Free chapter · Read without an account
Chapter 6
,*_MASARAUTAR FADAKATAM_*
*_Na Maryam Umar Abdullahi_*
( _Maman yusuf_)
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
***
*____________________________________*
🅿️age_6
.................. A firgice 'ya'yan gimbiya TINAYA suka ruga aguje suka fad'a akan gawar uwarsu suna wani irin kuka Mai tsuma zuciya , Wanda tsananin tausayinsu yasa jama'ar da dama fashewa da kuka ,
Matar tsohon Nan kuwa da yaranta suna tsaye sun kasa gaba sun kasa baya tsananin firgici tsoro hade da tashin hankali ne su ka yi masu dirar mikiya a k'ahon zuciya , musamman ma matar tsohon abun ya daketa sosai Wanda Nan take zuciyarta ta buga , Basu Ankara ba sai gani sukayi tana wani irin Aman jini bak'i k'irin , da sauri yaranta suka kamata suna jijjigata sai dai cikin yan mintina itama Rai yayi halinsa , ai kuwa wani irin ihu yaran suka Sanya Wana sai da Masarautar ta amsa wani irin Amo,
Sarki ZULAIMU dake can sama ganin zasu 'bata mashi lokaci Bai Gama bayaninshi ba ya bada umurnin a kwashe mashi gawarwakin da ma masu kukan ajefar dasu can wajan masarauta, haka kuwa akayi inda aka tarkata su aka fitar dasu daga cikin Masarautar gaba d'aya,
Jikin duka mutanen dake wajan yayi Sanyi kasancewar irin haka Bai ta'ba faruwa a tarihin Masarautar ba, wannan ya kasance sabon Abu a wajansu, Wanda lokaci d'aya wani irin tsoro da shakkar sarki ZULAIMU ya shiga zukatansu, Wanda shi kuma dama haka yakeso ,kuma shine burinshi ,
K'ure masu kallo yayi cike da nishad'i da farinciki ganin yadda tsoro Mai tsanani ya bayyana Akan fuskokinsu ,
Cikin k'ara daure fuska yaci gaba da magana kamar haka,
" A sabon tsarin wannan masarauta daga wannan rana kowane mutum dake zaune a wannan yankin na Fadakatam zai dinga biyan kudin haraji , Wanda kuma ya Zama Dole mutum ya biya ko hukunci ya hau kansa , haka kuma duk wani manomi da zaiyi noma acikin k'asata to ya sani idan har ya noma abunda zai noma to zai raba amfanin gonarshi biyu ya d'auki d'aya ya baiwa masarauta d'aya , sannan zansa a rufe wannan gari duk wani bak'o dake son shigowa garin Fadakatam to tabbas sai ya biya harajin shigowa garin tukunna ,wad'an Nan sune dokoki na farko da zan Fara kafawa kamun na fito da wasu Wanda a hankali ko wane tsari zai koma dai dai da yanda nakeso ,fatan zakubi doka , Wanda rashin bin dokata zai iya haifar da nadama,
Gaba d'aya jama'ar wajan sunkuyar da kansu sukayi tare da d'ora hannunsu na Dama Akan k'irjinsu alamar sun ji kuma sun amsa ,
Wani makirin murmushi ne ya su'bucewa sarki ZULAIMU kamun ya jinjina kanshi ya juya yabar saman I zuwa cikin fadar, ganin hakan yasa sarkin shela gayawa mutane zasu iya tafiya an sallamesu, haka suka dinga watsewa kowane jiki a sanyaye,
Mutanen garin fadakatam sun shiga tashin hankali irin Wanda Basu ta'ba tunanin zasu fuskanta ba , sun tabbatar da k'arewa tattalin arzikinsu yazo ,sai dai kowane yayi gumm da bakinsa wa junansu ma tsoron tattauna zancan sukeyi saboda yadda tsoron sarki ZULAIMU yayi tasiri a zukatansu,
Haka sarki ZULAIMU ya Fara shimfid'a wannan mulki cikin matuk'ar zalunci da rashin tausayi , inda lokaci d'aya ya k'ara Zama hamshak'in sarkin dake ji da arzik'i da mulki, yayinda gefe d'aya aka Ware matasa majiya k'arfi aka Fara horar dasu dabarun yak'i , duk da Masarautar fadakatam nada yawan dakarun yak'i kuma jarumai ,haka Bai ishi sarki ZULAIMU ba sai da yasa aka hada wasu tawagar matasa masu dimbin yawa ake Basu horo kala kala , saboda burinshi na mallake gaba d'aya nahiyar tasu ,Yana da burin duk wani sarki babba da k'arami ya zamana ya koma k'ark'ashin ikonsa ne sai abunda ya keso za'ayi,
.......................................................
A kwana a tashi a sarar Mai Rai , yau watan su gimbiya HIDAYA ukku a garin RIGASA inda daga ita har matar Malamin duba suke samun kulawa ta musamman daga sarkin RIGASA da mutanen garin , Matar Malamin duba a gidansu take zaune kasancewarta 'yar garin , yayinda gimbiya HIDAYA ke zaune a gidan sarki ,kasancewarta Mata ga babban sarkinsu kuma uwa ga magajin Sarkinsu, duk wannan kulawar da gimbiya HIDAYA ke samu Sam hankalinta ya kasa kwanciya kullum cikin tunanin mijinta da kuma halin da Masarautar fadakatam take ciki takeyi ,kasancewar suna samun labarin duk abunda ke faruwa a masarautar ta hanyar madubin tsafin sarkin RIGASA,
Yau ma kamar kullum zaune take a inda ta Saba Zama , cikin wani kyakkyawan lambu ,cikin muryarta Mai matuk'ar dad'i take rera maitocin wak'arta ga masoyinta sarki KUNTARU, Wanda suke nuna zallan kewarsa da begensa da takeyi, yayinda hawayen bak'in ciki ke yi mata kwaranya ,
A hankali matar Malamin duba ke takowa zuwa inda take , cikin matuk'ar tausayawa ta duk'a a gaban gimbiya HIDAYA tace
" Allolin zinari su k'ara maki nasara yake sarauniyar Fadakatam ,hak'ik'a banajin dad'i ganinki cikin damuwa , ki taimaka ki sauke duk wata damuwa dake ranki ba don komai ba sai don lafiyar magajin Masarautar fadakatam, yawaita damuwa a wajanki babbar barazana ce ga lafiyar sarkinmu, nasan abubuwan dake damunki ,Amma haka Nan Zaki daure tunda haka Allolin zinari suka kaddara Mana, hak'ik'a ni kaina inajin damuwar rashin mijina da tunanin halin da ya ke ciki ,Amma a. Haka nake daurewa Ina kore duk wata damuwa saboda cikin jikina , Wanda nasan shine cikon farincikin mijina , Wanda kema nasan duk da sarki KUNTARU baya raye Amma bashi da babban burin da ya wuce samun magaji, sannan cikin jikinki shine zai zama silar wanzuwar lafiya da tarwatsewar zalunci a masarautar fadakatam ,
Nisawa gimbiya HIDAYA tayi tace " inajin matuk'ar tashin hankali duk lokacin da naji labarin halin da talakawanmu suke ciki, gashi ba abunda zamu iyayi akai har sai Nan da shekara ashirin ,kamun lokacin bamu San iya adadin mutanen da aka kashe ta hanyar zalunci ba , bamusan iya adadin da wahala da yunwa zasu kashe ba, wannan tunanin Yana matuk'ar tada Mani da hankali ,"
duk'ar da Kai matar Malamin duba tayi tana cewa "kikwantar da hankalinki gimbiya Allolin zinari suna tare dasu kuma na tabbatar da zasu Basu kariya kamun lokacin da yariman masarauta zaizo, "
Jinjina Kai gimbiya HIDAYA tayi ba tare da ta sake magana ba ,inda matar Malamin duba ta dinga Bata labaran nishad'i don ganin ta kore mata kaso mafi yawa na damuwar da take ciki
*******************************
A hankali lokaci ke tafiya komai Yana sauyawa da tafiya dai dai da tsarin sarkin ZULAIMU, mulki yake shimfid'awa kamar mi yayinda gefe d'aya ake ci gaba da bawa dakarunshi horo kala kala, yaron sarki ZULAIMU Mai suna Zillak'i yanada shekara biyar a duniya inda shima aka fidda ke'bantaccen waje ake koyar dashi fad'a kala kala da duk wani dabarun yak'i ,sarki ZULAIMU na masifar son yaron shi ZILLAK'I Wanda yake Kira da yarima , don a yanzu sarki ZULAIMU bashida burin da ya wuce bayan mutuwarshi d'anshi ZILLAK'I ya gaji sarautar fadakatam, shiyasa tun Yanzu yake zuwa dashi fada tare da Fara koyar dashi wasu abubuwa na mulki , don yanason yaro ya taso da sani sosai akan abun da ya shafi mulkin garin,
Yau kimanin wata takwas da hawan sarki ZULAIMU mulki , inda cikin gimbiya HIDAYA yake da wata takwas da sati biyu,
Yau fada ta cika mak'il da dakaru kuma sadaukan sarki ZULAIMU ,Wanda yake matuk'ar jin dadi in ya kallesu don yasan lokacin cika burinsa na mallakar kananun garuruwa harma da manyan garuruwan dake nahiyar yayi,
Magatakarda aka Kira inda aka bashi umurnin ya rubuta takarda ukku a aika su ga garuruwan farko dake mak'waftaka da su , inda aka rubuta wasik'un kamar haka
" _Sak'o daga sarkin ZULAIMU sarkin masarauta Fadakatam, in Mai baka umurni da ka kasance Mai yimun mubaya'a da Kai da mutanenka , ma'ana Ina buk'atar mullkar garinka , ta hanyar Zama Mai k'arfin ikon fad'a aji a masarautar ka ,abun da nakeso shi za'ayi ,in ka amince Ina Mai gayyatarka fada ta don d'oraka ga dukkan dokoki na , in Dan kuma kana jayayya da hakan to zamu gwabza yak'i da Kai ,idan kaci yak'in zan bar maka garinka ,idan kuma ni naci ka da yak'i to da Kai da duk mutanen garinka da komai da kuka mallaka zai koma k'ark'ashin iko na ne ,sak'o daga sarkin ZULAIMU"_
Haka aka rubuta wad'an Nan wasik'u guda ukku aka tada d'an aike aka turashi Kai wad'an Nan wasik'u,Izuwa garuwan ,
Bayan kwana biyu da aika wasuk'un sai ga sak'on sarakuna biyu Akan nuna amincewarsu da sarki ZULAIMU Wanda sun amince ne abisa tilas sanin ko alama ba zasu iya yak'ar Masarautar fadakatam ba, yayinda d'ayan sarkin ya nuna rashin amincewarshi da hakan ,ai kuwa Babu Bata lokaci sarki ZULAIMU ya aika Masa da takardar yak'i Nan da kwana ukku ,
Hankalin wannan sarki da mutanenshi yayi masifar tashi inda suka Shiga shirye-shiryen yak'i ,shiri sukeyi ba na Wasa ba sai dai hakan Bai Hana su Shiga matsanancin tashin hankali da tsoro ba ,
Bayan kwana ukku tawagar sarki ZULAIMU ta wanzu a wannan garin inda aka dinga dauki ba dad'i tsakanin mayak'an Masarautar Dana sarki ZULAIMU , kasancewar dakarun Masarautar fadakatam jarumai ne na gasken gaske Wanda suka horu da sanin duk wata makamar yak'i , yasa Basu wani d'auki lokaci ba suka gama da su inda suka Kama na kamawa suka kashe na kashewa yayinda suka dinga bin matansu suna masu fyade Wanda duk umurnin Sarki ZULAIMU ne saida suka yiwa garin kaca kaca sannan suka nufi ainahin gidan sarautar suna zuwa suka Kama sarkin suka daddaureshi sannan suka Kama matanshi da yaranshi suka Yi masu fyade a gaban idonshi sannan suka dauki sarkin suka juya dashi Masarautar fadakatam, Wanda duk abunda suka aikata umurni ne ga sarki ZULAIMU,
Lokacin da aka shigo da wannan sarkin a d'aure farinciki ne ya Kama sarki ZULAIMU inda yayi wata irin kururuwa tare da Fara yiwa kanshi kirari ....... Sai da aka azabtar da wannan sarki na Tsawon kwana ukku sannan aka Tara mutane a gabansu aka fille mashi Kai,
Wannan al'amar yayi matuk'ar girgiza sauran sarakunan dake wannan yankin , kasancewar dukkansu ba Masarautar da take da k'arfin da Masarautar fadakatam take dashi , wannan yasa duk sarkin da aka aikama takarda Nan take yakeyin mubaya'a inda za'a shigo har garinshi a mulkeshi shi da mutanenshi,
Wannan nasarar da sarki ZULAIMU ke samu ba k'aramun k'ara ingiza izzarshi mulkinshi yayi ba zaluncinshi sai k'aruwa yakeyi ganin ya Zama gagara badau a duk nahiyar maganar shi kawai ake bi abunda yakeso akeyi cikin k'ank'anin lokaci wata Tara cif da hawanshi mulki amma ya samu girma da daukaka da wata irin dukiya da Babu sarkin daya ta'ba Tara dukiya irin wannnan a Tsawon tarihin k'asar,
______________________________
Yau tun safe gimbiya HIDAYA ta tashi da wani irin ciyon baya da Mara tun tana daurewa har sai da ta aika aka sanar da matan sarki, kamun kace mi sun hallara a d'akin da take , Babu Bata lokaci suka dubata inda suka tabbatar mata da haihuwa ce , Nan suka ci gaba da kula da ita duk wani taimako sunyi Mata Amma haihuwa shiru har lokacin da rana ta zo fad'uwa , hankalinsu yayi masifar tashi ganin lokacin sa'a na Neman wucewa gimbiya Bata haihuwa ba Nan suka zube suka rufe idanunshi tare da mik'ar da hannayensu suka fara jera Mata addu'a a wajan abun bautarsu lokacin da rana take gaf da rufewa alokacin haihuwan yazo gadan gadan ,kamun kace mi sai ga kukan yaro ya cika d'akin da suke , cikin matuk'ar murna da farinciki suka tashi suka Kama yaron inda suka nannad'e suka nufi fadar sarki ,
Yayinda sauran suka shiga aikin gyaran gimbiya HIDAYA.
___________________________
Lokacin da jaririn ya fad'o kukan da ya fasa yayi dai dai da wani irin gud'a da hayaniya da suka farke acikin d'akin Bauta ,gud'a ce Mai tsananin k'arfi da firgita bawa , aikuwa Nan take duk wani Mai rayuwa a gidan sarautar suka rud'e suka shiga d'imuwa da mamaki har ma da al'ajabi,, abunda suka sani ne irin wannan gud'ar bata faruwa har sai da dalili k'waya d'aya tal , shine haihuwar Wanda ya kasance magajin Masarautar fadakatam, wannan abun fa ya Sanya mutane a rud'ani sanin cewa gimbiya HIDAYA dai batada ciki bare ayi tunanin itace ta haihu , sannan tunda akaji wannan gud'ar to tabbas ko a Ina ne an haifi magajin Masarauta ne,
Al'amarin sarki ZULAIMU kuwa Zamu iya cewa yafi kowa shiga tsananin tashin hankali da rud'ewa inda Nan take ya bada izinin a Nemo mashi duka bokayen garin har ma da na wasu garuruwan don Yin bincike akan wannan al'amari...............
💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐💫⭐
*_MATSI MARTABAN KOWACE 'YA MACE_*
Kunsan mi yake Sanya namiji yawan yin Karin aure ? Sai kiga namiji baiwuce shekara daya ko biyu dayin aure ba amma nema yake ya sake yin wani , 🤔🤔 wasu mazan ra'ayinsu ne hakan Tara mata amma wasu da yawa basuda ra'ayin aure aure saidai sakacin mace kan iya janyo hankalinshi ga sakeyin wani auren, babu abunda namiji keso irin yaji gaban mace a tsuke a matse gam , Wanda dayawa wasu keyin sakaci da kula da wannan 'bangaren , namiji bayason yazo shiga mace yaji ya wuce sut sannan aciki yajishi yana yawo batare da ya cike wajan ba, abunda namiji keso shine a kullum yaji mace a game GAM yadda zai shiga da kyar sannan bayan ya shigan yaji komai zam zam ta yadda gabanki zai rik'esh gam , Wanda rashin wannan abun kan sa namiji yafara shaawar Karin aure ,
Wata da tayi haihuwa daya biyu shikenan saikiga gabanta ya saki ta bude sosai kuma Bata damu data GYARA ba , yakamata mata mu kula sosai ,,
*Wannan dalilin yasa mukazo maku da ingantattun kayan matsi da basuda illah ajiki , saboda duk abunda aka hada dasu to abubuwane masu muhimmanci da zasu Kara maki lafiya ajikin ki ba zancan cutarwa aciki ,*
*Sannan akwai gumba mai taken sha ki matse gumbace da take ciko mace ta ciki sosai tare da bata niima Wanda dama matsin ciki shine matsi*
*Akwai kuma yajin mata ga mace mai matsalar budewar gaba ko maijego da take bukatar cikowar gaba da matsewar gaba ko amarya da takeson ta ciko kota ina Wanda wannan yajin yanada matukar muhimmanci da amfani ajikin mace*
Daga taku mmn Yusuf mai kayan mata sokoto
***
*Yan kano da yan kaduna da katsina zanyi aike kuma kudin motar kyauta ne Maison kayanmu tayimun magana a hada da nata ,ngd*