Free chapter · Read without an account

Part 4

by Safiyya Haruna · Rumasa'u

RUMASA'U.


BY SAFIYYA.

WATTPAD @mrsjmoon.


Page 04.


Hajiya Aminatu ta tambayeta k'irjinta na harbawa.


Girgiza kai ta yi ta zame ta kwantar da fuskanta jikin mahaifiyarta wacce ke ta sharar barci.


Ajiyar zuciya Hajiyar ta sauke a hankali ta shafo fuskanta cikin yi mata dibara ta ce "In shi ne ki sanarmin kada kiji tsoro ina tare da ke ba zai iya yi miki komi ba." 


"Ni ban sani ba." Ta amsa hawaye na bin cheek d'inta.


"D'iyata sanar da ni kinji?"


"Momy bazan gane fuskansa ba sabida idanunsa a kulle ya ke da gyalle sai dai in naji muryarsa zan gane shi."


"Murya kuma?"


"Eh."


"Ya yi miki magana ne?"


"Sadda zaiyi dan ina rok'onsa shi ne ya yi ta dukana da zagi yana kirata d'iyar kwaroro mara gata kuma babba mutum ne." Ta k'arasa zancen cikin kuka mai sauti.


"Is ok dear kina da gata kuma shi ne d'an kwararo ba ke ba."


"Momy me ye kalmar ke nufi?"


"Kina jin yunwa?" Ta kaucewa bata amsar tambayar.


"A'a."


"To kwanta kiyi barci, nurse zata kula da ke zuwa gobe in munzo mutafi gida, ni ina sonki zanyi lelenki tamkar d'iyar cikina."


Motsa kai ta yi bata kuma magana ba ta zame ta kwanta idanun ta na kallon window har kuma lokacin Mahmud na tsaye a inda ya ke fuskan nan nasa a had'e.


"Ina jin tsoron wancan mutumin fuskansa ba dariya, ki ce ya tafi ban son ganinsa, ya yi kama da mugaye."


"Yi kwanciyar ki zai tafi amma ba mugu ba ne, sunarsa Uncle Mahmud."


"Mijin ki ne?"


"A'a."


"To shi wa ye?"


"Gidanmu d'aya."


"Amma ya akayi shi baida kirki kamar ke?"


"Bai sa ba da ke ba ne wata rana zakiga kirkinsa."


"Allah da ganinsa bai da imani ni ban son kallon fuskansa mai ban tsoro, mutane in basa dariya mugaye ne haka Inna Hure ta fad'amin."


"Wacece ita?"


"Mai bamu abinci ce ta cemin a zaurensu Mamana tasoma zama lokacin ina yarinya daga baya kuma ta gudu ba su sa ke ganinta ba sai bayan shekaru bakwai lokacin ina da shekaru goma. Inna Hure tana son Mamana mijinta ne bai son zamanmu a zauren sai ya yi ta zaginmu yana koronmu shi ne muka daina zama muka koma cikin kango, k'asar bishiya wata rana kuma ta kaimu bakin bola ta ce anan zamu kwana wanda dik in muje wurin bana iya barci sabida tsoro."


"Allah sarki sannu, insha Allah wahalarku ya k'are."


"Mungode Momy, wallahi bayan Inna Hure ban tab'a had'uwa da mai k'aunarmu ba kamarki."


Shafo sumarta Hajiya ta yi ta saci kallon window suka had'a ido da Mahmud ta watsa masa harara ya zunkud'a shoulder cikin tab'e baki, dak'uwa ta watsa masa tare da motsa lips ta furta "Gidanku." Murmushi ya sa ki cikin nuna ko ajikinsa, dawo da kallonta ta yi kanta ta ce "To ita Inna Huren bata tab'a baki labarin wani yazo nemanku ba?"


"Bata san kowa namu ba ta fad'amin."


"Ikon Allah, to Allah ya warware wannan sark'ak'iya."


"Amin. Momy kice wancan ya bar wurin tsoro ya ke bani." Ta yi maganar batare da ta yarda idanunsu ya kuma had'u da na Mahmud ba.


"Kiyi shiru kada ya jiyoki."


Kulle idanun ta yi gam hannunta kame da bakinta, addu'a Hajiya ta yi masu ta tofesu tare da rufesu da bargo wanda Doctor Fatima ta basu. Bajimawa ta fahimci barci ya d'auke ta. Windown ta nufa ta kulle tare da sakin labule batare da ta yiwa Mahmud magana ba. Tana shirin fita nurse d'in da zata kula da su ta shigo Alhaji Ahmad biye da ita.


"Sannu da k'ok'ari Hajiya." Ya ambata idonsa na kan mahaukaciya da d'iyarta ganin yarda suke barci cikin kwanciyar hankali wani sanyi yaji ya d'auka a ruhinsa.


"Yawwa sannunmu Hubby. Sai mu tafi tunda an samu mai kula da su."


"Ok muje."


Har sun fita Hajiya ta dawo "Dan Allah sister a k'ara sanyata cikin ruwan zafi dan har yanzu tana k'orafin wurin na ciwo."


"To dama kafin gari ya waye zan sanyata kamar sau biyu."


"Masha Allah, mungode."


"Bakomi Hajiya aiki na gari yiwa kai ne."


*

Suna kan hanya ta dubi gefen da Mahmud ya ke zaune "Kai wa ya sanar maka da inda mu ke?"


"Kaina."


"Ka rainani ko Mahmud?"


"Me na yi kuma Momy? Daga kin tambaya na baki amsa shi ne yazamo laifi?"


"Allah ya baka sa'a, ai duniya ce tana jiran na ciki balle wanda ya ke cikinta tsundum."


"Dady kana jinta ko? Zatayimin baki."


"Mahmud baka jin magana, shin me yasa zaka amsa mata tamkar irin da sa'arka ka ke magana."


"Am sorry Momy. Lokacin ina tare da abokaina sadda kuka iso asibitin shi ne bayan mun rabu na shigo da taimakon wata nurse na gane d'akin da kuke amma shin me ye had'inku da mahaukata da har kika iya zama kusa da su kina hira?"


"Kada na kuma jin ka kirasu da mahaukata."


"To me zan kirasu da shi wanda yafi mahaukatan?"


"Mahmud wallahi ina daf da sallamawa duniya kai tunda baka san darajata ba sai anyi maka magana kace anfi son Hamid da kai to ai zuciya ta na son mai kyautata mata ne, na tabbata inda Hamid ne ba zai tsaya ina fad'a yana fad'a ba."


"To kiyi hak'uri saharrin shaid'an ne da zuciya wacce bata da k'ashi."


"Allah ya shirya ka." Ta furta a tak'aice.


"Amin." Alhaji Ahmad ya amsa sannan ya d'ora da yiwa Mahmud nasiha ya natsu yana saurare kamar gaske wanda tamkar busar sarewa haka ta ke jin nasihar. A k'arshe Alhajin ya rarrashin Hajiya cikin lafuza masu sanyaya zuciya, kafin su isa gida tamanta komi dan har tana tsokanar Mahmud da tazuru. Wannan rashin rik'on nata ke k'arawa Alhaji Ahmad k'aunarta har ya ke jin ba zai iya had'ata da kowa ba ko da kuwa kyautar matar akabashi. (Mu daure muna zamowa masu sauk'in hali tare da rashin rik'o ga abokanan rayuwarmu domin wanna shima matakin kame zuciyar miji ne har ayita ceke-kucen mace ta mallake mijinta.)


*

"Mr. Abid ya dai? Na ganka a rikice?" 


Tsaki ya ja cikin b'acin rai ya soma bawa abokinsa Adam labarin dalilin da ya haddasawa ransa b'aci.


Zare ido Adam ya yi cike da tsoro.


"Me ye naga ka firgita? Ko kai ne ka lalata yarinyar?"


"Ban san iskanci Abid me zanyi da yarinyar da ko nonowa bata da su."


"Amma ai naga tana da kyau sannan iskancinka bai duba cikar mace da rashinsa in kuma ka manta ne sai in tuna maka yaran da ka lalata masu k'asa da shekarun d'iyar mahaukaciya.


"Abid wallahi zan iya farkeka in baka daina tuno min da abinda ya wuce ba. Abinda natuba ai ya dace ka manta lamarin tunda ba kai ke bada wuta da aljanna ba."


"Allah baka sa'ar farkeni dan na manta ina aboka da d'an daba ne wanda d'aukan ran mutum ba'abakin komi ya d'auke shi ba, sannan ko ba nk ke da ikon bada rahama ba ai ya bani damar tunasar da kai mugun aikinka na baya ko ka rik'a tuna kalman tuba."


"Kaga abokina mu bar zancen nan kada inyi aika-aika." Ya yi maganar cikin kwantar da kai kamar bashi ne ke zanzana ba cike da rashin kunya.


"Kanka akeji kuma. Dama school zan koma na biyo muyi sallama."


"Ok Allah ya kaika lafiya."


"Amin."


"Mukam ilimin zamani sai in anayi a lahira tunda mun sami na zagin jama'a to mungode Allah."


"Shege ai ko na addinin ma ba samunsa ka yi ba shi yasa lamuranka su ke a jagule cikin jahilci."


"To jikan Malam cikin fuska ya isa haka."


Dariya suka sanya gami da tafawa. Suka rabu cikin nishad'i shi yasa Abid ya kasa rabuwa da Adam dik da tazararsu mai nisa ne ta ko wani fanni, nasaba da tarin ilimin addini dana zamani amma ahakan suka k'ulla abokata musanman na iya yawon bin clubs.


Yana shiga gate d'in school kira na shigowa wayarsa parking ya gyara cike da jin masifa domin a zatonsa Muhsin ne ya kuma kiransa amma sab'anin hakan zai sunar Ummansa ya baiyana kan screen d'in gyara zama ya yi ya d'auka.


"Abid kana ina?" Ta ambata a hankali bayan amsa sallamarsa da ta yi.


"Zaria." Ya amsa shima a hankali.


"Au ka koma makaranta kenan babu sallama?"


"To Umma ya zanyi tunda Brother na son mannamin hauka kuma ya ce zai had'ani da ke shi yasa na tafi tun kafin zuciyana ta buga."


Bata kula k'orafinsa ba ta soma yi masa nasiha kamar yarda ta saba akan ya ji tsoron Allah a dik inda ya ke tare da gujewa tarayya da abokan banza dan kiyaye martaban gidansu da kansa.


"To Ummana zan kiyaye, kiyimin addu'a mai yawa kinsan final exam ke gabana."


"Insha Allah zaka sami abinda kake so in har ka gujewa b'acin raina, ka sani ko da ba na ganinka Allah na ganinka kuma yardan mahaifa na tafiya tare da yardan Allah ne dan haka faranramin shi ne matakin nasararka a dikkan lamuranka."


Shiru ya yi har ta gama nasiharta ta kashe wayar bai sa ke magana ba. Sosa gemunsa ya yi wanda ya ke cike da suma tamkar sheikh, sosai ya ke fito masa da cikar zati, mutane da dama basa yarda in aka fad'a musu cewa bayajin magana domin Abid yasan sirrin zuwa club ya cashe ya rungumi ladies son ransa amma fa bai yarda su san sirrin da ke trouser nasa dik kuwa nacinsu. 


"Oh nikam nasihan Umma na ta kurani ko na yi niyyar bud'e wuta akan baby sai inkasa, kai hak'ik'a Umma na tauyemin jin dad'in rayuwa." Ya furta cikin jan dogon tsaki ya jima zaune cikin motar kafin ya fitowa daga motar ya jingina jikinta yana bin 'yan mata da kallo cikin bak'in gilashin da ke sanye da shi. (Iyaye ku daure kuna fad'awa d'iyoyinku gaskiya koda basa so hakan zai rik'a sawa suna tuna maganar Allah tsoron gamuwa da shi na kuma nashe k'irjinsu, ko da basu gyaru yarda kuke so ba zasu rage wani abin. Haka ku daure kuna sanar da su karanta azkard'in Lahaula wata quwwata... Har zuwa k'arshenta sau goma safe da marece dan samun kariya daga aikata zina. Allah kashirya mana zuri'a baki d'aya. Amin.)


Yana tsaye wasu 'yan mata suka k'araso wurinsa kallonsu ya yi a d'age ya ja tsaki sai dik kunya ta kamasu amma da ya ke 'yan duniya ne sai suma suka jingina jikin motar nasa, k'amshin turerensa ya shak'a ya lumshe ido ya bud'e, cikin dibara ya shafo maransa jin yana son fad'awa wani hali wanda bai tab'a shiga ba akan d'iya mace, juya musu baya ya yi yana la'antar shu'umin turaren da suka sanya wanda ya tabbata na sihiri ne tunda gashi daga shak'arsa dire ya taso masa. Number Muhsin ya lalibo batare da ya shiryama hakan ba, sam ya manta fushi ya ke da shi.


"Brother wallahi ka yarda da bani ba ne, sam ban da masaniya akan aika-aikan." Ya ambata muryansa na rawa sannan wandonsa na motsawa.


"Yes na aminta da kai Abid dan Allah ka yafemin, rashin sani ne."


Tsalle ya doka cike da murna dan sam ya amanta gaban 'yan mata ya ke sai da yajiyo dariyarsu daf da shi ai da sauri ya koma cikin mota ya kunna ya fice mak'ale da wayar kuma yana fita harabar makarantar ya nemi sha'awar da ya taso masa ya rasa, cikin nishad'i ya cigaba da waya da d'an uwan nasa. (Ladies aji tsoron Allah ba sai kinbi bokaye sun kaiki ga halaka zaki sami abokin rayuwa ba, ki yi hak'uri ki tsarkake zuciyar ki sai Allah ya fito miki da abokin rayuwa ta hanyar raya sunnah amma watsar da martaba banaki ba ne face wulak'anta rayuwa a k'arshe kidawo fargar jaji lokacin da lokaci ya gama k'ure miki).


*

Washe gari bayan sister Asiya tayi sallar subahi sai ta kwanta kafin su tashi ta taimaka masu suyi wanka bisa rok'on da Hajiya Aminatu ta yi mata amma sai barcin nata ya yi nauyi dan bata farka ba sai da ranar dake fitowa ta window ya soma dukan fuskanta ta tashi a firgice ganin babu mutanen da ta ke kula da su a d'akin yasa tayo waje guje bako takalmi amma kowa ta tambaya amsar kenan bai gansu ba. Jikinta na tsuma ta lalibo number Doctor Fatima amma har ya gama ringing bata d'auka ba, haka ta yi ta jera mata kira amma bata d'aga ba.


Komawa d'akin ta yi ta duba toilet babu kowa takalmi ta sanya ta kuma fitowa hankali ta she ta nufi hanyar gate.


*Mrs j moon.*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.