tsananin Farin ciki ɗaguwar da za tayi karab idanonta Suka faɗa na Balarabe da Zuwansa kenan,yace bari yayi Mata zuwan bazata Khadija da ko Mayafi bata yaffa ba Sai ɗan kwalin kayan jikinta ta zaroo idano.
Balarabe kuwa Wani kishi yaji Lokacin da ta rungume Wanda ko fuskarsa be gani ba yana jin Wani iri a ransa Wani irin Kallo yake jifanta dashi Wanda yasa Khadija Kuma Wa cikin gida Wanda ita a tunaninta ganinta dayayi babu hijabi yasa yake ai ka Mata da kallon.
Balarabe kuwa Mota ya kuma kawai ya yi tafi yana jin Wani a zababen kishi na tasu Masa karatu ya kunna dan ya Samu zuciyarsa tayi Sanyi, daya rufe idanonsa kawai hangu ta yake lokacin da ta rungumeshi.
Khadija na Shiga cikin gida Hijabi ta Saka Mame na tambayarta ina Zata tace"ke dai kawai ina zuwa"
fituwa tayi inda ta ringa baza idano taga babu Shi babu Motarsa"ko dai gizo yake min ba zuwa yayi ba"ta faɗa a fili tana daɗa dubawa kumawa gida tayi ta Shiga ɗaki ta ɗauki Wayarta kiran layinsa tayi kusan Sau uku baya ɗauka,a jiye Wayar tayi tana cewa "ina ga aiki yake ko kuma baya kusa amma dana tammbayeshi Shi nagani ko kuwa?
kai abin da Ma maki ai be taɓa yi Min gizo ba......✍️
*MAMAN* *NABEELA CE..✍️*