Free chapter · Read without an account

18

by Khadeeja Candy · HAFSATU MANGA (Yarinyar Kauye)

Daga ita har shi a bathroom din suka kwana, shi yana zaune ita kuma ta jingina masa kamar matacciya. 

Sautin kiran sallah dake cikin fadar ne ya farka da su, shi ya fara bude idonsa dake cike da nauyin bachi, sannan itama ta soma motsawa tana jin jikinta babu karfi ko kadan. 


“Daga ni”


Ta fada tana wani bata fuska ita ala dole ya taba ta, tana dukan shoulder dinsa, kallonta kawai yai be ce mata komai ba har sai da ta lura da ita ce tana kwance a kirjinsa sannan tai hanzarin tashi sai kuma ta kasa saboda babu karfi a jikinta. 

Da kansa ya daga sannan shi ma ya tashi tsaye, da kansa rika kokarin rabata da tufafin dake jikinta, amman ta hana sai kokarin kokuwa take da shi.


“Ka bari bana bana so”


“Fine idan na dawo baki yi wanka ba, barori zansa su miki”


Be jira komai ba ya juya ta fita. Ta dade a zaune kamin ta samu karfin cire tufafin jikinta ta kunna shower. 

 Bayan ta gama tai alwala sai ta dauki tawul din dake gurin ta daura, ta saba fitowa a haka gida bata jin komai dan an ganta da kananan kaya ko kuma tawul kawai, but this time around tana jin nauyi sosai ta fita haka Zain ya ganta. 

Rasa tai yadda zata yi, ba zata iya maida kayan ba domin tana jin kyamarsu.


“Ka kawo min kayana”


Ta fada muryarta a dakishe, shiru be amsa mata ba, daman ta san ai ba zai amsa ba ko da wata dince ba ita ba balle ma ita ce, bude kofar tai a hankali ta leka dakin sai ta hango babu kowa, hakan yasa ta fito da sauri ta nufi wardrobe ta bude, gaba daya kayansa ne a ciki bubu nata ko daya, taya ma zata samu nata a ciki bayan ba a zo mata da komai daga gidansu ba. 

Jallabiyarsa ta dauka ta saka, duk kuwa da irin abunda zuciyarta ke raya mata matukar yaga ta saka kayansa sai ya kusa kasheta. 

A baki gado ta zauna tana kallon kofa kamar mai jiran shigowarsa. 


Thirty minutes later ya shigo dakin, tana ganinsa tai saurin tashi tsaye tana mursa yatsun hannunta. 


“Ban ga kayana ba, kuma ban yi sallah ba”


Ta fada tun be tambayeta ba, and ta manta tace masa bata sallah, tsayawa yai kallonta from head to toe she's mad, haka zuciyarsa take raya masa, ita kuma ta kasa daga kai ta kalleshi sai hawaye ya sauko mata, all what her heart keep telling her zai fada mata wata maganar marar dadi ko ya mareta. 


“Ga dakinki can nan dakina ne”


Dagowa tai ta kalleshi sai kuma tai saurin maida kanta kasa, kamar dai bata ji abunda yace ba ta cigaba da tsayuwa a gurin, har sai da ya karasa inda take ya dauki wayarsa ya fice. 

 Sannan ta fito daga dakin tana takawa a hankali kamar marar gaskiya, hagu ta fara dubawa sai ta hango dakuna biyu jere, mai bima nasa a bude yake yayinda dayan kuma yake a rufe, tana leka dakin sai ta dawo tayi tsammani ko yana ciki, sai ta nufin dayan dakin na uku tana tabawa taji kofar rufe da makulli, komawa tai dayan dakin data baro ta shiga. And the room is wow everything is perfect, duk da hankalinta baya jikinta a yanzu tasan an narka dukiya a dakin, kai tsaye wardrobe ta nufa tana bude taga an jera kaya daga sama har kasa. Bata tsaya choosing ba dan bata da damar wannan a yanzu, hannu kawai tasa ta janyo atamfar dake sama tana warwarewa tana gown. Sakawa tai sannan ta sake bude dayan bangaren babu komai sai veils. Mai dan kwauri ta dauka ta rufe kanta da shi, tsayawa tai tunanin gabas sai ta tuna inda taga yana kallon daya sallah nafila jiya. Tana kallon gurin ta hango Hijab da Carpet an aje mata saman kujerar dake gurin. Karasa tai ta dauka ta saka ta shimfida carpet din tai sallah sannan ta haye gado ta kwanta. 


“Farhat”


Can cikin bachi taji kiran amman hakan be hanata amsawa ba, dan tasan mai kiran zai iya mata komai idan taki amsawa. Saukowa tai daga kan gadon ta fito, sai ta hango plasma kunne tana aikinta shi kuma yana zaune saman cushion ya saka tv a gaba kamar ba shi yai kiran ba hannunsa rike da kofin ruwa. Hakan yasa ta sauko downstairs ta zo har inda yake zaune ta risina a kasa. 


Da ido ya nuna mata tea dake gurin, sai ta dauka ta sauri ta shanye gaba daya, kamar yace dole sai ta shanye, sannan sake kallonsa. 


“Na shanye”


Sai ya kalli maganin dake saman karamin plate kusan kala hudu, alamar ta dauka ta sha kenan. 


“Ni bana shan maga...”


Bata karasa ta dauki ganin ta zuba a baki ta rika taunawa sakamakon kallonta da yai, ba tare da ta jira ya bata ruwa ba haka ta rika taunawa tana hadewa. Yanzu kam he believe Farhat is completely mad, ba zai iya mika mata kofin ruwan dake hannunsa ba, dan haka ya aje kofin saman center table dake kusa da shi, sai ta dauka ta sha idonta na cika da kwalla. 


“Me kika ci?”


“Na sha tea sai na ci magani da ruwa”


“You fool me kika ci nace?”


“Ban ci komai ba, kayan suna nan dakinka”


Ta dauka kazar amarci yake magana wacce ta tarar a dakin jiya. 


“In na sake tambayarki kika min shirme sai na buga kanki da wannan table din”


Ya fada a tsawace yana nuna center table na gilas dake gefensa. 


“To ina ruwanka da abunda na ci, ka kyale ni mana”


Itama ta fada a fusace hawaye na sauka a idonta, tashi tai tsaye da zimmar komawa dakinta sai ta riko hannunta da karfi ya fisgota ta fado saman cushion din sai ya matse mata baki, babu irin karfin da bata sa ba amman ta kasa banbanre hannunsa daga kumatunta sai kuka take. 


“Me kika ci jiya?”


“Sinasir da miya”


Ta fada a wahalce, sannan ya saketa ta zauna dai dai yana aika mata wata tambayar. 


“Shi kadai kika ci?”


“Ee gidanmu ban ci komai ba, sai da na zo nan wata mai aikinku ta kawo min sinasir”


“Zaki iya ganeta idan kin ganta?”


“Ban sani ba, bakin mugu kawai, wai ina ruwanka da ni miyasa kake takura min ne? Ni ma mata ce ba baiwa ba but you treat me badly”


“No i didn't but surely i will... And what did you just call me mugu ko? Zaki san mugu soon”


Tashi tai ta nufi dakinta tana kuka.

Wayarsa ya dauka ya aikawa Abida sako, in few minutes tai knocked kofar falon. Bayan wani dan lokaci ta turo kofar ta shigo tasan in zata daummawa a gurin ba zai ce mata ta shigoba, gabansa ta zube tana kwasar gaisuwa.


“Kina tare da Farhat jiya ko?”


Damm taji gabanta ya fadi, tasan wa yake nufi.


“Ee mu muka tarbeta ranka ya dade”


“Waya kawo abincin data ci?”


“Falmo ce da Baba Laraba”


“Je ki kirasu”


Ta tashi ta sauri ta fice, gabata sai faduwa yake. Bata dade ba ta dawo tare da Falmo da kuma Baba Laraba duk suka zube kasa sua kwashi gaisuwa. 


“Waya kai abincin da Farhat ta ci jiya”


“Mu muka kai Ranka ya dade”


Hada baki suka yi gurin amsa masa 


“Gurin wa kuka karbo abincin?”


“Gurin Gimbiya Hameeda...”


Yayi shiru na dan wani lokaci. 


“Ita ta girka?”


“Aa Allah ya taimakeka Hajiya Hadiza ce ta girka”


“Taya aka yi kika sani?”


“Ni zan girka sai tace a bari tai ma surukarta girki da kanta”


“Shinkenan...”


Sai suka tashi suka fice da sauri idon Abida har ya cika da kwalla. He hold his phone again ya turawa Hameeda sako cewar yana nemanta. Ba bata lokaci sai gata ta shigo falon, for the first time after mutuwar yar'uwarta Zain ya kirata da kansa part dinsa. 


“Me kika saka a abinci da Hajiya ta girka na Farhat...?”


Ya fada be ko kalli inda take tahowarba, tsaya tai cak ta kasa karasawa a gurin tana kallonsa kamar an dasata a gurin, tambayar ta zo mata unexpected haka taji abun kamar sauka aradu kanta yai mugun tsawara, anya shine Zain din da yake fada mata zai zame mata fiye da da kuwa? 


“Answer me...!”


Ya katsa mata tsawa har sai da ta razana. 


“Ban gane ba ban fahimci me kake magana akai ba?” 


Ta tambaya muryarta na rawa hawayena na sauko mata. Sai a lokacin ya juyo ya kalleta tare da tashi tsaye ya nufi inda ta tsaya din. 


“You hear me, abunda kika sawa Haleema shi kika sakawa Farhat ko?”


“What do you mean?”


“I mean you kill my wife and now Farhat right? Ke kadai kika girka ma Haleema nama ta ci a daren da za a kawo ta gidan nan she told me kuma ana kawota ta rika aman jini babu asibitin da ban kaita ba amman aka rasa gano ciwonta time to time take ciwon ciki tana wannan aman shi yai silar rasa jaririn cikinta at the end ita ma ta mutu, and yanzu kin karbo abinci daga hannu Hajiya kin saka wannan abun a abinci Farhat ta ci ta fara aman jini, so lemme tell you something idan Matata ta mutu Wallahi kema sai kin mutu....”


Baya baya tai ta rufe bakinta tana hawaye, sai kuma ta juya da gudu ta fice daga falon, da kuka ta fito daga part dinsa ta nufi part din Dada Yalwa, tana shiga ta fadi kasa tana kuka kamar za a cire mata rai, cikin tashin hankali Dada ta fito daga dakinta ta nufo inda Hameeda take tana tambayar ba'asi. 


“Ke miya faru? Waya mutu?”


“Nayi nadamar haihuwata da akayi Dada, na yi nadamar zaman da nai a cikin gidan nan, bani da sauran gata da ina da shi da Yarima be wulakanta ni ba”


“Me ya miki?”


Ta riko hannayen Dada tana wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya. 


“Ya ce nina kashe Haleema yar uwata ta jini Dada Yarima ya ce ni na kasheta, yanzu kuma ina son na kashe masa Farhat”


“Me? Muhammad yana cikin hayyacinsa kuwa? Wane irin hauka ne wannan”


A nan Hameeda ta labarta mata komai daya faru, Dada ta kama hannun Hameeda suka nufi part din Zain da ita, tana shiga ta haushi da masifa. 


“Ai daman na san ba banza aka barka ba, idan ba asiriba taya zaka lakewa yarinya kamar wannan, abun be yi mata hakan ba sai ta kara maka da na kan gado wato ka bi ka haukace daga tashi da safe sai fara hatsaniya da Hameeda ko? An shigo cikin gida a rabaka da danginka ko”


Hayaniyar Dada ce ta fito da Farhat daga dakinta sai ta tsaya downstairs tana kallonsu. 


“Ke kuma munafuka ke kika kitsa masa cewar Hameeda ta saka miki wani abu a abinci ko, wato ki hadashi da yar'uwarsa, ai daman na san Ummi ba zata bar masarautar nan ta zauna lafiya ba, ta dauko bakin halin ubanta”


“Ya isa haka Dada ki daina fadar maganganun marasa kyau akan yar'uwata, abunda kuma na fada haka yake ita ce ta saka wani abu a abinci, so take ta kashe Farhat kamar yadda ta kashe Haleema and this around ba zaki tsalleke ba bana.... ”


Tasss Dada ta sauke masa mari a fuska abunda bata taba ba, ta fashe da kuka. 


“Ba kai ba ne Zain, baka tsaba daga muryarka haka kai magana ba, tunda Haleema ta mutu baka dorawa kowa laifi amman yanzu zuwan wannan yarinyar Hameeda? Na san baka samun jutuwa da Hameeda amman taya Hameeda zata kashe yar'uwarta, idan har zargi zaka yi sai ka zargi Hajiya Hadiza tunda ita ta dafa abincin ko kuma ka zargi wasu dabam amman ba Hameeda ba...”


“Ba laifin kowa bane...”


Farhat ta fada daga upstairs din da take tsaye tana kallonsu, sai duk suka daga kai suna kallon yadda take saukowa tana magaba. 


“Amman jinin da nake ba laifin kowa bane, ina da Ulcer mai tsanani wacce take sakani aman jini idan na wuni ban ci abinci ba, jiya kuma haka na wuni ban ci komai ba sai da aka kawo min sinasir da miya miyar kuma tana da yaji, wannan ne ya haddasa min aman jinin dana kawana ina yi jiya da dare, amman babu abunda aka sakawa abinci, Be tambayani kuma hankalinsa ya tashi shiyasa yai zargin ko wani abu aka sawa abinci, da ace ya tambayi dalilin aman jinin nawa da duk haka be faru ba, dan Allah kuyi hakuri”


Ta karasa maganar tana hade hannayenta yayinda ta tsaya daidai inda Zain yake tsaye yana kallonta. 


“Anki ayi hakuri munafuka, kai yanzu baka ji kunya ba? Gashi nan ta fada maka dalilin aman amman ka dauka ka ce Hameeda ce, to ka jira abunda zai biyo baya”


Tana kaiwa nan ta sake jan hannun Hameeda dake kuka har lokacin suka fice. Zain couldn't talk, saboda Farhat tayi embarrassing dinsa gaban Dada bayan kuma yasan haka shine gaskiya, he is straight forward hakan yasa baya iya boye abubuwa, and what he told Hameeda he mean it from the bottom of his heart. 

But why Farhat tai haka? Saboda kawai ta kunyata shi? Oh yes tayi ne dan ta bashi kunya, haka zuciyarsa ke raya masa. 

Yana kallonta sai ta juya da sauri ta haye stairs. Zaunawa yai dai kuma ya tashi ji yai duk gidan ya fita ransa, hakan yasa ya koma dakinsa ya dauki keys dinsa ya fice daga gidan. 


Gidan Anty Ummi ya nufa cikin mugun bacin rai, be san gurin da zaije ba a yanzu kayan gidan Anty Ummi. In few minutes ya isa saboda gudun da yake. 

Yana taba kofar yaji ta rufe alamar basu tashi ba kenan kasancewar yau weekend, knocked yai bayan kamar minti biyu Anty Ummi ta bude kofar tana sanye da kayan bachin. 


“Zain... Lafiya dai”


Be amsa ta ba har sai da ya zauna.


“Lafiya kalau”


“Aa ba lafiya ba, lafiya za a kai maka amarya jiya jiya ka fita da sassafen nan bayan kuma yau weekend?”


“Anty me zan mata?”


“Kamar ya me zaka mata what kind of rubbish is this”


“Mama na zo gani, ko zuciyata ta yi sanyi”


“Gata can”


Ta fada tana nuna masa inda take cike da jin haushi. Hangota yai can rabe jikin kujera ta takure kanta tana ta bachi.


“Haba Anty? Ji inda kika aje fa”


“Ta aje kanta dai, daga dakin su Amal ta dawo nan saboda sunyi fada na mata magana, shine tai fushi”


“Amman Anty idan Amal ce sai kinzo kin lallabata ta kwanta ko kuma ki dauko wani abun ki rufeta, miyasa ita kika kyaleta ta”


“Amal ka ce Zain Amal is my biological daughter”


“That's it that's it, Amal da wannan yarinyar duk daya suke a guna, idan yarki ce ake yi mta haka wani gurin ya zakaji? Farinciki? Sannan Amal ma bata wuce ta shiga halin da wannan yarinyar ta shiga ba, amman wannan abun da kike be dace ba, kuma ban jidadi ba”


Ya karasa a fusace sannan ya tashi ya doshi inda take kwance kasan tile, ya kai hannu ya taba sai ta farka a firgice. Hawaye ya bushe mata a fuska zaunawa yai a gurin ya maida saman jikinsa. 


“Mama”


“Uhmm ni bana son wacan matar ita da yarta, bana son su bana son zama nan”


Ta fada tana nuna Anty Ummi dake kallonsu.


“Miyasa”


“Tana min fada idan na dukar mata ya, kuma ita Ammal din ita take tsokana na, ni na gaji da nan ka kaini garin mu gurin Inna Ladi da Mamana”


Ta karasa tana fashewa da kuka. Wani irin tausayinta ne ya rufe shi, rumgumeta yai yana rarrashinta.


“Shiiiiiiiii zan kaiki gida amman ba yanzu ba, kina son muje yawu dake anjima ko?”


Ta gyada kai


“Zanje da ke yawo na siya miki ice cream da madara da chocolate kinji”


Ta gyada kai daga saman kafadarsa data kwantar da kanta. Anty Ummi ta tashi tsaye taba fadin


“Kana bani mamaki Zain, ka baro matarka ka zo nan kana lallaba wata”


“Karamar yarinyace wannan”


“Haka ne, na gani ai”


Daga haka ta shige dakinta. Shi kuma tashi tsaye ya kama hannun suka nufi kitchen, da kansa ya dafa mata indomie, sai surutu take masa labarin garinsu da kuma na Anty Ummi kamar be santa ba, wani gurin yai murmushi wani kuma har da yar dariya. Bayan sun gama suka dawo falo. Plate biyu ne nata daban nasa daban amman sai ta canja ta dauki nasa ganin nasa yafi nata yawa. 


“Sai kin cinye shi”


He said with funny face. 


“Kai ma sai ka cinye shi”


“Ai ni zan iya ai”


Tayi dariya. 


“Uncle”


Ta kirashi da sunan dasu Amal suke kiransa da shi kuma sunan da Anty Ummi ta fada mata ta kiranshi da shi. 


“Uhmm Mamana”


“Miyasa kai baka kwana a nan gidan?”


“Gidanmu nake kwana, nan ai gidan Antyna ne”


“Ina ne gidanku?”


“Wani guri ne can ciki gari”


“Zaka tafi da ni yau ko?”


Yayi shiru be ce mata komai ba, sai ta cire fork din dake cikin indomie dan har yau har gobe taki ta saba da cin da fork duk da irin kokarin da Anty Ummi take na koya mata. 


“Wannan na Mamana ne”


Ta kai loma daya a bakinta. 


“Wannan na Babana ne, wannan na Inna Ladi ne, wannan na laure ne, wannan na Anty Ummi ne, wannan na Amal ne....”


Haka tai ta jera lomomi har ta kai gareshi.


“Wannan naka ne, na ci maka kai ma”


Ta fada tana dariya, shi ma dariyar yai yana kallonta cike da burgewa. 


“Mama ina Babanki yake?”


“Nima ban sani ba, ban taba ganinsa ba mamana kuma mahaukaciya ce”


Indomie sa ya diba ya kai mata a baki ta karba ta cinye. Ido ya kura mata har ga Allah tana bashi tausayi. 


“Zain tashi ka koma gurin matarka”


Kamar daga sama ya jiyo muryar Anty Ummi. Tana fadar hakan ya wuce kitchen. Tashi yai tsaye yana fadin. 


“Kije ki wanke hannunki anjima zan kaiki yawo”


“Tau”


Ta nufi kitchen din da sauri shi kuma ya juya ya fice. Tana aje plate din Anty Ummi ta kalleta ta ce


“Je ki yi wanka fita zamu yi”


“Ina zamu je? Uncle ma yace zai fita da ni”


“Wani gurin zan kaiki inda za a kaiki garinku”


Duk da son da Hafsatu manga na zuwa gida sai ta ji babu dadi, kamar zata fasa kuka ta fito daga kitchen din. 


A harabar gidan ya hadu da mijin Anty Ummi suka gaisa har yana zolayarsa wai ango. A maimakon ya wuce gidan kamar Anty Ummi ta bukata sai ya wuce gurin abokinsa Ibrahim. 

 A wajen gidan ya tsaya ya kira shi a waya, ya sanar masa yana bikin gate 


“Ka shigo mana”


“Dan Allah ka fito kawai”


Ya kashe wayar. Ba a dauki lokaci ba sai ga Ibrahim ya fito fuskarta shimfide da murmushi. 


“Ango Ango Ango ka sha mai”


“Ka fara ko? Kasan bana son haka ai”


“Ko baka so ai dole muyi mana, miya fitar da kai da safen nan haka kana angon jiya jiya”


Tsaki Zain yaja kamin ya bijiro masa da maganar abunda ya faru a yau. Ibrahim was shocked a yadda yake tunani Hameeda zata iya aikata haka, but baya son ya furta wani abu akan abunda ya shafi family Zain.


“Amman kana da tabbacin Hameeda ce ta aikata haka?”


“Ban sani ba, amman alamu ya nuna haka kuma a yadda Hameeda take zata iya”


“It could be possible tunda ita ta girkawa Haleema abinci kuma abincin da Farhat ta ci ya kai hannunta, amman be kamata kai magana da ita hakan nan kai tsaye ba, wani lokacin kana abu kamar ba kai ba, a yadda kake fitowa kao tsaye kana fadawa mutane ko nuna abunda yake ranka wani amfani zai yi da wannan damar ya cutar kai, baka da tabbacin ita ta aikata hakan ko ba ita ba, and wannan abinci Hajiya ma ta girka you shouldn't talk to her”


“Hakan da nai zai tsoratata idan ma akwai hannunta a ciki, but na gaji Ibrahim yarinyar nan tana cutarda ni ta karkashin kasa, duk wani fada da muke da Dada ko Mai Martaba akanta ne, a yadda ta tsani Haleema zata iya mata wani abun makamancin wannan, i tot ta canja shiyasa na saketa na sake jiki da ita”


“Amman kai da baka son Farhat miye na damuwa idan ta mutu”


Cewar Ibrahim yana dariya. 


“Rayuwa ake magana a nan ba so ba, and tana karkashin kulawata a yanzu dukan abunda Hameeda zata mata ko wani yai mata a cikin familyna zai yi mata ne saboda ni so dole ne nai wani abu akai, and Hameeda har shaye-shaye take yanzu kasan masu shan kayan maye basa cikin hankalin kansu”


Ya karasa yana duba wayarsa dake ringing, number Ikram ce. 


“Mai Martaba yana nemanka yanzu, yace a duk inda kake ka zo ka sameshi yanzu kai da matarka”


Yana picking ta fada masa. Sai ya sauke wayar ya bude motarsa. 


“Mai Martaba na nema sai mun hadu”


“To Allah ya tsare zan kira ka”


Yai ma motar key ya kama hanyar kan wurin sarki. 

Yana isa fadar part dinsa ya fara wucewa. A lokacin Farhat na zaune gaban madubi tana saka sarka, da alama wanka tai sai dai fuskarta duk d kumbura kamar an daketa. 

Daga bakin kofar dakinta ya tsaya yana kallonta ta madubi kamar yadda ita ma take kallonsa. 


"Miyasa kika yi abunda kika yi dazu? Dan ki bani kunya? Ko dan ki sake sakani cikin wata matsalar?"


Juyowa tai ta fuskanceshi. 


"Ba ko daya"


"Tazo muje"


Kamar dai zata tambaya sai kuma wata zuciyar ta hanata, wardrobe ta bude ta dauko mayafin da dake sa launin atamfar dake jikinta ta rufe kanta, sannan ta nufi kofa already shi har kai downstairs. 

A tare suka fita daga falon daga ita har shi babu wanda fuskarsa ke dauke da walwala, shi dai ya hade rai kamar an masa mutuwa ita kuma tayi fuskar tausayi. Duk inda suka bi sai an kai har kasa ake gaishesu shi din be kula su ba, itama bata damu da amsarwa ba. Kamar dai jiya ta kofar data shiga jiya yau ma ta nan ta bi, banbanci kadan ne jiya kawota aka yi a matsayin amarya yau kuma ita da kanta ta kai kanta dan amsa kiran Mai Martaba. 


Babu kowa a fadar sai masu aikin gyarashi, gaisheshi suka rikayi har ya isa gaban wata kofar wacce ta sadasu da wani falon na dabam mai cike da kayan alatu, nan ma babu kowa sai ac dake ta aikinsa, ita dai tana biye da shi har suka wuce falo hudu sannan ya dauke wata hanyar mai kama da corridor ta nan ta hango garden din Mai Martaba, hannusa na dama ya kai ya tura wata kofar sai gasu sun fado cikin wani babban falo, bata yi sallama ganin shi a be yi ba, karasa yai sai ya zauna kasa yana fuskantar Mai Martaba ita ta zauna kusa da shi, Dada na zaune saman kujera tare da Hajiya Hadiza, Hajiya Maryam da Zara kuma suna a kujera daya, sai Hameeda dake zaune gafen Dada. 

Gyaran murya Mai Martaba yai yana kallon Zain. 


"Na fada maka kuskure daya daga matarka ba zamu dauka ba anyi haka?"


Zain yai shiru ya kasa amsawa ya kuma kasa daga kai ya kalli Mai Martaba. Hajiya Hadiza ta share kwalla da suka zubo mata ta ce


"Mai Martaba karka hukuntashi da laifin da ba nashi ba, laifinane domin ni n girka abincin da yarinyar nan ta ci, kuma wannan laifin ba nata bane kuma bana mutum daya ba ne"


"Sai dai idan kin so dorawa kanki laifi amman miye naki a ciki, ai yasan ke kika girka abinci amman daya tashi sai ya dora laifin akan Hameeda, kare da karau ma har da cewa yai wai ita ta kashe Haleema wannan magana ai ta girma"


Cewar Dada cikin masifa. Hajiya Maryam ta tabe baki.


"Daga zuwan yarinya jiya jiya har ta haddasa fitina, nan gaba abunda zata yi a gaba ai mai yawa ne"


"Lallai kam kara asan abun yi tun kamin abun yafi haka"


Cewar Hajiya Zara. Har Zain ya bude baki zai yi magana sai Farhat ta tari numfashinsa wacce suka ji muryarta kamar daga sama. 


"Allah ya taimakeka, dukan dan Adam ajizine, bana cikin daya daga cikin iyalanka amman wanda ya aje ni agidan nan yana da muhimmanci a gareka, dukan abunda Yarima ya aikata jiya laifinane domin ban fada masa cewar ina da ulcer ba, sai yai zato ko wani abun ne, hakan yasa ya kira ta ya tambaya ko akwai abunda ya faru, hakan yasa ta fasa kuka ta juye masa magana, amman bayan wannan babu abunda ya faru, Zain mai tsananin biyayya ne a gareka kuma mai jin nauyinka wannan ya hana shi yin musu maka abunda aka fada akansa, idan kuma Mai Martaba be yarda da magana ta ba, ina son ya bani alkur'ne na rantse masa da shi ko kuma ita Hameeda ta rantse akan anyi haka. 

Mai Martaba kai shugaba ne mai adalci da sanin ya kamata karka yanke hukunci bisa ga fushi, idan har zaka yanke hukuncin ka yanke min duk hukuncin daya dace da ni amman ban da na saki, karka cilastawa danka yin abunda Allah baya maraba da shi, na hadaka da girman Allah Mai Martaba ka tausaya mana.

Ina neman afuwarka akan abunda ya faru, ko wane adam ajizine dukanmu masu laifi ne, kai ubane a gareni sakancewar kao shugaba ne mai adalci da sanin ya kamata, kuma ina mai maka alkawari hakan ba zai sake faruwa ba"


Idon kowa yana kanta, bama kamar Hameeda da bakinta ke sake tana kallon ikon Allah, Zain kuma yana kallon tana yin abunda ba zai iya ba, domin indai shi zai kare kansa sai dai Mai Martaba yai masa abunda duk zai masa amman ba zai iya ba, abu na biyu kuma kowa na mamakin yadda ta tsoma baki ba tare da Mai Martaba ya bata umarnin hakan ba. 

Kallonta Mai Martaba yake, tun da ta fara magana ya yaba da hankalinta, a natse take fitar da duk wani kalamin dake fita daga bakinta tana kokarin fahimtar da shi abunda sauran suka kasa, gata sai hawaye take gwanin tausayi. 


"Karya take wacan wacan yarinyar munafuka ce au laiye zaki yi ki karyatata"


Cewar Dada tana jin kamar ta taso tazo ta daketa


"Zai iya zama gaskiya mana, ai kin san Zain ba zai iya musa abunda aka cewa Mai Martaba ba, kuma kullum Hameeda ce take kawo kararsa akan ya mata abu, amman shi be taba kawo kararta ba, kuma be taba musa maka ba"


Dada ta kalli Hajiya Hadiza wacce ta gama maganar yanzu.


"Ee daman can son Hameeda kike ba ni na sani, duk da goyon bayanki ya auro wannan tsitattaciyar magen, to Wallahi ta Allah ba taku ba"


. Mai Martaba yai gyaran murya a karo na biyu sannan ya ce


"Dukan abunda zai tashi hankalin iyalaina bana sonsa, babu ta inda mata ta fi yar'uwa, dan haka bana son ka bar zuciyarka ta yaudare ka fifita matarka akan yar'uwarka, abu na biyu kuma ban jidadin abunda Hameeda tai ba, dan bana son auren ba shi ke nuna duk abunda kika yi ko kika ce na cilasta masa abunda ba zai kawo kwanciyar hankali ba, fushi gaba zargi zargi duk ina son a aje shi a cikin iyalin nan, Matar Muhammad Yayarki domin ta auri yayanki dan haka kar na kuskura na ji kin mata rashin kunya, ba ke ba kuma kowa a cikinku ya ce zai nuna rashin tarbiya a gareta zai tsaba masa, ita kuma ina son ta kama mutunci da girmanta karta kuskura shiga sha'anin da bana nata ba, kowa ya rike girmansa da matsayinsa. Zain ya girme ki Hameeda be kamata ki masa karya ba, karya tana daya daga cikin abunda na tsana, karya tana zubarda mutumcin mutum da kimarsa, karya kuma ba abu ne da akasan wanda ya girma a cikin gidan nan da yinsa ba, dan haka ki bashi hakuri da matarsa.


Zain.."


Mai Martaba ya kirashi a natse sai ya dago ya kalleshi tare da amsawa. 


"Kai mai yanke hukunci, ina fatar nan gaba idan haka ya faru kai zaka yi hukunci ba ni ba, ka kai matsayin da zaka yanke hukunci ko bana nan ko kuwa akan abunda ya shafi masarautar nan ne balle kuma abunda a shafi iyalina, Allah ya maka albarka"


Wannan furuci da Mai Martaba yai ga Zain be yi ma Hajiya Maryam da Hajiya Zarah dadi ba, Dada kan kasa cewa komai tai ba dan komai ba sai dan hukuncin da Mai Martaba ya yanke be mata dadi ba, ba ta son cilasta masa ya cilasta ma Zain sakin Farhat nan, amman tana nan haushinta. Dan haka sai ta tashi ta bar falon. 

Hameeda bata da damar musa masa tace ba haka bane, hakan kuma da Mai Martaba yai ya nuna ya aminta da kalaman Farhat saman da nata. Sai da tana jin kamar akwai kaskanci a tare da ita idan har ta bawa Farhat hakuri, amman ya zatayi umarnin mai martaba ba bata da wata dabara bace ta bi. 


"Dan Allah Yarima kai hakuri"


Be amsa mata ba, sam be ma kalli inda take ba, sai ta kalli Farhat tana wani irin dauke numfashi kamar zata mutu, saboda bakincikin bawa Farhat hakuri. 


"Ki... Yi... Ki... Yi haku...ri..."


Farhat ta dago ta kalleta. 


"Ba komai na yafe miki"


Hajiya Hadiza tayi murmushi.


"Mun gode Mai Martaba Allah ya kara girma da lafiya, daman ni nasan Zain ba zai ce haka ba, Allah ya tsare gaba"


Da hannu Mai Martaba yai musu alama da su tashi su bashi guri sai kowa ya tashi ya fice, ban da Hajiya Hadiza wacce ta dauko masa sabuwar fira daman yau a dakinta ya wayi gari. 


Suna shigowa part dinsu Zain ya maida kofar falon ya rufe yana kallon Farhat data hade fuska kamar bata taba murmushi ba. 


"Da ya baki qur'an ki rantsen fa?"


"Ai ba zai bani ba, domin manyan mutane basa daukar irin wannan hukunci sai ya zama dole, so kaga Mai Martaba ya yarda da ni sama da Hameeda"


"Yarda da yai dake a yanzu ba shi yake nuna ki sake yin haka a gaba ba"


Ya fada as he command her. 


"Shi kadai ka iya, ni kazo nan kana min fada amman yanzu kanwarka take kokarin cin zarafinka a gaban Mai Martaba"


"Ban iya munafurci ba"


"To ni na iya sa ido kai kallo" 


Ta fada tana harararsa, har tayi gaba sai ua rikota ya dawo da ita da karfi ya matse gashin kanta. 


"This will be the last time da zaki harareni"


Wani irin kara tai tana kokarin kwatar kanta amman ta kasa, har sai da yaga dama ya jefar da ita saman kujera. 


*** *** ***


Bayan ta gama hada breakfast su Amal suka ci suka wuce islamiya, ita kuma ta shiga ta shirya cikin bakar abaya ta dauko jakarta ta fito falo inda Hafsatu manga take zaune tana jiranta, duk ta bata fuska kamar ba ita ba. Zaunawa Anty Ummi tai saman kujera ta kama hannun Hafsatu manga tana sauke ajiyar zuciya. 


"Baki son zuwa gidanku ne? Zan kaiki ne saboda ki samu kwanciyar hankali, nima na samu Zain ma ya samu, bana son fadan da kike da Amal kuma bana jindadin yadda Zain yake shige miki komai zai iya faruwa, sannan na kasa natsuwa da ke a gidan nan, ke kanki nasan kina son iyayenki..."


Ta tsayarda maganar sakamakon ringing din da wayarta ke yi, picking tai ta kara a kunne. 


"Hello Ummu, Subhanallahi gani nan zuwa"


Tana aje wayar ta kama hannun Hafsatu manga suka fice, bata zame ko ina ba sai gidansu, wato family house dinsu, gabanta sai faduwa yake saboda tasan ciwon Abbansu a duk lokacin da asmarsa ta tashi bata masa da kyau. 

Sai dai a yadda ta tararda yan'uwata da kuma Abbansu yasa hankalinta ya kwanta, domin ta sameshi zaune har ana dan taba fira da shi, zubewa tai kasa tana gaisheshi Hafsatu manga kuma ta tada kai sama tana kallon falon da aka narkawa dukiya, da dai dai take kallon hotunan dake manne a falon har ta kai kan hoton mutumen data taba gani a Jafatu Mall har ta dauko masa takardarsa data fadi. 

Wayarsa Anty Ummi ce tai ringing sai ta dauka tai yar magana, sai kuma ta tashi ta kama hannun Hafsatu manga. 


"Waccece wannan?"


Hajiyarsu ta tambaya.


"Yar makociyarmu ce"


"Allah sarki"


Daga haka Anty Ummi taja hannunta suka fice, motarta ta shiga suka kama hanyar samaru suna isa ta fito mota wani saurayi ya fito, bayan sun gaisa ta mika masa Hafsatu manga. 


"Ka tabbatar a hannun sarkin garinsu ka kaita, idan kuma baka samu kowa ba ka dawo da ita, kar wani abu ya same ta"


"Karki samu matsala, za'ayi yadda kika ce"


Yana fadar hakan yaja hannunta sai ta fashe da kuka. 


"Anty na daina bana son zuwa ba zan sake biki miki Amal ba"


Tsaye Anty Ummi tai tana kallonsu zuciyarta na sosuwa da tafiyar da Hafsatu manga zata yi, sai dai bata yi komai ba har ya sakata motar ya kama hanya. Sannan ta bude motarta ta shiga ta kamo hanyar gida. 


**** ***** **** 


FLASH BACK... 


Tana jin motarsa ta yi saurin jera kulolin abinci a dinning, ta shiga bedroom da sauri ta dauko dankwalinta ta daura ta fito tana dariya ta daukin dawowar mijinta. A bakin kofar falo suka ci karo da shi yana kokarin shigowa ita kuma tana kokarin fita. 


"Sannu da zuwa"


Ta furta tana dariya kamar yadda shima yake dariyar yana kallonta. 


"Yauwa ya gidan?"


"Lafiya kalau"


Ta karbi jakar kayan da ke hannunsa, tare suka karasa cikin falon, ya cire hular kansa ya mika mata ya bude aninin rigar shaddar da ke jikinsa ya zauna saman cushion yana sauke gajiya. 


"Kai Al-hamdulillah babu inda ya fi gida dadi, duk inda nake bana jin sakewa sai na dawo gida"


"Al-hamdulillah dai an dawo lafiya ya ka baro Lagos?"


"Lagos lafiya kalau"


"Ka huta ka yi wanka ga abinci can yana jiranka"


Ya kalleta zuciyarsa cike da so da kuma kaunar matarsa, sai ta mike tsaye tana murmushi ta nufi dakinsa dan aje kayan da ke hannunta. 

Bayan ya gama wankan ya zo falo suka ci abinci a tare, a yammacin ranar ta lahadi be labarta mata komai ba sai Lagos da abunda ke cikin Lagos, wani abun ya bata mamaki wani ya bata dariya a haka dai ta yi shawa'ar wata rana idan zai sake zuwa wani worship din zata bishi ta ga Lagos da kanta. 


Bayan sallah isha'i tana zaune daki a gaban madubi tana daura dankwalin atamfa ya shigo rike da wani dan karami abu mai kamar akwati fuskarsa dauke da murmushi kamar kullum, a gefen gado ya zauna yana kallonta itama sai ta kalleshi ta dauke ido. Hannunta ya kamo ta danka mata wani awarwaron azurfa mai dauki da sunanta wato Maman Hafsat. Tsalle ta yi ta dire tana ihu da murna.


"Habib Ina ka samo?"


"Na musamman ne ni nasa aka kera min shi a can Lagos din, kin san kin fada min idan Allah ya baki ya mace zaki saka mata Hafsat shiyasa na ce ya rubuta Maman Hafsat a jiki"


"Na gode sosai Allah ya saka da alheri"


"Amin, wannan kuma na yar mu ne Hafsat... "


Ya karasa yana mika mata karamin na yara mai dauke da suna Hafsat. Karba tayi sai dai bata murna kamar yadda take a karban na farkon, shafa awarwaron ta yi idonta cike da kwalla. 


"Kin fara ko?"


Ta share hawayen da suka zubo mata. 


"Kawai ina tunanin lokacin da zamu samu yar ne har mu saka mata awarwaron"


"Kina tunanin Namiji zamu samu?"


"Ina tunanin zuwan haihuwar ne Habib"


Sauka ya yi daga inda yake ya gurfana kasan kuiwoyinsa ya dora hannayensa saman cinyarta. 


"Rufaida, komai fa na Allah ne, sau nawa zan fada miki ki daina saka kanki a irin wannan damuwar, kin san matsalar ba daga ni ba ne, kuma ba daga ke ba ne, kawai akwai lokacin da Allah ya diba mana ne wanda dole sai mun cin ma adadin kamin mu samu haihuwar, kuma na miki alkwari ba zan sawa dan kowa wannan sunan da kike so ba sai yarki"


"Idan kuma Allah ya kaddara ba da ni zaka haihu ba fa?"


"Kai Subhanallah Rufaida ana baki kina roko, wannan wace irin magana ce haka, yau ma daga dawowata bata min rai zaki yi?"


"Ka yi hakuri Habib nasan haihuwa na Allah ne, amman abun yana damuna yadda yan'uwanka suke dora laifin a kaina yana damuna, kai kuma kaki ka yi musu abunda suke so, ni kake jawa kiyayyar ko jiya sai da Hajiya ta zo gidan nan tana rokona akan na barka ka yi aure, bata hana na mallakeka ba amman na barka ka yi aure tana son ganin jikokinta"


"Itama ta yarda kin mallake ni kenan?"


"Mi zai sa ba zata yarda ba? Dan me zata baka umarni kara aure kaki karawa? Kai kanka na tabbatar kana son ganin jininka Habib"


Ta sauka kasa daga saman kujerar tana rokonsa hawaye na kwaranya a idanuwanta. 


"Na hada ka da girman Allah Habib na rokeka dan Allah dan Manzonsa, ka kara aure dan Allah ka yi aure kamar yadda Hajiya da yan'uwanka suke so, kai kanka kana son ganin jininka Habib, kuma idan kayi aure zaka wanke ni daga zargin da yan'uwanka suke min na cewar na mallakeka, wata kila ma ka samu haihuwa kamar yadda suke so"


Mikewa ya yi tsaye ba tare da yace da ita komai ba ya fice ya bar mata dakin tana aikin kuka. Har ga Allah bata son mijinta ya kara aure, domin babu mace da take zaman lafiya da mijinta tana son shi yana sonta, ta so ya auro wata ko da kuwa yan uwansa suna sonta ne balle basa sonta, amman a yanzu ya zame mata cilas ta rokeshi ya yi auren saboda farincikin mahaifiyarsa ganin cewar shi kadai ta haifa kuma tana son ganin jikokinta. 


Ko wane gidan aure yana irin nashi kalubale da ma'aura suke samu kansu a cikin, wata ta kan zo da sauki wata kuma mai tsanani, wata akan samu mafita awarware wata kuma ta dauwama har a abada! Rayuwar auren Rufaida da Habib rayuwa ce mai kyau kuma abar burgewa ga kowa, irin yadda suke nunawa junansu so da kulawa kai kace a kwai daya suka fito, basa da matsala ta ko'ina, Habib baya son bacin ran Rufaida da ka bata mata rai kara ka bata masa kamar yadda itama take kokarin gujewa duk wani abu da tasan zai sosa nasa rai, hakan yasa mutane suke zargin cewa ta mallakeshi baya yi komai sai abunda ta ce, basu da matsala ta ko ina face rashin haihuwa da Allah ya jarrabi Rufaida da ita kamar yadda yake jarrabar wasu daga cikin bayinsa. Rashin samun haihuwa ita kadaice matsalar dake damun Rufaida da Habib, babu irin neman maganin da basu yi ba na gida da na asibiti, babu ranar da basa addu'a dare da rana akan Allah ya basu haihuwa, dukan asibitin da suka je ana fada musu cewar Habib bashi da wata matsala balle kuma Rufaida da mahaifarta take lafiya kalau kawai dai lokacin haihuwar ne beyi ba, wanda Allah ya riga ya rubuta adadin lokacin da hakan zai kasance, wanda bayi da yawa basu gane hakan ba, ciki kuwa har da yan'uwan Habiba da kuma mahaifiyarsa, sun kasa yarda cewar Rufaida bata da wata matsala, suna tunanin Habib yana fadar hakan ne kawai domin ya kareta, wasa wasa kiyayya ta fara shiga tsakamin Rufaida da yan'uwan Habib da kuma mahaifiyarsa, ganin an kwashe sharakara goma sha daya Rufaida bata taba batan wata ba balle bari (miscarriage), har ta kai Rufaida bata son shiga cikin yan'uwan Habib ko kuma ta kusanci Mahaifiyarsa saboda kori da habaici da ake mata. 


Mahaifiyar Habib ta yi iya hakuri da daga kafa wa Rufaida wanda take tunanin ya kamata ace Rufaida ta gano hakan da kanta amman kasa ganowa har sai da ta fito fili ta nuna mata tana son danta ya kara aure, da gangan Habib ya buga kafa da kasa ya ce shi ba zai kara aure ba, a tunaninsa idan har ya kara aure be kyautawa Rufaida ba, kuma zata shiga damuwa. Aka kida aka raya aka daka Habib ya tsaya kai da fata akan ba zai kara aure ba wai shi ya yarda daga Allah ne, wata kila lokacin haihuwar ne be yi ba. Lokuta da dama Mahaifiyar Habib takan sa Rufaida a gaba tana rokonta data bar danta ya yi aure saboda ya samu jikoki tana son ganin jikokinta saboda shi kadai ta haifa. 

Tun Rufaida na dauko abun wani iri har ta fahimce cewa Hajiya Larai wato mahaifiyar Habib ta yarda da zugar mutane da ke cewa ta mallake Habib baya ganin kowa sai ita kuma baya yin komai sai ta ce ayi. 


Wannan matsalar ce ta saka Rufaida a damuwa, ita da kanta ta zo tana neman ya kara aure amman ya ki wai shi bashi da ra'ayin kara mata biyu, idan ta matsa masa har kaurawace abincinta da shimfidarta yake amman hakan be dame ta ba, ita dai burinta ya kara auren kamar yadda mahaifiyarsa take so.


*** *** ***

Bayan ta gama kukan ta mike tsaye ta bi bayansa, a falo ta zame shi zaune saman cushion ya hada kai da guiwa ya noce kansa kana gani kasan damuwa ce tayi masa yawa. 


"Kana da son kanka Habib abunda yake faranta maka rai kawai kake, ko da kuwa hakan zai bakanta maka rai ne, kana kokarin ganin ka faranta min ko da kai naka ran zai bace sabo...."


"Saboda na san hakan zai dawo min da bakincikina i zuwa farinciki, dukan abunda zai faranta miki rai shi zai faranta min rai, miyasa Hajiya ba zata fahimci cewar rashin haihuwar mu daga Allah ba ne?"


Ya karasa mata tare da dagowa ya kalleta. 


"Miyasa kai ba zaka fahimci halin da Hajiya take ciki ka kara auren ba?"


"Na fada miki bana da ra'ayin mata biyu"


"To ka saki ni ka auro wata...!"


Ba shiri ya tashi tsaye da sauri yana kallonta tare da mamakin kalamin da ya fito daga bakin matarsa, duk irin so da Rufaida take masa yau har ta iya bude baki ta ce ya saketa ya auro wata? 


"Da bakinki kike cewa na sakeki na auro wata? Kin san abunda kike fada kuwa?"


Ta gyada masa kai hawaye na zuba a idonta. 


"Na sani, matukar hakan zan faranta ran mahaifiyarka da yan'uwanka da kuma kai kanka na yarda ka sakeni ka auro wata, kai kanka kana son haihuwa Habib ina karantar damuwar a fuskarka, ina ganin shaukin da ke fuskarka a duk lokacin da idanuwanka suka sauka akan yara, ina jin addu'o'in da kake yi cikin dare Habib, wata kila ni Allah be yi zan haihu da kai ba, miyasa ba zaka auri wacce zata haifa maka yaya ba?"


Ta taso ya nufota yana fadin. 


"Ke kadai zaki haifa min Hafsat Rufaida..."


Hannu ta daga masa tun kan ya karaso. 


"Karka sake shagaltarda ni da kalamanka, kar zuciyarka ta sake yaudaraka ka saba umarnin mahaifiyarka, ina jiye maka tsoron fushinta Habib ina jiye maka tsoron rana da zata fusata tayi mummunan furuci akanka Habib, ka ji tsoron Allah mahaifiyarka ita ta dauki cikinka tun kana kwana daya har ka kai wata tara ta haife ta raineka har ka girma ka hadu da ni na aureka, shin idan ban zame mata silar farinciki ba taya kai zaka zame mata silar bakinciki? Kai ma zaka zo dan da ka haifa ya tsabawa umarninka? Iyaye suna da muhimmanci Habib Annabimu sai da ya kira uwa sau uku sannan ya kira uba, ina son ka sani fushin Allah yana tare da fushin uwaye, kuma yardarsu tana tare da yardar Allah ina tsoron kar wata kai ma danka yai maka haka Habib-"


Tunda ta fara maganar yake kallon hawayen da ke zuba a idonta har ta kai aya, yasan gaskiya take fada masa amman shi kuma ya rasa yadda zai fahimtar da Hajiya da ita kanta Rufaidar yadda ya yarda da abunda Allah ya rubuta zai same shi. 


"Shikenan, zan kara auren shine burinki da na Hajiya ko? Da yan'uwana, daga yau matsalar kara aure ta wuce zan kara aure sai ki nemo min matar da zan aura"


Fashewa tai da kuka mai taba zuciyata ta nufi dakinta da gudu zuciyarta na mata mugun kuna saboda kalaminsa na karin aure abunda ko wace mace ta tsana. 


"Kin gani ko? Yanzu ma ba a tsira ba"


Ya fada yana ware hannayensa tare da sauke ajiyar zuciya, komawa ya yi ya zauna ya dafe kansa sai ga hawaye masu zafi sun gangaro daga idanuwansa zuwa kuncinsa.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.