Free chapter 路 Read without an account
11&12
MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE馃崚*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION馃馃徎*
____________________________
*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee馃グ)_
FreePege
*11&12*
Bayan sati biyu da faruwar al'amarin suka sake zama suka tsara wata wasikar wacce tafi ta farko rashin kunya da fitsara ta kara rufe fuskarta da Niqab ta tura yaro ya kaiwa Haruna maigadi......Wannan karon ma ya jima yana mamakin abinda yake rubuce a jikin takardar babu shakka duk inda yarinyar ta fito mara kunya da tarbiya ce. Murmushi yayi yana shafa gemunsa babu shakka zai so yaga wannan mara kunyar yarinyar dake so ta had'a shimfida dashi ta kuma sha yawun bakinsa. shi kadai yake dariya yana mamakin tsagerancin yarinyar......Ya samu Haruna yace masa duk sanda yaro ya kawo masa wani sa'ko ya tambayeshi wanda ya aikoshi." Haruna yace." Insha Allah zan kiyaye Motarsa ya bude ya shiga ya zauna da bisimillah a bakinsa. Haruna ya daga masa hannu hade da fatan alkairi.
Yana fitowa bakin titi ya hangeshi zaune gurin sana'ar sa cikin kwaleliyar rana ga wuta sai ci!! take a gabansa da wata katuwar roba yana liqe ta da hannu daya yake aikin sai zabga uban gumi yake. Ita kuma tana tsugune a gefansa da uniporm na makaranta a jikinta magana sukeyi ita dashi da alama suna cikin damuwa.
Wani irin yaji a tare dashi babu shakka da yana da iko da mutumin to da ya hana shi irin wannan sana'ar mai wahala zama a kan titi ga uwar wuta a gaban mutum mai cikakkiyar lafiya ma yaya zai ji to ballantana wanda yake da nakasa.
Tunda ta hango motarshi tana zuwa inda suke gabanta ya shiga dukan uku-uku! da sauri tasa gefen hijab dinta ta goge gumin fuskarta tana gyara zaman hijab din gabadaya ba taso ya hango wani nakasu a tare da ita.
Cikin nutsuwa ya sauke gilashin motar da fadin." Malam barka rana." Malam Habu dake aikin gabansa yayi gaggawar dago kansa da yalwatacciyar fara'a a tare dashi yace."Barka dai Nuraddin an fito.''?
Yace."Eh Na fito Malam ya kasuwa.''? Yace."Alhamdulillhi gashi muna ta fama." Yace."To Allah ya taimaka." Ya amsa da "Ameeen ya Allah Nuraddin kai ma Allah yayi maka jagoranci." Ya amsa yana dan kallonta da gefan idonsa.
Sai da ta gyara muryarta tace."Uncle ina kwana." Ya amsa yana kallonta ido cikin ido yace."Zaman me kike ba kije skull ba bayan kuma ga Uniporm a jikinki."
A sanyaye ta kalli mahaifinta. Malam Habu yasa hankici ya goge uban gumin da yake tsinko masa yace." Yanzu nan nake cewa tayi hakuri ta tashi ta koma makaranta ranar litinin za'a biya su hakkinsu."
Yace." Wace makaranta ce."? *Adamu na Ma'aji* dake goron dutse." shuru yayi yana nazari yace."Nawa ne kudin nasu."? Malam Habu shuru yayi dan baya so ya dinga dora masa nauyi.'' Murmushi yayi saboda ya san halinsa yace."Ta koma gida kawai idan na dawo da daddare zan zo za muyi magana.
Malam Habu yace."Aa da cewa nayi yanzu taje da dubu daya ta kaimu musu insha Allahu wani satin sai na cika sauran." Ya dan sosa kanshi da fadin."malam ban tari hanzarin ka ba amma ina neman alfarma a karbi uzuri na."
Malam Habu yace."To babu damuwa Nuraddin yanda ka bukata za'ayi ke Surayya kije gida sai na dawo." Mikewa tayi tana kokarin rataya jaka a kafadarta.
Yace."Malam a tashi lafiya." Yace."To shikkenan Nuraddin sai ka dawo Allah ya tsareka daga sharrin karfe.'' Ya amsa a lokacin da yake kokarin jan motar.
Motar tabi da kallo Malam yace."Tsayuwar me kikeyi ne? kije gida nima ina gama wannan aikin zan shigo na kwanta na huta.
Jiki a mace ta kama hanya tana tafiya salo-salo ita kam Allah ya jarrabeta da abinda yafi karfinta hausawa suka ce son maso wani koshin wahala.
*MAR'ATUS-SALIHA*
_(Itace Cikakkiyar Mace)_
*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu馃懌 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*
1- Maganin Sanyin mara
2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa
4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba
5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa
6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa
7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)
8-Maganin Basir mai tsiro
9-Maganin Basir mai kulle ciki
10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)
*11- Maganin Karin Ni'ima
12- Maganin K'iba mai kyau
13- Maganin Cikar Nono (Breast)
14- Maganin Hips
15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!
16- Maganin Matsi mai kyau
17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba
18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)
19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba
*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*
*****
*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*
Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp
Cikin wani irin yanayi na damuwa ta shiga gidan ta samu Innah na bakace gero kusa da ita zube sai kawai ta fashe da kuka wannan masifa ta isheta.
Innah Habiba ta ajiye fefan hannunta cikin fargaba tace."Ke menene haka babu sallama kawai kin shigo gida kin fashe da kuka.
Rufe fuskarta tayi da hijab ta cigaba da rizgar kuka tana neman daukin Ubangiji a cikin ranta babu shakka soyayyar guy itace ajalinta.
Innah Habiba ta rike hannunta murya na rawa tace."Me akayi miki Surayya wani ne abu ya faru a makarantar."? Shuru tayi ba tace komai ba sai shashshekar kuka takeyi.
Innah Habiba ranta ya baci ta buga matsa tsawa da fadin." Bafa nasan sakarci kin san halina bana daukar shirme ki bude baki ki fada min abinda yake faruwa.
Murya na rawa tace."Wallahi Innah ina tausayawa Babana da ina da yanda zanyi da na hana shi zama a cikin rana yana wannan sana'ar ta wuta."
Innah ta girgiza kanta cikin damuwa tace."Surayya ya za kiyi da ikon Allah kowa akwai hanyar abincinsa ki godewa Allah da ya bawa mahaifinka rai da lafiyar da yake fita ya nemo mana abinda zamu ci ai kowa da inda Allah ya ajiyeshi.
Ajiyar zuciya ta sauke tana girgixa kanta abubuwa da yawa sun taru sunyi mata yawa gashi bata kwanjin da za tayi maganinsu.
Tace." Yau Naga kin dawo da wuri.'' Tace."Sunyi korar kudin makaranta." Innah tace."Ikon Allah ashe har lokaci yayi.'' Tana goge fuskarta tace." Eh Innah wata uku ai kamar yau ne.''
Innah tace."Allah ya kyauta yanzu ya kukayi da malam din.''? Tace." Da har ya dauko dubu daya ya bani yace na kai musu zai cika sauran wani satin sai kuma Uncle Nuraddin yace na dawo gida."
Innah Habiba tace."To Allah yasa alkairi ne sai ki cire kayan makarantar kizo ki siyo mana Man gyada yau burabusko nake so nayi.
Ta 'bata rai da fadin." Nifa ina wallahi bana san cin wannan abin ke kuma baki da abinci sai shi.
Tace."Surayya a yanda kike fingi-fingi irin wannan cimar ce ta dace dake domin ta gina miki jiki amma ke na lura bakya so kinfi ga kayan kwadayi da kwalama."
Shuru tayi tana zumb'ura bakinta Innah tace."Gobe idan Allah ya kaimu sai ayi dambu ko bakya so." Ta'be bakinta tayi tace."Innah ai har gwara shi akan wannan burabuskon." Murmushi kawai tayi tace." Allah dai ya dauke ki ya kaiki gidan hutu da jin dadi sai kiyi abinda kike so.'' Babu kunya ta amsa da ameen ta mike ta nufi daki domin cire kayan makarantar jikinta.
Cikin tsabta ta fito da hijab mai mayafi a jikinta Ta kalleta da murmushi a tare da ita tace."Kwana biyu naga sai girma kike ko dai na kusa samun suriki ne."?
Dariya ta kyalkyale dashi tana boye fuskarta cikin hijab tace."Ke Innah."
Innah Habiba tana murmushi ta mika mata kudin da fadin." Man gyada zuryan zaki siyo gwangwani biyu sai ki siyo kuli-kuli gwangwani d'aya."
Ta kar'bi kudin da fadin.'' To shikkenan Innah sai na dawo." Tana kokarin fita ta kira sunanta ta juyo tana kallonta fuska babu walwala tace."Kada fa ki shiga gidansu Samira nasan halinki." Tace."Ba zan shiga ba ai." Tace." Na dai fada miki idan kika shiga zamu 'bata dake." A sanyaye ta fita daga gidan.......Tasan halin mahaifiyarta mafadaciya ce sam Innah Habiba bata daukar raini ko ga waye tana zaune a matsayinta na talaka bata nema a gurin kowa ba sai a gurin Allah kuma kullum cikin neman na kanta take ko a makota bata yarda wani yaci mutuncinta kullum cikin takatsantsan take.
Aikuwa kafin taje gurin siyo man sai da ta shiga gidansu Samira suka dasa hirar samari kamar yanda suka saba tana murmushi tace."Samira kin san me."? Tace."Sai kin fada.'' Tace." Dazu bayan mu rabu dake naje bakin titi gurin Baba domun kar'bar kudin makaranta kawai sai Uncle Nura yazo gurin a cikin motarsa........Duk abinda ya faru ta fada mata.
Samira ta zabga gud'a da fadin." Wallahi sakon mu ya fara isa gare shi tunda har kika ga yana miki kallon kasan ido kuma yace ki koma gida zai zo su tattauna da Baba to babu shakka sonki yake.
Cikin farin ciki tace."Wallahi Samira lokacin da yake min wannan kallon ji nayi kamar naje na rungumeshi saboda tsabar shauki mtwws guy nan ya tafi da imanina."
Samira ta bata hannu suka tafa tace." Wallahi ai Uncle din ne ya had'u ko wace mace zata so ya zama mallakinta gashi miskili mai aji da nutsuwa ko da yake Surayya kema kyakkyawa ce kawai abinda yayi miki cikas baqi da rama amma dubi hancin ki dogo ga ido da uban gashi sai kace wata 'yar itofia."
A sanyaye tace." Allah ni kuwa bana ganin kyau na da har ina cewa ki sato min irin man bleecing da Ummiyo take shafawa naje na siyo nayi haske ko zai ga kyawuna.
Samira tace."Aikuwa Surayya zaki kyau wallahi nima ina d'an gogawa idan na fakaici idonta sunan man white scret yana da kyau sosai kuma bashi da tsada ki siya ki gwada.''
Tace."Aikuwa zanyi wa Malam Wayo na karbi kudi a hannunsa sai nazo muje ki rakani kasuwa na siyo.''
Tare suka je suka siyo man gyadar a hanyar su ta dawowa suka ci karo da Shahid ya fito zai tafi kasuwa a kan mashing dinsa d'an kasa.........Surayya ta sha kunu tana dauke kanta.
Shi kuwa ganinta duk sai jikinsa ya mutu ya dinga bin ta da wani irin kallo yana lumshe idonsa.
Samira ta tsaya tana masa magana ita kuwa gaba tayi tana zum'bura baki waye kuma Shahid idan da akwai su Uncle a guri
Samira da sauri ta iske inda take tace." Ke Surayya wallahi baki da wayo waye ya fada miki haka ake rayuwar duniya ai ko baka san mutum baka fitowa fili ka nuna masa kawai ki kwantar da kanki gurin Shahid kiyi masa wayo ki samu abinda zaki samu nasan dai Malam ba zaiyi miki auran dole ba to kawai kiyi lufff kici kudin Shahid tunda na lura bashi da wayo.
A sanyaye tace."Samira Idan bana san mutum wallahi abin hannunsa ma bana so shiyasa ki kaga bana sauraran Shahid."
Tace." Eh ai ba nuna masa za kiyi ba kawai dai ni ina baki shawara ne kiyi kwance-kwance kici kudinsa.
Tace."To shikkenan Samira zan duba maganarki." Da wannan hirar suka isa gidan.....Innah ta kallesu tana girgiza kanta abotarsu har mamaki take bata gashi sam ita bata so saboda sanin halin mahaifiyar yarinyar bata da kyau Hajara munafuka ce ga biye-biyen malamai da bokaye.
Samira bata bar gidan ba har sai da Innah ta sauke burabusko ta zuba musu suka ci tare sabida rashin kwaici irin na Samira sai da tambayi Innah wai ta zuba mata wani ta tafi dashi gida daddare za taci....Innah Habiba ta dauko sabuwar silba ta cika mata taf da burabuskon......Samira tayi musu sallama ta tafi gida zuciyarta fes yau da daddare ta huta cin towon dawan gidansu.
_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*****
*****
*BINTA UMAR ABBALE*
*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*