Free chapter · Read without an account
Z
*Z*
Ana cewa Wai kafin ka Gama makaranta ka Kama Sanaa saboda idan ka Gama zaka fahimci me yasa a karshen national anthem ake cewa so help me God! A nawa bangaren ba talauci nayi ba sede a wañnan lokacin Jin dadi na ya Kare, farin ciki na ya datse, na Zama abinda na Zama yau. Se lokacin na fahimci menene girma da Kuma shekaru, se lokacin na gane rayuwar littafi ce idan wannan chapter ta Kare baka San meye a next chapter ba seka bude, wata kayi kuka, wata ka Fadi, wata kayi kuskure, wata kayi nasara Amma dukda Haka Dole ka cigaba da rayuwa, da Dadi ko Babu dadi, you've to move on even with the tiniest ounce of hope. Wannan shi ne rayuwa!
Watannin da Suka biyo baya muka tafi rural posting Wanda ya kasance shi ne clinical posting dinmu na karshe a training din mu, kullum muka zauna bamu da magana se zancen council, me zaa tambaya, ya zamu amsa, wani irin farin ciki zamuyi ranar da muka karba licence dinmu to practice. A kauyikan waje da cikin hadejia anan mukai posting. Dakkaiyawa aka fara posting dina, se aka rabamu da Zuhra Dake PHC Gawuna. Seda na Bada amanarta sannan na hau bus muka tafi, tunda na zauna a seat Dina kaina Yana Kan wayata Ina duba wasu sababbin topics da aka Kara a reproductive health,Kuma they're very important da Ina tunanin council zata dauki interest aka ta sako su. Muna zuwa muka hadu da In charge da Kuma staff din asibitin, Ina daga can baya Har aka Gama addressing sannan muka shiga ciki, straight muka wuce Maternity dinsu, mu uku a Haka rarraba mu. Ina zaune Babu patient se gida daya da tazo a 4cm Ina chatting Sega In charge din yazo da paper yace mu rubuta sunan mu, ni na fara rubutawa kafin sauran, a Haka ranar ta Kare se Kuma muka cigaba da zuwa a Rana na hudu Ina zaune wani attendant yazo yace
" Wacece Unaisa a cikin ku?"
Na dago nace
" Ni ce, me ya faru?"
Yace
" Dama yallabai yake son ganin ki"
Na mike nace
" Waye yallabai Kuma?"
Yace
" In charge"
Bance komai ba na bi Bayan shi har office din, dogo ne me kiba sosae, Allah ya taimake shi Yana da tsayi shiyasa kibar ba tayi Muni ba. Ina shiga nace
" Sir Ina kwana!"
Se ya cire glasses din shi yace
" Unaisa, zauna Mana"
Na danyi murmushi nace
"A'a sir ba komai"
Ya mike Yana fadin
" Be comfortable, office Dina kamar naki ne"
Oshey! Na fada a raina Ina hangame Baki, ya washe min Baki ya Kara min tayi Dole na zauna, yace
" Ke Yar Ina ce?"
Nace
" Birnin kudu Masaya"
Yace
" Oh yayi kyau, suanan Abubakar Amma kowa na Kirana Oga Habu, Zaki iya cemin Sadiq"
Kadan ne banyi dariya ba nace
" Tohm Sir ba damuwa"
Se yayi murmushi ya fara Bina da kallo which is so intense nayi saurin mikewa nace
" Sir I've to go, ana jimawa bus zata zo"
Yace
" To Unaisa, Amma Ina son ki, Ina son nayi ta hudu Dake kiyi shawara"
Nayi sauri na juyo, he looks happy saying that, nace
" Sir ta hudu fa?"
Yace
" Eh! Gidan ki daban Zan saki ai kedin ta gaban mota ce!"
Na gyada Kai na na fita Ina Masa dariya, Wai ta hudu. Ina komawa school na bawa Zuhra labari ta dinga tsokana ta. Shi Kam Cànîm da daddare da ya Kira nake bashi labari ya Bata Rai ya fara fada
" Kinje kina Masa dariya Dole zaice Yana son ki Mana, of all mutane se shi ma, ta hudu this is an insult"
Na danyi dariya Dan banga abin fushi ba, min riga mun saba duk lokacin da wani ya nuna interest a kaina se na bashi labari shima ya Saba, bansan me yasa wannan din ya Bata Masa Rai
" Dariya kike ko?"
Nace
" Cànîm Kai kadai nake so fa, meye abin fushin kasan I'm not the type that laughs Haka kawai, I'm not friendly self"
Yace
" Na sani, I'm jealous"
Nayi dariya irin I've defeated him nace
" Yace Ina da kyau, Wai kyau na ne ya burge shi"
" Zan saka ki fara saka nikaf fa, ya zaice Haka, see I'll Sue that man"
Nayi ta dariya nace
" Kana ta zuzutawa kamar irin nafi kowa kyau dinnan"
Yace
" Baki sani ba? Don't joke with me Babes ke kyakyawa ce, a idona kinfi kowa kyau"
Na saki murmushi Ina fadin..
" Awnnnnn..."
Da daddare Zuhra tace min tana spot bleeding, na dubeta nace Mata Kuma ba period bane? Ta dalla min harara tace
" Ai kallon ki kawai nake, Wai Unaisa ba Zaki iya tambaya ta kice ciki ne Dani ba, sede kawai ki ta kula Dani why are you like this?"
Nace
" Zuhra I'm sorry, kawai bana son irin wannan tambayar shiyasa"
Kamar Wasa cikin dare se Zuhra ta tashe ni tana ta kuka Wai marar ta kamar zata balle, I was like what? Na sakko da sauri na kalla time karfe uku, na Isa gareta na kunna lantern Dan Babu wuta, nace
" Zuhra bleeding kike?! Innanlillahi wa inna ilaihil rajiun!"
Ta fara kuka tana cemin
" Ki Kira muje asibiti, I don't want to loose this baby"
Na dauki wayata na rasa wa Zan Kira cikin Daren, kawai se na Kira class counsellor din mu, mace ce Kuma a quarters take zaune, so tana gani tayi picking na fada Mata abinda yake faruwa, tace na shirya Zuhra kafin ta karaso, na shirya ta na dauki abubuwan da zamu bukata sannan na tashi security dinmu aka bude hostel da gate muka fita, tana cikin mota ita da mijin ta suna jiran mu, ta dinga ma Zuhra sannu har mukaje, aka karbe mu inata adduar Allah yasa threatened ne, Amma jinin da yake zuba kadai nasan sede incomplete abortion, tana son cikin saboda most time zanga tana ta shafa shi Amma ban taba Mata maganar ba se yau da mukai. Ana dubata aka cemin wani ya fita zasu karasa fitar dashi, tana Jin Haka se kuka, Mummy kamar yadda muke Kiran ta ta dinga lallashin ta, seda aka stabilizing dinta sannan Mummy ta tafi, Ina nan har asuba idona biyu, se da nayi Sallah sannan na dawo kanta na samu har an fitar da sauran, bleeding din ya tsaya ta fara bacci, na rike hannunta Ina jin kamar Nike jinyar, ta rame tayi fari nasan she might need blood. Seda gari yayi haske sannnan na dakko wayata na Kira Anna na fada Mata halin da ake ciki, tace na Kira Anty Yusra da Yaya Khalifa na fada musu ita Kuma zata taho yanzun Kuma zata fadawa Dada. Yadda Yaya khalifa ya rikice I felt really bad for them. Gari na Gama wayewa Anty Yusra tazo Muka koma amenity, anan aka ce zaa Kara Mata jini Dan ta zubar da yawa, Anna ta karaso lokacin har an cire jinin tayi wanka taco abinci, kusan lokaci daya suka iso itada Yaya Khalifa, ai kuwa tayi ta kuka shima Yana Taya ta, duk se Naga abun odd dama ni kadai ce a ciki, tuni na fice na Basu guri. Seda tayi kwanaki uku sannan aka sallame ta, se kawai Suka wuce dutse, min Sha Yan dubiya har Mamaa seda tazo ta bada sakon Abiey ba zai zo ba baya gari.
Bayan nan se muka fara Shirin council, mukai depending project, ranar birthday Dina Wanda ban taba celebrating ba, in fact idan banki da sauran Google account Dina Basu tuna min ba to tabbas bana tunawa. Bansan ya akai Cànîm ya lura ba har ya tuna, ranar banyi bacci da wuri ba na tsaya muna kallon film da Zuhra, 12am nayi naji shigowar message, na duba Naga birthday wishes na dubi Zuhra nace
" Hajiya yau birthday dina Ashe"
Ta fara min waka sannan na tura Masa reply, the following morning Ina kunna data Naga ya turo min receipt na payment, banma gane na meye ba se na Kira shi, kunsan me yayi min? Wai yaga advert din classes akan business promotion shi ne yayi min payment nayi joining classes din, it was a wonderful gift da aka taba bani, a class din na koya yadda Zan fadada business Dina, yadda Zan mayi picture nayi advertising ba karamin support bane wannan da bana taba mantawa. Bamu hadu dashi ba se ranar da muka kammalla council, tun safe yazo ya jira har muka Gama abinda zaayi sannan na same shi a office din lecturer dinmu Kuma Friend din sa. Yana zaune Wanda ya tuna min ranar Dana Fara ganin shi a office din Oga Salis, wannan Karan wayar shi yake dannawa Babu komai a gaban shi, yana Jin sallama ta ya juyo Yana sakar min tattausan murmushi Wanda yasa naji kamar Yana tafiya da dukkan gajiya ta, na zauna Ina gaishe shi yace
" We're neither student Nurses nor potential Nurses but Registered Nurses inshallah!"
Na saki murmushi Jin dadi nace
" Amin Amin I'll make you proud"
" I'll love that"
Ya saita wayar shi yayi min hoto inata dariya wadda kana kallo kasan a cikin farin ciki nake. Bayan shi ya sani na dawo yayi Mana hoto sannan muka fito daga office din zuwa motar shi, yace
" Ina son muyi officiating relationship din mu, kima Anna magana zanyiwa Mummy magana"
Nayi murmushi nace
" Inshallah, yau Zan fada Mata magana, ehen zancen Amra kace tana son koyan saka, she can come se in koya Mata"
Yace
"Zata hi Dadi dama wajen age din ki take, sannan bonding din ki a hadejia ne ko?"
Nace
" Yeah idan auren yazo I'll transfer to Dutse tunda kaima kace can zaka koma"
Yace
" Eh na fara planning gidan ma, na saya filin architect Dina nake jira ya Gama zana plan din"
Nace
" Allah ya Sanya alkhairi"
A wañnan lokacin Ina hango mu munyi aure, na Samar Masa dawammma men farin ciki, da yaran mu kusan Ashe me nake Yi? Building a castle in the air! Ya Shiga mota sannan ya Miko min katuwar gift bag tare da fadin
" Nayi tunanin duniya na rasa me Zan siya Miki, Amma dai nace lemme just make you smile a bit"
Na karba Ina Masa godiya ba tareda na bude ba, Ina tsaye ya tafi sannan na koma hostel, tare da Zuhra muka zazzage kayan box ne me sarka, dankunnen, bracelet da ring da sticker a jiki na ta_kwalam_jewels' Ina following handle dinta a ig Kuma Ina ganin yadda take saka qualitative and fashionable jewel, se tararruka da Kuma kayan Zaki su chocolate. Sedan karamin card da aka baje kalaman soyayya a ciki, Kai Al'amin karshe ne!
Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to ***