Free chapter · Read without an account
15
Kuka tai sosai har sai da Anty Ummi ta gaji da rarrashinta, sannan tai shiru idonta duk ya kumbura ya canja kala.
“Ina ciki matsala Anty sun kasa fahimtata, nayi nadamar fallasa sirrin nan da nai da ace ban yi haka ba da Anty Rukaiya tana nan a raye da basu cilasta min aurensa, da yanxu ina cikin garin gusau da zama, sai dai naji d abunda Auwal yai min...”
Cikin kuka take magabar, Anty Ummi jikinta duk yayi sanyi, ko Farhat bata fito fili ta fada mata ba, tasan da ita take da ace bata fadawa Anty Rukaiya ba da duk abun be kwabe kamar haka ba. Cikin rashin kuzari Anty Ummi ta kama hannunta ta rike.
“Farhat ki kaddara haka Allah yaso a gareki, maganar Bashir kuma ba zaki taba shiga hannunsa da sunan aure ba matukar yan'uwanki zasu yarda ki auri wani”
“Bani da wanda zan tsaida Anty, na kori kowa saboda Auwal shi kuma ya juya min baya ya canja min, bani da waya ma balle har na kira wani...”
“Baki bukatar kiran kowa Farhat matukar zasu aminta ki auri wani to Zain zai aureki...”
Cike da zarani da firgici ta kalli Anty Ummi baki sake.
“Yes na san baku jutuwa, amman bamu da wata mafita bayan wannan”
“Idan akwai wanda na tsana a duniyar nan kamar mutuwata Zain ne Anty kin sani, shima kuma ya tsaneni, wannan abun ba zai taba yiyuwa ba”
“Ke dai kike tsanenshi, amman shi yana kaunarki, kawai dai halayinki ne baya so wanda nasan shi ma a yanzu ya daina, domin sai da ya zubar da kwalla akan abunda ya sameki, shi ma da kansa yake cewa da ace zaki amince da ya aureki...”
Sanda kanta tai kasa ta hade yawun bakinta, ita kanta tasan wata karya da hankali zai dauka, wannan kam bata shiga ba.
“Bayan shi ba muda wata mafita Farhat, kunma ina ganin ya cancanta ki auri Zain ko dan alakar dake tsakaninmu, sannan kuma Auwal ya gane kuskuren da yai ta hanyar ganin kin aure wanda ya fishi komai, mulki kudi kyau da komai ma”
“Ba zan iya ba Anty ba zan iya auren dan'uwanki ba, nafi tsanarsa fiye da Ya Bashir, idan har na yarda na aureshi shima cutuwa zan yi”
“Ba zaki cutu b Farhat na miki alkawari, kuma indai har na isa dake na kai na rokeke abu kiyi min to ki amince da auren nan saboda da ni!”
Da sauri Farhat ta kalleta tana girgixa kai hawaye na cika idonta.
“Idan har baki amince da auren nan ba Farhat, ba zan sake zuwa garin nan ba, ba zan taba mantawa da wannan butulcin da kika min ba har abada, kuma na rabu da ke kenan!”
Anty Ummi na kaiwa nan ta tashi tsaye ta dauki jakarta tana fadin
“Gobe ko jibi zai zo ganinki idan kin ga dama karki fito, ko kuma ki fada masa baki sonsa sai nasan kin cika yar halak”
Juyawa tai ta fice Farhat ta bita da kallo baki sake tana hawaye.
YARIMA ZAIN POV.
Yana yin parking ya fito cikin bacin rai ya nufi Mr Zain rooms, sai da ya kai dakin da Hafsatu take sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tura kofar ya shiga. Doc Hafsat ya samu tare da ita suna taba waya da alama game ta kunna mata ko kuma wani abun take nuna mata a ciki.
“Ina kwana, Doc Ibrahim ne ya kirani yace na zo naje da Hafsat yayi min bayanin komai, amman sai zuwa anjima idan zan wuce zanje da ita”
A tare ta jeru nasa bayanin, kai kawai ya daga mata ta karbi wayarta dake hannun Hafsatu manga ta fice. Kusa da ita ya zauna ba tare da ya kalleta ba ya fiddo wayarsa ya kira Ibrahim be yi picking ba ya shigo dakin hannunsa rike da wayar tana ringing.
“Miyasa zaka fada mata komai? Ce maka nai ka turo min ita?”
Ibrahim din be amsa masa ba be kuma daina murmushin da yake ba, sai da ya zauna.
“Zain ka cika matsala Wallahi, matukar muna son Hafsat ta rike mana yarinyar nan dole ne mu fada mata gaskiya, beside baka da wani gurin kaita daya wuce can, kasan dai Anty Ummi tace ba zata karbeta ba, ba kuma zaka kaita gidanku ba, ina zaka kaita?”
Iskar dake bakinsa ya busar ya kalli Hafsatu manga wacce ta kwanta saman hannayenta.
“Zain, ina tunanin ya kamata ka amince da bukatar Anty Ummi”
“Ko da hakan na nufin na cutu? Kai ma ka zabi bangareta”
“This is not the right time to take anyone side, kawai ina baka shawara ne ga abunda nake ganin ya dace”
“Auren Farhat kamar salwantar da rayuwata ne Ibrahim and you know it”
“Ita bata salwantar da tata rayuwar akanka ba? Saboda kai aurenta a farin ya mutu? Saboda kai mijinta ya daketa har tai miscarriage, ka manta lokacin da Mai Martaba ya koreka ita ta dauki kaddarar zama da kai, a gabana ta furta cewar dan'uwanta yafi mata mijinta, ya fi mata yayanta kuma rayuwar dan'uwanta tafi mata rayuwar aurenta ko da hakan na nufin karshen rayuwarta ne, dukan abunda zai faranta maka rai Anty Ummi tana kokarin yinsa ko da kuwa ita zai bakanta mata maka rai ne, Anty Ummi da Hameeda su suka fi kowa baka gudummawa a lokacin da aka shiga takaninka da Mai Martaba ko ka manta hakan?
Zain kai da kanka kake fada min kana neman ranar da Anty Ummi zata bukaci wani muhimmin abu kai mata saboda ta san tana da kane kuma dan'uwan da zai iya share mata hawayenta, amman yau kai da kanka kake son zubar hawayenta....? Am totally confused”
Zain yayi saurin mikewa tsaye saboda hawayen da suka cika masa ido ya nufi window yana saka hannayensa aljihu.
“Idan na amince da auren Farhat, nai yaya da Hameeda?”
“Mai Martaba yafi son ka fiye da komai daya mallaka a duniyar nan, zai goya maka baya ka auri matar da kake so, kuma dole na Dada Yalwa da Hameeda su sakar maka marar yin fitsari, dole ne ka zama Namiji Zain, ko za a kada a raya karka yarda ya janye ra'ayinka akan aurenta matukar ka gabatar da ita a gurin Mai Martaba, aurenta saukeki ne a gareka Zain, zaka samu damar zama da Yarinyar nan a cikin gidanka...”
Shiru ne ya biyo baya dakin yai tsif kamar babu kowa a ciki. Zuwa can Zain ya juyo ya kalli Ibrahim.
“Ka tunatar da ni abunda be kamata na manta ba, zan yi komai saboda farincikin yar'uwata kuma uwata...”
Ya karasa yana girgiza kai, sai Ibrahim yai murmushi ya tashi yaje ya dafashi.
“Good, abu na biyu kuma ina son ka amince yarinyar nan ta zauna gurin Hafsat da zarar ka yi auren sai ka maidata hannunka”
Zain ya kalli Hafsatu manga data bata fuska garin lake kafada har munduwar hannunta ta fadi, dan Murmushi ya sakar mata yaje ya dauki munduwar ya kama hannunta zai saka mata sai ya tsaya kallon sunanta dake rubuce. H A F S A T aka rubuta a rarrabe, wani abun mamaki munduwar ta azurfa ce mai tsada irin azurfar nan da sai wane da wane ke sakawa idan ma ba wanda ya sani ba babu wanda zai banbanceta da zinari.
“Waya siya miki wannan abun hannun?”
Ta nuna sama.
“Babanki?”
Ta girgirza kai alamar a a.
“Mamanki?”
Ta gyada masa kai, kama hannun nata yai ya saka mata, fuskarsa da mamaki.
“Wannan azurfar mai tsada ce, anya yarinyar nan yar hudun hijira ce kuwa?”
“Alamunta ya nuna haka, itama kuma haka tace”
“Amman waya taba wannan zinarin haka mai sunanta?”
“Azurfa ce”
“Amman yayi kama da gold, mamanki mai kudi ce?”
Ibrahim ya karasa yana tambayarta, sai ta girgiza masa kai idonta na cika da kwalla.
“Tace mun mahaifiyarta mahaukaciya”
“Amman.... ”
Zain ya daga masa hannu.
“Karka takura mata dan Allah, bata da bakin amsa tambayoyinka a yanzu”
Sai ya kama duka hannayenta biyu ya hada guri daya ya rike yana mata murmushi.
“Mama Doc zata tafi da ke gidansu ki zauna na wani lokaci kamin Anty Ummi ta yarda ki zauna gurinta”
Ta lake kafada tana hawaye, alamar bata yarda ba ita ba zata zauna ba.
“Zata kula da ke sosai kuma duk abunda kike so zata miki, kuma kullum zan dinga zuwa ina dubaki, zan siya miki duk abunda kike so”
Ta kara bata fuska tana ta hawayen dole. Hakan yasa Zain jin babu dadi.
“Kina son madara da nama?”
Ta gyada kai da sauri.
“To zan dinga siya miki kinji?”
Ta sake gyada kai, sai yasa dayan hannunsa ya share mata hawayenta, sannan ya mike tsaye ya kalli Ibrahim.
“Ka fada mata bata bachi ita kadai saboda tana tsoro, kuma idan zata kwanta ana mata addu'a, sannan k tambayeta nawa za a rika biyanta every month or week”
“Wow...”
Cewar Ibrahim yana dariya. Zain be kula shi ba ya fice hannayensa zube a aljihu.
Misalin uku da rabi ya tashi aiki kai tsaye gidan Anty Ummi ya wuce, cikin kuzari ya tura kofar falonsa ya shiga zuciyarsa na mugun bugawa kamar zata fito. Yana shigowa ta juyo ta kalleshi fuskarta da murmushi tana kokarin cire hijabin da ke jikinta.
“Yau kuma an tuna damu dirar rana aka mana”
“Na dauka fushi kike da ni”
Ya fada, bayan ya zauna saman kujera. Sai tai murmushi ta soma nade hijabin tana cewa.
“Akwai wata rana da muka yi fada da kai saboda littafin makarantana da ka yaga, sai na dauki fushi da kai bana maka magana, da Mama ta lura da hakan sai ta kirani ta umarceni da na kama hannunka, sai na kama na rike cikin fushi, sai tace saki fuskarki Amina, karki sake fushi da dan'uwanki komai zai miki kiyi hakuri shi yaro ne, wata rana kuma ke uwarsa ce kinga uwa ai bata fushi da danta, ina son ki so dan'uwanki fiye da komai a duniyar nan, baki samu komai a ko wane lokaci amman ban da mahaifiya da mahaifi da kuma yan'uwa, kuma babu wani abu mai maye gurbinsu har abada!
A lokacin ina da shekara goma, amman Allah ya bani hankalin da ban sake fushi da kai ba, komai zaka min zan kyaleka ko da raina ya bace, idan kuma naga wanda zai taba ka sai inda karfina ya kare, akan wannan turbar nake har yau, ban yi fushi da kai kana karaminka ba ba zan taba fushi da kai yanzu da girmanka ba, ko da nayi fushi da kai na dan lokaci ne idan shaidan ya ribance ni amman ba mai dorewa ba”
Ta kai hannu ta share hawayen idonta, sannan ta tashi tsaye ta nufi hanyar bedroom dinta tana fadin.
“Yau ban je aiki ba, kauye naje kuma ban samu na girka abinci ba, ka hada wani abun ka sha kamin na dora girki”
Tashi Zain yai tsaye ya saka hannayensa aljihu ya ce.
“Idan har auren Farhat na nufin farincikinki na shirya aurenta.... Zan kuma koyi hakurin zama da ita daga yanzu...”
Da sauri Anty Ummi ta juyo ta kalleshi.
Dawowa tai ta zauna tana cigaba da masa kallon mamaki.
“Amman miyasa?”
“Saboda ke Anty, yau idan naje gida zan sanar da Dada da Mai Martaba cewar akwai wacce nake so”
Hannayenta biyu ta daga sama tana yi ma Allah godiya. Shi kuma ya tashi ya fice zuwa gurin motarsa, idan ya tuna saboda Anty Ummi zai yi sai yaji kuzari da son yin haka, ta dayan bangaren kuma yana tunanin irin zamantakewar da zasu yi. Daga Gada biyu zuwa kan wurin sarki tafiyar awa daya yai har da wani abu, saboda yanayin driving din da yake, yana faka motarsa kansa yai mugun sarawa har cikin zuciyarsa, cikin rashin kuzari ya fito daga motar ya nufi part dinsa.
Saman cushion ya zauna ya lumshe idonsa yana maida numfashi a hankali.
“Saboda ke ne kawai”
Ya fada yana bude idonsa. Sai kuma ya tashi ya shiga bedroom dinsa, kayan jikinsa ya cire ya bude drawer ya dauki tawul ya daura ya shiga bathroom, yana shiga ya raba jikinsa da tawul din ya kunna shower yai tsaye ruwan na dukan kansa, sai kuma ya juya ya jingina hannayensa jikin tile din ya rufe idonsa.
Ya samu kusan minti talati a haka, sai da yaji kiran sallah la'asar a masallacin dake cikin fadar sannan yai wanka ya fito a gagauce ya shirya ya fita domin baya son ya rasa jam'i. Bayan ya sauke farilla ne ya shiga part din Dada dan ci abinci duk kuwa a kasancewar an kai masa nasa a part dinsa.
A falo ya sameta zaune daya daga cikin bayin gidan tana matsa mata kafafunta, dayar kuma tana bare mata ayaba.
Yana shigowa dakin duk suka sanda kansu kasa domin su kansu sun san kallo na daya daga cikin abunda Yarima Zain ya tsana, kusa hada baki su kai gurin gaisheshi muryarsu har rawa take, ba azabtar da su yake ba, amman yana musu kwarjin da ko motsi yai sai sunji kamar numfashinsu zai dauke. A kujerar dake facing dinta ya zauna yana gaishe fuskarsa cike da annashuwa kamar da gaske farincikin ne har cikin ransa.
“Dada sannu da gida”
“Wannan farincikin na minene? Da har tasa kai mana dawowar rana a yau?”
Ya fadada fuskarsa da murmushi.
“Na wani albishir ne mai girma wanda kuka dade kuna jira, ke kawo min abinci”
Ya karasa yana kallon mai bare mata ayabar. Jiki na rawa ta tashi ta nufi inda dinning din Dada yake, Dada kuma tai dariyar daya bayyana hakoranta biyu na maka tace
“Labarta min naji, indai mai dadin ji ne kana da babba goro...”
Dagowa yai har zai yi magana sai Abida ta shigo fuskarta cike da damuwa sai da ta fara zubewa kasa ta gaishe da Zain sannan ta fadi gaban Dada ta kwashi gaisuwa, sai kuma ta zauna gaban Dada fuskarta kamar zata fasa kuka.
“Akwai wata magana ne...”
Dada ta tambaya tana kallon yanayinta. Murzar hannunta take kamin ta soma magana kamar da tsoro.
“Allah ya taimakeki, Gimbiya Hameeda tana daki tun jiya bata fito ba, ta kuma min gargadi da kar na kuskura na shiga dakinta har sai ta bukaci hakan”
“Bata da lafiya ne?”
Dada ta tambaya cike da kulawa.
“Allah ya kara miki nisan kwana, nima ban sani ba”
“Jeko bude dakin”
“Ta hanene ranki ya dade idan har na bude zata iya min mugun wulakanci...”
Tashi Zain yai ya fice daga falon, kai tsaye part din sisters dinsa ya nufa wanda a cikin dakunan ne Hameeda take da nata. Yana isa ya tura kofar dakinta ya shiga.
Tsaye yai cak sakamakon arba da idanuwansa suka yi da kayan mayen dake saman gadon Hameeda, ita kuma tana gefe daya ta makure guri daya ta hana ta sharar bachinta. Kallon kayan maye kawai yake yana mamakin inda ta samo su, yaushe ta fara shaye-shaye?
Karasawa yai kusa da gadon ya dauki kwalbar yana dubawa, fuskarsa cike da damuwa da kuma mamaki. Kara matsawa yai ya kai hannunsa yana tashinta, firgigit ta bude ido ta tashi zaune tana kallonsa idonta a juye kwalli duk ya bata ido ya dararo har saman kumatunta.
Zuwa can kuma ta zabura tana kokarin rufe bakinta, hakan ya tabbatar masa da cewar sai a yanzu ta gane shi kenan.
“Waya baki wannan?”
Tai shiru sai rabon ido take kamar munafuka.
“Answer me....!”
Tsawar daya daka mata ne yasa tai saurin sauka daga kan gadon ta koma can gefe, sai kuma ta nufo kofar ta kulle.
“Doc.. Doc... Ne... Ya bani.. Shi.. ”
Ta fada muryarta na gargada, ido Zain ya kura masa yana karantar gaskiyarta, ita kuma ta kasa daga kai ta kalleshi, sai wani munafukin numfashi take dan kawai ya jita.
“I and Doc Hashim ne kawai Mai Martaba ya yarda su duba iyalansa? Shi ya rubuta miki wannan? I will call him”
Yana juyawa, sai tai saurin faduwa kasa ta rike masa kafa tana kuka.
“Dan Allah karka kira shi, ka rufa min asiri karka fadawa kowa”
“Waya baki? Yaushe kika fara shaye-shaye?”
Dago kanta tai ta kalleshi.
“Ni na siya, bana samun bachi ne shine ya iya ina sha dan na riga bachi”
“Mi kika rasa da har zai sa ki rika shayeshaye? Kin san halin da Dada zata shiga idan taji wannan labarin? Mai kike tunani zai faru idan na sanar da Mai Martaba?”
Tashi tai tsaye ta nufin gurin window ta tana hawaye.
“Na rasa komai, da fari Mahaifiyata ,mahaifina, sai kuma yayata, daman tuntuni na dade da rasaka, ba ni da wanda zai saurareni ya bani shawara akan wasu abubuwan, ba ni da kowa na rasa kowa, ada kana saurarena kana bani shawara akan wasu abubuwan ina maka kallon dan'uwa kuma abokin fira, yayata ma tana nan tana fada min gaskiya, amman bana gani sai a yanzu dana rasata nake gani nayi rashin da ba zan taba maye gurbinsa ba har a bada,
Ba zan taba yafewa kaina ba, na musgunawa Haleema, tayi ta bani shawara amman ban dauka ba, yanzu na rasa ta na rasa kowa, Dada ba komai take fahimta ba, na koma ni kadai ba ni da kowa...”
Ta zube masa tana wani irin kuka mai taba zuciyata tare da zubewa kasa ta rike lalulayen window da karfin gaske. Zain ya hade yawun dake bakinsa zuciyarsa na sosuwa da kalamanta.
“Ki tattara duk wani abun maye nan ki dora saman gadon nan, otherwise na fadawa Mai Martaba... Lastly wash your face ki zo falo Dada na nemanki”
Yana kawai nan ya juya ya fice. Part din Dada ya dawo ya zauna inda a gurin daya zauna dazu.
“Lafiya take?”
“Kanta ke dan ciwo sai kuma jiri, amman zata fito yanzu”
Ya fada yana misalta irin yanayin da Dada zata shiga idan har taji Hameeda tana shaye-shaye.
“Bari naje na dubata”
Tana kokarin tashi tsaye sai yai saurin dakatarda ita.
“No Dada gata nan fitowa”
Sai kuma ya kalli Abida.
“Abida akwai abu a kan gadon Hameeda jeki kwashe min komai kisa a leda ki kai min dakina”
“An gama ranka ya dade”
Ta tashi da sauri ta fice daga dakin. Hannu ya kai ya bude plate din da aka aje masa abinci sai kuma yaji ba zai iya ci ba, Hameeda ta tsaya masa a rai, zuciyarsa nata raya masa ita din abar tausayi dukan abunda ta fada gaskiya ne tana da bukatar wani kusa da ita, yasan yanayin gidansu sisters dinsa duk ji suke da kansu ko kuma ko wacce da mahaifiyarta a gidan, ita kadaice sai ragowar wadanda ake riko ne basa da iyaye a gidan, amman a waje suna da iyaye amman ita fa? Ba uwa ba uba, gashi ta tashi a hannun Dada bata saba da kowa ba sai shi da Dada da kuma Haleema duk da kasancewar ita Haleema ba a gidan take ba.
Sallamarsa ce tasa ya dago ya kalli kofar, wata tafiya take daidai hijab din dake jikinta na kokarin tadeta ta fadi kanta a kasa ta zauna kusa da Dada.
“Muhammad yace kanki na ciwo”
Dada ta fada tana shafa kanta cike da tausayinta da kuma kulawa.
“Ee ina son bachi ne”
“Aa idan Muhammad ba zai dubaki ba, sai a kira Doc Hashimu ya dubaki”
Sai Zain yai karaf yace.
“Na bata magani.”
Daga Dada har ita Hameeda din kallonsa suka yi, sai kuma Hameeda ta maida kanta kasa tana fadin
“Ee ya bani magani, shiyasa nake son na kwanta”
“To je ki kwanta Allah baki lafiya”
Sai da ta amsa da amin sannan ta tashi ta fice, Zain ya bita da kallo zuciyarsa nata raya masa abubuwa.
*** *** ***
Around 4pm Doc Hafsat ta isa gida tare da takwararta Hafsatu manga, da fari Hafsatu tai kafuwar kin shiga gidan har sai da Doc ta lallabata sannan ta yarda ta shiga shima dan ta rike rigar da Doc Hafsat take sanye da ita.
“Assalamu Alaikum ga bakuwa.... ”
Doc Hafsat na saka kafarta cikin falon ta fadi haka cike da annashuwa, daman ta sanar da su tun lokacin da Ibrahim ya sanar da ita. Sai Momy ta amsa mata da far'ah tana taba hannayenta.
“Lalle marhabun da bakuwar gidanmu.. Maraba da ke”
Dukansu fuskarsu a sake take, daga Momy har Auwal da kuma Sapna. Kusa da Yayanta Auwal Doc Hafsat ta zauna tana fadin.
“Amman fa bakuwar tsoron mutane take”
Auwal ya kai hannu zai rikata sai tai saurin shigewa jikin Hafsat, amman hakan be hanashi fisgota ba.
“Indai tsoron mutane kike kin shiga uku da ni, fada min inda na sanki dan ni nasan na taba ganin wannan fuskar”
Ya fada yana lasa hancinsa, buge masa hannu tai tana murguda masa baki.
“Really ashe dai kema yar duniya ce”
Sai duk suka sa dariya har Momy, ita kuma tai saurin rufe fuskarta wai taji kunya. Hannunsa yasa ya janye mata nata hannun daga fuskarta yana kokawar rabata da katon Hijab din dake jikinta, a dayan bangaren kuma yana ta kokarin tuna inda ya san fuskarta.
“I remember, ki ce na kade ranar nan, ga fuskarki nan, a lokacin ina sauri zanje aiki kuma na bi ta gidansu Farhat”
“Au ita ce?”
Cewar Momy.
“Yeah amman yau ta min kyau sosai kamar ba ita ba”
“Ai dole tai kyau Doc Zain fa yake kula da ita”
Hafsat ta fada tana dariya.
“Amman kin san shegen doctor nan ya sha da ni, assume as I'm ace kamarsa ya tsaya yana katsa min tsawa ban rama ba, i tot wani yayanta ne ko jininta that time i was very stupid da ban rama ba Wallahi”
“Kai dan sarki ne fa, kuma asibitinsa ce”
“Dan sarki? Like seriously? Ina ruwana da sarautarsa idan sarautar yake takama da ita mu kuma muna takama da kudi da kuma mulki, fada min akwai uban daya isa ya takani?”
“No amman Dsp ai komai da muhallinsa”
“Yeah amman ya shamace ni da yawa”
Sapna ta kalleshi
“Ni fa ban gane kan maganar ka ba”
Sai ya labarta musu abunda ya faru bayan ya kadeta, domin acan farko ya fada musu cewar ya kade wata amman be fada musu yadda abun ya faru ba.
“Wata kila kadewar da ka mata ne ya haddasa bata magana”
“What”
Ya fada yana kallon Doc Hafsat.
“Yes aiki aka mata a halshenta be fada min dalilin jumuwanta ba, amman baya rasa nasaba sa wannan kuma har yanzu bata magana idan tana son abu sai dai ta nuna, gashi ba a san inda kowa nata yake ba”
“Ayyah”
Momy ta fada cikin tausayawa. Auwal kuma ya kalli Hafsatu manga cike da tausayi ya aje Hijab din dake hannunsa sama kujera ya daga ta ya zaunar saman kafafunsa.
“Am sorry dear it wasn't intentionally”
Har ga Allah tausayinta duk ya rufe shi, musamman da yaji shine dalilin rashin maganarta.
FARHAT POV.
Kana ganin yadda take tafiya kasan dole aka mata, fuskarta kamar bakin hadari babu annuri ko kadan a tare da ita. Tana zuwa ta juya masa baya.
Shi kuma sai yai murmushi ya sauke hannayensa ya ce.
“Ki kwantar da hankalinki Farhat ni ba zan miki dole ba, ko can baya ni ban nemi a hada aurena da ke ba, iyayenki ne suka ga dacewar hakan shiyasa suka gabatar min da ke ni kuma ba zan iya musa musu ba saboda yarana suma ina son su samu farinciki”
Yayi Shiru tare da sauke ajiyar zuciya sai kuma ya cigaba.
“Na zo ne kawai dan na fada miki, ko kuma na baki shawara, idan akwai wanda kike so ki fito da shi kamin lokacin da aka dibar miki ya cika, no ba zan cilasta miki zama da ni ba, amman karya nake na ce bana son ki Farhat, son ki ne ya jani na kasa hakura har na kusa fadawa halaka, abunda ban aikata a waje ba nai unkurin aikata shi a cikin gidana, da ace na san da zuwan wannan ranar da ban furta wata kalma a gareki ba, kuma da nasan hakan zai yi silar mutuwar Rukaiya da ban furtata ba ko da kuwa hakan na nufin ajalina ne... Nayi nadamar abunda nai....”
Wani banza tsaki ta buga masa ta juyo ta dawo cikin gida ta barshi can waje.